← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 112

Sashe 85

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuba mata idanuwansa yayi sbd shima ganin yakeyi bazai iya fuskantar Amminsa batareda ita ba sbd baitaba samun sabani ko irin wannan yanayin ba da Amminsa ba tinda yazo duniyaba dan haka sai yakejin kowace lissafi ta kwace masa akan hakan,
Ya rasa girmansa da tinaninsa da zafinsa da mulkinsa da komaima duka akan muryan da Ammi ta daga akansa sbd bacin rai bayan yanada tabbacin itama tinda take babu wanda ya taba sakata wannan daga muryan da fushin idan ba shiba.

Kallansa Bahar tayi tareda sanyaya idanuwanta akansa ta bude baki da qaramin sauti me taushi tace

'Zaka iya sbd Amminka ce'

Baice komaiba ya saka kai cikin bangaren kai tsaye yana wucewa take bayin ciki suka fara jerowa suna fitowa.

Itama bahar shiga tayi sedai baya iya wucewa ciki ba kai tsaye kitchen tafara nufa tana jin fargaban haduwa da Ammin ta bude fridge ta dauki fruits da batasan me zatai da suba ta zuba a plate me kyau ta fito kitchen din ta nufi palon ta shiga kirjinta na sake harbawa.

Maa tenya ce a palon zaune tareda maa sakina dan haka maa sakinah bata juyowaba kallo daya tayi mata taci gaba da wayar datakeyi ita kuwa maa tenya juyowa tayi gabaki daya tana kallanta cikeda mamakin inda ta fito sbd tin dazu take nemanta sbd Ammin data saka a kirata.

Cikin tsananin nauyin kafafu ta qaraso gurinsu ta kasa kallansu cikin sanyi ta gaidasu.

Maa ce ta amsa batareda ta kalletaba tenya kuwa sai datai shiru kafin ta amsa mata tana daidai nan Ammi ta fito daga palonta tareda NUAB wanda gaida Ammin yayi kawai bai iya cewa komaiba ya fito suka fito tare batareda sakewan fuska daga Ammin ba sbd tana kan maganarta na idan bai sauko dinba bazata taba shiryawa dashi ba duk da kuwa a zuciyarta tana jin tsananin damuwan kalaman nata akansa sbd karfin hali kawai takeyi tana masa zafin sbd irin NUAB din baya ganewa ta sanyi sai da hakan.

Bahar datake tsaye ta saukewa idanuwanta tana kalla da kyau a natse sbd ance baa ganta ba a dazun to ina taje tinda safen..

Sauke idanuwa Bahar tayi tareda kanta a qasa tana kasa kallan Ammin jikinta na sanyi zuciyarta na bugawa wanda hakan ya saka Ammin dakatawa cak tsaye tana kallanta kafin ta dawo da kallanta akan NUAB daya dakata shima ganin yanda kowa yai tsuru ana kallan Bahar din wadda itama kusan take bada kanta ta hanyar kasa kallan ko daya daga cikinsu.

Ammi ce ta bude baki kai tsaye cikin daure fuska sosai tace

'Daga ina kika fito?
Ina kikaje na aika nemanki akace bakya nan??

Dagowa tayi ahankali tana kasa kallan Ammin tace

'Ammi...' shiru tayi tana rasa abin fada sbd bata iya karya ba bata saba yiba kuma faduwan da gabanta yakeyi akan kallan da Ammin ke mata ya saka ta rikice sai kawai idanuwanta sukai rau rau.

Baci ran Ammin yayi ta daka wata tsawa me karfin gaske tana cewa

'Karma ki fara hawaye a gurin tambayarki nayi daga inda kike'

Maa sakinah ce ta bude baki zatai magana NUAB ya daga mata hannu a natse yana qarasowa gaban Bahar din ya saka hannunsa a natse ya kama nata ya janyota xuwa gaban Ammin suka tsaya ya dago jajayen idanuwansa da sukai ja sosai zuciyarsa na wata irin radadin yanda Amminsa ta sauya masa a lokaci daya ya bude baki yace

'Tana tareda ni,daga gurina ta fito,nine na buqaci zuwan nata Ammi'

Wani irin mamaki ne me karfi da girman gaske ya cike Ammin sbd bata taba dauka zai iya bada amsarba kuma bata taba kawo tinanin Bahar ta sake ko kallan inda NUAB din yake bare zuwa garesaba dan haka amsar taxo mata a bazata da wani irin takaici da nauyi me girma.

Tenya ma dataji hakan nauyin maganar taji tana tsananin fatar tambayar Ammin ta tsaya daga nan sbd idan ta sake wata tambayar dukansu zasu ji abinda zai sakasu kunyarsa bawai shi yaji kunyarsu ba dan haka ta saka bakinta a maganar da cewa Bahar ta wuce ciki.

Maa sakinah ma datai niyar saka baki shiru tayi sbd abar maganar a iya nan kada Ammi ta zaqe aji kunya.

Ammin ma rasa abin fada taji kawai ta kama fushin datake kai ta bude baki tana kallansa bayan bahar ta wuce tace

'Ya mukai da kai akan Bahar??
Menene kake kokarin yi??
Meyasa zaka ringa kebewa da ita?
Daga yau na yanke kowace irin kebewanku harsai ka fara sanin darajar mahaifinka da sanin yanda zaka bisa kafin na baka marainiyar Allah.

Shiru yayi tareda kafe Ammin da idanuwansa da sukai wani irin ja akan wanda suke ciki sbd a karo na biyu a lokaci daya Amminsa ta sake yanka masa zuciya da kalamanta,
A yau shi sabon mutum ne daya zabi farin ciki da umarnin mahaifiyarsa koda kuwa a zuciyarsa yanada qin hakan dan haka koda ya fito a yau ya fito a matsayin 'dan daya karbi farin ciki da zabin mahaifiyarsa ya zabi aurenta da sultan da shi kansa sultan din sbd Ammi tanasonsa dan haka daga nan ayau daya fito bangaren sultan din zashi a karo na farko yaje ya gaidasa a matsayin uba kuma mijin mahaifiya amma sai gashi ayanzu Ammi ta sake yankarsa da sabbin maganganu masu zafi.

Numfashi ya sauke a hankali mai sanyi da rashin sauti kafin ya bude baki ya furta

'Nagode Ammi,ki wuni lafiya'

Juyawa yayi yaiwa su Maa sai anjima suma ya fice daga bangaren batareda yaji a zuciyarsa kalman Ammin ko daya a ransa ta shiga ba bare tasiri akan Bahar dan kuwa idan har zata kasa rabuwa da sultan akan soyayyar datake masa bayajin tanajin abinda yakeji akan tata 'yar itama dahar zai iya ko kuma kwana a rayuwansa batareda ita ba bare rabuwa ko ace an shiga tsakaninsa da ita bayan igiyoyin aurensa dake kanta.

Yana ficewa kai tsaye kaman yanda ya tashi da sabuwar niyar bin sultan yasar a matsayin uba daga yau din sbd Amminsa kai tsaye bangarensa ya nufa take aka isar da sultan zuwan LEUL boyem din shima daya kwana da tsantsar kewan kaunar soyayya daga 'dan nasa cikin jin nutsuwa da sanyin jin zancen ya karba ziyaran ta NUAB din.

A karan farko da suka zauna a matsayin uba da 'da a natse aka gabatar musu da zazzafan tea na jinin boyems aka jere nuab baisha ba sbd a koshe yake sultan ne kadai yasha a natse yana amsa gaisuwan NUAB din wadda yayi masa a taqaice shima sukai shiru sai daga baya NUAB ya kira aleey ya shigo da takardar sanarwa auren iyayen nasa daya buga tareda saka stamp dinsa na sultan a jiki aleey ya ajiyeta a gaban sultan din kan table cikin girmamawa yana juyawa.

Kallo daya sultan yasar yayiwa takardar ta sake wani murmushi me sanyi yana ajiye cup din hannunsa a natse sbd batareda NUAB din ya furtaba a taqaice ya amsa auren da zuciyarsa.

Ajiyan zuciya ya sauke bai dauki takardarba ta sarauta ya sake fidda sadakin Ammin a karo na biyu ya ajiye a gaban NUAB din yace

'Ina sake gabatar maka da sadakin mai girma Ayanaah ghaz'

Kallan zinarin yayi tareda miqa hannu zai dauka cikin nutsuwa da izzar mulki sai Sultan din ya sake ajiye masa wasu silallan zinarin masu kauri a jere yace

'Wannan sadakin neman auren mahaifiyarka daya ne Sakinah wa Amintacce na Kadir a matsayin tukuicinta daga gareni na toroka gareni.'

Dakatawa NUAB din yayi cak daga daukan sadakin Amminsa yana dagowa a natse cikin kamewa ya kalli sultan din wanda shima shi yake kalla.

A daidai wannan lokacin kuwa Haile tana zaune Asim ya sameta da labarin zai bar boyem take taji kaman an zare mata hankali cikin mummunan rikicewa ta kallesa tana rasa abin fada daga ita harsu Aslam da ayanzu sun zama daga ido sai kunne.

Suna kallo ya fice dan haka a cikin mummunan yanayi ta miqe ta shirya ta nufi bangaren sultan dan tattauna matsayin da suke dashi a ayanzu masaurautar ita da yayanta.

Tana isa bakin bangaren sultan da bayinta dake take bayanta su kusan hudu ta tadda securities din NUAB alaman yana ciki dan haka bata tsaya ba tana kokarin saka kai kadir ya fito da takardar sanarwar auren sultan yasar da ayanah ghaz wadda idanuwanta suka sauka akai ta dakatar dashi ta fixgi takardar tana budewa gabaki daya ta karanta ganinta na neman disashewa daidai nan itama maraki ta iso bakin bangaren tazo ga sultan.
#MAMUH
09033181070
[09/01, 12:50 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

158
Jiri ne me karfin gaske ya dibi hailen tayi baya da sauri bayinta suka tarota shi kuwa kadir da babu abinda zai tsaidasa ko hanasa isarsa wannan sakon daya fi masa komai daukan sakon yayi yana barin gurin dan isar dashi ga yan jaridun masarauta dake jiransa dan harya kirasu.

Maraki data kawo gurin da mamaki me girma ta kalli haile tana boye mamakin nata sbd tasan koma menene ya kusa saka haile faduwa me girma ne kuma akan sarauta ne sbd ita burinta akan neman mulki ya qare sabanin ita burinta na shekaru shine sultan yasota kona qanqanin lokaci ne.

Rawa kafafuwa da hannuwan haile suka fara ahankali ta gyara tsayuwanta tana son hana mugun tashin hankalinta fita agaban maraki data iso amma lamarin neman fin karfinta yakeyi sbd abu ne da bata taba ko a mafarko kawo zai yiyuba musamman tinda sun manyanta sunada 'dan daya zama har sultan me zasuyi da wani daura aure a tsakaninsu,
Me hakan ke nufi?
Me sultan yake nufi?
Irin wannan son yakewa ayanah tin farko kokuwa dai 'danta ne ya sakasa aurenta dole?
Dan kuwa sultan bazai kai wannan shekarun ba yayi shaawan auren wata ayanah daya gama yayinta bayan idan yaso zai saka a kawo masa imebētis ko nawa yakeso idan ma wani abin yake buqata.

Maraki datake kokarin saka kai a palon na sultan cikin karfin hali haile ta katseta da cewa

'Gwara ma kada kiyi saurin shiga sbd ayau baida lokacin kowa a duniya bayan matar daya aura batareda sanin kowaba a duniyar sai yanzu ne zancen zai bayyanarwa duniya a karan farko sultan dayayi mulkin boyem ya aure wishmarsa.'
Chapter 85 · 0% Book details