← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 112

Sashe 92

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabaki dayansu kofar suka juyo suna zubawa ido sbd shigowanta ya shigo musu da wata irin kamshi me tsananin sanyi daya kama jikinta sosai kaman wacce akewa shirin sabon aure sbd duka basirar tenya ta gyaran Amare da shiryasu ta fiddota akansu wannan karan wainda duka kayan qamshinta dasuka gama kama jiki da suturar su bahar din hatta wayoyinsu sun kama qamshin kai me karatu zaka iya samunsu tsaf a gurin SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387,
Qamshin da zaka samu a jikinsu Leylah da Bahar din tsaf zaka samu komai da komai da duka abubuwan gyaran jiki da tabbataciyar qamshi da hatta gashin kanki da panties naki zasu ringa fidda qamshi me sanyin da ko zama kadai a kusa dake zai bawa ruhin mijinki nutsuwa ki tintibi SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387.

Kallan mamaki dukansu suke wa Leylah wadda kwata kwata ta dena zuwa bangaren sedai a waya take kiran mamin ta gaidata sai kuma can baa rasaba take zuwa ta gaida mamin sai kuma yau gata kuma da wannan lokacin na dare.

Akan Asim daya nutsu yana ginginar da bayansa jikin kujera tareda tattara nutsuwansa guri daya ya kafeta da fararen idanuwansa suka maida kallansu sukaga yanda imaninsa gabaki daya yake kanta yana kallanta.

Takowa leylah tayi a natse tana jin gabanta itama yana dan faduwa sbd ganin wanda bata taba tinanin ganiba a lokacin dan haka ta kasa dagowa tai qasa da kanta tana jin idanuwansa tsaye cak akanta yana mata kallan dayake kashe duka jikinta.

Haile kafe Asim da ido tayi cikin tsananin mamakin yanda ya mace mata a zaune ya tsayar da nutsuwansa akan mace.

Mutuwa ta sake jin jikinta yayi sbd wata sabuwar balai da masifar ce take bayyanar mata dan kuwa a yanda take gani a yanzu Asim ya gama susucewa akan leylah dake jinin Ayanaah shikenan shima rasata zatai wa ayanah kenan,

Leylah na isowa cikin girmamawa ta zauna gefen kafafun mamin tana bude baki ta gaidata a natse.

Daqyar Haile ta iya bude baki tana shiga wani sabon yanayi ta amsa tana kasa dauke idanuwanta daga leylah da gabaki daya ta sauya tayi wani irin hasken daukan ido da cikowa tayi mulmul kamar amaryar dake cin amarci da sabon ciki.

Su Aslam ta juya tana gaidawa suma cikin girmamawa da tambayan kwana biyu tana kokarin nuna sakewanta da girmamawa garesu.

Suma amsawa sukai suna kallan Asim wanda fuskansa tafara sakewa da sanyi suna mamakinsa da gane abinda ya tsayar dashi kenan.

Kaman bazata kallesa ba sbd yanda take jin tsananin nauyi amma kuma sbd nuna girmamawanta garesa gaban mahaifiyarsa saita dago a natse ta kallesa da idanuwanta dasuka qara haske sosai idanuwansu suka hadu take ya sarqe da yawun bakinsa yafara tari a hankali yana dan kamewa sbd ganin idon kowa na kansa mamaki na neman kashesu.

Gaidasa tayi tana dauke idonta batareda jiran amsa ba.

Amsawa yayi yana dan gyara murya kafin ya juya ya kalli haile data koma kaman me zaman takaba sbd yanda fuskanta tayi kalar tausayi ya bude baki yace

'Mami sallama Leylah tazo miki gobe zasu wuce Anjom gabaki dayansu asalin garinsu Ammi sbd hidimar bikin da zasuyi kuma ita Ammin ba dawowa zataiba acan zata zauna tukuna so ba tafiyan dawowa ce yanzu ba idan suka tafi shine taxo miki bankwana..'

Ba haile ba hatta su Aslam juyowa sukai gabaki daya suna tsayar da idanuwansu a kansa cikin rikitaccen yanayin kasa fahimtar me yake fada sbd barin ayanah boyem gabaki daya kaman yana nufin barin Sultan yasar barin boyem din gaba daya ya koma can da zama.

Meryam mahaifiyarsu ta maida idanuwanta akai tana kallan yanayinta sbd jan da fuskarta da idanuwanta sukai a take hannuwanta na dan rawa ta dunqule su tana hana leylah dake gefenta ganinsu tanajin kaman numfashinta na toshewa a kirjinta,

Sultan barinta zaiyi ya koma garin imebēti dinsa da zama shikenan kaddararsu ta zama tarihi ko me?
Da bataji hakan ba da sedai idan zai tafi taji kokuma idanma ya tafi ko me?
A karo na biyu na karshe zai sake nunawa da bayyanawa duniya Imebēti dinsa ya zama akan kowa da komai yabarta anan ba miji,ba 'da ba mulki ba daraja ba farin ciki ba walwala.

Wannan itace kaddarar da bazata taba dauka da yadda ba dan kuwa a yanxu anxo karshe komai ya qare ya wuce limit din daukanta,
Asim ma barinta zaiyi yabi leylah shima acan zai rayu sbd a yanda take gani yanzu gabanta Asim akan leylah tsaf zai koma can yayi rayuwan dayake buqata ita shikenan ayanah ta kwace komai ambatarta da zallan tsoffin 'yaya a gabanta da tulin baqin ciki tana rayuwa a karkashin iko da mulkin 'dan Ayanaah wanda batada darajar da ko kallan arziki daga garesa,wallahi tallahi bazai yiyuba bazata yadda ba.

Rawa jikinta ya fara idanuwanta na rinewa wanda ya saka meryam ma datake cikin tinani kala kala akan ita dai kada sultan ya tafi batareda anzo neman auren nata ba duk da wlh ko can ita anjom din tsaf zata saka a samesa a nema auren acan hadda daurawa ma idan ta kama kawai dai ita burinta kafa Mamin ta shiga tashin hankalin da zaayi wata babbar tashin hankalin dazai saka ya sake ciresu daga rayuwarsa yace haryanzu bin hudubar mamin sukeyi.

Tasowa tayi ta dan daure tana kallan leylah tayi mata fatan Allah ya kiyaye tareda fatan ayi bikin lafiya a watse lafiya ya kuma bada zaman lafiya.

Asim ta kalla wanda duka halinda suke ciki baisaniba dan baima lura ba tace masa leylah din ta tafi ta kwanta tinda akwai tafiya gabanta ga dare yayi.

Miqewa yayi a natse batareda jin komaiba ya miqawa Leylah din hannu wadda ke kokarin tashi daga qasan tana jin ba dadi sbd zaman datai a qasan da qaramin ciki.

Satar kallan Haile data fice hayyacinta tayi tana qin kama hannun nasa sai dayaga zata sake komawa dabas ya saka hannuwansa biyu ya kamata yana tadata gabaki daya cikeda kulawa ta bude baki tayi musu da safe ba wanda ya isa amsawa se meryam tana binsu da ido har suka fice Asim din na riqe da hannunta.

Suna fitowa time ya fara kalla yaga duka duka mintinanta shida da baro bangaren Ammi bayan yasan a qalla anbata kusan mintina talatin xuwa arbain dan haka daukanta yayi cak sbd kafarta ma kada tayi tafiya a gane
Kai tsaye bangarensa ya nufa da ita yana kallan kyakkyawar fuskanta da ita shi take kalla tana shiga tsoro tana ce masa Maa zata bata ransu su duka idan tasan ta qara gaba daga bangaren Mami.

Murmushi me hade da tsantsar farin ciki ne ya taho masa yana kallan bakinta dayake maganar yakai bakinsa akai yayi mata wani kiss me tsantsan sanyin daya kashe bakinta yace

'Ta kwantar da hankalinta ina zuwa daurin auren Kadir bazan dawoba saita san yanda zatai dani matiqar ba tareda ke zan dawo ba'

Kaman a mafarki taji maganarsa dan haka ta kafesa da ido tana kasa motsawa sbd jin yanayi me sanyi yana ratsata dan kuwa daman damuwanta idan acan anjom ko anan zata zauna bayan bikin batasan makomarma inda zata zauna ba.

Tambayarsa maanar abinda ya fada tayi a natse shima cikin nutsuwan ya kalli cikin idanuwanta ya fada mata duk inda zaiyi rayuwa ta tabbata da ita zaiyi a duk inda take so bayan boyem.

Ajiyan zuciya ta sauke tana jin farin ciki na ratsata da batasan lokacinda ta saka hannuwanta biyu ta zagayo wuyansa ba ta rungume tana lumshe idanuwanta farin cikinta na bayyanuwa.

Suna isa bangarensa a palonsa suka zuba ya zaunar da ita a cinyarsa yana kama fuskanta kai tsaye ya hade da tasa yana hade bakinsu yafara mata wani lafiyayyan kiss me tsananin shauqi da nutsuwan da basu taba samuba a tsakaninsu yana mannota jikinsa.

Acan dakin maa tenya kuwa wayar mai girma Sultan NUAB ce ta shigo wayarta inda kai tsaye ba kowace irin kwana a zancensa ya sanar da ita ba kowa ya bawa matarsa ya tafi da ita Anjom ba bayan ita kuma duk abinda sukeyi ayisa a gama kafin isowansa daurin auren wanda matiqar kafarsa ta sauka qasar babu abinda zai sakasa barin Queen dinsa.

Mamakinsa zuwa yanzu ya dena bata shock ko bugawan zuciya dan haka da angama kawai ta bisa dan haka ta tabbatarda suna isa akan bahar zatafi maida hankalin aikinta dan kuwa zatai mata gyaran da idan ta dawo zata jima a gyaren sbd a yanzu zasu dade batareda suna ganin juna ba.
#MAMUH
09033181070
[13/01, 5:22 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

166
Duk yanda suka shagala basu bari sun wuce lokacinda zaa gane bata bangaren Maminsa ba dan haka babu abinda ma yayi mata kawai yar soyayyarsu sukai ya dawo da ita har kofar bangaren ya sake rungumeta yana kissing gefen fuskanta tareda jin kaman bazai iya jiran ranar daurin aurenba zai wuce gaba yabi bayansu idan suka wuce.

Daqyar sukai sallama ta shige ya juya yana jin qamshinta da nasa na tashi duka a jikinsa ya sauke ajiyan zuciya yana jin farin ciki mara iyaka cikasa wanda ya manta rabansa ma dashi.

Itama tana shiga ba kowa dan haka a kofar dakin maa tenya ta tsaya ta sanar da ita dawowanta sbd batason ta shiga jikinta duka qamshinsa yakeyi ta silale ta wuce dakinsu.

Ko data je Bahar na kan waya da NUAB yana fada mata yanda zata kula da kanta ita kuma tana kwance kaman mara lafiya a dunqule cikeda kasala da mutuwan jiki muryanta na fita a kasalance tana neman hanasa zaman lafiyar zuciya da gangar jiki.

Leylah zare hijab dinta kawai tayi tana nufar toilet harta fito suna wayar itama zuwa tayi ta kwanta xuciyarta fes tana jin yau damuwanta da duka baqin cikinta yakau.
Chapter 92 · 0% Book details