← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 112

Sashe 79

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bahar ce ta fito da wayar Ammin a shirye cikin kayan shan iska marasa nauyi sosai riga da wando ta nufi dakin Ammin ta shige.

Wayarta ta kawo mata ta gaidata tana shigewa gefenta ta zauna tana amsa tambayan datake mata akan wayarta data ga sakon gaisuwan da zarah yar tenya datake aiko mata kullum.

Anan leylah ta sameta ta gaida Ammin itama tana ficewa dan wayarta da Mum dinta ke kira dan amsawa.

Bata fito dakin ba Maa ta shigo dakin dauke da tray din dayake dauke da madarar data dafa mata me karfin gaske ta ajiye kan table tana zaunawa akan kujera itama tana shiga firar da sukeyi cikeda kulawa sunayi akan wani hukuncin da Abaa dinta ya taba yankewa batareda ya iya mulki sosai ba a anjom suna dariya maganar na shigar Ayanah datake jinta har zuciyarta da farin ciki da dariyan jin yanda Abaas yayi mulkin anjom batareda taimakon kowannensu ba shi kadai.

Sakinah ma dariya takeyi suna maimaita lokacinda yake tamkar mace bayason ace shine zaiyi mulkin Anjom yafison Ayanah tayi ya bita.

Bawa bahar din mug cup din dayake fidda hayaqin madarar Maa tayi ta karba suna cigaba da firar su cikin nishadi da kewan Abaas wanda a yanzu koyaushe adduarsu bata yankewa akansa da sauran iyayensu da Nurat.

Fara sha tayi a hankali tana dan bata fuska kadan sbd karfin madarar dan haka bakinta ya mutu ta rage magana tana sha a hankali tana saurarensu tana murmushi da yar dariya jin irin kuruciyar da mahaifinta yayi wanda firan take mata dadi sosai sbd batada labarin da ako yaushe yake mata dadi da bata gajiya da sauraro irin firar mahaifinta.

Nishadi sukeyi sosai suna firar tana sauraronsu tana murmushi tana shan abinda yake hannunta a natse tana lafe gefen Ammi.

Qamshinsa ne ya fara ratso su dan haka maa dake dariya sosai ta dago ta kalli kofar daidai nan ya sako kai da sallamarsa me nutsuwa da kamewa tareda wani irin iko.

Ammin itama kofar ta kalla har lokacin fuskanta dauke da dariyarta me kyau datake tino mata farin cikinta na baya data rasa a tareda rayuwa da iyaye da yan uwanta.

Ganin nishadin dasuke ciki ne ya sakasa qarasowa fuskansa daukeda wata natsatsiyar annushuwa da kwanciyan hankalin da shima yake tattare dashi wanda kasancewan 'yar Ammi a boyem din yake basa.

Zaunawa yayi a gefen Ammin a natse cikin kwanciyan hankali ya kalleta ya gaidata cikin kulawa da kauna kafin ya maida kallansa kan Maa itama ya gaidata.

Amsawa sukai dukkaninsu cikin kulawa da kauna suna kallansa da sauyin dayake tattare dashi na wata sabuwar nutsuwa da kwanciyan hankalin dasuke iya hanga a tattare dashi amma ba wanda zai iya tambaya.

Kan Bahar ya dawo da kallansa a natse ya kalli cup din hannunta da abinda yake cikinsa tana sha ahankali batareda ta iya dagowa ta kallesa ba sbd batason ma Ammi taga ko kallansa tana yi.

Maa ce ta kalleta tace

'Yar Ammi bazaki gaida Sultan guda ba gashinan kinyi shiru?

Faduwa gabanta yayi ta dan dago ta kalli Maa din wadda ta kafeta da ido,
Kan Ammi ta maida kallanta taga Ammin ko kallanta bataiba dan haka ta juyo da idanuwanta a hankali akansa ta kallesa shi kuwa ya kafeta dasu kaman zai janyota jikinsa.

Bude bakinta tayi cikin nutsuwa da kokarin sakewa tana hana kowace fargabanta fita ta gaidasa.

Sai a lokacin ya dauke idanuwansa daga kanta sbd yanda komai nata ke shigarsa a daki daki,
Zai iya kasa riqe kansa ya kama hannunta sbd jin sautin muryanta da yanda ta gaidasa din tana kallansa da mayun idanuwanta dake warware duk wani lissafinsa.

Amsawa yayi kafin a sake cewa komai ta miqe a natse da cup dinta a hannunta tabi ta gefensa ta fice daga dakin tana bar masa wani qamshinta daya shiga hancinsa dakyau.

Wani numfashi ya hadiye yana kamewa dakyau batareda yabita da kallo ba harta fice tukuna ya dawo da nutsuwansa cikakkiya akan iyayen nasa suka fara magana.

Maa ce ta kallesa tana gyara zamanta da dukkanin nutsuwa tace

'LEUL kaje ka samu ganin mahaifinka kuwa?
Duka munsan kasan baya nan tsawon wannan lokacin yana can tareda mu a uk dan haka tinda ya dawo ya kamata duk matsayin da kake dashi kaman yanda kazo ka gaida mahaifiyarka kayi mata barka da dawowa shima kaje ka samesa kayi masa gaisuwa da barka da dawowan sbd duk koma menene kowa yakeji matsayinsa na uba,sarki,Mahaifi kuma mijin mahaifiya ya wuce komai'

Shiru Ammi tayi sbd yanda zuciyarta ke harbawa da yanda komai zai bayyana NUAB ya fahimta,

Shi kuwa shiru yayi yana sauraran Maa din,
Tinda ya dawo sun hadu so daya dayaje ya samesa da kansa suka gaisa amma bayan nan basu sake haduwa ba sbd bayajin akwai abinda zasu iya zaunawa su fuskanci juna su tattauna a tsakaninsu.

Numfashi ya sauke me sanyi da nutsuwa kafin ya dago ya zubawa Ammi idanuwansa sbd duka wannan maganganun yasan abinda takeso aka isar mata a gurinsa,
Itace take son ya samu Sultan su daidaita sbd zuciyarta na son hakan,
Zuciyarta bazata iya fifita son datake masa akan na sultan ba shiyasa take masa hakan har itace ayau take kasa masa magana sedai ta saka ai masa magana duka akan sultan.

Dawo da kallansa yayi akan Maa ya bude baki baki a natse yace

'Insha Allah Maa'

Yana fadar hakan sallama yayi musu ya miqe ya fice batareda ya cewa Ammin komaiba sbd koyaushe akan sultan sosa zuciyarsa takeyi tareda danne matsayinsa na 'danta dayake yaqi da jin zafin sultan akanta amma sai tana mantawa da hakan tana zabar sultan kuma tana boye masa tana daukansa da masa kallan wanda yake tsakiyarta da farin cikinta na son rayuwa da mutumin da 'yanci wannan ya kasa bata yana matsayin sultan wanda yake kam mulki sama da shekara talatin.

Yana fitowa Aleey kallo daya yayi masa yasan zuciyarsa ba dadi dan haka babu doguwar magana suka wuce Fada dake cike ana jiransa ayau akwai taro da zaman fadar.

Koda suka isa fadar tsit koina yayi sbd shigowansa da aka sanar.

Yana shigowa kowa kansa yayi qasa niimar gurin na gauraya a natse da qamshinsa da zuwa yanzu duk wanda yake shiga fada dashi yasan qamshinsa hakama zazzafan kwarjininsa ya gauraye gurin.

Koda ya isa kan karagar mulkin boyem din tini Aleey ya isa ya tsaye a gerenta daman keelah na tsaye daga bayanta cikin jikinsa babu kalar makamin da babu a soke boye.

Yana zaunawa daga waje securities masu karfi suka dakatar da kowace irin kaida kawo a hanyar fadar ba shiga ba fita saiya fito kuma kowa zai samu yancinsa.

Kusan wuni yayi a fadar bai samu kansa ba sai kusan yamma dan haka yana fitowa daga fada kai tsaye aika sakon zuwansa akai gurin sultan yasar wanda yayi mamakin jin zuwan nasa duk da Ayanah ta sanar masa a waya cewan Maa dinsa sakinah tayi masa magana amma kuma shima daman yana buqatar ganin nasa dan haka koma menene zuwan na NUAB din zai kawo yana shirye dashi dan kuwa lokaci yayi dazaisan uwarsa ta auru.

Shi kansa NUAB din ayau yana son fuskantar sultan ne a karo na karshe insha Allah akan mahaifiyarsa wadda a yanzu baida ikonta yana son yayi masa iyaka da ita sbd kaucewa abinda babu a addini hakama a karan karshe zai sanar masa da zai bar boyem da ita bazata taba dawowaba da zama.

Wannan tabbatacciyar magana ce da zai tabbatar masa sbd shine me cikakken ikon mahaifiyarsa ayanzu idanma sultan din ya manta zai tinatar dashi hakan a tsanake sbd yasan ya rasa damarsa har abada.

Saida yayi wanka ya huta bayan sallan magrib ya nufi bangaren mahaifinsa wanda yake zaune a natse shima yana jiransa da sadakin mahaifiyarsa daya ajemasa yana jiran ranar basa.

Koda Sultan me mulkin boyem LEUL NUAB ya iso bangaren sultan me murabus yasar kadir yana tsaye bakin kofa yana jiran isowansa cikin nutsuwa da Girmamawa.

Aleey ne da keelah a tareda shi sbd ziyarar bata buqatan hayaniyar tsaro tinda gurin mahaifinsa ne yazo.

Kadir ne yayi masa rakiya da iso har palon da sultan yake hutawan yana zaune yayi fresh dashi hutu da kwanciyan hankalin da duk yake nema a rayuwa yanzu ya samu duniya tasan ya mallaki Ayanah ghaz halak malak kadai ya rage wanda shi baya buqatan hakan idan 'danta kawai ya sani ma ya ishesa duk da idan har danta ya amince ya karbi aurensu to dole duniya zata sheda ta sani sbd tsaftata alaqar.

Dagowa yayi yana zaune kafarsa daya akan daya yana duba abu a waya fresh fruits a table din gabansa kallan Fuskan NUAB yayi wanda shima huta da kwanciyan hankali da wani azababben iko da izza ke bayyana tattare dashi na zafin mulki ta uba data uwa da kuma na empire din kansa daya kafa.

Aura ce ta cike gurin ta uba data 'da dake nuna zallan iko da izza dan haka ficewa kadir yayi a hankali a natse yabarsu su kadai.

A 1 seater din dake facin sultan yasar NUAB yake zaune ya dago cikin nutsuwa ya kalli mahaifinsa bai ji komaiba na damuwa ko wani yanayin a natse ya bude baki ya gaidasa yana kallan abubuwan da sultan din zaiji daga bakinsa.

A natse sultan ya amsa yana qarawa da masa kirarin sarauta a natse dan bude filin da abinda zai gabatar masa.

NUAB dayake sauraransa numfashi ya sauke yana dagowa ya kallesa cikin isar iko da izza zai fara magana sultan ya miqa hannunsa gefensa ya dauko silallan zinarin dake gefensa ya ajiye a gaban NUAB din da suke dauke da sunan Ayanah ghaz baro baro a jiki.
#MAMUH
09033181070
[06/01, 10:35 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

152
Yana ajiye wa bayansa ya mayar a natse ya jinginar a kujeran dayake zaune har lokacin kafarsa daya na akan daya ya zubawa NUAB idanuwansa wanda shima a natse ya dago idanuwansa masu kyau ya kalli sultan din kafin ya maidasu a natse akan abinda ya ajiye masa a gabansa ya zuba musu ido yana kalla.

Shiru sukai dukansu idon kowannensu na kafe akan abinda yake gaban nasu suna kalla,
Chapter 79 · 0% Book details