← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 112

Sashe 13

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa cewa komai Maa sakina tayi ta bar gurin ta nufi dakinta zufanta na sake tsananta tareda tashin hankalinta sbd bata San wane yaqin tashin duniya ne wannan zaayi ba ace matar da igiyoyin auren NUAB suke kanta itace dan uwansa yake so a matsayin imebeti,

Tayaya wannan muguwar kwamacalar zata fara?
Tayaya ma zata fara zuwa isar da wannan mugun sakon da zai Yadu zuwa safe kuma babu Wanda duk duniya ya isa ya Hana hakan tinda har sultan ya Riga ya saka hannu babu abinda zai Haba Ayi hakan.

Wani nauyi kirjinta yayi me tsananin gaske ta fara kaida kawo tsakiyar dakinta tana Jin har numfashinta yana daukewa sbd matiqar aka fara shirinta aka fara wanketa da ruwan lallen dazai wanketa tas to ta tabbata dai ta ASIM ce Wanda ko ita matiqar NUAB ya Bari akaiwa Bahar dinta hakan batajin zata iya yafe masa wannan laifin har abada dan kuwa ba amanarta ce ita kadai ba Bahar din shine ma asalin Wanda amanar tata taje hannunsa.

Tenya ajiye tata takardar sakon tayi sbd sai gobe amma dai a cikin Daren ta aika sakon a shirya bangaren wanke imebetin da tsiminta tareda wanketa a inda sai kamanninta sun sauya sbd yanda zata koma,

Farin cikin Dayan sakon tafara tareda Leylah cikin farin ciki me yawa da tsananin gaske,

Ayanah ma datake cikin tinanika da saka ido sosai Akan sauyin datake gani a tattare da Sakinah bawai dan zata cutatar da ita ba sedai tana ganin kaman akwai abinda sakinah take boye mata na damuwa ayanzu dan koyaushe bata iya hada ido sosai da ita kaman baya hakama gabaki daya hankalinta yana kan sabuwar baiwar datake tsananin son sake gani Akan abu biyu datake son sake gani da ji akanta amma ayanzu farin ciki mai tsananin gaske ta samu kanta na auren Wanda shine zai hadata da yar uwarta Rabin jikinta da sukai shekaru masu yawan gaske basu hadu ba,

Tsananin farin cikinta na ganin Zuhrah ne,
Zata ganta zata kalleta a gabanta koda kuwa basu furta su yan uwa bane zasu kasance a gaban juna a matsayin sirikan da zasu hada iri zasu hada zuria yayansu zasu auri juna zumuncinsu da suka rasa sbd rashin yanci zai dawo daga karshe zata rungume yar uwarta da zuciyanta da ruhinta suke tsananin buqata,

Wannan sune babban abinda ya saka farin cikin auren yake dake kame kowane saqo na zuciyarta da gangar jikinta dan haka Kai tsaye takejin tamkar tafi kowa matsuwa da Ayi auren.

Leylah kuwa Jin tayi farin cikinta yana danne baqin cikin datake cikinsa na Bahar da NUAB amma a yanzu sassauci da farin ciki take jin zuciyarta fes.

Maa sakinah kuwa kallan lokacin Daren takeyi tana Jin zuciyarta na sake tsinkewa da tashin hankali,

Bahar take tsananin son gani a lokacin sbd tafara ji daga gareta ko akwai maganar data taba shiga tsakaninta da ASIM hakama taga halinda take ciki sbd matiqar sakon ya kai bangaren NUAB a Daren to batajin akwai Wanda Zai iya rintsawa kaf masarautar amma koina tsit takeji dan haka take saka ran sakon bai isa can ba.

Zulluminta na qaruwa tana sake kallan Agogo tana danne zuciyarta Akan ta jira safiya waye sbd yanzu dare yayi,

Haka dare ya fara ratsowa tana Zaune daram a kujera ta kasa motsawa bare kwanciya sbd kowane lokacin Jin takeyi yaqi Zai iya narkewa a masarautar dan haka hankalinta yake tashi sbd ita Bahar din kadai takeji,

Daqyar taga gari ya fara haske dan haka ta fito ta fice Kai tsaye batareda kowa ya tashi ba ta nufi bangaren NUAB.

Tin daga nesa ta fahimci sabbin da qarin securities dinsa masu yawa ya qaru duk da ya halinta baya a tsaye guri daya Kai tsaye kofa suka bude mata ta shige Bayan ta gama ware ido a cikinsu bataga alamar zancen ya iso bangaren ba dan haka tana sako Kai makeken lafiyayyan palon Kai tsaye dakin Bahar din ta nufa ta budesa ta fada batareda tinanin komai ba.

Ko data shiga Bahar din na Zaune Akan daddumar datai sallar asuba bata tashi ba tayi shiru ta zubawa gabanta idanuwanta da sukai jajir sbd kukan kadaici da kewan mahaifinta ta kwana tanayi Wanda ya saka fuskarta kumbura sosai.

Shigowan Maa ya sakata dagowa a natse cikin sanyi tana ganin itace wasu hawaye masu tsananin dumi suna gangaro mata ta miqe tsaye tana qasa da kanta cikeda sanyin jiki sbd jinta takeyi tamkar a kejin da babu iska ko kadan sbd gabaki daya ko hasken rana bata sake gani ba tinda ta shigo bangaren.

Kama hannunta Maa sakinah tayi cikin nutsuwa ta jata zuwa bakin sofa suka zauna ta dan sake kama hannunta cikin kulawa da tausasa harshe tareda boye damuwan datazo da ita tace

‘Bahar ba nace ki rage yawan kukan nan ba??
Baida amfani zaki kamu da wata ciwon idan Kina yawan kukan nan ki Dena’

Wasu hawayen ne suka ciko idanuwanta amma basu gangaro ba ta dago kyawawan idanuwanta zatai magana aka bude dakin Kai tsaye a natse Wanda ya sakata dauke kallanta daga kofar wasu hawayen masu tsananin baqin ciki suna gangaro mata ta fasa wani sabon siririn kuka a hankali zuciyarta na cikewa da baqin cikin samun kanta a rayuwar da Sam bazata iya ba da kuma samun Wanda take ganin asalin asali baisan menene hankali ba,

Maa sakinah cikin nutsuwa ta juya sedai batasan lokacinda ta dawo da fuskarta ba cikin wata irin rikicewa da kunya da takaicin kasa riqe kanta datai tazo bangaren a daidai wannan lokacin.

Farin wandon bacci ne a jikinsa dogo har qasa amma babu Riga a jikin nasa hakama wandon bai hau daman cikinsa da kyau ba iya inda qugunsa ya fara ya tsaya Ana ganin tambarin sunan farin tomford tight short din dayake jikinsa ta saman Wanda Zai iya saka mata da yawa rikicewan ganinsa a hakan,

Gashin kansa me tsayi ne daure da qaramin black Band a tsakiyar kansa bai Wani kamu ba sosai fatar jikinsa sai daukan ido takeyi,

Akan kunnuwansa dake bacci yaji shigowan mutum palon dan hakane ya fito kuma Kai tsaye nan ya bude dan dubawa sbd ya fahimci yarinyar na tasting din patience nasa bai tsammanin ganin Maa sakinah ba dan haka dakatawa tayi daya kofar tareda bude bakinsa ya gaidata ta amsa batareda ta juyoba duk a rikice sbd ta kasa iya juyowa kallansa a hakan.

Ko bahar din bai kalla ba ya juya yabar dakin yana kallan time a agogon dayake palon ya koma bedroom dinsa.

Maa sakinah kasa magana tayi sukai shiru dukkaninsu na tsawon mintina kafin Maa sakinah tayi karfin halin fidda takardar data dauko tazo da ita ta budewa Bahar din tace

‘Bahar akwai wata doguwar magana ne a tsakaninki da Li’ul ASIM?

Numfashi Bahar ta sauke a sanyaye ta girgiza Kai,

‘Kinsan takardar menene wannan Bahar?
Abinda yasa na fara tambayar ki wannan takardar daga sultan ta fito dauke da sunanki da sunan Li’ul ASIM an zartar da hukuncin basa ke a matsayin imebētinsa…..

Cak hawayen Bahar din suka tsaya daga tsiyaya ta dago ta kalli Maa sakinah cikin wani irin sabon mamakin da bata taba shigaba.

Takardar ta kalla da idanuwanta tana kokarin karanta abinda yake rubuce amma ganinta ya kasa zama daidai ta sake kallan Maa sakinah tace

‘Maa dan Allah zan koma GHAZ bazan iya rayuwa anan ba dan Allah Inason komawa’

Cikin sabon nauyin daya danne kirjin sakinah ta girgiza Kai idonta yana ja tace

‘Bahar bazaki taba komawaba a yanzu sbd akwai aure a kanki Wanda babu Wanda ya San dashi hakama yanzu gashi Kina a matsayin imebetin ASIM Wanda kinma riga kin zama a rubuce dan haka babu abinda zai fidda ki BOYEM kuma matiqar dai a raye kikeso fitar’

Girgiza Kai Bahar tayi tana jin jikinta yana daukan zafi tace

‘Maa babu ko daya a cikin biyun danake so auren da imebetin bazan iya rayuwa anan ba’

Dakatar da ita Maa sakinah tayi sbd da alama zancen bai iso nan ba dan haka bata fatan ya iso tana nan dan haka Miqewa tayi sbd maida takardar kafin ma asan ta dauko hakama ko yayane hankalinta ya kwanta datasan babu maganar komai data hada Bahar dashi ASIM din data danganci kowace kalmar soyayya wadda zata iya zama cikin matsalar hakan amma tinda babu taji dan sauki zata jira taga idan NUAB zai iya kubutar da Bahar din daga wannan mummunan kaddarar dake shirin hawanta ga kuma nasa auren na biyu dake shirin hawa kansa shima.

Miqewa tayi zata fice Bahar tayi saurin miqewa tana gyara babbar rufar sallar dake jikinta tana biyota a baya.

Wucewa Maa sakinah tayi batama San Bahar din na bayanta ba saida suka Kai tsakiyar palon Maa ta juyo tana kallanta da mamaki tareda rage sautinta tace

‘Bahar ki koma zamanki a nan yanzu shine babban tsaron da zaki samu da kariyar da kaf BOYEM sultan ne kadai ya isa ya fiddo ki amma bayanshi babu Wanda ya isa.

Girgiza Kai Bahar tayi tana cewa

‘Bazan iya zama ba ni kadai Maa dan Allah mu tafi tare’

Girgiza Kai Maa din ke kokarin yi Bahar tayi saurin yin gaba cikeda tsananin damuwan bazata iya tsayawaba ma bare ta zauna idanuwanta na sake cikowa da hawaye.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

83
Fitowa Bahar tayi da sauri daga kofar palon tana kokarin qarasa fitowa securities suka miqe gabaki dayansu suna tabbatarda tsare kowace kofar batareda sun dauke idanuwansu akanta ba,

Jin tayi kaman zata Dora hannu akai ta zunduma Ihun da ko zuciyarta zata samu sassaucin abinda take ji ta juyo ta kalli Maa tareda fara tsiyayar hawaye ta riqeta da dan karfi tana cewa

‘Maa kada ki barni anan dan Allah ki tafi dani Zuciyana fashewa zeyi dan Allah Maa’

Yar hayaniyar ce ta fidda aleey Wanda kunnuwansu suke sharp shima Akan kowace motsin bangaren daga waje.

Ganin Bahar ya sakasa qarasowa yana dauke idanuwansa daga kallanta shima ya bude Baki ya gaida Maa kafin ya gaida Bahar din wadda batama jin komai tsananin quncin barin bangaren take ji.
Chapter 13 · 0% Book details