← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 112

Sashe 94

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasancewan masu anjom suna gidan ya saka kowace motsi me hayaniya ya dauke a gidan sbd a basu daman hutawa dakyau.

Babu wanda ya farko ko fito a cikinsu sai bayan karfe daya kusan ma biyu,

Sallah da wanka ta sake yi sai a lokacin ta janyo wayarta tana kunnawa tareda kunna wifi na gidan sbd basuda layikan qasar dole iya wifi zasuyi amfani dashi suyi amfani dasu WhatsApp da sauransu.

Password din aka kawo mata daki ta saka take sakonsa kuwa ya shigo wanda tana gama karantawa murmushi me sanyi ta sake tana lumshe idanuwanta sbd tafar jin kewansa me tsanani a yanzu da basama qasa daya.

Kiransa ta saka ta WhatsApp yana dauka a natse cikin wani irin sanyi suka sauke ajiyan zuciya tare tana qarawa da murmushi me sautin daya shiga kunnuwansa ya sakasa sake lumshe fararen idanuwansa yana ambatar cikakken sunanta cikin nutsuwan da itama saida tsigar jikinta ta tashi ta bude baki daqyar ta amsa tana gaidasa cikin basa girmansa na miji kuma sultan.

Yanda tayi gaisuwan ya sakasa fidda wani murmushi me nutsuwa yana amsawa tareda fara binta da tambayan hanya da gajiya da baqunta da kuma missing nasa.

Amsa masa tai duka a kasalance tana fada masa missing kuwa tanajin kaman idan ta dade batama gansa ba Amminta bazata sake gane lafiyanta ba.

Murmushi me sautin nutsuwa ya sake sakewa yana jin kalman tata har cikin kwakwalwansa yace

'GHAZs princess kada ki janyo aikin da bazaki iyaba fa sbd Anjom bata da nisa gareni matiqar kina can'

Itama murmushin ta sake tana cewa

'Hmmn anan dai ai ko kazo ko masaukinka bamada'

Murmushi kawai ya sake bai bata amsar maganar ba sbd shida yakeda mata da uwa a gari a masarauta ai zancenta neman magana ne kawai.

Fira suka cigaba dayi a natse a kasalance har tsawon lokaci ba hayaniya ba daga murya har suka gama tukuna ta ajiye wayarta tana fitowa tabar leylah na shiga wanka dan ko anan a daki daya suke yanxu da suka saba.

A palo ta tadda su Ammi duka sun fito kusan kowa waya yakeyi banda maa sakinah datake dining tana sake gyara yanda tsarin abincin da ake jere musu a dining tana bada umarnin abubuwan da zasu kawo.

Gurin maa sakinah din ta nufa tana tayata aikin tana dan lafewa gefenta sbd sam tafara jin ta rasa me ke mata daidai.

Suna gamawa daidai su Ammi sun gama waya dan haka taje ta zauna gefen Ammi tana musu sannu da gajiyan hanya tana dan sake neman kokarin kwanciya.

Dining suka suka nufa dukansu suna zaunawa leylah nafitowa itama dan hakaa tare sukaci lafiyayyan abincin da aka cike dining dasu kusan kala uku.

Suna gamawa a palo suka zauna kowa da abimda yakeyi itada dai tana kwance lafe gefen Ammi jikinta yayi dumi kaman me shigar zazzabi Ammin na jinta tayi shiru tana shiga nazarinta sbd gabaki daya ta sauya da qananun ciwo da kasala.

Batai mata tinanin komaiba musamman ciki sbd batajin tayi haduwa sosai da NUAB da zatai saurin samun ciki hakama yaushe rabon su ma da juna dan haka ta ringa mata fadan ta rage san jiki da yawan kwanciya.

Maa sakinah ce kadai tafara zargin akwai wani abu a jikin Bahar din sbd yanda ko cin abincinta ya sauya sam batason abinci sosai yanxu sai tea da abincin ruwa ruwa,

Maa tenya ma bata kawo tinanin komaiba sbd ta dauka abubuwan datake basu ne yake saka kasalan da yawan sauye sauyen appetite tinda yanawa wasu matan hakan.

Leylah ma maa sakinah na ankare da ita duk da ita kwata kwata laulayinta ya bace gabaki daya kawai cika take sake yi tana kiba.

*****kwanaki sikai suna hutawa dakyau sunje ziyarar bangaren kabarin iyaye da dan uwansu sunyo musu addua tareda fidda sadaka me yawa aka rabawa yan gari hakama sun fita sun zagayo gari sun dubo gari kuma gari ya dauki dawowan asalin masu garin dan haka ake jin tamkar haske da rahamar garin ta qarasa dawowa mutane sunyi farin ciki da murna sosai wasuma hadda kuka.

Su kuwa tinda suka dawo basu sake fita koina ba sbd yawo baya cikin dabiun jinin kowane dan sarauta kuma basu saba daman dan haka maa tenya bude aikinta tayi tafara cigaba dan ma bikin na sake matsowa.

Hidimarsu suka maida hankali suka fara sosai ta biki hankali kwance anata kashe dukiya me yawa da zama busy dan kuwa sosai aka fara gayyato mutane,

Ita kanta yayanta dukansu sun taho suna anjom sun iso da wuri kuma zasu kwana biyu suga mahaifiyarsu da kyau ko bayan bikin kafin su koma kuma kowa da hannu bibbiyu da kauna da sakewa aka tarbesu ba babbanci a tsakaninsu dasu Bahar dasu da yayansu yan mata da suka taho dasu duka dan haka gidan ya sake cika sosai da samun hayaniya.

Daga sultan har NUAB har Asim babu wanda a cikinsu baya cikin tsananin matsuwa da zuwan ranar daurin auren musamman Asim da baya komai bayan shirin barin boyem daya gama daga anjom bayajin zai dawo daga can zasu wuce da matarsa gaba dan haka ya zama busy sosai da kuma dagewa gurin cusawa mahaifiyarsa sabawa da rashinsa dan kuwa zamansa din baida amfani gwara tafiyar ya fara aiki ko wasu businesses din tinda nan a zaune yake zaman banza sbd babu jinin boyem dazai taba aiki a wani guri cikin qasar boyem hakama a cikin masarautar ma bazai taba samun aikin ba sbd NUAB ne me mulki hakama a yanzu da Kowa rayuwan aure zaiyi ya zabi yinta a wani gurin daban kawai da iyayensa daban dana NUAB da BAHAR.

Haile da har lokacin ta kasa yadda da 'danta barinta zaiyi hakama sultan barinta zaiyi zarewa tayi gabaki daya kwana takeyi kuka wuni takeyi baqin ciki da qunci,

Umarni da duk wani tashin hankalinta bai saka Asim ya janye barin boyem ba wanda dan haka ta koma roko da magiya amma ya kasa fasawa sbd wasu manyan dalilinsa da bai bude mata ba amma hakan shine mafi daidai kuma yana shirye da tafiya da ita dan itama ta samu sauyin guri ta samu salamar zuciya idan zata yadda da hakan amma sam taqi yadda haukacewa kawai take neman yi takai har cikin baccinta take ambatar sunan Ayanah ghaz tana maimaitawa tana hawaye.

Sultan ma ya zaunar da ita ya sake sanar da ita tafiyarsa wadda ta sakata rasa dukkanin sauran hankalinta musamman dayake fada mata zai jima kafin ya dawo hakama idan ya dawo nan din itama zai jima mata kafin ya sake komawa anjom.

Kaman daga sama yana gama fada mata maganar ta bude baki tana kallansa da idanuwanta da suka bushe jajir tace

'Sultan dan Allah ka saki ayanah ghaz ka barta tinda ta riga ta koma qasarta,
Zaka iya mun hakan ni mahaifiyar 'yayanka??
Kaman zan mutu nakeji,zuciyata zata buga,baqin ciki da qunci zai kasheni'

Kallanta ya tsayar da idanuwansa yanayi a natse cikin nazarin yanayinta daya fara kamata ya karanta dakyau kafin komai sbd tabbatarda lafiyarta kalau.

Ganin alamu sun nuna kalau take ya dauke idanuwansa daga kanta yana ajiye wayarsa gefensa ya bude bakinsa yace ta tafi kawai.

Sake maimaita abinda ta fada masa tayi tana kallansa idanuwanta na sake ja

Bude baki yayi yace

'Kije kiyi hakuri bazaki samu abinda kike fadan ba,
Bana auren mace na saketa a rayuwata musamman macen dana jarabtu kafin samu,babu abinda zai sameki ki cire damuwa ki danga duka quncinki zai yaye'

Yana gama fada mata hakan ya nuna mata kofar ficewa da hannunsa daya dan yana buqatan tafiyar tata dan yanda kalamanta suka sosa zuciyarsa dan bai taba tsammanin kai tsaye magana irin wannan daga gareta ba.

Bata iya cewa komaiba ta fice tana hadiye wani qullutu me nauyi da daci daga maqoshinta tana komawa bangarenta.

Wuni tayi a daki babu wanda ya sake ganinta hatta yayanta duk yawonsu sun kasa ganinta tana daki ta rufe taqi fitowa.

Kasa nutsuwa hankalinsu yayi suka ringa jin damuwa dan haka suka zauna jigum jigum gashi Asim ma bayanan ya fita tin safe yana wajen masarautar ma.

Sai dare ta bude kofar dakin ta fito
Ga mamakinsu tayi wanka tayi shirinta tsaf ta kira babbar baiwarta ta sakata ta dafa mata shayin sultan zataje tiraka yau din.

Aslam na jin hakan ta miqe taje ta karba aikin ta dafa masa da kanta ta shirya komai tana farin cikin dawowan mamin tasu daidai dik da ba doguwan walwala a fuskanta kaman ma ta gama saddakar da rayuwa meryam ke gani a tareda ita din.
##MAMUH
09033181070
[14/01, 12:07 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

168
Aslam na gama hadawa ta kawo ta ajiyesa yana shirye a cikin wasu lafiyayyun tea set masu kyan gaske sabbi harma da dabino da zuma masu kyau duka ta jere ta ajiyewa Mamin wadda tace su tafi kawai idan ta gama abinda take zata kai masa.

Karfe goma sha daya ta baro bangarenta ta isa bangaren sultan din ita kadai sai baiwarta daya data dauko mata kayan suna isowa ta karba ta shige kadir ma dayaga zuwanta tini yabar bangaren ya tafiyarsa bangarensa saida safe kuma.

Ko data shiga sultan din ya gama komai na shirin bacci yana zaune dakin ba haske sosai yana waya a natse cikin kamala da kwanciyan hankali da Ayanah ghaz wadda take jin nutsuwan wayan dashi itama.

Haile daga fahimci da waye yake wayar wani abun ya sake zuwa ya danne maqoshinta amma kuma tinawa da daga yau baqin cikinta ya qare ya sakata ajiye kayan hannunta a kan table din gabansa tana bude baki tayi magana wadda ta sauka kai tsaye a cikin kunnuwan Ayanah.

Wani iri Ayanaah din taji musamman data kalli lokaci sai kawai taji kirjinta yayi nauyi itama da wani kishinsa me sanyi amma kuma tasan basu kyautaba sbd daga yanzu tasan matiqar yana boyem daidai irin wannan lokacin to na matansa dan haka cikin nutsuwa tai nasa saida safe bata jira amsarsa ba ta kashe wayar tana ajiyewa a gefenta tareda sauke numfashi me sanyi tana hana kanta jin komai.

Shima acan bangaren baiji komaiba sbd hailen dan haka ajiye wayar yayi gefensa yana kallanta a natse.
Chapter 94 · 0% Book details