← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 112

Sashe 33

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuraim daya lura da yanayinta ne ya dan kwantar mata da hankali sbd zuwan nasu yanada mahimmanci tinda shiga takeson samu da damar da zata auri namijin dayake zuciyarta,

Basusan yariga da ya auri bahar ba dan haka sunada tabbacin zai auri leylah din koda ma ya auri bahar dinne ai ya kasance itama zata iya shiga,

Shuraim baida mugun hali ko daya halayensa daban suke dana yar uwar tasa sedai shikuma ya fita tsananin kishi da tsananin so sbd yanda yake kaunarta da mum dinsu komai yana iya yi akansu hakama kowa yana iya batawa akansu shi haka tasa kaunar da halin yake sam akansu baya duba daidai da abinda ba daidaiba amma bayan wanna baida munin dabia da hali ko daya hakama shima yayi kararu sosai me zurfi fiyema da leylah din sbd a yanzu yana akan matsayin cikakken likita ne.

Kafin su tafi irin kaunar da zuhrah kewa Bahar itama yasake gigita zaman lafiyar zuciyar leylah duk da tasan kowane irin so mum dinta zataiwa bahar bazai taba wuce wanda take mata ba ita data haifa amma sam bata jin zuciyarta daidai akan irin kaunar da dukansu suke mata musamman ta Ayanah datafi komai gigita mata zuciya sbd a bayyane yake ayanah zata iya bada rayuwarta akan bahar din.

Suna wucewa shima NUAB ya shiga wani irin busy na harkar sarautar boyem din daya buqaci dukkanin dokoki da sharudda da kaidojin mulkin msarautar boyem din masu zafi a gabatar masa dasu kaf da tarihinsu da inda suka samo asali da kuma hukunce hukuncensu sbd yana son shafesu kaf ya budewa boyem sabon tsarin mulkin da zai tabbatar musu da shine LEUL BOYEM yake mulki hakama har abada wainda zasuyi mulki bayansa zasu samu yancin da sarakunan baya da kamanninsu basu samu ba,

Manyan fada cikin tashin hankali da tsaka me wuyar wannan tsari da bayanan daya buqata wainda zasu zaqulo asalin asalin boyem suka fara shirye shiryen wannan umarnin nasa da allah kadai yasan waye da waye zasu rasa matsayi da sunansu da zuriarsu har abada.

Aleey ma kusan yafi kowa zama busy sbd shine zai tabbatarda hada kowane bayani da tabbatarda gaskiyarsa da komai tareda fidda duk wani hukunci akan hakan da sultan LEUL boyem zai fitar tareda sabbin dokokin mulkin qasar wainda gabaki daya boyem da duniyarta suke jira cikin zullumi da fargaba da jiran tsammani.

Bahar ma da maa sakinah hankalinsu kwantawa yayi basa cikin damuwan komai allah ya sakowa bahar din dangana da samun nutsuwa sbd koba komai ta hadu da jinin Abaa dinta biyu da suka rage a duniya da kuma yake fatar ta hadu dasu tayi rayuwa a cikinsu sbd yasan ko da rayuwarsu zasu bata kariya da duka kaunar datake nema da gata a duniya.

Maa sakinah ma sakewanta tayi tana cigaba da kulawa Bahar tareda tattalinta da gyara abarta sbd yanda itama bahar din ta gashi hankalinta ya kwanta bata ganin NUAB sbd bai sake shigowa tin ranar dan busy din dayayi sosai bai nemeta ba kaman yanda itama ta tattarasa ta ajiye gefe.

Babu abinda Maa sakinah take so a yanzu bayan samar da ilimin boko me kyau da zurfi ga bahar amman batada daman fadar hakan dan haka ta tsaya a iya koya mata dan abubuwan data sani wayewa da sauransu duk da nutsuwa da wata irin kamun kai da izzar dake cikin jininta ta sarautar data gada ya saka baka iya gane batada irin wayewan da zurfin ilimin boko yake bayarwa.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

105
Acan boyem kuwa tinda su Ayanah suka isa gabaki daya rayuwarta ta dawo mata baya farko,

Tayi kuka, tayi baqin ciki, tayi inama baya ta dawo, tayi baqin cikin ganin wannan ranar data wayi gari ita daya batareda kowa nata ba a cikin jinin ghaz sedai yayansu,

A kabarin da akaiwa iyayensu daga baya a cikin masarautar ghaz din da kabarin abaas dayake jere dana iyayen nasu ta durkusa tayi musu addua me tsayi tana wani irin kukan daya saka sultan janyeta suka bar gurin,

Jamaar anjom tsoffinsu da sukasanta tin a baya wainda allah yayi suna raye dama wainda basu santa ba sunyi farin ciki me tsananin gaske na ganinta,

Sun taru sunyi jimami sun cika masarautar sun mata gaisuwan iyayenta da abaas tareda kokawa juna kaddararsu data raba kowace ahalin datake anjom babu gidan da bai samu mummunan kaddarar shekarun bayan ba na iftilain daya fadowa anjom din.

Har tsakiyar dare sosai suna garin sai da sukai asuba tareda jamaar garin suna kokarin bankwana su tafi Su zuhrah suka iso.

Isowan zuhrah ya saka sultan barin Ayanaah a garin ya koma jirgi dan kuwa suna buqatan lokaci me tsayin gaske a cikin gidan da shine asalinsu shine abu na karshe daya rage musu na ahali da asalinsu.

Ayanah a lokacinda ta hada idanuwanta da zuhrah bayan shekaru masu tsayi na rayuwarta kasa motsi tayi bare cewa komai hakama kukanta daukewa yayi tsaf sai ajiyan zuciya kadai ta iya ringa saukewa tana bin zuhrahn da kallo ita kuwa kuka takeyi me tsananin gaske tana kasa fuskantar ayanah daga qarshe zubewa tayi a kan kafafunta tana kama kafafunta tana kuka me tsanani.

Tsawon lokaci ayanah din bata motsa ba tana jin kukan yana ratsata kafin ta motsa a hankali ta kama zuhrah din ta miqar da ita tsaye ta rungumeta ahankali jikinta a matiqar sanyaye ta bude baki da sautin daya sake saka zuhrah mummunan yanayi tace

'Yene Zuhrah,
Daga karshe kin dawo gareni Zuhrah,
Allah ya bamu ikon qarasa rayuwarmu a cikin ta juna a tare tareda 'yayanmu'

Rungumeta zuhrah tayi itama da karfin gaske suna qanqame juna da tsananin karfi zuciyarsu na samuwa da cike gurbinda har abada insha Allah ya cike kenan.

Kabarin iyayensu da dan uwansu suka koma kafin suka sake komawa dakin mahaifiyarsu anan suka shige dan anan zasu sake kwana kafin su koma asalin birnin qasar inda sultan yake jiran Ayanah a lafiyayyar daular daya sauka.

A nan anjom suka kwana wanda kafin safe leylah ta kusa zarewa ta rasa hankalinta sbd mummunan halinda takejin tana cikinsa na rayuwa a garin dama inda suke din dan kuwa a maqale da mahaifiyarta take sam ta fice hayyacinta.

Babu wanda ya maida hankalinsa akanta a cikin su biyun sbd abinda yake kansu shine ya damesu,

Fuskokinsu da idanuwansu kadai zaka kalla kasan suna cikin mugun hali sbd sun kumbura sunyi jajir ba kyan gani hakama ko muryoyinsu basa fita.

Daqyar leylah taga gari ya waye karfe tara tayi anzo daukansu da securities din sultan da wasu mahaukatan motocin da suke iya shiga kowane daji da bindigogi.

Ta riga su Ayanaah fitowa ta fada mota da sauri tana sauke ajiyan zuciya ta kalli Shuraim dayake gaba dan shima bai kwana anan ba komawa yayi yau aka dawo dashi,

Cikin wani irin yanayin dayake fitowa daga qasan zuciyarta ta kalle shuraim bayan sun zauna a cikin lafiyayyan jirgin ruwan dazai bar dajin garin gabaki daya dasu ta sauke ajiyan zuciya tana kallan shuraim tace

'A hakan kake tinanin zan iya hada miji da illiterate macen data taso anan?
Tayaya ma zata iya rayuwa a tsakanin ni na SULTAN din da mukeda tarin ilimin da batada shi?
Bama zan iya zama da jahila ba sbd ilimin nawa 'yayan dazan haifa.....

Shuraim ne yayi saurin dora hannunsa akan nata cikin wani irin salon da Ammi data tsare leylah din da ido bazata gane ba ya dan dakatar da ita yana fuskewa.

Ayanah shiru tayi tana kallan Leylah cikin sanyi da nutsuwa hakama wani nauyi yana danne kirjinta da batajin komai a cikinsa yanzu bayan zallan kauna da soyayyar bahar wadda itace zata kasance uwa kuma ubanta.

Zuhrah ma da zancen ya ratsa zuciyarta da kaifi tareda rakaici da baqin cikin jin hakan daga bakin 'yarta akan 'yar dan uwanta kallan ayanah tayi a sanyaye sedai ganin ayanah ta dauke idanuwanta ahankali akan leylah din batateda tace komaiba ya saka itama tayi shiru kowama yayi tsit har suka isa ba wanda yace kala.

Suna isa kai tsaye masaukin sultan aka nufa da ayanah su zuhrah kuwa a ranar suka bi jirgin dare suka koma.

Ayanah tinda ta dawo sultan ya fuskanci damuwa sabuwa dake tattare da ita dan haka a daren bai samu nutsuwa ba saida yaji damuwarta wadda kai tsaye ta sanar masa tanason bahar tabar boyem ta tafi wata qasar karatun datake son ta sauya rayuwarta ya bata yancin zabar raayin auren NUAB ko sabaninsa.

Sultan daya fahimci daci da radadin dayake zuciyarta akan bazata taba iya barin bahar ta samu tangardar rayuwa ba NUAB yace ta fara sanarwa,

Girgiza kai tayi cikin nutsuwa tareda bude baki tace

'Nice zan dauki nauyin karatunta da kaina banason NUAB yayi mata komai akan duk abinda ya shafi neman iliminta'

Sultan hakan shine yayi daidai da nasa raayin akan Bahar wadda Ayanaah zata tsayawa tai mata gatan komai kaman yanda Kowa iyayensa ke tsaya masa su basa ilimin daya kamata dan haka kai tsaye ya kira kadir ya bada umarnin komai na bahar da karatunta ya kammalu a cikin qanqanin lokaci.

******Ayanah batai raayin baro kasarta ba a kwanaki kadan dan haka kusan sati uku suka share a qasar batareda kowa ya taba samunsu a waya ba sbd hatta tenya su Zuhrah tabi ta koma.

A bangaren kadir ma cikin wata irin rashin bata lokaci da tsayuwa cak akan umarnin sultan din ya nemarwa Bahar kusan komai da ake buqata na karatu a qasar UK sbd sunada manyan connections.

Sai da sukai wata guda cif a qasar suka diro boyem wanda yayi daidai da lokacin tafiyar bahar da NUAB baisan da itaba hakama daidai dawowan haile da yayanta hakama tsawon wannan lokacin BAHAR da NUAB din basu taba haduwa ba.

A ranar da suka dawo a ranar saura kwanaki kadan a tafiyar bahar din wadda zata tafi tareda maa sakinah a gidan da aka tanadar musu acan domin rayuwa a cikinsa.

A daren Ammi tana isowa ta kira NUAB ta sanar dashi wanda yayi shiru ya rasa abin cewa zuciyarsa na wani irin daukan zafin dayake ciki tsawon wata gudan nan da sukai basa nan sbd sultan daya gama shan gabansa akan mahaifiyarsa.
Chapter 33 · 0% Book details