← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 112

Sashe 55

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata tafi koinaba tana nan tareda NUAB ashe' maa sakinah ta fada batareda bawa zancen mahimmancin da leylan zata fahimta ba tana cigaba da kokarin aikin data shigo yi na hadawa Bahar lafiyayyan dahuwan nama da madara me zafin gaske da zataiwa hadi me kyau dazai taimakawa abinda ya sameta mai tsananin kyau da karfi.

Saka hannu Leylah tayi a aikin batareda tasan na bahar bane sbd kawai tanason jin magana a bakin maa sakinah a cikin dubara dan tabbatarda shin acan bahar din ta kwana kokuwa a tsakar dare ta koma dakinta hakama duk tinaninta tinda NUAB a gidan ya kwana to shine zaawa breakfast din da wuri wuri haka dan haka ta sake zaqewa tana aikin tana jeho tambayoyin da babu wanda ta samu amsa me amfani daga gurin maa din.

**Shi kuwa a lokacin daya fito already Aleey ya fito cikin kayan sanyi shima na jiias ya shiga mota harma ya tada ita ta kalli gate dan haka NUAB din na fitowa motar kawai ya fada aka wangale musu gate sika fice batareda doguwan hayaniyan da NUAB baya so ba,

Kai tsaye gurin wani qwararran likita suka nufa wanda yana duba NUAB din dole ya saka masa ruwa tareda allurai masu karfi sbd wasu boma boman zafi ne na karfin shaawansa daya kasa sake mata sbd kasa tantance kansa ma dayayi zuwa ga karfin lamarin suka ringa buga jininsa wannan zazzabin ya rufesa dan karansa na farko ne.

A cikin asibitin aka daura masa ruwan a floor din karshe wanda kuma aka hana kowa isa floor din a lokacin har sai yabar asibitin tukuna.

Aleey kuwa kasawa yayi ya tsare musamman ganin wani bacci me dan karfi ya dauki NUAB din wanda hankalinsa ya rabu gida biyu tinda ya baro amma kuma bayajin zai iya barin ko mace likita ta duba masa ita a wannan yanayin datake bare namiji dan haka ya zabi wainda suke iyayenta su mata musamman maa sakinah da a baya ya lura wanka ma kaman tayata wanke kai takeyi dan haka sune kadai wainda zuciyarsa ta nutsu dasu.

****Maa tenya wata irin gashi da magani masu karfin gaske data hada na abubuwa take ta ringa mata wainda suka ringa farfado da bahar din cikin matsananciyar azaha suna sake sumar da ita tana son tayi kuka me karfi amma ko karfin kukan babu sedai jikinta ya ringa wani irin bari tana qamewa tana ficewa hayyacinta,

Kusan awa biyu da rabi suka bata a toilet din tana mata abu daban daban har suka kammala ta samu dawowan hayyacinta kadan tayi wanka suka fito ta taimaka mata ta saka doguwan rigar bacci me karfi sosai ta saka kayan sallah duk da taimakon Maa din tukuna tai sallah a zaune daqyar,

Tana gamawa maa sakinah ta kawo mata instant charcoal data buqaci a kunno mata taka ta zuba masa magani shima ta saka bahar din dake kuka sosai a kai tana rawar jiki tana qanqamewa kaman zata shige ko gani sosai batayi sbd kumburan idanuwanta da fuskarta.

Kasa kalla maa sakinah tayi ta juya ta fice zuciyarta na sake shiga damuwa.

Bayan ta gasa mata gurin da kyau da wuya tukuna tenya ta kaita ta kwantar da ita sbd jikinta dake tsananta fizga da zazzabi me karfi.

Madaran da aka dafa aka kawo mata wannan karan da leylah data biyo maa din ake tana sako kai idanuwanta akan zanin gadon dake yashe a tsakiyar dakin suka fara sauka take kayan hannunta suka subuce mata tenya tayi saurin tareda tana kallanta sedai leylan ta gama ficewa hayyacinta idanuwanta kafe akan bahar kafin ta juya idanuwanta ta kalli wutar da aka gama gasa bahar din take ba wata wata ta fahimci meya faru jiri ya rufe idanuwanta sbd zuciyarta data ke dena bugawa ahankali.

Saurin ajiye kayan hannunta tenya tayi tana tareta da saurin ta zaunar da ita kujera kafin tayi magana wani amai na mummunan tashin hankali ya tasowa Leylahn ta miqe tana ficewa daga sauri tayi dakin Ammi ta fada toilet sedai aman baya iya fitowa ma sbd tsananin tashin hankali da rawar da jikinta yakeyi.

Fitowa tayi toilet din hannuwanta na wata irin rawa da kakkarwa ta dauki wayarta tana saka kiran Asim sbd tasan mutuwa ma kila zatai gwara ta fada masa tin kafin ta mutu yasan abinda ya faru a daren yau da duniyarta ita dai ta tsaya cak numfashinta sarkewa yakeyi kishi yana neman kasheta ido rufe.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:58 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

128
Rawa hannuwanta keyi wayar na kasa zama daidai a hannunta sbd tsantsar tashin hankalin datake ji ga idanuwanta basa gani sosai sbd wasu zafafan hawaye da suka cikesu,

Subucewa wayar tayi qasa ta fadi itama ta zame qasan tai zaman dabas tareda fashewa da wani irin kuka me tsananin ciwo da tarin baqin ciki har lokacin rawa hannuwanta keyi sosai.

Kukan takeyi sosai tana rufe bakinta da tafukan hannuwanta biyu sbd kada a jiyota dan batasan kukan me zata ce tana yi ba,

Sosai take kukan tana qarawa ta daga hannuwanta biyu ta dora a tsakiyar kanta ta kaman ance mata yunar da zuhrah sun mutu ta ringa rerowa.

Lokaci me dan tsayi ta dauka tana rusa kukan da ko sautinsa batada ikon fitarwa bare bayyannar da baqin cikinta ko fadarsa dan haka ya kasance kukan kurame a wahale tayisa harta gama ta miqe kafafunta na kasa daukanta dika daidai ta nufi toilet ta fada sbd so takeyi tayi waya da Asim da gaggawa,

Tana shiga fuskarta takeson wankewa amma sai data sake tsayawa gaban madubi ta kalli fuskarta ta sake fasa sabon kuka me sauti dan a toilet ba wanda zaijita kuma ta kunna ruwa dan haka sake murya tayi tai kukanta me isarta tukuna ta wanke fuskarta har zata fito ta daure ta dakata tayi wankanta gabaki daya tukuna ta fito.

Tana fitowa bata iya shiri yanda ta saba ba doguwan riga kawai ta saka ta zauna kan sofa tareda sake daukan wayarta ta saka kiran Asim wanda yake kwance yana bacci sosai.

Yankewan wayar tayi be dauka ba ta sake saka kiran harta yanke bai dagaba dan haka bata tsaya ba taci gaba da danna masa kira baqin cikinta na komawa takaici tayita kiran tana jin babu gantalalle kamansa.

Ganin bai dauka ba ya sakata sake fusata tana kasa hakura dan wlh saita fada masa sbd shima ya shiga mugun baqin ciki ya kuma ji tiririn da zuciyarta ke ji shima.

Ganin baida niyar dauka ya sakata zarar gyalenta qarami ta nada a kanta ta fice batareda ma kowa yasan fitar tata ba,

Tana fitowa harabar gidan taga securities ga mamakinta sai suka barta ta fita ba takurawa sbd su a gurinsu Bahar ce dasu Ammi basada ikon fita koina sai ance su barsu su fita dan haka ita har gaidata sukai cikin girmama batareda sakin fuska ba dan fuskarsu batada sakewa ko kadan kuma a ko yaushe hakan suke.

Tana fitowa taxi na kawowa ta tareta kai tsaye ta fada tabar gurin zuwa masaukinsu.

Tin kafin ta isa take cigaba da kiran daga karshe ganin ya tabbata sakarai ya sakata nemo numbern Shuraim ta saka kiransa dan shima a masauki daya ya sauka dasu duk da ba floor daya suke ba.

Kira daya ta yanke shima bai dauka ba ta sake tsoki tana cigaba da kiransa yaqi dauka shima dan haka kashe wayarta ma tayi gabaki daya tana jin kaman zatai bingida ta fashe tsabar baqin ciki goma da ashirin wani akan wani.

Tafiyar mintina masu dan dama sukai kafin suka isa driver na parking ta fito tai scanning ta biya ta juya zuwa ciki idanuwanta jajir a rufe da masifa.

Lift ta hau tana jin kaman dana sanin kwana a can gidan sbd shedar da abinda gashina nan zai kashe ta,
Gwara ace bata saniba bata gani ba da zuciyarta zata cigaba da bata tabbacin babu abinda ya faru tsakaninsu duk da ko a yanzu tana tabbatarda bawai samun Bahar kaiwa ga shimfidarsa na nufin yana sonta bane ko yadda da ita a matsayin queen tasa dan kila ma sauke buqatarsa kawai yayi akanta dan samun gamsuwa shikenan.

Tana isa dakinsu buga kofar tayi batareda kakkautawaba duk da baa hayaniya a gurin amma bazata iyaba gabaki dayama ta fice hayyacinta so kawai takeyi ta dasawa Asim baqin ciki shima dan haka ta sake buga kofar tana qin tsayawa.

Cikin baccinsa me nisa ya jiyo buga kofar daga qurya dayake dan haka ya bude idanuwansa masu dan kyau da suka ciga da bacci yana yaye lallausan bargon dake jikinsa ya ziro kafafunsa yana miqewa tsaye ya nufi kofar ransa na baci da hakan dan kuwa qaida ne baa buga kofar dakunan duk gurin daya kasance babba irin haka sbd bame kudin dayake son hayaniya.

Yana isa kofar a fusace ya bude sai kawai yaga Leylah wadda ta turesa ta shigo ciki idanuwanta jajir,

Shima rufe kofar yayi yana biyota ciki yana binta da kallo zaiyi magana ta katsesa da cewa

'Daman bacci kazo yi kenan a qasar batareda samun abinda ya kawoka ba,
Nayi dana sanin aurenka harma na iya biye maka akan zaka samar mana abinda dukanmu muke so gashinan komai ya lalace mun kana nan kana baccin Asara sbd dani kadai nake kokarina da yanzu ban shedar da wannan mummunar ranar ba....

Hawaye ne suka gangaro mata ta share da karfi tana kallansa tace

'Idan har kana kan bakarka akan Bahar to ka shiryawa auren bazawarar da dan uwanka ya gama maidawa cikakkiyar mace,
Ayau dan uwanka ya cika sunnar aurensa dayake kanta wanda hakan ya haramta maka ita har abada matiqar NUAB yana raye koya saketa bakada ikon aurenta...

Wani kallan batada hankali ta haukace yake mata cikin takaicin zancenta yace

'Are you high on something??
Nace are you high or wat??
Me kike fada?
Kada ki sake fadamun wannan zancen kisan me zaki fadamun idan kanki da zuciyarki nada matsala sbd akwai abinda bazan iya dauka ba so better be very very careful'
Chapter 55 · 0% Book details