← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 112

Sashe 7

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Auren yar YUNAR ga NUAB yana nufin zai tsaya masa a gurin karban mulkin BOYEM,
YUNAR zai zabi tsayawa duk Wanda ya zama Siriknsa a cikin magadan biyu,
Tayaya zai zabi NUAB ‘dan mistress Akan ASIM Wanda a bayyane da duniya shine dan dayafi da’a da kwantarwa manya kai,
ASIM shine Wanda ya cancanta ya bawa aurar yarsa,
ASIM ne ya kamata ya zabi tsayawa Akan karban mulkin BOYEM me zaisa ya zabi dan ta’adda?
Baisan halinsa da rayuwar da yakeyi ba Wanda yana buqatar sani dan kuwa Mamee muna tsananin buqatar ‘yar YUNAR ta kasance Matar ASIM ba NUAB ba,
Mame kota halin yaya kada ki bari dan Allah NUAB ya samu Leylah YUNAR a matsayin mata idan ba ASIM ba sbd aurensa da ‘yar nada kashi casain na alaman nasara Akan ASIM mame dan Allah kada ki bar hakan ta faru…..’

Yanda take maganar cikin tashin hankali da mummunan baqin cikin daya danne zuciyarta kaman zatai bindiga ta buga ya saka meryam ma hankalinta tsananta tashi da Wani irin zallar tsoro da zullumin daya saka idanuwanta jajir dan kuwa faduwar ASIM yana nufin tasu faduwar a abinda suke tsananin so tamkar mutuwa.

HAILE da zuciya ta gama cinyeta Wani zazzafan radadi zuciyarta ke yi dan kuwa idan ma adalci zaayi ASIM dinne ya fara zuwa duniya dan haka shine ya kamata a fara bawa macen a daura masa aure kafin daga baya Ayi maganar NUAB Wanda batajin ma yanada niyar auren a rayuwarsa dan kuwa ta’addancinsa kadai ya sakawa gaba,
Tayaya sultan zai mata wannnan mummunan cin fuskar a Idon duniya ya zabi fara yiwa dan mistress dinsa aure Akan ‘dan sunnarsa,
Tayaya zata iya barin YUNAR ya tsayawa NUAB ba danta ba?
Tayaya zasu iya barin NUAB ya samu wannnan saar ta auren ‘yar YUNAR Bayan ga ASIM dinta….

Jajir idanuwanta sukai Wanda tsananin ja da baqin cikin dayake cike dasu da jini da zuciyarta idanuwanta har wasu ruwan da ba hawaye ba suka tara,

Shigowan ASIM din Wanda tamkar jininsa zai Kama da wuta hannuwansa har wani rawa sukeyi ya sakasu kallansa su dukan kowa idanuwansa na tsananta ja sbd suna ganin tsantsan fushinsa da bacin ransa tareda baqin cikinsa a bayyane kenan shima ya samu labarin,

Zaunawa yayi a kujera yana kasa bude baki sbd fushinsa yayi yawan da bazai iya magana kai tsaye ba,

Shiru sukai dukkaninsu kowa da baqin cikin dayake cinsa,

Sai Bayan mintina masu tsayin gaske ya bude Baki cikin radadi me bayyana yace

‘Ko zan rasa rayuwata bazan Bari NUAB ya shiga tsakanina da abinda nakeso ba,
Akanta na shirya bayyanannan yaqi dashi da mahaifinsa sbd shine yake tsayawa haukar NUAB din kowace iri dan haka wannan Karan mutuwa ce kadai zata rabani da ita’

HAILE da kalaman sukai mata Wani irin dadi da Jin sassauci tace

‘Ko ni bazan taba barin ya sameta ba koda hakan na nufin aikata kowane irin aiki saina tabbatarda sun rabu rabuwa da har abada’

Aslam ma Jin tayi sanyi na samun sassauci na dan ratsata ta kalli ASIM din tanajin nutsuwar daya kasance yana son Leylah din dan sun dauka bazai sota ba bazai kishin kasa samunta ba dan haka dukkaninsu suka Ji sun dan samu relief na zasu Hana auren da dalili me karfin gaske.

********kai tsaye bangarensa ya nufa da ita bata ma ganin gabanta sbd yanda yake riqe da hannunta datake Jin azabar riqon da yayi mata amma idanuwanta da zuciyarta sun rufe da ‘dacin da harma bata Jin komai dan haka bata bude idanuwanta sai lokacin da taji ya saki hannunta da karfi tayi baya idanuwanta na budewa jajir itama sbd har cikin ranta bata kaunar ganinsa dan ganinsa ba mummunan auren dayake tsakaninsu tinawa ba hadda rasuwar mahaifinta dan haka kokarin sake rintse idanuwanta takeyi cikeda baqin cikin kasancewa tareda shi…….

Saukar hannunsa Akan rigar dake jikinta ya fizgo da karfin gaske yana rabata biyu daga jikinta ya sakata bude idanuwanta masu girman gaske da kyau sunyi ja ta sauke akansa tana riqe hannunsa da karfin gaske tareda bude baki a Karan farko muryanta ya sauka kunnunesa da tsananin fushi tana kallan cikin tsakiyar idanuwansa da kowa baya iya kalla tace

‘Ābidehali?¿

Jajayen idanuwansa ya dago da Wani irin tsananin Zafi da fushi tareda bacin ran gaske ya kalli bakinta daya furta kalmar da duk duniya babu Wanda ya taba furta masa hatta uwa da ubansa kuwa kaf duniyarsa babu Wanda ya taba kallan fuskarsa ya furta masa wannan kalman da zata iya ajalin dik Wanda ya furtata,

Yana da hankali take tambayarsa????
Shi LEUL take tambayar yanada hankali???
Menene hankali?
Batasan koda Yazo duniya baida hankali ba?
Batasan baisan menene hankalin ba?
Ina ta samu zarrar yi masa wannan kalmar?

Qarasa fizge rigar yayi cikin wani irin sabon rashin hankalin dayaji yana shigarsa data ambata sbd Allah ne kadai yasan yanda ya danni mahaukaciyar zuciyar tasa bai yaga Kayan jikin nata tin acan ba.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

77
Dago idanuwanta tayi da suka tsananta Wani irin Jan da hawaye masu tsananin radadi suna cikowa a cikinsu ta kallesa hannuwanta na kare jikinta duk da akwai wata qaramar halfvest din a cikinsu,

Ayau ta fuskanci tozarci da baqin cikin da bazata taba mantawa ba daga Wanda batajin har abada zata manta,

Wani mummunan baqin ciki ta Hadiye ta bude baki zatai magana ya juya ya bar gurin har lokacin hannuwansa har wani rawa sukeyi yana isa kofa ya fice tareda rufe kofar da karfin gaske daya sakata rintse idanuwanta tana silalewa qasa ahankali wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta.

Su aleey dake palo a tsatsaye babu Wanda ya dago kai a cikinsu kowa Kansa sake yin qasa yayi daya fito din tamkar guguwan wuta zata tashi haka fuskarsa tayi Wani ja ya fice daga palon suka biyo bayansa,

Suna fitowa kallan securities din aleey yayi yace su tsaya su tsare bangaren tinda princess din GHAZ tana ciki.

Komawa sukai bakin kofar shiga ta farko data shiga palon suka tsare shi kuma aleey yabi Bayan NUAB din zuwa gurin kiran Amminsa da shine ya fiddosa tin farko.

Tin kafin su isa aleey a fidda wayar sa ya Turawa Maa sakina sakon taje bangaren NUAB Princess din GHAZ tana can.

Maa sakinah dake Zaune tana kallan time a agogon wayarta na rashin dawowan Bahar har lokacin zuciyarta cikin wani zullumi da rashin sukuni take dan haka miqewa tayi tana nufar dakin bayin bangaren dake Bayan kitchen dinsu dan dubowa.

Tana shiga kitchen zata bi ta kofar kitchen din zuwa dakin nasu sakon aleey ya shigo wayarta tana dubawa kirjinta yayi Wani dummm Wani sabon zullumin da fargaban idan ba Wani abin ne ya samu Bahar din ba dan haka dawowa tayi tana fitowa daga kitchen shi kuma NUAB a lokacin ya shigo harya saka kai a palon farko ya shige dan haka basu hadu ba ita kuma kofa ta nufa kai tsaye ta fice,

Aleey dayake kofar gurin ta hadu dashi baice mata komaiba sbd baya magana ko wace iri idan baisan Meye a zuciyar LEUL dinsa ba dan haka kai tsaye bata tsaya ba itama sanin bazai taba fadar komai ba batareda izini ko umarnin NUAB ba dan haka cikin wani sanyin jiki da kafafu ta nufi bangaren nasa dan dubo meya samu Bahar dinta.

Ko daya isa securities da suka San matsayinta a gurin maigidansu dama Bahar din basu hanata ba kai tsaye bude mata kofa sukai da girmamawa me girma ta shige.

Tana shiga babban lafiyayyan palon nasa dayake tsit komai na palon tsarin rayuwarsa ce ta Russia da taste dinsa,
Qamshinsa ne koina yake cike da niimar iskar da kake shaqa dan babu abinda bai gama kamuwa da tsadadden qamshinsa ba da baa jinsa a gurin kowa,

Kallan koina tayi tana rasa ina ma zata ga Bahar din dan haka kai tsaye bude muryanta tayi ta Ambaci sunan Bahar din wadda sautin muryan Maa din na shiga kunnenta ta fasa wani kuka Mara sauti a hankali sbd bazata iya fitowa ba babu Riga a jikinta.

Sake kiran sunanta Maa tayi tana tinkarar dakin datasan ba shine na NUAB ba dan nasa dakin sam idan bame gyaransa ba babu me shiga shima Wanda yake gyaran a cikin Yaransa ne babu bawa ko daya dasuka yadda dashi Akan komai na maigidansu dan haka sune securities sune kuma bayinsa ba wata dama ko yar qanqanin da kowa yakeda ita ta iya cutatar dashi sbd sun tare tako Ina rayuwarsa da tasu rayuwar.

Maa sakinah na isa dakin kai tsaye murdawa tayi ta bude idanuwanta suka sauka kan Bahar din wadda take durqushe a qasa ta rufe jikinta da tafin hannuwanta.

Faduwa gaban Maa yayi da karfin gaske har kafafunta na rawa ta ta iso gurinta da sauri tana isowa ta janyota jikinta ta rungume da karfi tana Jin faduwan gabanta na tsananta tace

‘Bahar meya sameki?
Meya faru na ganki hakan?
Ya akai?

Lafewa jikin Maa din tayi tana fasa sabon kuka tareda qanqameta tana bude baki tace

‘Inason barin nan Maa,Inason komawa ANJOM maa.’

Saurin sake rungumeta Maa tayi tana Jin zuciyarta na sosuwa da abinda ya faru koma menene,

Bata taba Jin zata tirsasa Bahar a zuciya da rayuwar NUAB ba sbd dukkaninsu babu Wanda zata iya yiwa dole Akan dan uwansa,
Bahar amanarta ce da Abaas ya damqa a hannuwanta data karba zata riqe da rayuwarta da karfinta harsai rayuwarta tabar jikinta,

Dukkanin soyayya da kaunar datake wa Ayanah zata bawa Bahar irin wannan kaunar ne sbd daga ranar da Ayanah tasan waye Bahar zatai baqin ciki da kukan tsanar kanta da ‘yar Abaas dinta ta kasance a qarqashinta da sunan baiwa.

Idanuwanta da sukai ja ta rintse tana budewa ahankali ta saukesu Akan Bahar da fuskarta tayi ja sbd kukan datake yi sosai a jikinta.
Chapter 7 · 0% Book details