← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 112

Sashe 15

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana barin bangaren kafin ta isa bangarensu aka fara shigowa da wasu irin Kayan al’adar shigar Leylah lalle komai na sake daukan harama.

Zama tayi a tareda Ayanah a palon tana tayata farin cikin dole da hidimar datake yi zuciyarta na sake ninkuwa a cikin tarin baqin ciki da zullumi tareda Neman mafitar da a yanzu itama ta yadda Bahar din tabar BOYEM tin bama yanzu ba sbd wadda ma take anan din sbd ita batasan wacece ita ba gashinan tana farin cikin NUAB yayi aure da wata daban batareda tasan da akwai Bahar din a duniya ba.

Kaman daga sama batareda sanarwar komai ba qamshinsa suka fara jin a sako Kai dan haka a tare suka juya da kansu hanyar shigowa palon suka kalla daidai nan yake sako kansa yana sanye da three quarter din farin jeans na Hss da farar sleeve shirt ta anioyosh fuskarsa Amminsa ta kalla cikeda mamakin ganinsa a lokacin duk da bai shigo ba yau din amma yanzu ba lokacin shigowan tasa bane,

Gaidata yayi cikin kulawa da kauna tareda rankwafo wa yai kissin tsakiyar kanta a hankali kafin ya Hadiye wata nutsuwan datake calmin nasa ya juyo ya kalli Maa sakinah itama ya gaidata nutsuwansa na hade har lokacin,

Amsawa tayi zatai magana ya Katseta cikin nutsuwa da cewa

‘Ina take??

Kallansa Maa sakinah tayi tareda dan satar kallan Ayanah wadda ta kallesa da dan mamakin wa yake tambaya.

Kasa basa amsa Maa sakinah tayi tana kokarin miqewa dan barin palon ya sameta a daki sai idanuwansa suka sauka Akan tarin Kayan dake palon ya tsayar da idonsa Akan rubutaccen sakon da dole daga sultan ya fito.

Amminsa dake cikin mamakinsa dana sakinah kallan inda ya tsayar da idanuwan nasa tayi tareda daukan sakon tana miqa masa da cewa sakonsa ne tin jiyan aka kawo nan sbd baya masarautar ya fita.

Kallo daya yayiwa sakon yaga abinda yake rubuce a cikinsa baice komaiba ya karbi sakon yabi Bayan Maa sakinah data silale daga palon idanuwansa na fara sauyawa sbd karshen riqe nutsuwansa da yakai.

Yana ficewa Amminsa ta bisa da kallan mamaki da shakka tareda fargaban kada yaje gurin sultan da wannan fushin data fara gani a idanuwansa dan haka ta miqe ta bi bayansa.

Yana fitowa a palon farko ya tadda Maa sakinah ta kasa shiga daki itama tana jiransa idanuwanta jajir kanta har wani bugawa yakeyi sbd tsananin ciwon halinda take ciki.

Yanayin yanda ta gansa yafara sauyawa ya sakata bata iya doguwar magana ba ta miqa masa takardar da tenya ta Bari ta sakon zaman Bahar imebetin ASIM,

Karban sakon yayi da hannunsa batareda ya bude ba ya tabbatarda abinda yake ciki sbd yanayinta dan haka dago idanuwansa da sukai jajir yayi ya kalli Maa sakinah ya furta

‘Ina take??

Da tarin damuwan dake Neman saka zuciyarta bugawa Maa sakinah ta bude Baki muryanta na rawa tace

‘Tin jiya an tafi da it…..

Dago idanuwansa da suka sauya a take ne zuwa ja da hancinsa yayi ya kalli Maa sakinah din wadda tama qasa qarasa maganarta sbd wucewa yayi Kai tsaye rubutaccin sakwannin biyu na hannunsa daya a hagu daya a dama.

Amminsa dake tsaye cikeda mamakin da wannan Karan ta kasa boye wa bin bayansa da kallo tayi harya fice ta dawo da idanuwanta dakyau cikin wani irin zullumi Akan Maa sakinah wadda tana juyowa ta ganta a bayansu ba tsammani ta tsaya cak tana kokarin sauya yanayinta dan boye mummunan tashin hankali da baqin cikin datake ciki.

Kaman daga sama Ayanah taji itama kanta ta jefawa sakinah tambayar

‘waye yake magana akai?
Wacece yaketa maimaita tambayan tana ina?
Baiwar da aka tafi da ita?
Baiwar datake imebētin dan uwansa?
Menene yake faruwa?
Meye a tsakanin sa da baiwar?

Rintse idanuwa Maa sakinah tayi sbd yanda kalmar baiwar da Ayanah ke ambata ga Bahar taje yanka zuciyarta kaman yanda a can baya take ji idan an kira Ayanah din da sunan imebēti,

Wani nauyi da radadin kalman da ake jiran Bahar din da ita be yake yankan zuciyarta ga tambayoyin Ayanah din suna qara daukan zafi dan kuwa da gaske so take sai taji menene abinda yake faruwa da sakinah take kokarin tsayawa NUAB gurin Kaucewa auren ‘yar jininta Zuhrah da batajin zata taba barin su biyun nasarar Hana auren da zai hadata da yar uwarta su sake hada zuriar Bayan Wanda suke cikinta ta haihuwan yayansu a zuria daya.

Kasa amsa kowace tambayarta Maa sakinah tayi sbd batasan tayaya zata iya fadar komai Akan Bahar ba musamman yanzu da take cikin mummunan hadarin da komai zai iya faruwa dik da tana jin NUAB bazai taba barinta zama imebeti ba sbd kalma ce daya tsana da jinin jikinsa.

Juyawa tayi batace komaiba Ayanah a riqe hannunta riqo mai karfin daya sakata juyowa a sanyaye ta kalleta cikin matsanancin halin riqewa da danne bakinta da zuciyarta jikinta na sake mutuwa sosai ta tsayar da idanuwanta Akan Ayanah din tace

‘Sunanta AYANAH BAHAR,ita din ba baiwa bace,
Ita din jinin mulki ce itama’

Tana fadar hakan ta zare hannunta a hankali tabar gurin jikinta na nauyi daqyar ma take daga kafafunta.

Ayanah kasa motsawa tayi daga inda take sbd daukewa da tinaninta yayi tareda tsayawa guri daya cak Akan tsananin son gani Bahar ta fuskanci abubuwan dake tattare da ita masu sake sarqe tinaninta.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

85
Fadar a cike take suna tattaunawa Akan auren dazai kasance da kuma harkar qarin tsaron masarauta a lokutan bikin tareda Sauran abubuwan da suka shafi tattaunawansu ta iya su palace officials,

ASIM na fadar dashi ake komai sbd daman ya saba zaman fada sosai dan komai dayake biye dashi kut da kut dan shirin karban mulki tintini.

Kaman daga sama muryan Sarkin fadar ya bude Baki tafara sauka kunnuwansu na isowan LEUL BOYEM Wanda tin daga nesa securities na bakin fadar suka sauke kawunansu kaf a qasa suna masa Barka da zuwan da babu rahamar amsawa a tattare dashi hakama bayin gurin kaf dinsu zubewa qasa sukai sukuma kansu a qasa suna Dakatar da kowane dogon motsi.

Gabaki daya duk Wanda yake cikin fadar juyowa yayi ga kofar zuciyoyinsu cikeda zullumin a wane yanayin yake Ayau kuma.

ASIM dake Zaune a kujeran zamansa me matsayin magajin BOYEM Wani murmushi ya sake mai kyau batareda ya juyo kofar ba ya kalli NUAB Wanda yana sako kansa a ciki gurin yayi tsit sbd Aura dinsa,

Jajayen idanuwansa da sukai mugun ja da fuskarsa ya dago babu Wanda ya kalla sai sultan Kai tsaye Wanda shima shi yake kalla Bayan ya kalli abinda suke hannunsa.

Tsit gurin ya sake dauka sbd yanayin ya dumama gurin gabaki daya musamman yaran NUAB din dake bakin kofar shigowa a tsaye tamkar babu imanin ko kallan rahama a tattare dasu.

Babu Wanda ya motsa babu kuma Wanda yace kala NUAB akai tsit Ana jira wasuma a cikin manyan fadar sun fara dauke idanuwansu daga kansa sbd a bayyane suke iya ganin zafaffiyar wuta ce take cin jinin jikinsa daya kasa bude bakinsa yayi magana tukuna sbd yaqin dayake yi da kalamansa Akan mahaifinsa Wanda Amminsa ta dauresa da alkawarin bazaiyi rigima dashiba har abada.

Sultan dinne ya fara bude Baki cikin nutsuwa yana kallansa ya saki murmushi me kyau da ikon dayake hannunsa yace

‘Zuwan LEUL BOYEM a babbar fadar yau yana nufin akwai abu me mahimmanci Wanda muke sauraron Ka me GHAZ da Moscow’

Wani irin Zafin daya saka jijiyoyin hannuwansa fitowa ne ya ratsa idanuwa da kirjinsa yana sake damqe sakon dayake hannuwan nasa da karfin gasken da pins din dake maqale dasu suka shiga hannuwansa sosai suna fidda jini tamkar baa jikinsa ba sbd babu abinda yake ji a jini da zuciyarsa Bayan ya tada BOYEM gabak dayanta ya rufe tarihinta.

Daga kafafunsa yayi ya qara Taku biyu ya sake kallan sultan ya daga sakon hannunsa na dama ya ajiye a gaban kafafunsa ya dago ya bude bakinsa da muryan data saka manyan fadar dan sake kimtsawa sbd tabbatarda ba lafiya me girma a yau din dan kuwa abu biyune da zasu iya babbaka fadar suke faruwa a gurin na farko fushin dayake tattare da NUAB Wanda basu taba ganin irinsa ba dan kuwa bayyanar jijiyoyin jikinsa kadai Zai iya saka mutum shiga damuwa me tsayi ta tsoro,

Sai kuma abu na biyu shine kaf duniya babu Wanda ya taba dawo da umarnin sultan idan ya fita a rubuce koda kuwa na hukuncin Kisa ne Akan ‘yaya da matanka dakai Kanka ma kuwa matiqar sakon ya fita to ya gama tabbatuwa kenan har abada ba sauyi.

Amma Ayau a cikin fada a gaban kowa da sultan din LEUL BOYEM yana dawo da umarni a rubuce kaman yanda aka akaisa wannan babbar ranar tashin hankali ce ga kaf BOYEM din.

‘Wannan sakon kyautar auren da aka aikawa Mahaifiyata ne Wanda ban karba ba na dawo dashi a gaban wainda suka sheda kyautar su sheda dawowanta’

Dayar sakon na hannunsa na hagu dayafi yiwa damqar data saka har lokacin hannunsa jini yakeyi fitarwa kadan kadan ya dagata a hannunsa idanuwansa na tsananta daga halin da suke ciki ya ajiye a gaban kafar sultan din ta hagu ya dago tareda Hadiye Wani mummunan Zafin gaske ya miqa hannu Aleey daya iso da takardar data fito daga bangaren LEUL BOYEM da nasa stamp din na sarauta da bai taba amfani dashi ba ya Dora masa ya qara ajiye wa a gaban kafar sultan ya dago muryansa na sake sauyawa zuwa yanayin daya saka gabaki daya Yaransa dake baya saukar da kansu sbd sun San yakai qarshen qololuwan fushinsa da basa iya dauka.

‘Wannan sakon daukan ran duk Wanda ya kalli MATAN DA AURENA YAKE AKANTA NE BARE KALMAR DA ZATA IYA DAUKAN RAN AHALIN DA DUK MUTUM YAKE DASHI’

Gabaki daya wutar fadar daukewa tayi manyan fadan a rikice suka kallesa zufan Kai tsaye yana feso musu take sai kuma sukai saurin sauke kawunansu kaman wadda ake maganar Kar a kalla tana gurin zuciyoyinsu na harbawa da Wani irin mummunan shock din da basu taba shigarsa ba.
Chapter 15 · 0% Book details