← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 112

Sashe 82

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A sanyaye take nufar bangaren cikin nutsuwa da tinani kala kala bayinta na biye da ita kansu a qasa har suka sako kai a hanyar bangaren wanda tin daga nesa securities suka hangota hadda aleey dake cikinsu a daren sbd ya kasa shigewa miqewa sukai dukkaninsu aleey ne da kansa ya bude mata kofar yana tsananin jin dadi da farin cikin ganinta tareda jin wata nutsuwa na shigarsa sbd yana tsananin son sanin halinda NUAB yake ciki amma ba ikon shiga dan haka ya kasa barin waje yana cikin securities din dan bazai iya rintsawa ba koya shige.

Barka da zuwa sukai mata a natse dukansu batareda ta iya amsawa ba itama aleey kadai ta iya magana dashi a qataice tana wuce yana biye da ita har kofar shiga ciki ya bude mata ta shige bayin na biye da ita.

A palon farko suka dakata suna ajiye kayan dake hannunsu a table a jere suka juya suka bar palon da bangaren gabaki daya suna komawa inda suka fito.

Suna ficewa aka rufe koina na bangaren sai a lokacin Aleey ya sauke ajiyan zuciya me dan sanyi yana nufar lafiyayyan palonsa ya shige ya nufi bedroom kai tsaye ya shige yana nufar bathroom dan fara wanka tukuna ya huta.

Acan ciki itama ajiyan zuciya me sanyi da sauti ta sake a tsakiyar palon tareda kallan hanyar palonsa na kurya tana jin zuciyarta da jikinta na sake sanyi,

Sake sakin nunfashi tayi me nutsuwa kafin ta durqusa ta dauki tray din din da aka jere mata din ta nufi hanyar dakin.

Tana isa ba maganar knocking sbd tasan baya cikin yanayin da zaa damesa da buga kofa koma yanayin da zai iya cewa a shigo koma yazo ya bude dan haka kai tsaye bude kofar palon tayi ta shiga a natse tana rufewa koina tsit da rashin haske sosai baya palon dan haka kofar bedroom ta kalla tareda daga kafarta ta nufi can din.

Bude dakin tayi a natse ta sako kai tana shigo idanuwanta akan sofa sbd san ganinsa amma baya gurin.

Qarasa shigowa tayi tana rufe dakin da bayanta a natse kafin ta tako zuwa tsakiyar dakin da shima akwai haske amma bame sosai ba.

Duba dakin tafara yi da idanuwanta koina amma bata gansa ba dan haka ta ajiye kayan hannunta akan table tana zubawa hanyar bathroom idanuwanta da sukai laushi amma bataji motsin komaiba dazai nuna alaman yana can.

Juyawa tayi gurin curtains din hanyar pool dinsa data gani a bude tana kalla kafin ta fara takawa ahankali zuwa gurin.

Ba haske sosai a gurin shima hasken bakin pool dinne kadai daya zagayesa kadan kadai a gurin,

Akansa idanuwanta suka sauka yana cikin ruwan ya baya kofar baya gashinsa me tsayi a asake bayansa kadai take iya gani dan haka ta dakata daga inda take tsaye tareda sauke boyayyar numfashi me dumi jiki a mace tana kallansa batareda ta iya matsawa ba ko juyawa ba.

Tsawon sakanni ta dauka a hakan kafin ta daga kafafunta tafara takawa a natse tana nufarsa,

Bayansa ta iso a hankali cikin nutsuwa ta durkusa tana sauke gwiwowinta a qasa tana dan zaunawa kadan akan kafafunta gap da bayansa dan har gwiwanta na dan taba bayansa daga sama da iya shi kadai ne a waje sauran jikin yana ruwa zaune.

Bai motsaba kuma har lokacin idanuwansa basu bude ba a rufe suke cikin tsananin halin da zuciyarsa take ciki tana dauke duk wata rahamar gangar jikinsa.

Idanuwanta ta saukar akan kunnensa ta bayan nasa taga yanda yayi wani irin jajir wanda yake nuni da halinda yake ciki dan haka ta rasa abin fara fada sai kawai ta rankwafo sosai cikin sanyi da nutsuwa takai miqa hannunta a natse ta dora akan fatar kunnensa ta shafa cikeda wata irin kaunar me karfin gaske da baki bazai iya fada ba da kulawa tareda fidda wata irin numfashi me zafi daya feso damuwan da tsananin sanyin da jininta yake ciki wanda ya sauka ahankali kan kunnensa da gefen fuskansa ya sake rintse idanuwansa ahankali batareda ya budesu ba yana jin wani irin zafi na sake taso masa da ratsa zuciyarsa sbd yanda numfashinta ya bayyanarda damuwar datake ciki.

Wani sanyi jikinta ya sake yi batareda da dauke hannunta daga kunnensa ba ta saka dayan hannunta suka akan gefen fuskansa ta shafa a natse tana sako kanta ahankali gefen fuskansa ta bayansa zuwa gabansa sbd batasan wace kalman zata fara da itaba a yanzu dole shi takeson ya fara magana tukuna tasan me zata iya fada masa sbd rage masa damuwan dake zuciya da ruhinsa.

Yanda ta sako kanta gefen fuskansa ta sauke idanuwanta masu laushi akansa tana kalla cikeda kulawa da jin kaman ta zare masa duk abinda yake ji numfashinta na sauka ahankali ahankali kan gefen fuskansa duminsa yana ratsasa yana dawo da tinaninsa akan abinda zuciyarsa take ciki na damuwan da iyayensa dashi suke ciki a daren.

Bude bakinta tayi a cikin tsananin sanyi da nutsuwa da kulawa can qasan maqoshi gap da kunnensa tace

'Please...' Shiru tayi tareda jan wani numfashi mara karfi da sanyi tana rasa abin fadar kafin ta sake bude baki ta kuma furta

'Kada kayi damuwa dan Allah,
I cant se...

Bata qarasa ba sbd yanda muryanta ke rawa ya bude idanuwansa da suke jajir a wani slow yana saukesu a fuskarta.

Kallanta yakeyi batareda kyaftawa ba ko kadan itama shi take kalla da wani gaze dayake sake juyawa kowace irin tinanin dake kansa..

Amminsa ce mace daya da a duk duniya yake iya komai akanta,.ayau ta masa baraza akan matsayinta datake dashi a rayuwarsa akan abinda zai iya ajewa idan tace kawai ya aje batareda ta saka masa wannan zazzafar kalmar ba,

Sai kuma Ayanah bahar wadda itama akanta zai jurewa da fuskanta kowace irin yanayi....

Cikin idanuwanta ya kalla yana sauke numfashi me zafin daya daki fuskanta a hankali ta lumshe ido ta bude akansa kafin ya motsa a hankali tareda dago hannunsa daya ya miqa mata yana rufe idanuwansa tareda hadiye wani nauyi dayake tsaye a maqogoransa ya budesu akanta.

Zare hijabin dayake jikinta tayi ahankali tana ajiye wa gefe cikin nutsuwa kafin ta miqa masa hannunta ta kama nasa tana takowa ahankali zuwa cikin ruwan yana riqe da hannunta batareda ya sake ba.

Ratsata sanyin ruwan sukai ta sauke ajiyan zuciya me dan karfi tana qanqame hannunsa dake riqe da nata tana rintse ido sanyin na ratsata amma kuma tana buqatan isa garesa dan basa nutsuwa da sassaucin dayake buqata.

Isowa tayi gabansa tana kallansa shima ya bude ido yayi mata kallo daya ya janyota cikin jikinsa a natse ya shigar da ita tsakiyarsa ya rungumeta tsamtsam da kyau yana sauke ajiyan zuciya me sanyi suna cikin ruwan.

Shiru sukai tana lafe a kirjinsa tana jin yanda zuciyarsa ke bugawa da karfi tana harbawa da wani irin karfin da har a gefen fuskanta dake kwance a kirjinsa..

Lokaci suka dauka me tsayi a hakan kafin ta iya dagowa ta kallesa jin bugun zuciyarsa ya fara daidaita yana ragewa alaman ya samu saukowan abunda yake jin kaman zai kashesa sbd yankarsa da kalman Amminsa ke yi har lokacin sbd tana tinanin shine asalin matsalar dake tsakaninsa da mahaifinsa,

Abinda bata sani ba shine da ace ta zaunar dashi ta sanar masa kaunar mijinta takeyi babu abinda zai hanasa basa dama ya kaunacesa koba yanzu ba ahankali sbd ko aljani Ammin tace tana kauna ko ta hada wani abin dashi zai kaunacesa ya sosa fiyeda qima,

Duk zafin dayake ji akan sultan sbd ita ne badan sbd kansa ba sbd shi bayajin yana buqatan kaunar kowa a duniyar bayan tata,
Sbd itane ya taso da jin zafinsa ya rayu a cikinsa amma ta kasa gane hakan harma take ikirarin yanke alaqarta dashi.

Numfashi ya sauke yana jin baida saura kuzari kowane iri akan Ammin da Sultan sbd sun tabbatar masa da sune suke gabansa tinda ta sakasa sauke kowane irin zafinsa a hanya mafi radadi da ciwo da karya zuciya da kuzari,

Ayau yaji sa shi ba kowa bane matiqar iyayensa na gabansa bazai taba zaka kowaba sbd kaman dagasa sama ne Ammi tayi ta sheqe,
Sultan ya fada masa ya maimaita masa shi ba kowa bane a gabansa face 'dan daya haifa da dole yana gabansa duk izza da mulki da iko da isarsa.

Bahar data sake zagayesa da hannuwanta tana qanqamesa ahankali ya kalla yana kallan fuskanta dake bayyanar da tarin damuwa da sanyi harma da tausayi,

Soyayyarta ce ta fara tasowa tana cike kirjinsa da ruhinsa tareda sanyaya jininsa daya gama sanyaya ya dagota ahankali yana kallan fuskanta itama shi ta dago tana kalla a natse ganin fuskansa ta dan sake cikin karfin hali.

Hannuwansa biyu ya saka yana bude gaban rigarta dan zare mata kayanta da sukai mata nauyi a cikin ruwan sbd jiqar da sukai.
#MAMUH
09033181070
[08/01, 10:34 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

155
Kasa motsawa tayi tafara sauke idanuwanta zuwa qasa tana jin yana bude gaban rigarta a natse..

Yana gama bude gaban rigar zarewa yayi a natse ya cire mata ita gabaki daya ya sake cikin ruwan yana sake janyota jikinsa ya hade su ya saka hannunsa cikin ruwan yana saka hannuwansa biyu yayi qasa da doguwar wandon kayan baccin,

Black bralette bra ce a jikinta da black panties da suka rage a jikinta ya janyota da kyau ya shigar da ita jikinsa ya rungume yana lumshe idanuwansa ya rufe yabarsu ahakan suka sake yin shiru.

Dena jin sanyin ruwan tayi itama tana zagayesa da hannunta daya dayan hannun na kirjinsa ta kwantar tareda kanta tana jin bugun zuciyarsa yana gama daidaita ta bude ido ta dago ta kallesa tareda dagowa da kanta ta bude bakinta tace ya taho.

Kama hannunsa tayi daya da nata ta janyosa a natse suka fito ruwan,

Tana fitowa ruwan gabaki daya sanyi ya ratsata me karfin data dan kama hannunsa dayake nata da dan karfi tinda ba wani kayan a jikinta.
Chapter 82 · 0% Book details