← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 112

Sashe 80

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultan jiran tambayar NUAB yakeyi duk da yasan bazai taba tambayarba koda zasu shekara a hakan koda kuwa menene bazai taba bude baki ya tambaya dinba sedai shi daya ajiye koma meye ya fada da kansa idan ba hakan ba zai gaba abinda ya kawosa ya miqe ya ficewansa.

Dan haka ajiyan zuciya mara sauti sultan ya sauke yana maida kallansa kan fuskan NUAB wanda ya dago shima yana kallansa ya bude baki yana kai hannunsa daya a natse ya tura silallan gaban NUAB din yace,

'Ina gabatar maka da sadakin mahaifiyarka Ayanah ghaz me girma Sultan LEUL boyem wanda aka daura auren sha ashirin ga watan daya gabata,
A yanzu ba kaine kake da cikakkiyar iko akanta ba nine mijinta,nine mahaifinka,nine Sultan dinka'

Kallansa NUAB ya dago yanayi da dukkanin idanuwansa yana jin maganarsa na sauka kaman baisan meyake fada ba sbd yasan zai iya fadan komai akan ya mallaki Ammin dan haka a natse ya maida idanuwansa akan zinarin gabansa yana kallan sunan Ammin dayake bayyana baro baro akai ya kalla tsawon mintina kafin ya dago da idanuwan ya sake saukewa sultan yana jin zuciyarsa na fara daukan zafin daya manta rabon da zuciyarsa ta dauka,

Bude baki yayi a natse yana kallan sultan din yace

'Ammin tasan da maganar dake gudana nan din maana tasan da aure a kanta??

Sake gyara jinginar zamansa sultan yayi yana sake murmushi me kyau da nutsuwa yana kallan NUAB din yace

'Kaine da baka saniba nake sanar dakai a yanzu sbd ka sani din Sultan dan Amarya'

Numfashi me dumin daya fara zafi NUAB ya sake kalmar na zafafar zuciyarsa ta tafaso sa ya sake kallan sultan da kyau yace

'Aure irin wanda kayi mata a baya na bata matsayin wishmah ka sake bata sbd bansan Ammina zata iya aure batareda sanina ba ko izinin dan kuwa a duniyarta kaf yanxu ni kadai ne waliyin aurenta da bada aurenta'

Ajiyan zuciya me sanyi da nutsuwa sultan ya sauke yana kallan NUAB din yace

'Aure ne mukai wanda kana buqatar nutsuwa ka fahimta hakan,
Ba raayinka ni nake nema ba,ba kuma izininka nake nema sbd mune muka haifeka bawai kaine ka haifemu ba,
Aure ne kaman kowane aure da akeyi me daraja da baa buqatan dogon bayani,
Amminka tana jin shakkar yanda zaka dauki lamarin ne ya saka aka ja lokaci batareda ka saniba ba amma tinda yanzu ka sani ka sani mahaifiyarka tayi tinanin abinda zaka dauka kafin ta amincewa auren dan haka a yanxu daka sani saka albarkanka kawai take buqata ba bacin rai da fushi ba.'

Yana gama fadan hakan miqewa zaiyi NUAB ya kallesa idanuwansa jajir zuciyarsa na wata irin tafasa da bacin rai me tsananin gaske da fushin dayake taso masa yace

'Kanada raayin hakan meyasa bakaiba tin a shekarun baya datake tsananin buqatan hakan?
Meyasa baka yantata ba a lokacinda hakan yakeda amfani?
Meyasa sai ayanzu?
Sbd ka kaine me juya rayuwanta a yanda kaso a lokacin da kaso sbd ita ba kowa bace face baiwar da aka saka kudi aka siya?

Yankar zuciyar sultan maganganun sukai ya dago idanuwansa shima da sukai ja ya kalli NUAB din cikin jin zafin maganar yace

'Eh sbd nine me juyata a yanda naso da kuma bata matsayin da duk nakeso sbd nine na siyota ba kaiba,nine me ita da cikakken iko da ita a kaf rayuwarta ba kowa ba,a yanzu danaga lokacin auren yayi shima gashinan na aure ta auren da ba wanda yakesa ikon sakawa ko hanawa idan ba ni dinba.'

Gama maganarsa yayi daidai da shigowan ayanah din wadda ta kasa nutsuwa da haduwan tasu saida ta iso dan haka kallan NUAB takeyi da idanuwanta da suka sauya sbd fargaban abinda zai iya biyowa baya,

Juyowa NUAB yayi ya kalleta da idanuwansa dake tsananta ja maganganun sultan sun gama buga xuciya da jininsa dan kuwa ko ayanzu ya fada masa uwarsa ba kowa bace face baiwarsa da zaiyi dik yanda yaga dama da rayuwarta,

Wani irin kallo yakewa Ammin yana jin ta gama rusa duk wani karfin zuciya da kuzarinsa ya bude baki yace

'Ammi kina ji da kunnenki ke din ba kowa bace face baiwar da aka saka kudi aka siya,
A hakan kika kuma zabarsa akan duka radadi da baqin cikin dana rayu a cikinsa sbd ke'

Rintse idanuwa Ammin tayi tana isowa gurinsa zata kamasa ya miqe tsaye yana kallan sultan wanda ransa yayi mummunan baci yace

'Ban karbi auren ba sbd nine me bada auren dan haka......

Wata irin tsawar da tinda sultan yake babu wanda ya taba yiwa ita ya sakarwa NUAB din wadda dakin gabaki daya saida ya amsa take Ammi ta shiga tashin hankali tana kallan sultan din kafin ta kalli NUAB wanda jikinsa ke wata irin rawa sosai idanuwansa jajir fuskarsa tayi ja.

Su kadir dasu aleey harma da maa sakinah data taho tareda ayanah a kunnuwansu tsawar me karfin gaske ta sauka wadda ta saka kowannensu qasa da kai jiki na sanyi da wata irin fargaba da damuwa batareda sun motsaba gurin ya sake daukan tsit.

'Zaka dena fadamun duk maganar dataxo bakinka kowane matsayi kake dashi kuwa daga yau sbd duk abinda kakeji kake taqama dashi nine na bakashi sbd nine na haifeka,
Nina na baka sunan dakake amsawa yau,
Nine na na baka jinin iko da mulki da izzar da duk kake ji a kanka da jininka,
Nine na baka kariyar da kake taqamar ka rayu ayau,
Nine na hana kaina duk kwanciyan hankali da farin cikin da duka mulki yake bayarwa nai watsi da girma da iko na na fixgeka daga hadarin dayake tattare da rayuwarka na baka dalilin daka zama jarumin dayake tsaye a gabana yanzu,
Nine na bawa mahaifiyar taka kariyar data rayu a cikin cikakkiyar kwanciyan hankalin da kake ganinta a gabanka a yau,
Nine wanda ya tsaya ya tsayu akanka na baka kariyar da bazaka taba zama abinda ka zama abinda ka zama ba a qasar da ba taka batareda na taba baka dalilin rauni ba,
Ni ba ubanka ne kadai ba daya kawoka duniya ni saviour dinka ne,
Ni sultan dinka ne,ni ubangidan mahaifiyarka ne sannan ni ayanzu mijin mahaifiyarka daga karshe ni masoyinta ne da 'dan da muka haifa bai isa ya saka sharadi a gabanmu dan haka ka aje matsayinka na sulta a komai nine ubanka da you must learn how to talk and respect me to the core...'

Da wani irin zafin gaske ya qarasa maganar wadda take fita da karfin gaske cikin bacin ran da babu wanda ya taba gani wanda ya saka Ayanaah kallan NUAB wanda shima rawa jikinsa yake sosai har lokacin jan idanuwansa kaman zasu kama da wuta sbd ayau ya tabbatarda idan aka haifeka angama shan gabanka duk kuwa abinda kake ji dashi ko kake dashi dan kuwa abinda yake ji yafi wuta ci a jininsa amma baida yanda zaiyi bayan tsayawa yana sauraran gorin da ubansa ke masa shida uwarsa bama tareda ita tasan hakan ba.

Dago idanuwansa yayi ya kalli sultan din wanda ko kallansu ya dena sbd tafasar da zuciyarsa ke yi shima ya gaji da zafi da fushin NUAB dayake tolerating tin yana yaro wanda yana masa uzuri ne sbd yasan zafin son dayake wa Amminsa dashine ya saka ya tashi da jin zafin rashin ganinsu a tare amma sam ya kasa gane cewa son dayake masa ne yake sakasa jin tsananin zafinsa daya kasa zabarsu da Amminsa akan kowa bayan shi kuwa yafisa jin zafin ciresu da yayi daga jikinsa sbd basu kariyar da ayanzu suke tsaye tareda juna.

Magana NUAB din zaiyi shima cikin kololuwan quntata da maganganun Amminsa ta katsesa da tsawa me karfin gaske itama tana riqosa cikin damuwa da rasa abin yi tace

'NUAB mahaifinka ne kome kake ji zaka hadiyesa ayanzu batareda ka bayyanaba sbd tinda ya haifeka ya gama maka komai,
Kome laifinsa a gurina ni na yafe masa sbd nasan dalilinsa daga baya na hakan hakama ko babu dalili tinda zamansa nakeyi dole zan fuskanci damuwa da baqin ciki na zamantakewa wanda gashi a yanzu ya wuce,
Ka aje komai ka bar komai ka bari zuciyarka datake tsananin sonsa ta karbesa,
Ka aje fushinka ka fuskanci matsayinsa daya wuce komai da kowa...
Ayau ina fada maka ka dauka umarni ne ko shawara ko baki koma menene ayau ina fada maka ka ajiye duk abinda kakeji bazaka sake disrespecting nasa ba zaka girmamasa zaka bari zuciyarka ta karbesa matiqar kanason naci gaba da rayuwa a matsayin mahaifiyarka........

Da wani irin slow me mugun zafi da wani duhu da wuta dayake ganin suna ci a idanuwansa da kirjinsa ya juyo yana kallanta fuskarsa na qarasa komawa jajir ba kyan gani yana kasa motsawa bakinsa na mutuwa daga furta kowace irin kalma.

Shi kansa sultan din dago jajayen idanuwansa yayi ya kalli Ayanah din wadda idanuwanta sukai jajir wasu hawaye masu tsananin radadin kalman data fada suna gangarowa daga idanuwanta sbd tasan ayau NUAB zai shiga mafi qunci da radadin zuciyar dabai taba shiga ba jin hakan daga bakinta.

Wani irin sanyi dukkanin jikinsa yafara a hankali sbd ayau ya samu kalman datai breaking zuciyarsa kacakaca a take batareda qara kowane second ba.
#MAMUH
09033181070
[06/01, 2:31 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

153
Hawayen fuskarta dake gudun sosai ya saka sultan takowa gabanta har lokacin zuciyarsa daci take masa sosai sbd ganin yanayi halinda suke ciki a tsakaninsu da babu wata kauna ko soyayyar data wuce tsakaninsu dan kuwa sune haske idaniya da ruhinsa da ayau yake tsaye sbd soyayyarsu daya riqe ya hana kansa sakewa ga kowane irin challenge har suka kawo inda suke yanxu amma gashi suna tsaye cikin jin zafin juna maimakon kaunar dayake fatar su rayu a cikinta.

Rintse idanuwansa da har wani radadi sukeyi NUAB yayi jijiyoyin hannuwansa dana kansa duk sun fito.

Bai iya cewa komaiba ya juya a hankali yabar palon idanunsa na fidda wata zafi,
Chapter 80 · 0% Book details