← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 112

Sashe 59

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma tata kaddarar kenan akan bahar,
Namijin datake tsananin so fiyeda rayuwarta ya zabi bahar ya mutu akanta,
Ayau ma mijinta datake aure shima bahar dince rayuwarsa,
Yayi mutuwar da zai iya barin duniya akan bahar........

Hannu ta dora akan kirjinta tana jin wani irin radadin azaba yana keta kirjinta yana saka hannuwanta rawa ta soka kanta a cikin kafafunta tana fasa wani irin kuka me karfi da tada tsigar jikin itama tana jinta ayau tamkar mara gatan da batada ko asali bare zamowa yar jinin sarauta,
Tana jinta yau tamkar ba 'yar mai girma yunar dayake da babban matsayiba dazai iya komai akantaba....

Lokaci me tsayi suka dauka a wannan mummunan yanayin kafin sukai shiru dukansu a inda suke suka raba tsakiyar daren babu wanda ya dago,

Ciwo ne me karfin gaske ya taso ya rufe Asim wanda ya ringa fizga sbd rawar sanyi dan haka dole itace ta miqe ta taimaka ta kamasa suka isa gado ta kwantar dashi ta rufesa ta dauki waya ta kira Shuraim wanda a cikin daren sosai ya shigo dakin idanuwansa jajir bai samu baccin ba shima.

Duba Asim din yayi yace suna buqatar kaisa asibiti sbd kaman attack ne yake kokarin samu.

Manager suka kira take a tanadi motar da zaa kai Asim da ita wadda aka fitar aka taho da gaggawa aka daukesa aka fita dashi zuwa asibiti Shuraim na tareda shi dan hanasa rasa hayyacinsa gabaki dazai taimaka sosia.

Suna isa asibitin aka shige dashi dan taimaka masa shikuma shuraim da aka dakatar dasu Leylah ya riqe a jikinsa tareda cire rigar sanyin jikinsa ya saka mata akan kayanta data wuni yau dasu sbd ko shirin bacci basuda daman yi.

Zaunawa sukai suna jiran tsammani batareda ko iya magana a tsakaninsu ba dan babu me energy.

Har asuba suna zaune tukuna suka samu shiga zuwa dakin da aka kai Asim din ya samu bacci me karfi ya daukesa ya koma kaman bashiba a ciwon da bata taba tsammanin zai iya kamasa akan so ba.

Sallah sukai a dakin kafin ta zauna akan sofa tana lumshe ido bacci ya dan fizgeta shuraim ya jinginar da ita yace ta dan rintsa kafin Asim din ya tashi.

Hakan kuwa tayi take bacci me karfi ya dauketa shi kuma ya fice daga dakin.

Karfe goma sha daya na rana Asim ya farka lokacin harma taje tayo wanka ta sauyo kaya ta dawo tana zaune ta tsaresa da ido tana kallo.

Bude idanuwansa ya hada idanuwansu kai tsaye ta sauke ajiyan zuciya batareda ta motsa ba shima ita yake kalla yana lumshewa ahankali cikin rashin kuzari da mutuwan zuciya.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 11:29 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

132
Shiru sukai a hakan tsawon lokaci kafin ta iya motsawa a hankali ta isa garesa tai masa sannu kafin ta taimaka masa ya tashi zaune idanuwansa jajir sbd bacci da damuwa.

'Thank you' ya furta mata a hankali da sautin da baya fita sosai,

Doctors ta kira suka zo suka sake dubasa suka ga ba buqatan ajiyesa daman dan haka suka sallamesa kawai.

Itama bata wani bata lokaci ba sbd bata son asibiti ta kira drivern da hotel suka basu yazo ya daukesu suka koma.

Suna shiga dakin ruwan wanka ta taimaka ta hada masa ta kamasa har cikin toilet din tukuna ta fito.

Breakfast tayi order ba bata lokaci kafin ya futo har ankawo dan haka ta kawo masa har kurya ta jere a table ta nemi guri ta zauna tana kasa kunna wayarta har lokacin sbd bata buqatan jin kowa kadaici take so a rayuwarta yanxu.

Yana fitowa daga shi sai towel iya qugunsa ahankali ya tako ya iso ya zauna yana goge jikinsa ahakali kafin yayi dan gajeran shiri ya saka kayan shan iska yaxo ya zauna gefenta tare sukai breakfast sbd itama bata samu sakawa cikinta komaiba har lokacin.

Ba wani abincin kirki suka ci ba yasha magani ya miqe yaje ya kwanta tareda rufe idanuwansa
Itama a inda take din ta kwanta tareda runtse idanuwanta.

Shuraim ta wayar Asim ya kira yayi musu bankwana yabar Oxford ranar ya wuce sbd bazai iya zamaba damuwa ruguza rayuwarsa zatai ya lalace a banza akan wainda sun zaba tasu rayuwar sun zubar da kowa da rayuwar kowa dan haka bazai bari tasa rayuwar baqin ciki yayi sanadintaba duk da yana jin radadi da qunci me yawan gaske.

Tafiyan shuraim ya sake saka rayuwan Leylah damuwa da kadaici da qunci dan haka take son Asim ya warware suma su tafi.

******acan gidan Kuwa koda su leylah sukai musu saida safe suka tafi babu wanda yake cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyan hankali sbd tinanin wane irin likita ne kuma zai iya yiwa Bahar abinda zaifi wanda sukai mata dan kuwa a yanda tenya tayi mata wannan gyaran na al'ardasu me karfi batajin akwai wata sauran ma matsalar data rage bayan ta qin sake jiki da bahar din tayi dan kuwa ko a lokacin zaa iya sake shigarta batareda kowace irin tangarda ba amma NUAB ya kalli tsabar idonsu ya tambayi tafiyarta bata koma daidaiba bayan shine mai aikin daya kawo hakan kuma ba yanda zaayi tafiyarta ta koma daidai kai tsaye sbd ba qaramin gurza tasha ba,

Kunyar daya sakasu itace mafi girman punishment da suka karba a gurinsa sbd ita dai tenya ma data rayu a irin wannan aikin babu wanda ya taba mata maganar data kusan kama da hakan a kaf tarihin aikin nata hakama yanzu akan 'yarsu yake musu wannan maganar,

Allah suka godewa da Ammi bata nan yayi wannan laifin mai girma da zai iya ganin fushinta me girma sbd alkawari da burin datai bazai taba kebewa ta hakan da Bahar ba harsai ta kammala karatu anyi zama akan matsayin auren,

Amana me karfi Ammin ta bar musu akan Bahar wadda basu taba kawo hakan a rayuwarta yanxu ba dan haka basajin ma zasu iya fada mata abinda ya faru zasuyi shiru kaman yanda shima NUAB sukai shiru suka kasa fada masa inda Ammin take haryanzu.

Bayan tafiyar shuraim da shine karshe zaman jigum sukai suna dan kokarin manta kowace irin zance ma da abinda ya faru saiga kiran Ammi kaman daga sama.

Kallan wayar tenya din dake ringin sukai a tare kafin suka kalli juna kafin tenya ta tattaro karfin hali tana basarwa ta dauka cikeda farin cikin jinta suka gaisa sosai tace musu wayarta ta fadi ra shafe ne sai baa kawo wata ba sbd suna yawon asibiti amma yau ankawo mata wasu wayoyin har biyu,

Bahar ta tambaya sbd ita tafara kira tayita ringing bata dauka,

Wata maganar tenga ta shigo da ita tana kawar da maganar bahar din kafin dai a samu su dawo daga asibitin cikin dare.

Sun jima suna waya sosai harma da sakinah kafin ta sake tambayar Bahar sakinah tace tana can ta duqufa karata wayarta na caji.

Da wannan suka rufe zancen tana kashewa ta saka kiran NUAB wanda a daidai lokacin sun isa masaukinsa kenan dan haka a natse ya dauka wayar yana kama hannun Bahar cikin nasa a natse zuwa ciki se Aleey na bayansa.

Gaisawa sukai hankalin kowannensu a kwance batareda ma yanada alaman nun mata yana Uk kuma yasan bata nan ba bare abinda tai masa.

Har suka isa daki waya yakeyi da Ammin akan wasu abubuwan daban cikeda kauna da kulawa tsawon lokaci kafin sukai sallama daidai lokacinda ya jiyo daga gaban windon daya tsaya bayab shigowansa lafiyayyan dakinsa yana wayar.

Akan bahar ya sauke idanuwansa bayan ya juyo din yana kallan yanda idanuwanta sukai jajir suna cikowa da hawaye cikeda wata irin tsoro da shakkar kada yafadawa Ammi wani abin,

Wayar hannunsa ya daga ya sake saka kiran aleey akan isowan likitar daya buqata tazo dubata kafin yakaita gurin wadda ita kadaice ya yadda da ita likita mace akan bahar wadda take Birmingham kuma acan zai kaita da kansa ta dubata.

Yana gama wayar ajiyewa yayi a kan table dake tsakiyar dakin yana qarasowa gaban bahar din ya kama hannunta saida ya rankwafo mata kaman zai kai fuskarsa a tata ya shaqi qamshinta me sanyi wanda ya sakasa jin temperature din dakin ta masa daidai tukuna ya dagata batateda ya mata daukan kwance ba ya isa har kan sofa ya zaunar ya zauna gefenta daidai lokacin wayarsa ta sake daukan ringin ya juya a natse ya kalla yaga aleey ne dan haka daukan wayar yayi a natse batareda ya sake hannunta ba ya fara sauraron wayar wadda yake masa bayanin ticket din tafiyansu bai samuba saiya kai gobe kaman irin 11 haka.

Baice komaiba yana gama saurara a taqaice kawai yace ba damuwa ya kashe wayarsa,

Duk yanda taso hana kanta magana akan lamarinsa sbd batajin tanada energy na gardama ko hayaniya dashi ganin yayi shiru yana duba wani sakon a wayarsa a natse hankali kwance ya sakata kallansa tareda dan sauke numfashi kadan ta bude baki ba karfi tace

'Banajin inada sauran buqatan kowane likita na warke sosai a maidani gida kawai'

Bai dagoba ya kalleta amma ya dakata daga abinda yakeyi a wayar ya tsaya cak har saida ta sake bude baki ta sake cewa

'I said banajin ina buqatan kowane doctor ayanzu....

Dagowa yayi da idanuwansa ya mata wani kallo na seconds ashirin kafin ya sake maida kansa a wayar hannunta sbd bayajin tanada zabin da har take fada

Time ta kalla zuciyarta na sake shiga fargaban alamun datake gani na zata kwana a nan din kafin ta tafara kokarin nufar kofa wanda ko taku biyu bataiba ya kama hannunta har lokacin yana abinda yakeyi ya janyota da dan karfi kadan ta yo baya ta fado akan kafafunsa ya zagayo hannunsa me riqe da wayarsa a qugunta yana cigaba da karatun abinda yake karantawa.

Sake miqewa tayi da karfi tana jin kome zai faru bazata yadda ta kwana anan dinba dan kuwa tsoro kashi biyu take ji masu tsanani,
Na farko abinda zai iya yi mata da kuka tsoron dawowan ammi wanda tinda ta kunna wayarta kila dawowa zatai bazata yadda ta sameta gidaba sbd itama ta mata kyakkyawar kasheta akan kebewa da kowa a duniya da rayuwarta.
Chapter 59 · 0% Book details