← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 112

Sashe 18

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tattaro nutsuwa aleey yayi sbd yanason fahimtar kowace amsa na tambayar da zaiwa Maa din.

Farawa yayi da fada mata komai daya faru wanda ya sakata silalewa a qasa ta zauna da karfi tana tabbatarda shikenan ta rasa Bahar,

'Maa kiyi tinanin koina da kikasan zaa iya Kai matan masu jinin boyem gyara da sauran su wankan,
Kiyi tinanin idan basa inda aka saba to inane guri mafi cancantiwa da zaa tafi Dan cika irin wannan al'adar??

Rintse idanuwa Maa sakinah tayi tareda jin bazata iya ma magana ba ta a girgiza Kai kawai alaman batada masaniyar akwai inda kaf masarautar zai kama da gurin cike wannan al'adar sbd guri daya ne basa can kuma Dan haka duk inda suke ba gurin wankan al'adar bane kawai guri ne dayake tamkar kowane bangare so tsarin dole ze kasance daban Kila.

Shiru aleey yayi kafin ya kalleta ya sake Bude Baki yace

'ina Ammi?

Bayanin zuwan Asim da ficewansa datama Ammin tayi masa wanda ya saka aleey din tsayar da tinaninsa akan Ammin wadda bata fita koina tinda take bayan chambers din sultan bata taba fitowa zuwa koina,

Ina Zata tafi yanzu data fito din?

Numfashi mara sauti aleey ya sauke tareda juyowa kansa yana sake daukan zafi ya kalli securities dinsu dake tsatsaye a gurin yace a fito da drones gabaki daya.

Fitowa akai dasu ana kokarin connecting komai shi kuma Kai tsaye cikin system na security room din masarautar gabaki daya yafara kokarin kutsawa ta laptop din daya ajiye gabansa yana tattara hankalinsa guri daya.

Gadan gadan suka fara aikin leqawa da ganin kowane Sako dake cikin masarautar duk da tanada tsananin girman da bazasu iya a qanqanin lokaci ba aikine da zasu yisa a har tsakiyar dare ko zuwa gobenma wadda Babu lokaci,

Acan cikin fada lamarin komai ya sake daukan zafin gaske sbd sama da Ghaz Boys ashirin ne a cikin fadar a tsaye a shirye da mahaukan makaman da suka dauke duk wata niimar dake gurin da zagayenta hakama securities na bakin fadar duk sun tsaresu tareda karbe kowace irin waya dake hannun kowa da kowa tin daga manyan fada har securities da wanda yake gurin tareda tsayar da kowace security cam dake gurin da zagayenta Dan haka tsit kake ji Babu wanda yasan meyake faruwa a cikin masarautar gabaki daya securities manya manya dake masarautar basu sani ba Dan basu taba tinani ko daukan akwai kowane irin threat a cikin masarautar ba.

Kaman yanda aka tsare fada haka aka tura wasu securities din suka sake tsare hanyar ficewa zuwa gate din farko na daga ciki kuma haka aka dakatar da motsin kowane irin bawa dake cikin masarautar.

Rashin fitowan NUAB yake sake tabbatarda tsananin zafi da mummunan hadarin da yanayin yake ciki a masarautar sbd fitowansa na nufin abubuwa da dama wanda zasu iya zama alkhairi ko sabaninsa.

*****AYANAH da idanuwanta suke wata irin rufewa kafafunta na rawar datake kokarin hanata isa inda take nufar gabaki daya abubuwa ne suke dawo mata daban daban akan NUAB da sakinah dama maganganun datasan NUAB bai san dasu ba Amma ta jisu a bakinsa da kuma bayyanar Baiwar datake jin bazata iya tinanin komai a kanta ba sai ta saukar da idanuwanta akan abinda takeson tabbatarwa.

Ko data iso bangaren boyayyun marasa Imanin securities din dake gurin da sultan ya saka batareda akwai me ganinsu ba Kai tsaye waya suka daga suka kira bangaren Sultan Dan isar da bayanin.

Salman ma dayake daga nesa a labe yana ganin inda ta shige din Kai tsaye juyawa yayi yabar gurin Dan isar da sakon ga uban gidansa.

Buga kofar Kai tsaye ayanah tayi da hannunta dayake tsananin rawar da zuciyarta keyi.

Baa dauki lokaci ba aka Bude kofar cikeda mamaki me girman gaske,

Tenya ce ta Bude kofar mamakinta na tsananin qaruwa take kallan ayanah din sbd bata taba sanin ayanah na fitowa koina ba a rayuwanta bayan zuwa tirakar sultan Dan kuwa ko bangaren 'danta NUAB bata taba zuwa ba..

Wucewa Kai tsaye cikin ayanah tayi batareda ya iya cewa komaiba sbd bakinta ya gama mutuwan da bazai iya furta komaiba,

Biyo bayanta tenya tayi tana kokarin tambayar abinda yake faruwa Amma sam ayanah ta gama fita hayyacinta Bahar kadai take son gani,

Dakunan dake bangaren tafara bi taba budewa daya bayan daya tana qarasa rikicewa da tashin hankali gabaki daya,

Tashi hankalin tenya yayi da bayin da suke bangaren sukai tsuru tsuru cikin fargaba tenya kuwa binta takeyi a rude da tsoron idan ba sake dawowa ciwon ayanah din yayi ba tana tambayarta lafiya.

Bata jin abinda tenya take fada kwata kwata cigaba da bin dakunan takeyi a mummunan Hali,

Dakin da Leylah take a ciki ne tana video call da mahaifiyarta ayanah ta Bude da karfi daidai lokacinda Leylah ta juyo da sauri cikin tsoro fuskar zuhrah gabaki daya ta bayyana akan makeken screen din ipad dayake riqe da hannunta kuma a daidai lokacin ayanah ta bayyana a dakin idanuwanta a rufe tana dubawa bata ga Bahar ba ta juya batareda ta kalli screen din da zuhrah take bayyane ba ta tsayar da idanuwanta akan ayanah wani irin ja me raradin gaske yana gauraye idanuwanta.

Miqewa Leylah tayi cikin tashin hankali da tsoro tabi bayan ayanah batareda ta ajiye ipad din hannunta ba tana ambatar sunanta cikin wata irin kulawa da farbaba Amma gabaki daya duniya ayanah Babu abinda take ji take buqatan ganin bayan Bahar.

Dakin dayake kusa Dana Leylah din ta Bude hannuwanta na tsananta rawan data sakata fadawa dakin Kai tsaye a daidai lokacin Bahar ta fito wanka daga ita sai towel babba.

Cak Bahar din ta tsaya tareda ja baya cikin tsananin mamaki da farbaba me karfin gaske zuciyarta na harbawa.

AYANAH ma cak ta tsaya tata zuciyar na tsananin harbawan datake fatar kada abinda take son tabbatarwa ya tabbata sbd hakan zai nufi abinda bazata taba iya dauka ba a zuciyarta.

Takowa tafara yi kafafunta duka biyu suna rawa tareda kafe idanuwanta da sukai mummunan ja akan Bahar.

Qasa Bahar tayi da kanta zuciyarta na harbawa sosai bazata iya kallan ayanah ba sbd fuskar mahaifinta ayau sak da sak take gani a cikin tata.

Su tenya da Leylah kasa motsawa sukai sbd matsananin mamakin daya kame har kafafunsu.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

89
Ba zaton kowa ayanah ta tako kafafunta daqyar ta tsaya gaban Bahar batareda tace komaiba ta Kai hannunta Kai tsaye ta kamo hannun Bahar seti da inda tasan daidai lambar abaas take rubuce a jikinsa ta saukar da idanuwanta wanda suke qara tabbatarda saitin gurin,

Rawa hannunta ya fara ta riqe hannun Bahar din da karfi tareda Bude bakinta yana rawa tace

'AYANAAH BAHAR??
AYANAH ABAAS??
AYANAH GHAZ?????
AYANAH BAHAR ABAAS GHAZ????

Rintse idanuwa Bahar tayi da karfin gaske wasu hawaye masu tsananin zafi da tashin hankalin gaske suna gangaro mata wanda ya saka ayanah yin baya da sauri jiri me karfi yana dibanta.

Zuhrah ma da adaidai wannan lokacin idanuwanta da kunnuwanta suke shedar mata komai wani mummunan jirin ne ya dibeta wayar hannunta na subucewa tana faduwa.

Tenya ce tayi saurin riqe ayanah da numfashinta ke kokarin yankewa.

Wani mummunan Abu ayanah ta hadiye a kirjinta tana sake kallan Bahar batareda kyaftawa ba ta kuma maimaita sunanta cikakke tareda riqota da hannuwanta biyu ta jijjigata da karfi tana cewa

'Ayanah ABAAS???

wani kuka mara sauti me tsima zuciya Bahar ta kuma fasawa tareda zubewa qasa tana dafe kirjinta dake make tsananin nauyi.

Ganin hakan ya tabbatarwa da ayanah rayuwarta tazo karshe wani mummunan Jiri ya kuka dibanta ta zube a gurin numfashinta yana yankewa.

Cikin mummunan tashin hankali su tenya da itama take cikin mummunan tashin hankalin da Babu shiri ta dauki  ayanah din tareda bayin da suka taho da ita zuwa bangarenta hankali a tashe.

A daidai wannan lokacin Salman shima ya isa ya sanar da haile inda Bahar din take sbd bai Samu Asim a bangarenta ba kafin ya nufi kofar bangaren sultan ya sanar da Asim wanda yayi mummunan laushi.

Dare ya fara Sako Kai a lokacin Amma Babu ta inda sauki yake koina tashin hankali ne kwatsam sai ga Sako daga bangaren Ammin zuwa bangaren NUAB da sultan akan halinda take ciki numfashinta ya dauke cak.

Aleey ne dole ya isar masa da sakon wanda ya sakasa fitowa duhun daren har lokacin Babu jijiyar jikinsa data koma ta kwanta idanuwansa jajir.

Yana isa halinda yaganta a ciki ya sakasa Kai tsaye juyowa ya nufi bangaren sultan wanda yake zaune a daidai lokacin shima yana zaman jiran isowansa.

Kafin isowar NUAB bangaren Asim su kuma suka bar gurin Kai tsaye shima bangarensa ya nufa ya hada cards dinsa da passport da dukiya me yawa ta kudin dollars bayan tarin dukiyar dake bankunansa ya fito da shirin guduwa da Bahar a cikin daren bayan ya saka salman ya masa ready da komai na fita masarautar.

Kadir ayau yanayin da NUAB din yake ya sakasa kasa shiga sbd yau akwai babban almarin da zai iya zama me kyau ko mara kyau a tsakanin uba da 'da.

Da wata irin aura dake cike da zafaffan fushinsa da tafarfasan jininsa ya iso a cikin takun isa da Iko ya zauna a kujeran dake kallan mahaifinsa.

Kallansa sultan ya dago yayi a natse zaiyi magana NUAB ya dago nasa idanuwan da Babu rahama a cikinsu ko daya ya miqo hannunsa dayake dauke da zanen numbern mahaifiyarsa ta bauta ya Tarawa sultan din tareda kafe idanuwansa akansa ya Bude Baki da muryan data saka gashin jikin sultan gabaki daya miqewa yace

'zan tabbatarda baka Manta wannan ranar da burinka zai cika na shekaru,
Zan tabbatarda sai kayi Dana sanin sauka akan mulkin da nine zan hau'

Cikeda samun cikar tsofaffen burin da nauyinsa yake danne a kirjinsa na shekaru sultan ya ce

'ina maraba da hakan SULTAN NUAB ALMAZZ Mai boyem da GHAZ'

*****A daidai wannan lokacin ne su aleey sukai nasarar gane inda su Bahar din suke Dan haka Kai tsaye suka nufi bangaren da tarin securities da full loaded guns da suke a shirye da harbi tareda umarni me Karfi na kawar da duk wanda ya shiga gabansu,
Chapter 18 · 0% Book details