← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 112

Sashe 41

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya aiko masa sakon a rubuce da stamp dinsa na ya dakatar dashi daga fita kowace qasa har sai bayan tsawon shekara biyu sbd ya samu hutawan sauka daga mulkin shekaru sana da talatin tareda zuba masa sabbin bayi da securities a bangarensa duka a matsayin basa hutu da kulawan daya kamata,

Ko a wancan lokacin da sakon ya samesa kai tsaye yasan bawai hutun NUAB yake nufiba ya basa a matsayin tausawa da nuna kulawa kaman yanda masarautar da duniya ta dauka yayi hakan ne dan hanasa isa ga mahaifiyarsa dayake jin ya dauke kenan har abada daga rayuwar sultan din,

Yayi hakan ne dan hanasa fita koina kuma shima shiyasa tsawon wannan lokacin bai taba tafiya koina ba yana cikin boyem da kusan fiyeda rabin bataliyarsa da ayanzu suka tare a boyem dan bude sabuwar ghaz da boyem a qasa daya,

Ko ayau ma sultan din tinaninsa daya ne akan wannan particular dokar ta NUAB akan imebētis dan haka baji komai sbd batareda sanin NUAB dinba ya basa wata babbar damar da itace burinsa daya jima dashi akan Ayanah ghaz dan haka kai tsaye a cikin daren shima ya fidda takardar da kadir ya isar a fada wadda washe gari zaa gabatar da ita a fadar wadda itama sabon sultan yana cikin abinda ya soke matiqar ba zaman taro me mahimmanci akeda shi a qasa ba da ake buqatan zama da duka masu matsayin fada to ya sake zaman banza na fadar an sauya tsari zuwa manyan offices sabbi masu tsari da aka gina a cikin masarautar kusan hawa hudu tamkar wata babbar sabuwar palace kowane shugaban fada yanada office dinsa me zaman kansa da securities dinsa da mataimakansa tareda p.a,

Shi kansa Mai boyem din office sabo da babu kamarsa a boyem aka gina masa a floor din karshe da babu kowane office bayan nasa hade da lafiyayyan palo da bedroom me girman gaske dayake hade da bathroom harma da yar closet din hutawansa a ciki idan yaso harma da gurin cin abinci duka a guri daya sai office din Aleey dayake farkon shigowa floor din daga ka fito lifter wanda shima nasa yake babba da toilet lafiyayye kadai a cikinsa dan haka tsaro da security din da floor din yakeda shi yafi na koina,

Bayan sabuwar ginin offices din ba palace officials wata sabuwar ginin bangaren sultan LEUL NUAB me boyem akai acan Asalin bangarensa da aka sauyawa maana ana hade kusan bangare uku aka maidasa daya tareda yi mata tsarin da babu kamarta kaf a masarautar hakama tsarin ginin yanda akasan yana rayuwa da buqata,

Chambers din Sultan NUAB itace bangaren datafi kowane bangare kyau da tsari tareda daula a cikin boyem,

Komai na bangaren nasa akan tsarin mulkin bature yake,
Hakama bangaren mahaifiyarsa anyi masa gyara na musamman tareda sauya musu komai hakama sauran gurare da dama an sauya musu tsari wanda ya saka masarautar zamowa tamkar sabuwar masarauta ga sabbin tsare tsare da security cameras nako ina da aka sauya.

Bangaren Asim bai taba hakura ba da Bahar sbd bai taba jin soyayyarta ta rage bare fitaba daga zuciyarsa dan haka tinda ya samu cikakken bayanin barinsu masarautar zuwa uk da zama take boyem da masarautar boyem din harma da mulkin boyem din ya fice daga ransa yaji yana son barin qasar zuwa duk qasar da bahar take da zama,

Haile na ji tana gani Asim ya koma mata mummunan kaddarar da bata taba zata ba akan soyayyar da babu alkhairi a cikinta,

Bata taba tsammanin akwai macen da kaf duniya Asim zai so fiyeda burinsa da dashi ya girma ba,

Asim ya mutu rayuwarsa ta mutu batada Sauran amfanin da suke buqatarsa dashi hakama yana nan yana macewa da zama marar amfanin NUAB yana can yana gudanar da mulkinsa na gina sabuwar duniya ga boyem hankalinsa kwance hankalin uwarsa a kwance a wata qasar hakama hankalin sultan a kwance yana hutawa tamkar babu su a duniyar sbd kwata kwata tinda ta dawo taqi zuwa tirakarsa sbd tsanarsa datake ji me tsananin gaske da batada burin daya wuce barinsa duniya kuma bai taba nemanta ba tinda taqi zuwar masa maraki ce kadai take zuwa tirakarsa wadda itama a yanzu batada burin a wayi gari ace sultan din baya duniya ta huta tasan kowa a cikin su ukun ya rasa an huta dan kuwa a duk zuwan datake shimfidar sultan din bata taba ganin soyayyarta ba a tattare dashi ko so daya wanda take da tabbacin ba kuka haile bace Ayanah ghaz ce a zuciyarsa.

Su aslam zuwa yanzu sun saddaqar da rayuwa ga qarewa a gagare ba aure sbd a yanda Asim ya koma babu sauran amfani ga tsayuwa akan burin da nacewa nemar masa sarautar boyem dan haka suka zubawa sarautar allah ido da jiran damar dawowansa daidai.

A bangaren Leylah kuwa duk yanda zatai ta isar da kanta ga NUAB babu kowace hanya ta toshe sbd a yanzu ko ganinsa sai me babban rabo da matsayi dan kuwa kwata kwata sun dena ganinsa har ita har mum dinta wadda duka baifi so biyu yazo har bangarenta ya gaidata ba sedai yana aiko mata gaisuwa duk jumaa akai akai sbd bata matsayinta na uwa a garesa.

Duk lokacinda zai taho gaida mahaifiyarta saita sake mutuwa me zurfi akansa sbd gabaki daya ya sauya daga LEUL NUAB a yanzu ya koma cikakken SULTAN LEUL NUAB dinsa me tsantsar kwarjinin dayafi na baya.

Haukacewa take neman yi akan rashin samuwarsa dan haka ta cire kunyarta ta sanar da mahaifinta aure kawai takeso ayi mata ta gaji da jiran maganar aurenta data kwanta da NUAB din ita dai a tada maganar ayi mata auren koda shi bayaso ita tana so.

Maganarta tayi tasiri sosai a zuciyar mai girma yunar wanda shima zuwa lokacin yana ganin ya bada duka lokacin daya kamata ya bayar na barin NUAB yagama shiryawa akan mulkinsa duk da yayi farin ciki sosai da hatta Shuraim ya samu matsayi me girma a cikin tafiyar sarautar ta NUAB wadda Aleey kai tsaye ya saka sunansa a ciki dan hanasa tafiyar daya samu cikakken bayanin tafiyar zaiyi zuwa uk a bakin Mum zuhrah lokacinda sukaje gaidata dan haka kai tsaye ya saka alaman tambaya akan tafiyar da bai samu cikakken dalilin yinta ba a binciken dayayi bayan jinta dan hakanne ya gabatar da sunansa da wasu boyayyun hujjojin daya saka NUAB amincewa batareda yasan asalin dalilinba.

Bawa Shuraim matsayin ministern hukunce hukunce ya saka zuciyar iyayensa farin ciki sosai dan kuwa ya shiga cikin royal politics kenan zai fara kutsawa a sarautar qasar,

Su Ammi ma da suke can sunyi farin ciki sosai da hakan sbd ganin NUAB yafara jan dan uwan nasa a jikinsa,

Haile data samu labarin maganar auren da yunar yake kokarin sake tadawa akan yarsa wadda bazata iya barin NUAB ya aureta ta rasa damarta ta karshe ba akan cire bahar daga rayuwa da zuciyar Asim ba shiryawa tayi a cikin daren takaiwa sultan yasar ziyarar da bai taba tsammani ba dan haka babu kowace irin sauyi a yanayinsa ya karba zuwanta tareda bata damar kasancewa dashi.

A bangaren nasa ta kwana wanda da safe kafin ta wuce ta isar masa da buqatarta da rokonta na nemawa Asim auren leylah a gurin mai girma yunar.

Kallanta sultan yayi a karo na farko bayan lokaci kafin ya juya buqatar tata a zuciyarsa ya sauke numfashi a natse kafin ya bude baki yace ya amsa buqatarta a yau zai aika sakon takardar neman auren leylah wa Asim.

Farin ciki taji ya sauka a xuciyarta bayan watannin data share a cikin quncin baqin ciki tayi godiya tareda ficewa dan kuwa a gaggauce zata tabbatarda an daura auren dan matiqar aka karba auren a kwana uku kafin a samu matsala take son a daurasa.

Tana ficewa shi kansa sultan bai tsaya komaiba ya aikawa yunar sakon wanda yana isar masa shima bai ga illar hakan ba tinda ga dukkan alama NUAB baida raayi kuma shi bazai zabi kwadayin mulki ya aurawa leylah Sultan din da baya buqatanta ba dan haka kai tsaye ya maida saukon bada auren nata ga Asim wanda shima sultan sakon na dawo masa ya buqaci auren da gaggawa sbd yasan zaa iya samun matsala gwara ayi sa su daidaita kansu daga baya.

Koda sakon auren ya isa kunnen zuhrah har yunar ya karbi sadakin auren wanda take aka fidda sanarwar daurawa ranar jumaar da saura kwana hudu dan haka batai wani baqin ciki ko damuwa ba sbd tafi kaunar leylah din tayi aure ta cire NUAB a ranta sbd Bahar daya riga ya aura batason duk abinda zai lalata ko kawo matsala ga kaunarsu da yar uwarta ayanah dan haka da hannu bibbiyu ta amsa auren kafin ta kira leylah dan sanar da ita babban lamarin dake shirin faruwa.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

114
Leylah na shigowa lafiyayyan bedroom din mahaifiyarta ta nufota a natse yanayinta a dan sanyaye sbd bacci ta tashi dan tin kafin baccin nata sakon kiran mum din ya isa gareta amma sbd tayi shirin baccin hutawa na rana shiyasa bata taho ba saida yammar bayan ta tashi taci abinci tayi wanka ta nutsu amma jikinta hakanan yake mace har lokacin da sauran yanayin baccin datai,

Zuba mata ido Zuhrah tana kallanta a lokacinda take tahowar tanajin tausayinta sbd gabaki daya ta sauya harda yar ramewa tayi sbd kwallafa rai akan wanda takeda tabbacin ba lallai ya taba yi mata so na soyayya ba tinda gashinan bahar din ma da already aurensa yake kanta ba sonta yakeyiba yama mance da ita bare ita da baima aura ba,
Hakama bayan hakan tayaya zata iya barin son zuciya yakaita iya barin leylah ta auri NUAB bayan yana auren bahar wadda tin kafin asan ma zasu zo duniyar akai alkawarin aurensu a tsakanin iyayensu wato abaas da ayanah,
Gwara dai suji da dayan ciwon rai da damuwan Bahar daya tattara ya watsar akan su qara sa wata damuwar dan haka ta sake jin qwarin gwiwan gwara leylah din tayi aurenta da Asim din tinda shima baida matsalar komai a gurinta bataga kowace illar ba a bayyane dashi.

Zaunawa leylah tayi tana kallan Mum din ta sauke ajiyan zuciya tareda bude baki tace
Chapter 41 · 0% Book details