← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 112

Sashe 10

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsayar da idanuwanta Ammin tayi Akan hannun na NUAB tana Jin zuciyarta na sosuwa da abinda Ayau take sheda wa tana kasa ko kyafta idanuwanta daga hannun Wanda kamar a mafarki number dake rubuce a hannun Bahar din ta bayyana seti da daidai numbern NUAB din Wanda suka jeru Akan idanuwanta da suka tsaya cak tareda bugun zuciyarta tana kasa motsawa bare fidda kowane irin Numfashi harya kawo gurinta ya ratsa gabanta ya wuce da Bahar bata motsaba Wani irin nauyin kirji da Juyawa taji kanta nayi Wanda ya sakata dafa bango ganinta na Neman daukewa ta daddafa batareda kowa ma dayake cikin shock ya lura da itaba ta koma dakinta ta zube a bakin gado tana dafe kirjinta tana kasa yadda ko kadan da abinda ta gani sbd ganin numbern ta bauta a jikin yarinyar ya dawo mata da sak irin numbern Abaas dinta ce,

Girgiza kai tayi da sauri tana sake dafe kirjinta sbd tinaninta dayake Neman rikicewa,

Mantawa tayi da abinda NUAB yayi sbd ganin numbern a idanuwanta ya mantar da ita komai a daidai yanzu Bayan dawowan radadi da tinanin rabin rayuwarta dan uwanta Abaas datake rokon duk inda yake Allah kada ya dauki ranta bata gansa ba Allah ya bayyanar mata dashi.

Leylah kuwa acan palon Wani irin daci da nauyin kirji ne me Zafin gaske ya rufeta idanuwanta na sauyawa zuwa ja da wasu irin hawayen baqin cikin da bata taba dandanaba suna zuwar mata ta kafe kofar daya wuce da baiwar wadda sai Ayau take ganinta dakyau dan kuwa har tenya batai noticing baiwar ba wadda harta samu matsayin shiga dakin sakinah ta zauna da irin Kayan da suka gani a jikinta.

Shi kuwa yana fitowa da ita harya nufi kofar ficewa ya dakata cikin zafi yaje har lokacin,

Sakin hannunta yayi tareda saka hannu daya ya bude gaban rigarsa kai tsaye batareda tsayawa bude botiran gabanta ba haka botiran suka zube qasa gabaki daya sbd yanda ya bude gaban rigar ya zarewa lafiyayyar farar fatarsa dake Wani irin daukan ido da kakkarfan jikinsa suka bayyana.

Sake janyota yayi da karfi gabansa Wanda ya sakata fadowa Kansa sedai bata iya barin jikinta da nasa ya qarasa haduwaba ta saka hannunta kai tsaye ta tare kirjinsa hakan ya hanata fadawa kirjinta ya hadu da nasa,

Saukan tafin hannunta Akan kirjinsa ya saka ya kalli hannun nata da jajayen idanuwansa kafin ya kalleta itama shi din ta kalla tana dauke hannunta fuskarta a cike da baqin shaqar numfashin dayake cakude qamshinsa ta ja baya tana dauke idonta gaba daya daga bangaren dayake shima kallanta ya dauke nasa Idon tareda sake Kama hannunta ya jata ya fice da ita tana kokarin kwacewa da karfi amma ba daman kubuta ko kadan sbd irin riqon da yayi mata.

Yana fitowa aleey kallo daya yayi masa yaga ba Riga a jikinsa yake yabi bayansa kawai batareda furta ko kalma ko daya ba suka nufi bangarensu.

Maa sakinah kasa zama tayi ta koma tsakiyar dakin ta dawo bakinsa ta sake komawa ta dawo a sanyaye ba karfi a jikinta zuciyarta da kirjinta na nauyi,

Maa tenya qarasowa gurinta tayi tana kallanta cikeda mamakin abinda yake faruwa tana sake shiga mamakin sukunin data rasa gabaki daya take kaiwa da komowa,

Cikin mamaki da zullumi tace

‘Sakinah menene yake faruwa?
Waye wannan baiwar?
Yaushe ma aka kawota bangaren nan?
Daga ina aka kawo nan bangaren?

Kasa amsawa sakinah tayi Bayan juyowan datai ta kalli Leylah dake tsaye kaman zuciyarta zata Kama da wuta me tsanani ta dawo da kallanta kan tenya din ta bude baki zuciyarta na tsananta damuwa tace

‘Ba baiwar kowa bace’

Tana fadar hakan kasa dorawa da komai tayi ta juya ta nufi kofa kai tsaye tana kasa jira tabi Bayan NUAB din Wanda take tsananin tsoron kada tsananin fushinsa yakai sa ga yiwa Bahar din Wani abin.

Ficewa tayi tabi bayansu kai tsaye tabar tenya da bin bayanta da Wani irin kallo hakama Leylah Wani kallan baqin ciki da tsanar sakinah din tabi ta dashi sbd ganinta da baiwar da batasan meyasa NUAB dinta zai Kama hannunta ba,

Tsanar baiwar taji me karfi da tsananin gaske tana shigarta sbd irin fushin data gani yana cin idanuwa da jikin NUAB a zuwan nasa tabbas bana tsana bane bare ace laifi tayi koda kuwa laifi tayi dole tanata zarrar da har yasan da itace tayi laifin Yazo hukuntata sbd NUAB kaf masarautar Bayan mahaifiyarsa da mahaifinsa kila babu Wanda ya riqe kamanninsa bare tinawa dashi ko wayene amma wannan ace yasan da itace tayi laifi harma yasan a inda take kuma ya gane itace a tsaye ya Kama hannunta…..Jin tayi batama buqatar tsanarta hukuntata kawai zata saka ayi na iya kallan mijin dayake matsayin nata harma ta iya barin jikinta da baida daraja haduwa da nasa.

Maa sakinah tana fitowa kai tsaye bangaren NUAB Din ta nufa Wanda tin daga nesa jikinta da idanuwanta suka tabbatar mata ba lafiya ba dole akwai abinda ya faru sbd Yaransa gabaki daya a tsaye suke da wasu mahaukatan bindigogin da zasu fasa kan mutum kai tsaye babu bata seconds hakama da alama kwanan tsaye zasuyi yau motsi kadan Zai iya zama ajalinka.

Duk hasken dayake zagaye da bangaren a kunne yake koina ya haske ta yanda ko sauro ya wuce zaka iya ganinsa.

Tin tana doso wa suka gane itace dan haka suka dan sassauta makamansu tana isowa babu Wanda ta kalla a cikinsu suma sadda kai sukai qasa amma babu me alaman motsawa bata hanyar wucewa.

Aleey ne ya iso ya bata hanya da Kansa ta wuce ya bita a baya kai tsaye palon ta shiga.

NUAB din baya palon yana dakinsa yana kokarin calmin Kansa ta hanyar tsayawa bakin window iska me sanyi tana kadasa yana fidda Numfashi me Zafi yana saukewa wutar dake cinsa tana sauka ahankali ahankali amma saima ta jima sosai kafin ta gama fita dan hakane ma kowa yasan bame sake ganinsa sai kuma gobe.

Maa sakinah kai tsaye dakin datasan Bahar din na ciki ta nufa ta bude a natse tareda shigowa tana kallan Bahar din dake bakin gado ta dunqule tana sauke numfashin itama kuka ya kasa zuwar mata sbd tsananin baqin cikin NUAB din.

Maa sakinah na tinkarota ta dago kanta ta kalleta da jajayen idanuwanta kafin ta maida kanta tana Jin kaman zata fasa kirjinta sbd Zafin dayake mata.

Maa Zaunawa tayi kusa da ita tana dafa bayanta cikin rikicewa tace

‘Bahar me yake faruwa ne Wai?

Sake dawowa Bahar tayi ta kalli Maa din tana rasa abin fada sai datai mintina kafin ta iya bude Baki zatai magana Wani qamshinsa me karfi da nutsuwa da sanyi ya shiga hancinta da karfin gaske.

Kasa maganar tayi ta kalli rigar dake jikinta ta miqe tsaye tareda zare rigar ta jefar tana Rintse ido da karfi ta bude tana komawa bakin kujera ta zauna tana dafe kanta dayake sarawa sbd haukar dayake Neman cinna mata irin tasa tinda shi baida hankali saiya maidata mahaukaciyar itama.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

80
Maa sakinah dawowa gefenta tayi tana shafa bayanta a natse tana Dena tambayar sbd ganin kaman Bahar din zuciyarta a kufule take abinda bata taba gani ba a tareda ita tinda ta dawo hannunta.

Shiru sukai kowa zuciyarsa da abinda take tinani amma ba damar fada,
Lokaci suka dauka shiru kafin Maa sakinah ta sauke Numfashi zata koma tinda dai ta tabbatarda kila NUAB ya sauka daga koma menene ya bata masa rai dan haka tasan bama lallai ya fito ba sai kuma gobe,

Miqewa taje kokarin yi Bahar ta riqe hannunta da sauri tana shigewa jikinta ta rungume tana girgiza mata kai alaman dan Allah kada ta tafi tabarta ta jirata su koma a tare.

Shiru tayi kafin ta koma ta zauna ahankali tana sake shafa Bayan Bahar din wadda har lokacin gashinta yakeda Sauran sanyi gana ac yana shigarta dan haka saita dan dunqule a cikin jikinta tanayin shiru a sanyaye.

Anan dole sakinah ta kwana tareda Bahar din wadda suka kwana kusan kowannesu bai samu ya rintsa da kyau ba tinani da damuwa sun Haba hakan,

Kwanan Maa sakinah a bangaren NUAB ya tabbatarwa dasu tenya da Leylah da suka kwana kusan a Zaune suma sbd tsananin mamaki da tashin hankalin kenan tabbas itama baiwar acan ta kwana bangaren nasa,

Babban abinda ya Haba idanuwan Leylah ko kwatanta rintsa wa shine shin a ina baiwar zata kwana a bangarensa hakama yanada ikon kwanciya da ita ba laifi bane ba illa bace tinda baiwar ce zata iya zama imebetinsa,

Wani sabon nauyi me tsananin radadi ne yake sake danne zuciyarta duk ta Tina da hakan sbd zata iya zama fiyeda abinda ake iya tinani idan wata macen ta fara kwanar mata da miji ba ita ba,

Ayanah ma da suke son ganin halinda zata shiga Akan hakan idan taji sun kasa samun ganinta sbd a shige ta rufe dakinta Wani irin hali tinani da zuciyarta suke ciki na ganin abinda ya saka zuciyarta gabaki daya tashi Akan Abaas Wanda zuwa yanzu ta tabbatarda matiqar yana raye bazai taba kawowa yanzu bai nemeta ba indai ya samu yancinsa sai idan yana cikin bauta haryanzu Wanda tina hakan zuciyarta bazata dauka ba sbd shekarunsu sun tafi sosai ta yanda haduwansu da sake rayuwa da juna da junansu damar na sake qaranta,

Washe gari tinda safe Maa sakinah ta Baro bangaren tareda Baro Bahar acan wadda take bacci sbd Bayan asuba zazzabi ne na sanyin gashinta daya shigeta ya rufeta dan haka magani ta fito ta samar mata a lafiyayyan kitchen din palon na ruwan zafi sosai da ginger ta kawo mata tasha tana gamawa bacci mai dan karfi ya dauketa Wanda Maa tasan zata jima tanayi dan haka ta tafi ta dawo daga baya.

Tana komawa lokacin tenya na dakinta itama baccin Sai a lokacin ya dauketa dan haka dakinta ta nufa Bayan ta dubo itama Ayanah baccin takeyi me karfin da bata samu yi ba a Daren takeyi.
Chapter 10 · 0% Book details