Sashe 44
Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda aka kai leylah bangaren mijinta babu wani tsayawa dogon bayani aka barota suna ficewa ta miqe daga babban lafiyayyan palon ta wuce bedroom din da aka sanar da ita shine nata bayan guda biyu da suke extra dayan nasa ne wanda yake hade da wani lafiyayyan palon sai dayan dayake nesa kadan da nata din wanda yake extra ko dan baqi tukuna guda daya daga can kitchen wanda yake na bayinta.
Bedroom din ta shige ta rufo kofarta tareda saka key ta fara zare kayan jikinta dake zuba qamshin da duk ya dameta zuciyarta na suya da tafasar baqin ciki ta wurgar dasu ta fada bathroom ta wanke duk qamshin jikinta da adon duka ta fito ta saka kayan bacci tayi kwanciyanta tana jin tafi Asim din matsuwa dasu bar masarautar su tafi inda zatai rayuwarta yayi tasa kafin tasan matakin dauka akansa dan kuwa bazata taba yadda daci gaba da zaman aure dashi ba.
Shi kansa Asim din baida niyar fitowa bare ganinta ko abinda ma zai tina masa da wata macen yake aure a yanzu ba Bahar ba dan haka har safe basuji ko motsin juna ba.
Washe gari bayin da aka aiko daga bangaren Mameensa suka iso dan fara aikinsu dan haka ko da sukai breakfast da sauran ayyukan har suka gama bata fitoba tana daki sai karfe goma sha daya ta fito sanye da riga da wando masu fadi sosai ta nufi dining da wayarta a hannunta tana duba sakon Shuraim dayake ta kiranta bata dauka ba tana bacci.
Zaunawa tayi batareda ko amsa gaisuwan bayin nata ba aka zuba mata abinci taci sama sama ta koshi ta miqe tabar gurin ta koma palon ta zauna har lokacin idanuwanta da fuskarta basu koma daidai ba a kumbure suke jajir sbd ko a daren jiyan tayi kukan baqin cikin ranar daren aurenta na farko ta kasance da wani ba NUAB ba dan kuwa sa NUAB ne da kanta zata kai kanta garesa dan raya masa daren amma a yanzu batajin ko hannu zata iya hadawa da Asim bare shimfida ya jira bahar kaman yanda zata jira NUAB.
Tana nan zaune shima ya fito yana fidda qamshinsa da shigar kayan shan iska shima ya nufo palon yana waya kallo daya yayiwa inda take ya wuce yana ci gaba da wayarsa sbd ganin itama ko kallansa bata dago tayiba batasan yama fita qin aurenba dan shi zai iya keta kowane irin hadari akan Bahar wanda ita ba lallai ta keta akan NUAB ba.
Breakfast dinsa yayi ya gama ya miqe ya baro ya sake shigewansa basu sake ganin juna ba sai dare wanda ko data fito ta iso dining din yana kai dan haka juyawa tayi zata bar gurin ya bude baki yace
'Ba buqatan wannan takura kan ki kwantar da hankalinki sbd ba kinsan waye a gabana da zuciyata,
Ita nake da raayin aure haryanzu kuma bazan huta ba saina tabbatarda na mallaketa a rayuwata so just calm down Miss'
Dakatawa tayi daga inda take din tsaye maganar na shigarta da qani sabon takaici da baqin ta rasa me suka gani a bahar din suke nace mata,
Koma dai menene tinda abinda take so kusan shi yake so na raba NUAB da bahar zata kwantar da hankalinta ta ingisa yayi mata aikin da zata samu abinda takeso hankali kwance.
Ajiyan zuciya ta sauke tareda juyowa ta dawo ta zauna dining din ta kallesa a karan farko wanda shima ita din ya dago ya kalla suka hada idanuwansu a cikin na juna ta fara dauke nata taba bude baki tace
'Tinda kasan nima ba kai nakeso ba to da sauki zan zauna dakai nima kafin na samu tawa mafitar a cikin taka da zaka samu'
Murmushin takaici ya sake kawai batareda ya ce komaiba yaci gaba da cin abincinsa itama tafara ci hankali kwance.
Wuni sukai suka kwana biyu babu wanda yaxo bangaren nasu aka barsu suka huta sosai dakyau kuma suka fahimci juna akan tsayawa manufa daya ba takurawa dan haka suka sake nutsuwa suka dan kwantar da hankalinsu da kwallafa rai a sabon buri me karfi.
Maa sakinah ana sati daya da gama bikin ta tattara ta komawarta sbd Bahar da koyaushe data dameta ta dawo ta dawo.
Maa sakinah na tafiya Asim da leylah suka fara gajiya da matsuwan kiran Ammi wadda tace zata kirasu su taho idan ta gama hada musu komai amma shiru ba kowane kiran,
Leylah gajiya tayi ta cire kunya ta kira Mummynta tayi mata maganar tafiyarsu honeymoon din amma zuhrah ta shareta sbd bazata iya yiwa ayanah maganar ba kuma koyaushe suna waya.
Asim daya kasa hakura kuma bazai iya cigaba da jira ba fara shirya musu tafiyar yayi da kansa kai tsaye,
Koda haile taji tafiyar da suke kokarin yi din bata damu ba bari tayi suje su yawota duniyar su dawo tukuna ta dorasa daga inda ta tsaya dan haka da kanta ta tayasu shirin tafiyar ta hanyar fara yiwa leylah sabbin shirye shiryen gyara da tsimawa da gyaran fata.
Biye mata kawai sukai akan gyaran muradi dai su samu su tafi subar boyem,
A lokacinda Maa sakinah ta koma Uk cikin mamaki ta tadda Ayanah na fama da mura me karfin gaske data kaita har kwanciya asibiti kuma basu fadawa kowaba suka boye shiyasa ma bahar da hankalinta ya tashi sosai ta takurawa Maa din ta dawo sbd ganin ayanah a asibiti ya tada hankalinta sosai ta shiga tsoro sosai.
Ciwon nata ne ya hana sam ta tada maganar zuwansu leylah honeymoon din datai alkawari saita warke,
Zuhrah ma bata saniba sbd tana kokarin waya da ita dan kada ta gane.
Sultan da NUAB kuwa kwata kwata a kwana biyun dena waya tayi dasu wanda take hakan ya sakawa sultan tinanin ba lafiya ba.
Tenya ya kira personally ya tambayeta abinda yake faruwa ta sanar dashi suna asibiti da Ayanah har lokacin sbd kaman sanyi ne ya shigeta sosai amma tafara jin sauki.
Shiru yayi kafin ya kashe wayar kawai ya ajiyeta gefensa tsawon mintina masu dan tsayi kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayar ya saka kiran kadir.
Kadir na dauka cikin nutsuwa ya sanar masa ayi masa shirin tafiya uk a kwanakin da bazasu wuce sati daya ba.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee
117
Kadir amsawa yayi da tabbacin cika umarnin dan haka yana kashe wayar ya saka kiran hada tafiyar shima,
A daidai wannan lokacin Shima Sultan LEUL me boyem shirin barin qasar yakeyi zuwa Moscow sbd wani babban business meeting da zaiyi da manyan business tycoons dinsa da suka jima suna son ganinsa ba dama sbd sarautar daya tsaya daidaitawa dan haka a yanxu ya basu damar ganinsa zasu hadu a Moscow suyi meeting din dan bazai hade GHAZ business dinsa ba da sarauta dan haka a karan farko bayan hawansa mulki zai bar qasar boyem yayi tafiya zuwa wata qasar dan haka keela ne wakilinsa da zaa bari da sauran manyan masarautar da zasu kula da komai kafin dawowansa.
Koda labarin tafiyar Sultan LEUL zuwa Moscow ya riski Sultan yasar jin yayi ya samu wata nutsuwa da kwanciyan hankalin tafiyarsa a natse duk daman NUAB kome zai zama a rayuwa bazai iya hanasa duk abinda yayi niya ba kawai dai ya zauna ne a bisa umarnin nasa sbd bayyanarda zaman lafiya a idon duniya a tsakaninsa da 'dansa tare kuma da hanasu samun hayaniya a wannan lokacinda NUAB din yake buqatar tattara hankali da nutsuwansa akan abinda yake gabansa na daidaita mulki tareda kuma bawa ayanah cikakken hutun dataje yi kafin ya isa gareta amma a yanzu dayaji batada lfy babu abinda zai hana isarsa gareta bayan mutuwarsa amma jin tafiyar da NUAB zaiyi saita sake basa nutsuwa dan yasan a yanda ya dade baya Moscow to zai kwana biyu sosai acan kafin dawowansa.
Ko kwana biyar baayiba da maganar ta isa ga sultan yasar tawagar Mai girma Sultan LEUL NUAB ta daga zuwa Russia wanda yana barin qasar boyem masarautar ta sake tsit sbd ba wata mulki kuma sai me qasar ya dawo.
Ita kanta haile suna jin fitar Sultan NUAB daga masarautar ajiyan zuciya suka sauke itada yayanta a tare suna fatar har abada kada ya dawo ya hadu da ajalinsa acan.
Asim ma numfashi da ajiyan zuciyar farin ciki ya sauke yana jin kamar an sauke masa wani mummunan nauyi sbd a yanzu kam zaiyi tafiyarsa a saa da farin ciki NUAB da shegunsa basa boyem hakama basa uk suna wata qasar da fitowansa ba yanzu ba dan haka ya sake bada qaimi a gurin ganin tafiyansu ta kammalu,
Ita kanta leylah tinda taga NUAB yayi tafiya gabaki daya ta tada hankalinta akan suyi su isa uk dan ganin takeyi kamar zai iya wucewa can ba Moscow din ba gwara su isa su samu bahar kafin ya isa ya ganta ta sauya ya iya sauya tinaninsa akanta.
Yanda ta takurawa Asim din akan tafiyar har fada sukai sosai yayi mata gorin marasa zuciya akan namiji itama tai masa gorin maye akan mace ba dadi dai suka rabu a daren sai kuma gashi da safe sun shirya kaman basuyi yar gorinba a daren sukaci gaba da shirinsu na tafiya.
Tafiyar NUAB da kwana biyu jirgin sultan yasar shima ya daga zuwa uk wanda ya saka Haile kusan mutuwa sbd baqin ciki da mamaki me girma sbd ta gama shirinta tsaf akansa shima na kaudasa 'dansa NUAB da ayanah basa nan daga ita sai yayanta a masarautar sbd yanzu baima sa imebēti ko daya daman tin daga kan ayanah bai qara dauka ba wainda suka rage guda biyu suma ya sallamesu kwanakin da NUAB ya fidda sabon tsari daman an dade da shafe tarihinsu basada amfani ko daya zaman kadaici da jin dadi kawai sukeyi.
Maraki ma koda sakon Sultan na tafiyar ya sameta a wayarta kasa dauke idanuwanta daga kan sakon tayi tayi shiru zuciyarta na qullewa da baqin cikin da shine zai zama ajalinta tin na shekarun quruciya datake kwasa haryanzu bata dena kwasa ba,