← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 112

Sashe 62

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba amfanin zamansu a tare yanzu tinda daman sun amince zama da juna ne sbd cimma burikansu amma ayanzu da hakan ta faru ba amfanin zaman sbd shi dai a yanzu ya rungumi kaddara ya hakura da wannan burin nasa da yasani har ya mutu bazai taba dena son bahar ba bare wannan radadin daya dasu a zuciyarsa dan haka zai sauwake mata dan kada ya cutatar da ita da aurensa.

Da daddare bayan sun gama cin abincin da babu wanda yayi magana a cikinsu cinsa kawai sukai da damuwa fal a ransu,

Magana zai mata ta miqe tabar gurin tana wucewa kurya dan wanka tayi shirin bacci duk da tanason magana dashi ayau din kaman yanda shima yakeson magana da ita,
Ita tanason masa maganar komawansu ne sbd zamansu anan din baida amfani.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 11:29 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

135
Wanka leylah din ta shiga tana shiga yana shigowa dakin shima ya nemi guri a sofa ya zaune dan shi already yayi wanka da shirin bacci kayan maccin hk ne a jikinsa masu santsi da suka zauna dakyau a lafiyayyan farar fatarsa ta jinin boyem.

Tana fitowa sanye da bathrobe pink gashinta na tsakiyar kanta a daure kasa da band pink shima sbd kusan komai nata na amfanin cikin dakinta is pink,

Qamshin shower gel din mai tsada da kyau ne ya kado masa yana shiga hancinsa ya san ta fito ya dago kansa ahankali sbd nisan da yayi a tinani me zurfi baiji karar fitowan ba,

Kallo daya yayi mata ya dauke idanuwansa daga kanta yana ajiye wayarsa dake hannunsa gefensa yana juya maganar da zai fara fada mata a baki da zuciyarsa sbd a jinin boyem da boyem babu saki babu rabuwa matiqar ba akwai kwakwaran dalili me girman gaske da manya zasu zauna a tattauna,

Amma shi basuda wani dalilin wannan rabuwan da zasuyi bayan ta basa son juna,
Shi daga yanzu dazai sauwake mata bayajin zai iya rayuwa a boyem kuma sbd babu abinda ya rage masa acan bayan memories da zasu damesa su ringa dawo masa da rayuwansa da kurakurensa na baya daya ringa aikatawa akan karagar mulkin da Allah ya hana masa kuma a yanxu ya tabbatarda akwai dalilin da Allah ya hana masa dan haka zai rungumi kowace irin kaddararsa a cikin biyun nan ta rasa mulki data rasa macen da akanta ne zuciyarsa tasan abubuwa da dama na kwarai bayan zallan mugunta da munin zuciyar daya taso cikinsu,

Leylah ma zaunawa tayi ta dan shirya sama sama jiki a mace tana gamawa ta miqe taje inda kayansu suke jere a closet ta saka kayan bacci riga me kauri sosai da san tsayi kadan sai safa sbd sanyi dayake shiga ta tafin qafa.

Ajiyan zuciya ta sauke lokacinda ta gama harta nufi gado zata kwana sai kuma ta kasa sbd har ga Allah gida takeso son barin qasar nan takeyi da gaggawa dan haka fasa kwanciya tayi ta zauna bakin gadon tana facing dinsa kaman ynada shima ya dago ya kalleta ya sauke ajiyan zuciya ya bude baki yace

'Inaga ba sauran amfanin zaman nan da mukeyi tinda dai kowannenmu ya sani babu dayanmu a xuciyar juna,
Zaman aure zamuyi daga yanzu bawai zaman wata deal ba dan haka idan har babu soyayya ko kauna ko daya babu amfanin zaman wanda zai iya zama illa da cutatuwa a garemu musamman keda kike mace zaki zauna ne a guri daya ki karar da rayuwar a cikin rashin farin ciki da quncin da baasan yaushe zai qare ba......

Shiru yayi sbd nauyin da muryansa tayi tana karyewa tareda gangar jikinsa wadda take dan rawa sbd har lokacin mahaifiyarsa da bacin rai da baqin cikin da zata shiga idan taji abinda yakeda niyar yi zata shiga hakama da rayuwar Leylah din da zata sauya amo zuwa karba wani sunan da baima hau kanta ba na bazawara...

Ita kanta leylan fahimtar menene yake shirin faruwa da rayuwanta ya sakata sunkuyar da kanta hannuwanta na dan wata irin rawa sbd zamtowanta bazawara shine mugun abu na karshe da batai tinanin zai shigo rayuwanta ba,

Koda a baya take ikirarin auren NUAB ta rabu da Asim tana fatar ne ta auresa a matsayin matar data rasa mijinta ya rasu baya duniyar bawai sakinta akai ba kuma a yanzu da duka buri da hope dinta sukai shattering bata kawo zawarci shine abu na farko da zata fara tarba ba a cikin wannan baqin cikin,

Rintse idanuwanta tayi ahankali wasu hawayen da batasan dasu ba suka gangaro suka sauka akan hannunta dayake kan cinyoyinta yana dan rawa ta dunqule ta qanqame zuciyarta na qarasa fashewa tako ina.

Kasa kallanta yayi sbd kasa da yayi da kansa yana kasa cigaba da maganar sbd yanda jikinsa shima yake dan rawar,

Shiru sukai kowa a cikin mummunan yanayi har lokacin hawaye gangarowa sukeyi daga idanuwanta,

Daqyar ya iya karfin halin sake bude baki yace

'Ina rokon yafiyarki Leylah yunar akan kaddarata data lalata taki,
Zan baki yancinki sbd ki samu rayuwan datafi zama dani dan babu abinda yake cikeda da tawa rayuwan bayan qunci da rashin samun tarbiya da koyarwan daya kamata...leylahh....

Wani kuka me sauti ta fashe dashi wanda ya kasa riquwa ya sanyashi yin shiru yana dagowa ya sauke idanuwansa akanta,

Ganin irin kukan datakeyi ne dayazo mata gabaki daya ya sakasa tasowa da sanyin kafafu ya isa gareta da sauri sbd rawa jikinta keyi sosai ya saka hannuwansa biyu ya tareta tana kokarin zamewa qasa ya dagota ya sake zaunar da ita gadon yana dora mata kafafunta akan gadon ya kasa kallan idanuwanta dake kuka tana kallansa sbd ya gama tarwatsa mata rayuwa kaman yanda ya fada zai bar mata illar da zata kashe rayuwarta koda ta rabu dashi kuwa sbd kaf duniya bame dauke mata suna da matsayin bazawarar da Asim Almazz ya gama da ita ya saketa.

Hannuwanta duka biyu ya kama da nasa yana dagowa ya kalleta yana jin ciwon rayuwan da suka samu kansu wadda daga karshe ga inda ta kawo su ta ajiye bame future a cikinsu.

Zame hannunta tayi tana jin kaman zata mutu sbd baqin ciki kukanta naci gaba da fita yayi saurin sake riqe hannunta ya bude baki yace

'I'm sorry Leylah yunar,
Leylah yunar zaki samu rayuwa me kyau a gaba indai kin rungumi kaddar da ni na riga na runguma...

Sake qwace hannunta tayi jikinta na rawa ta bude baki cikin tsananin zafi da radadin dayake neman kasheta tace

'Bazan yafe maka ba Asim Almazz,zan tsaneka har karshen rayuwata sbd zaka dora kalma da matsayin zawarci akaina,
Rayuwata ta lalace,rayuwata ta zama mara zabi bayan na karban duk abinda zaa taho mata dashi sbd kawai zan zama abinda baa zama a boyem,
Rayuwata zata rasa darajar da kowace macen boyem take dashi tawa darajar zatai raunanan da babu gyara a cikinta, i will forever hate you Asim Alm......

Rungumeta yayi da sauri jikinsa na wata irin rawa yana girgiza kai yana cewa

'Bazaki rasa darajarki ba zaki samu yanci ne daga rayuwa da wanda baida future,
Wallahil Azeem Leylah bansan wace rayuwa zanyiba yanzu,
Banda gurin zuwa nayi rayuwa,
Banda rayuwar farin ciki da kwanciyan hankalin datake jira na a gaba sbd na sani zan girba duk abinda nayi ne ko mahaifiyata tayi.....

Turesa tayi da karfi kukanta na wata irin tsanantar data ringa rawan jiki sosai sbd itama tasan abubuwan dake jiranta na girban abinda tayi sunada yawa wannan ma shine farko da alama dan haka takejin hukuncin yayi mata tsauri....

Rungumeta yayi da karfi shima yana hawayen masu gudu da radadi yana kasa magana yanaji tana turesa tana dukansa da karfi tana cewa ta tsanesa a rayuwanta hartayi laushi ta dena motsi kukan kawai takeyi tana qanqamesa zuciyarta na qarasa shattering.

Sake qanqameta yayi shima a jikinsa yana cigaba da gangaro hawaye masu zafi daga idanuwansa sbd abinda ya fada da gaske yakeyi baida rayuwa a gabansa dan baisan ta inda ma zai fara ba,
Rayuwa a boyem ta fice kansa da baima san ta yanda zai koma can yayi rayuwa ba rayuwar da kadaici ne kadai da qunci tareda rashin abinyi zasu cikata....

Wannan tinanin yake cin zuciyarsa yana karya duka karfi da garkuwan jikinsa hawayensa suka tsananta gudu suna sauka tareda fara fidda wani sauti na kuka mara dadin ji dayake fitowa daga asalin kirjinsa yana ratsa dakin wanda ya saka leylah tsit da nata kuka tsigar jikinta na tashi sbd radadin dayake bayyana a nasa kukan ya wuce nata.

Qanqameta yake sake yi yana kukan kansa aqasa idanuwansa a rintse,

Dagowa tayi daga jikin nasa a hankali hawaye na gangaro mata ta kallesa da jajayen idanuwanta ta saka hannunta daya ahankali ta tallafo fuskarsa dake qasa tana girgiza kai da murya me rawa tace

'Na yafe maka Asim Almazz,zan yafe maka,
Wannan kukan yana bani tsoro ka dena pls banason ji....
Asim almazz rayuwa zatai maka kyau a gaba insha Allah tinda ka yadda ka karbi kaddara zaka sauya...Asim nima na yadda da kaddara zan rayu da sunan bazawarar da Asim almazz ya sak......

Bude idanuwansa yayi akanta yana kallanta da jajayen idanuwansa dake cikeda hawaye itama shi take kalla ta sake kai hannunta dayake rawa fuskansa ta shafi hawayensa ta bude baki tace

'Na shirya ka sakeni'

Sauke kanta tayi sbd jiran amsarsa da zata bata yancin rabuwar,

Jin shiru ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna ta bude baki da tsananin sanyin jiki da gajiya zatai magana ya kama fuskanta ahankali ya hade da tasa tareda hade bakinsa da nata yana zira harshensa cikin tsakiyar bakin.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 11:29 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

136
Qanqamesa tayi da hannuwanta dake kirjinsa hawaye naci gaba da gangarowa daga idanuwanta masu zafi tana jin yana fara kissing dinta da wani irin zafi da sanyi duka a lokaci daya,

Bata iya motsawa sbd a quncin da dukansu suke ciki ayanzu babu me iya banbance buqata ko rashinta da suke ciki ayanzu ba,

Matseta sosai yayi jikinsa yana sake shigar da bakinsa sosai a cikin nata yana mata wani lafiyayyan tsotsan dayake ratsata ahankali yana sakar da jikinta a cikin nasa tana rufe ido hawayen ciki suna qarasa gangarowa hannuwanta na dan fara rawa wadda bata kukan datakeyi ba tin farkoba,
Chapter 62 · 0% Book details