← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 112

Sashe 75

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe goma sha daya saura Ammi ce tafara fitowa Maa sakinah na kitchen tareda su naima suna kokarin shirya table da breakfast sbd tasan kowane lokacin yanzu kowa zai iya fitowa.

Tana zaunawa palon da wayarta a hannunta tana duba sakon Sultan daya shigo mata fuskanta tana hana murmushinta bayyana sbd abinda ta karanta tenya ta fito tana waya da Fatee yarta ta bawa Ammin waya ta gaidata sbd tayita kiran wayarta tin jiya bata samu.

Da sakewa da kulawa Ammin ta gaisa da fateen tana tambayarta yara da sauran abubuwa cikin sabo sbd akwai sabo da kauna sosai a tsakaninsu.

Suna gama wayar tenya ta kalleta tana jero mata labarin abinda fateen ta fada mata suna dariya hankali kwance.

Maa sakinah ce ta iso suka gaisa tana wucewa dining ta jere abinda ta dauko tana dawowa gurinsu bata zauna ba take shiga zancen nasu.

Su naima ne suka qarasa shirya dining din kafin suka taho a jere kansu a qasa suka gaida Ammi ta amsa suka fice daga palon gabaki daya suna komawa kitchen dan basu daman breakfast a natse.

Leylah ce ta fara fitowa a shirye cikin doguwan riga black datai mata kyau sosai gashinta a daure tsakiyan kanta yana lilo sbd dan qaramin mayafin rigar data dauro a kanta is transparent kuma a gefe ta dauro sa.

Qamshi me sanyi take fitarwa ta qaraso ta zauna gefen Ammi tana gaidasu cikeda girmamawa da dan jin nauyi duk da babu wanda yasan ba anan ta kwana ba sai Maa sakinah kuma bata nuna komaiba cikeda kulawa ma take amsata tana tambayarta ya karfin jikin nata.

Dining suka nufa suka zauna sukai breakfast dinsu sbd Bahar bata tashi ba har lokacin.

Suna gamawa suka zauna a palo suna fira sai ga Zuhrah ta iso da wasu daga kayan Leylah bayinta na dauke dasu dan daman batason zamanta acan din gwara anan Amminsu zatai mata nasiha da fada ta sakata tattarawa ta koma bangaren mijinta.

Suna cikin fira Sai ga Bahar ta fito sanye da wando na dior masu fadi da sukai mata kyau sosai musamman dayake kalan black ne gashinta a sake yana daukan ido duk da ba wani gyara sosai yasha ba sama sama ta gyarasa.

Fuskanta tayi wani irin fresh tana glowing tamkar ba wadda suka taho da ita a cikin matsananciyar damuwa ba,
Qamshinta me sanyi da shiga zuciya ne ya shiga hancinsu suka juyo suna kallanta tana tahowa a natse hannunta riqe da wayarta tana duba sakon Neesah dake tambayarta yaya ta hadu da sultan kuwa.

Qarasowa tayi ta zauna gefen Mum zuhrah tana kallan Amminta cikeda kunya da tsananin kewanta datake jin tanayi ta gaidata.

Dagowa Ammin tayi ta zuba mata ido tana kallanta cikeda kauna da kewa itama ta sauke ajiyan zuciya ta amsa tana miqa mata hannu da sauri ta tashi ta kama tana komawa gefenta ta rungumeta tana ciko idanuwanta da hawaye da sautin sanyi tace

'Ammi kiyi hakuri'

Shafa kanta Ammin tayi tana cewa

'Ya wuce amma duk da hakan zanyi magana dashi zaiga bacin raina'

Shiru bahar tayi tana kasa cewa komai gabanta na dan faduwa.

Salmah ce ta kawo mata breakfast a jere cikin wata lafiyayyar tr3y ta ajiye akan table dake gabanta tana juyawa takawo mata madara din da maa sakinah ta dafa mata tinda safe bayan ta sake zafafa shi yana tiriri ta ajiye mata tabar gurin.

Chips ne da kebab na qoda dayaji carrots da peas sai ketchup da fresh fruits masu sanyi harma da kusan kankara a cikin glass bowl da small fork na ci a ciki soke.

Madaranta ta fara dauka tana sha ahankali tana jin zuciyarta fes Amminta ta dena fushi da ita hakama hakanan ganinta zagaye da iyayenta ya saka zuciyarta jin nutsuwa da farin ciki.

Tana shanye madarar ta ajiye cup din ta dauki fork tafara cin chips din a natse tana sauraron firar su Ammin tana dan chat da Neesah data kasa barinta ta zauna kalau.

Shigowan qamshinsa ne daya ratso palon a natse cikin sanyi yana ratsa hancinsu da gauraya numfashin niimar gurin ya saka dukkaninsu yin shiru suna sanin shine ya shigo bangaren,

Bayi fara ficewa sukai tas dan haka koda ya qarasa isowa palon iyayen nasa ne kadai a zaune dukansu kallo daya sukai masa suka dauke idanuwansu sbd kwarjininsa da haibarsa data cika idanuwansu.

Qarasowa yayi a natse idanuwansa suna kan Amminsa wadda itama shi take kalla.

Gefenta daya Leylah ce a zaune daga ciki kenan sai dayan gefen nata na kusa Bahar ce a zaune kusa da ita sosai dan haka yana qarasawo gefenta da Bahar din ke zaune ya iso a natse ya zauna cikeda kamewa sa ikon dayake yawo a jininsa.

Dago idanuwansa masu haske da kyau yayi ya gaida iyayen nasa daya bayan yana amsa tasu gaisuwan kafin ya tsayar da idanuwansa akan Amminsa wadda kewanta ce tafi komai ya yawa a tattare dashi yanxu sbd ya dade sosai bai sakata a idanuwansa ba tinda tabar boyem a baya sai yau din dan haka numfashi me sanyi da nutsuwa ya sauke yana gaidata cikeda kulawa da kauna.

Amsawa tayi a daidai lokacin su maa suka miqe suka bar gurin hakama leylah aka bar Zuhrah da Ammin sai Bahar wadda ta kasa motsawa sbd tsakiyar da suka sakata qamshinsa na shigarta da kyau yana kashe duk wani kuzarin jikinta.

Jin tayi maqoshinta da cikinta sun cushe da abincin datake cusawa dan haka ta ajiye plate din a hankali tana kasa juyawa ta kallesa ta dauki bowl din fruit dayake gabanta koda su idan taci zasu iya wucewa tunda basuda karfi.

Magana yafara yi da Ammi a natse idanuwansa na kan yatsun hannunta farare tas masu tsayi dasuke daukan idanuwansa tana sakawa a cikin bowl din ta dauko water melon jajir da ira datai sanyi yankan cubes ta nufo bakinta da ita ta bude baki ta saka tana taunawa ahankali.

Kasa hadiyewa tayi sbd jin idanuwansa akanta tsaye tsaf.

Motsawa tayi a hankali tana son miqewa tabar gurin taji saukan tafin  hannunsa akan nata daya data dafa zata tashi.

Sarqewa tayi da wani irin karfi sbd rikicewa me karfi ta kasa juyowa ta kallesa bare hannuwan nasu da suka hadu sbd su Ammi dake zaune sunata magana batareda sun san meyake faruwa ba.

Ammi ce ta dan juyo ta kalleta cikin kulawa tana mata sannu
Daqyar ta hadiye abinda ke bakinta tana gyadawa Ammi kai ahankali cikin fargaba.

Zare hannunta zatai Amma jin ya juyo da hannunta ahankali ya hade tafin hannuwansu ya sakata faduwan gaba me karfi tana kokarin sake sarkewa Ammi ta juyo gabaki daya tana kallanta tace

'Yayi miki sanyi da yawa ki ajiye tinda kinsan kina fama da zazzabi kwanakin nan'

Ajiye bowl din tayi da hannu daya tana dagowa a natse cikin sanyi ta kallesa shima idanuwansa ita suka kalla a natse da kamewansa batareda shakkar komaiba.

Wani irin taji na mutuwan jiki da irin kallan da yayi mata ta sauke idanuwanta tana zame hannunta da dan sauri tana kallan Ammi wadda idanuwanta suka kan Zuhrah kafin ta dawo dasu akan NUAB wanda ya dago idanuwansa a natse daga kan Bahar din yana dawo dasu akan Amminsa wadda ta dan kame fuska sosai sbd kaman taga Bahar yake kalla.

Bahar na ganin hakan itama ta miqe a natse cikin sanyi tabar gurin tana qin juyowa sbd jin kaman idanuwansa akanta.

Tana barin gurin shima bai wani tsaya magana dasu Ammin ba musamman tinda ba ita kadai bace mum zuhrah na gurin magana bazata yiyuba a tsakaninsu dan haka ya bar bangaren.

Yana fita wayarta date hannunsa ya sake riqewa a natse sbd a tsakiyarsu wayan take dan haka ya dauko.

Office dinsa ya nufa na cikin masarautar tinda ya wuni ya kwana be leqa ba.

Itama bahar tana barin palon dakin maa ta nufa acan ta shige mata maa din na biye mata cikeda kauna da kulawa.

Bata ankara da wayarta bata nan ba saida tai kusan rabin wuni a dakin maa ta fito ta duba wayarta koina bata ganta ba ta nufi har dakinta ta duba bata ganta ba dan haka taje ta karbi wayar maa ta kira tata wayar.

Kira kusan uku bata ji ringin nata koina ba dan haka ta bari sai kowa ya watse idan koina yayi tsit zuwa koda yamma ne ko irin bayan magrib haka kowa ya shige zata iya jin ringing nata idan ta kira.

Dakinta ta koma ta janyo laptop dinta tana duba abubuwa na classes nata da sauransu.

Leylah ma data zo ta zauna kusa da ita tana waya daqyar ta gama wayar tana jin zazzabi da kaman amai yana taso mata tana gamawa toilet ta fada ta dade sosai a ciki tana amai kafin taji sauki sauki tayi wanka ta fito jikinta da zazzabi sosai.

Shiryawa tayi lokacin magrib ma ta riga tayi tana yin sallah ta zube a gurin tana dunqulewa.

Ita ma bahar din ajiyewa tayi tayo alwala tayi sallah tana idarwa ta miqe tabar dakin ta tafi dakin Ammi.

Acan takai har ishai sukai tareda Ammin ta dawo daki tayi wanka tai shirin bacci har zata fita cin abinci zuwa dining ta tina wayarta bata hannunta har lokacin dan haka ta sake komawa dakin Ammi ta dauko wayar Ammin ta fito da ita tana sake kiran wayarta.
#MAMUH
09033181070
[04/01, 7:27 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

148
Ko data fito da wayar Ammin dakinta tafara nufa dan kiran wayar tata tana shiga ta tadda Leylah na toilet ta zauna bakin sofa tana saka kiran wayarta,

Ringing tayi harta yanke bataji komaiba ta sake saka kiran ga mamakinta sai taga an dauka dan daka takai wayar kunnenta ta dora tareda bude baki da muryanta ne dadi tace

"Maa kece??

Shiru akai mata wanda ya saka dago wayar ta kalla taga tata dince dai ta kira dan haka ta sake kai wayar kunnenta zatai magana sautin numfashinsa daya fitar ya sauka a kunnenta ta dakata cak tana kasa cewa komai tareda kasa yadda wayarta a hannunsa tayaya?

Yunqurin Aman Leylah me karfi ne ya sakata kallan kofar toilet din tana kashe wayar hannunta datake neman rikitata sbd jinsa,
Chapter 75 · 0% Book details