← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 112

Sashe 106

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko Aleey hutawa sukai abinsu hankali kwance da jiran ranar tafiya tazo musamman komai na wucewansu Moscow daga can daya gama musu shirin komai kaman yanda LEUL ya bada umarni.

Shi kansa Asim hutu yake buqata sosai dan haka shima babu wanda ya sake ganinsa nysah ma da zasu wuce sedai suka zo bangarensa cikin basa girman matsayinsa da ayanzu ganinsa ma sai ansanar masa sukai masa bankwana yayiwa yayanta kyautar zinari me kyau ya bada motoci daga bangarensa aka kaisu har airport.

Bayan ya samu damar hutawa dakyau komai ya fara tafiya daidai likitocin da zasu fara duba matarsa da cikinsa akai akai a matsayin antenatal ya nema dan su fara bi masa lafiyan babynsa ana kiyaye girmansa cikin koshin lafiya har zuwa lokacin haihuwansa.

Leylah farin cikinta haka kawai take jinsa,kome take a yanxu farin ciki takeji batajin damuwan komai ko shakka bare fargaba sbd babu abinda a yanxu ubangijinta bai bata ba bayan jiran haihuwa lafiya musamman yanda Asim yake bayyanarda soyayyarsa me tsafta akanta da cikinsa dake jikinta.

******Acan Anjom suma hankalinsu a kwance yake da sabuwar rayuwar da kusan kowa ayanzu ya samu,

Sultan yana samun sauki sosai sosai sbd likitocin dake bibiyan lafiyarsa cikin kwarewa da kulawa,

Ita kanta Ammi wata irin kulawa take basa dakyau kaman qaramin yaro gashi anan babu kowace takurawa ko rashin sakewan tarin bayi da jamaar masarauta hankali kwance suke rayuwa ba kowane shamaki ko kiyayewa kauna ce a bayyane da soyayya me zafi da basumasan suna bayyanawa ba,

Su maa sakinah sosai suke tayata bayyanawa da bawa sultan dukkanin kulawanta da soyayyarta dan hakanne ma yake samun saukin sosai sosai sbd har takawa yafara yi da kansa sedai da yar sanda me kyau da aka tanadar masa hakama a cikin bedroom dinsa zuwa palo da bathroom da dining duka yana iya tafiya zuwa da kansa batareda komai ko sandar ba idan zai fito ne gurin jamaar gari da mutanen fadar masarautar anjom din daya sake musu sosai da kulawa zaman majalisa sukeyi suyi firarsu sosai da labaran tarihin anjom dayake duk sun manyanta kamansa dan haka suka zama abokan firarsa tinda bawai zuba mulkin akeyiba kawai rayuwar kwanciyan hankali da nutsuwa tareda kaicewa daga hayaniya da nauyin mulki da sarauta ya sakasu dawowa nan dan haka anan din ma bawai mulkin zasuyiba kawai dai duk wani abin dazai taso dayake buqatan mulkin sarauta zasuyi fuskancesa aji dashi a wuce gurin batareda ana zaman fada ba irin sosai tinda Ayanah ce a matsayin me mulkin Anjom din shi kuwa bazai iya barinta daukan wannan nauyinba zai tayata ji da komai a cikin nutsuwa da sanyi ba hayaniyar mulki tinda an zuba hukumomin zartar da hukunci da adalci wa kowa a garin hakan ya dauke nauyi sosai na sarautar anjom din.

A bangare daya tattali da kulawa sukeyi wa Bahar da cikinta sosai musamman da tafiya zatai daga hannunsu ta tafi gidan miji sai kuma haihuwa idan ya aminta da barinta dawowa haihuwan kenan.

Ita kanta Bahar din tinda Amminta ta dawo ta warware sosai ta koma kaman ba ita dinba laulayin duka ya saketa lafiya kalau take jinta kaman batada komai duk da masifar son cikinta takeyi kaman yanda kowa yakesonsa sbd tana son ganin jininta dana NUAB hakama jinin da shine kadai yake nata jinin na asali wanda take fatan yaxo lafiya ya rayu lafiya.

Maa sakinah ma hakanan take jin jikinta na sanyi itama kuma a kwanakin sbd kwanakin auren da suketa qarasa tahowa tanajin kaman ba ita din bace zatai auren data gama fidda rai da tsammanin yinsa tin a kuruciya ta cire rai kuma Allah bai bata iko da damar ba sai ayanzu data manyanta dan haka sai tana jin fargaba ma dayin auren da tsoro.

Ga Kadir haryanzu basu taba kebewa sunyi ko gaisuwa ba sedai su gaisa a cikin mutane kaman koyaushe batareda ta iya kallansa ba dan jin takeyi kaman bazata iyaba.

Maleketenya kuwa ba abinda ya dameta shirin Amare takeyi back to back har saida ana saura kwana uku cif bikin ta gama komai datake musu tsaf daga nan aka fara shirin gagaruman walimar da zaayi ta Bahar da Maa din amma dai ita maa bata cikin kowane shiri na amare Bahar ce kawai akaiwa shirin Amaren Ghaz a ranar da zaayi walimar kenan.

Dukkanin masu ado da kwalliyan dazasu shirya bahar daga Boyem aka daukosu musamman hakama kusan garin anjom a cike yake da 'yan jarida da media da baqi da qarin tsaro tako ina a hakan ma cikin mai boyem bai isoba sbd a wannan karan duniya tasan bikin aurensa akeyi hakama ansan yana tafe anjom kowane lokaci.

Leylah data matsu ta isa Anjom din jin tayi kaman ta riga su Asim din isa sbd su saima daren ranar zasu isa Amma sam yaqi barinta tafiyar dan baiga abinda zai sakasa barinta tafiya ita dayaba da ciki a jikinta duk da yasan tareda tsaro zata isa amma bayajin nutsuwar hakan gwara kawai ta jira su isa tare.

*******Baccin Safen data saba A ranar walimar wadda daga ita sai daurin auren gobe shi takeyi hankali kwance abinta su kuwa masu shirinta suna babban dakin da aka ware dan shirinta acan sun jere komai tinda safe suna jiran ta gama baccinta koda kuwa ze kai rana ko wuce nan ma to zasu jira sai tagama ta tashi tukuna ayi mata komai sbd asalin ikon da a yanzu itace zata ringa bugasa a qasar boyem kaf da sbd a yanzu datake Queen Bahar mata guda daya tak ga Sultan NUAB ALMAZZ itace macen datafi kowace mace daraja a boyem din da kewayenta sbd matsayinta,

Sbd kasancewanta a anjom yanxu da kowa yasani ana fara bikin ya saka ba iya daga boyem ba masarautu da dama sun aiko gudunmawar bada tsaronsu ga Anjom da tarin dukiya mai yawa da bayi masu yawa tako ina wanda ya saka gabaki daya garin ya sake rikicewa da harkar mulki da dukiya kawai tareda arziki.

Tin ana saura kwana uku da bikin babu wanda ya sake saka bahar a idanuwansa sbd hana kowane ido sauka akanta da cikinta sbd sauyawanta gabaki daya zai saka duk wanda ya dora idanuwansa akanta ya kasa daukewa hakama ta shiga matakin da babu wanda zai sake dora idanuwansa akanta sbd zamanta cikakkiyar matar Sultan me boyem a duniya yanzu dan haka kallanta ya zama kusan haramun ga kowa bayan shi sai dolenta maana iyayenta dana mijinta sai kuma bayinta na kusa da ita sosai masu hidimarta wainda suke wainda Amminta ta zabesu tin yanzu su naimah ne tin na baya.

Ayau din da wani irin yanayi me wuyan fassarawa ta tashi musamman da Ammi itama tin jiya take jin sanyin jiki sbd rabuwa da Bahar din shikenan kuma sai dai ziyara,
Hatta maa sakinah sanyi jikinta yayi na rabuwa da bahar tinda ita da Ayanah suna tare zasu qarasa rayuwa tare insha Allah tinda duk inda mazajensu suke basu taba rabuwaba suna tare.

Kafafunta ta ziro qasa tana miqewa tsaye tashinta bacci kenan karfe goma da rabi harma da mintina.

Wayarta tafara juyawa ta kalla a natse tana sauke numfashi me hade da ajiyan zuciya me sanyi sbd yau kwanansu uku kenan cif basuyi magana da juna ba sbd zuciyarsa data kasa riqe jinta batareda yana ganinta a gabansa ba kuntar da duka kwanciyan hankali da nutsuwansa hakan yakeyi dan haka suka dena waya kwata kwata sedai text wanda shima sai so daya a wuni ranar gobe yake jira ranar da zai kalleta a zahirance ya karbeta a matsayin matar daya karba kenan har abada sai mutuwa ta riga ta shiga hannunsa da gidansa kenan.

Bathroom ta nufa tana zare rigar sama ta kan kayan baccinta tana isa ta shige tana rufo kofar.

Brush tayi tana gamawa ta qarasa zare komai nata ta isa ga ruwan wankanta da baa jima da hadawaba ta farka ta saka kafafunta ta shige ahankali tana rufe idanuwanta sbd wani dumi da qamshi da suka ratsata lokaci daya.

Ta jima sosai tana wankan kafin ta fito daure da towel me dan girma a jikinta tana goge gashinta da wani ta iso gaban mirror ta zauna tana kallan kanta tana goge jikinta cikin sanyi da nutswa tana jin kowace gabar jikinta na fidda wani sirrin qamshin daya kama fatarta dakyau dakyau.

Shiryawa tayi tana saka wata doguwan riga mara nauyi ta yafo mayafi mara nauyi shima ta fito ta nufi dakin Ammi wadda taketa waya da mutanenta dake mutunci sosai da hulda dasu wainda suka hadu a nadin sarautar 'danta kuma suke shige mata sosai a yanzu kowa hulda yakeson yayi da ita sbd ya samu shiga gurinta dan matsayinta.

Mutane da yawa ta gayyata kuma a ranar suketa sauka a qasar suna isowa anjom da securities dinsu cikin farin cikin kasancewa a gurin hidimar bikin auren Sultan LEUL NUAB.

Ammi na gama waya kallanta tayi tana cewa

'Kiyi breakfast ki tafi masu shirinki suna jira sbd zaa dauki time kafin gamawa gashi mutane nata isowa kuma Kinsan ba wanda zai iya ganinki'

Dan lafewa tayi gefen Ammin tana jin itama kaman bazata iya barin Ammin ba shikenan gwara a yanzu suke yanzu yafi mata tana gaban Amminta shima yana matsayin mijinta din tafison hakan.

Maa tenya ce ta shigo ta kawo mata abinci da kanta tana zaunawa gefe ta tafara bude mata komai tana cewa taci ta shanye maganin dayake cup gashinan ta ajiye mata.

Miqewa tayi ta fice sbd tanada ayyuka da yawa a gaban,

Tana fita maa sakinah wadda itama gyara ya saka ta sauya gabaki daya ta koma tamkar ba itaba ta qara wani irin haske sosai tayi fresh tana daukan ido ta iso ta zauna gefenta tana waya da mahaifiyar Haile data kira tana mata Allah ya sanya alkhairi da fatar zaman lafiya da farin ciki me dorewa har mutuwa.
#MAMUH
09033181070
[19/01, 1:46 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

180
Abincin taci a natse da kwanciyan hankali tana dan duba chats dinta datake yi da Neesah wadda ta isa boyem din da asubar yau jirginsu ya sauka Aleey ne yaje da kansa ya daukota ya kawota gurin leylah kafin su tashi wucewa a gobe da ita zasu iso.
Chapter 106 · 0% Book details