← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 112

Sashe 6

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tenya na Zaune palo Bahar ta shigo ta gaidasu itada Maa Sakinah ta shige dakin Maa din kai tsaye Wanda sam tenya bata damuba sbd tinanin Wani aikin zatai a ciki dan haka firarsu suka ci gaba da Leylah wadda take tenya takejin har a zuciyarta tana karban auren Leylah dari bisa dari duk da sakon bai isa ga LEUL din ba Sai a gobe insha Allah sultan zai isar masa sbd jiya da yau din duka daga sultan har NUAB da kowa hutun dawowan sultan din akeyi daga gobe zaman fada zai Dora.

Wankanta tayi tai sallah ta Zaunawanta a dakin har akai ishai tanayi ta kwanta bacci koda Maa a shiga mata da fruits da madara tada ita tasaka tasha tukuna ta koma baccin.

Washe gari haka suka tafi yau kam sosai ASIM ya zauna da ita yana mata tambayoyin da suka ja zance yafara yawaita a tsakaninsu Wanda hakan yake basa dukkanin mutsuwan dayake buqata ita kuma shine mutum na biyu bayan Maa sakinah dinta da matsayinsa ya wuce nata amma yake kokarin sakewa da ita dan haka a natsenta ba hayaniya take amsawa kowane zancensa.

Yau da farin ciki sosai yake sbd firar daya samu yayi da ita yana sake gamsuwa da kowace irin rayuwar da zaiyi da ita.

Ayau dinma a tare suka fito da yammar dan tafiya zuciyar ASIM fes Akan tunanin daya yanke na isar wa da sultan sakon ya shirya karban imebetin farko kafin aurensa dan kuwa yanason Bahar ta zama tasa har abada ya shirya tsaf Akan fuskantar komai dazai hanasa mallakarta Bare babu tinda baiwa ce batada ikon kanta hakama bame ikon Hana hakan koda kuwa shi sultan dinne sbd halascin Masarauta ne.

Acan fadar sultan ma kai tsaye sako ne da yammar ya isa bangaren LEUL me boyem na takarda basa auren LEYLAH YUNAR BOYEM a matsayin tukuicin Barka da dawowansa gida Bayan shekaru.

Aleey ne ya karbi sakon kuma shine ya bude ya fara ganin abinda yake ciki dan haka sunkuyar da Kansa yafara yi a natse yana kasa fadawa NUAB din sbd sanin aure daya ma dayake Kansa bai karbasa ba yama manta dashi kila bare aure na biyu Wanda yake na sarauta ne har abada NUAB din bazai karbesa ba.

Jin shirun aleey din ya saka NUAB din dayake Zaune sanye da fararen kayan sanyi a jikinsa dagowa ya zuba masa fararen idanuwansa baice komaiba ya miqa masa hannu sbd yasan koma menene aleey shakkar isar masa dashi yakeyi bare kuma daga sultan sakon yake.

Da sanyin jiki tareda girmamawa Aleey ya miqa masa takardar me dauke da stamp ma masarautar Wanda shine sakon auren da zai fita a matsayin sanarwar hadin auren.

Karantar sakon yayi har karshe yana ganawa ya dunqule takardar ya jefar yana jin ransa da zuciyarta na mummunan baci da wata irin tafasa baisan waye ma yarinyar da ubanta da ake magana akai ba.

Acan ma sakon ya isa ga mahaifiyarsa wadd akai tsaye ta kirasa a waya tana nemansa sbd sanin zai iya samun sultan Akan hakan dan haka ta buqaci ganinsa da gaggawa dan kuwa ita hadin auren yayi mata dan kuwa bazata qi yar Zuhrah ba tinda Allah bai bata ikon cika burinta ba Akan ‘danta.

Koda kiran Ammin ya shigo wayarsa zuciyarsa takai qololuwan fusata dan haka miqewa yayi kai tsaye ya fito su Aleey na bayansa a kame sbd ganin bacin ransa a saman qoli yake.

Tinkaro gefen sukai daidai ASIM ma ya iso tareda sakaman dasu Bahar ja bayansa amma ita tana daga gefensa.

Aleey a karo na biyu idanuwansa a Yauma sun sake tabbatar masa da abinda ya kasa yadda dashi a Karan farko ganin Bahar a tareda ASIM dan haka satar kallan NUAB yayi daidai Wanda yake gaban ya dan tsaya tareda kallan ASIM Wanda ya dakata sbd tinanin gaidasa aleey zeyi kaman daga sama aleey din yace

‘Barka da yamma Ms Ayanah Bahar’

ASIM da maganar ta kashesa cikin iko da isa yace

‘Baiwa tace ta musamman bakin Ka ya San yanda zai fada sunanta…..

NUAB dayake gap da saka kai bangaren Amminsa dakatawa yayi cak tareda dan dago idanuwansa da suke jajir sbd fushin dayake tafe dashi sbd yaji lokacinda aleey a Ambaci sunan sedai bai tsammaci amsar data fito daga bakin ASIM ALMAZZ ba….
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:49 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

76
A cikin nutsuwa da wata irin izza ya juyo a hankali idanuwansa dake jajir suna dagowa tamkar Wanda suke a buge sbd wani zazzafan yanayin dayake cikinsu na abinda ya gama kunno wutar jininsa da kuma abinda kunnuwansa suka ji masa yarinyar da igiyoyin aurensa uku suke kanta da sai ayanzu ne ma da aka ambaceta yake tina hakan Wani yake kira da baiwarsa.

Akan fuskar Aleey ya fara sauke idanuwansa sbd ya samu direction kai tsaye na wacece Bahar din a cikin bayin dake tsaye cikeda Wani irin tsoron ganin maza biyu masu BOYEM da kanta tsaye a gurin daya niimarsa ta dauki Zafi take,

Aleey da NUAB din yana dakatawa shima ya dakata da maganar da zaiyi yana qasa da Kansa dan kuwa yasan duk abinda ya Dakatar da tafiyar NUAB mai zafi ne dan haka gabaki dayansu Yaransa qasa sukai da kai kowannesu shirye da raba ASIM da rayuwarsa batareda shakkar komai da abinda zai iya biyowa idan NUAB yace Ayi to yi din zasuyi.

Kallan bayin yayi da idanuwansa masu girgiza Wanda aka kalla dasu a Karan farko ya bi bayi da kallan tsaf yagansu gabaki daya da uniform da komai iri daya,

Gabaki dayansu kasa riqe kallansa daya sauka akansu sukai duk da kansu na qasa cikeda fargaba da tsananin girmamawa zubewa qasa sukai gabaki daya bayin kaf.

BAHAR saida kowa ya zubewa tukuna ta motsa zata zube qasa din itama zuciyarta na Wani irin nauyi da radadin baqin cikin kasancewanta anan a Karan farko,

Sauka gwiwowinta zasuyi qasa ASIM da zuciyarsa bazata taba daukan ganin macen dayake tsananin so kuma macen da zata zama imebētinsa zuwa wishmarsa ta durqusawa NUAB dan haka kai tsaye hannu ya miqa zai riqota dan hanata kafafunta kaiwa qasa.

Hannunsa na isa gareta aleey yayiwa hannunsa Wani irin riqo da hannunsa daya tareda dagowa da sauri da Wani irin mamakin dayake hade da bacin ran da bai bayyana duka ba sbd babu kuma Wanda yake da ikon kai hannunsa jikin Bahar da aurensu yake kanta ko waye kuwa.

NUAB kuwa da zuciyarsa ta gama qara fusata hakan daya faru ya tabbatar masa waye Bahar din dan haka idanuwansa ya rintse da karfi tareda budesu akanta ya miqa hannu cikin wani irin fushin daya saka su aleey sake yin qasa da idanuwansu ya damqi hannunta ya jata yana Juyawa daga inda ya fito tareda fasa shiga gurin Ammin nasa.

ASIM da zuciyarsa ta gama quluwa tana wata irin tafarfasa fizge hannunsa yayi cikin tsantsan tiriri da kishin dayaji na Neman kashe zuciyarsa da dukkanin gangar jikinsa ya daga hannu zai shararawa Aleey lafiyayyan Marin rashin da’ar da yayi masa daya daga cikin securities dinne ya sake riqe hannunsa Wanda bai tsaya wata wata ba ya sakarwa security din wata mummunan Marin daya saka fuskarsa jajir.

Sauran securities din cikin girmamawan da batada amfani garesa suka dan saukar masa da kai bisa umarnin aleey daya kallesa ya bude baki yace

‘Allah ya Huci zuciyar Li’ul ASIM’

Yana gama fadan hakan ya juya yabar gurin yana ban Bayan ubangidansa da gabaki daya rahamarsa ta dauke sbd Zafin dayake tafasa a jininsa na fushin dayake hawan gobara a yanayinsa,

Sauran suma gabaki dayansu bayansu suka bi Ana barin ASIM a gurin cikeda Wani irin tafasa da jininsa ke yi a gurin sbd NUAB ya gama wulaqantasa da bayyanarda shirin yaqi a tsakaninsu dan kuwa hakan da yayi masa zai iya bayyanar da tasa zazzafar qiyayyar sbd abinda yayi a gurin yafi yaqi da gabar dake tsakaninsu na gadar mulki,

Zai iya hakura Bayan yaqi da dukkanin kokari idan yayi ya rasa mulkin BOYEM amma kuma Akan Bahar bayajin a bayyane ma zai iya barin ko uwar NUAB din a raye bare NUAB din dan kuwa sedai ya rasa ransa gurin yaqar hakan dan kuwa Bahar tasa ce akanta zai iya fuskantar kowa,
Zai iya tsayawa gaban kowa ya bugi kirjin ita tasa ce dan haka NUAB koma me yake nufi da hakan da yayi a yanzu dan kawai tana baiwar mahaifiyarsa to tabbas zai nuna masa baiwa ce ita daga shi har ita sunada iko da ita cikakke dan haka zai shayar dashi mamakin da zai girgiza dan kuwa a ganin idonsa zata zama macensa imebētinsa.

Barin gurin yayi Salman na biye dashi shima tasa zuciyar kaman zata fashe suka isa bangaren queen haile ASIM din ya shige idanuwansa jajir baya ganin komai daidai tsabar baqin cikin dayake Neman kashesa.

HAILE dake Zaune tareda su Aslam suna hutawa a palon hutawanta Kayan marmari da abubuwan hutawan cike Jere a gabansu duk da ba Wani dadin rai suke cikinsa ba dan kuwa suna Zaune a gurin labarin auren ‘yar mai girma YUNAR daya bawa NUAB Yazo kunnuwansu ya lalata gabaki daya Sauran dan farin cikin rayuwar daya rage musu zuwa sabon baqin ciki me girman gaske dayake Neman makantar da HAILE wadda ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Aslam wadda tafara zantika cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki me girman gaske hannuwanta har suna rawa idanuwanta jajir take cewa
Chapter 6 · 0% Book details