Sashe 87
Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi ganin ko kofar palo bata taba fita ba a kwanakin ya sakata dauke idanuwanta akanta data saka sosai tareda kafewa da tsarewa dan ko shi kansa a kwanakin bai shigoba sam iyakacinsa da Ammin a waya su gaisa shikenan sbd ba time hakama yana hana kansa ganin Bahar ne a yanzu dayaje buqatar time me yawa na aikin.
Leylah ta samu sauki sosai ta fara sakewa sosai dan kuwa ganin yanda Bahar take maqale da waya a hannunta tana duba text din mijinta tana replying nasa ya sakata fara bawa sakwannin Asim mahimmanci dan shima kusan kullum saiya mata da safe kafin kuma kullum da daddare saiyazo wanda hakan ya saka ya dan fara sabawa da maa sakinah sbd yanda ta daukesa 'da dagaske sbd leylah.
A ranar daya cika kwanaki biyar tana zaune ta gana sallan ishai dinta kenan kira ya shigo wayarta tanaji kaman bazata duba ba ta miqe daga daddumar sallah datake ta nufi wayar.
Ganin wanda yake kiran ya sakata tsayawa cak tana zubawa wayar ido harta yanke bata iya motsawaba sbd mamaki dan kuwa rabonta da jinsa da ganinsa kwana biyar yau cif.
Text dinsa ne ya shigo wanda ya sakata daukan wayar tana budewa tareda zaunawa a sofa sbd kafafunta da suke mutuwa da wani sanyayyan farin.
Bude sakon tayi wanda taga kalmominsa qataice.
'Tea'
Karantawa ta sake yi tareda sake wani kyakkyawar murmushi
Sanyi me nutsuwa yana ratsa zuciyarta.
Ajiye wayarta tayi tana zare hijabinta ta nufi kofa zata fice sai kuma ta dawo ta dauki wayarta sbd duba wasu abubuwan ta sake nufar kofa ta fice zuciyarta na sake cikewa da sanyi kowane second.
Leylah data ga irin murmushi da sanyin daya ratsa Bahar din tana zaune tana rubutawa Asim amsar sakon daya aiko mata itama akan sai ya gamo da Mameensa zai shigo zuwa anjiman ya ganta kafin ya wuce bangarensa.
Miqewa tayi tana bin bayan Bahar din da cewa
'Menene kike wannan farin cikin haka har jikinki yana nunawa'
Wata murmushin Bahar ta sake sakewa tana qarasa ficewa da cewa
'Ba komai'
Ko data fito ba kowa a palo koina tsit kowa na dakinsa Ammi ma da alama ta shige kenan sbd yanzu raba kwana suka sake yi bata zuwa koina gurin sultan sai ranar kwananta wanda sai gobe bayan kwana shida hakan zata zagayo mata sbd 3days suke yi hakama a kwanakin daga haile har Maraki ba wadda ta taba zuwa kwana gurinsa har gwara haile taje so daya sukai ba dadi sosai da kuma sako maganar Asim wanda kai tsaye sultan ya fada mata itace ta lalata rayuwar Asim din dan haka matiqar rayuwa a wani gurin daban zai bawa rayuwar Asim sabuwar maana da sanin darajar kai ya basa go ahead da cikakkiyar damar tafiya koina ne kuma zai tsaya masa a amatsayin uba dan haka daga yau din ya dakatar da ita daga kawo masa magana kowace iri ce akan Asim shi zai tsayawa Asim din daga yanxu ya cireta a ciki ta tsaya matsayinta kawai na uwa sauran yayan nata kuwa taje daman nata baida sauran kowace irin matsala dasu bayan Nysa dake aurenta.
Kusan dora hannu akai ta rusa ihu haile tayi lokacin data dawo bangarenta daga gurin sultan da wannan zantukan tareda tabbatar mata da gaskiyar Matsayin Ayanah a zuciyarsa shine yakeda burin aurenta tin daga ranar farko daya sakata a idanuwansa bawai 'danta ne dayake sultan ba ya aura masa ita dole kaman yanda take fada kuma zata iya yadawa duniya hakan dan haka ya dakatar da ita tin daga da maganganu masu buga xuciya sbd ta rasa da tsantsan radadi da zafin kishin ayanah din zataji ko da yarjewa Asim da yayi na barin boyem yaje ya gina rayuwarsa duk inda yake so kuma yayi mata iyaka me karfin gaske da zafi akan hakan,
Kaida kawo ta ringa yi a palon tana kaida kawo tana jin kaman zata zare tanajin sultan ya gama da kowane bangare na rayuwarta ya kasheta ya kashe yayanta ya watsar,
Dukkanin abubuwan data debo shekaru tin kuruciya tana aikatawa cikin rashin imani da tausayi tana kashe mata yan uwanta da ciki a jikinsu sbd kada su haifa masa namiji imebētis dinsa duk dan kada kowace ta taba daraja a idanuwansa har abada bayan ita daga karshe gashinan imebētis da a kaf rayuwarta su tafi dauka mafi rashin daraja dan tafi kaunar bayi akansu sune suka rabata da komai data rayu tana ginawa,
Imebēti ta zama macen da ayau tafi kowace mace daraja a boyem bayan itace me wannan matsayin.
Zubewa tayi a zaman yan bori akan kujeran tsakiyar palonta na kurya tana dafe kanta wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta ta furta sunan ayanah ghaz da karfi tana fasa kuka me sauti tareda rufe bakinta tana zamewa qasa kukanta na fita da dukkanin karfinta bakinta a rife jikinta na rawa.
****Bahar data nufa kitchen nutsuwa tayi ta ajiye wayarta tana duba kitchen din dan duba abinda zata fara dauka dan hada masa tea din wanda da kanta zata hada masa.
Motsawa tayi tana fara kunna gas tareda dora qaramar tea pot din dazatai amfani da ita.
Naimah ta kira tafara tayata aikin sbd hadda cake ta kwaba sharp sharp da zatai toasting ba baking ba.
Maa sakina ce ta iso kitchen jin motsinsu tana kallan abinda sukeyi.
Tambayar me sukeyi tayi tana daukan tissues ta nufi fuskan Bahar din tana goge mata gefen fuskanta da kulawa tana cewa
'Meyasa bazaki bari ayi miki aikinba kikeyi da kanki duk zaki bata jikinki'
Kunyar maa din taji kadan ta dago tana cewa
'Ai nama gama Maa'
Hannu Maa din ta saka tana rayata gasa cake din wanda duka duka baifi guda goma ba suka gasa dan haka ta dauko guri zatai mata shirinsu.
Tea din Bahar ta juye a tea set itama tana barin kitchen din zuwa dakinta sbd Maa ce zata hada ita kuwa dik ta bata jikinta sosai.
Kaya kawai taso sauyawa amma Leylah ta bita da cewa qamshin gasa abu da qwai kawai takeyi dan haka dole tayi wanka a natse tana jin kaman kada taje kai masa ta aika kawai sbd Ammi kada ta gane ta sake fita.
Leylah datake ganin yanda take slow slow tana shakka da fargaban zuwa time ta daga kai ta kalla taga karfe goma harta wuce sosai 11 ma ake magana dan haka miqewa tayi a natse tana saka hijabi me tsayi tana cewa
'Muje na rakaki saina dan motsa jikina nima dana kwana biyu ban fita koina ba'
Jin hakan ya dan saka Bahar jin karfin tafiyar a sanyaye ta miqe tana saka hijabi me tsayi sosai itama akan kayan rigar baccinta me dan tsayi kadan amma tanada kauri.
Fitowa sukai Bahar na satar kallan hanyar zuwa dakin Ammi wadda take tsit da alama tama yi bacci.
Suna fitowa Maa itama batama bari suka sake haduwa ba ta shigewarta sbd kada Bahar din kunya ta sakata aika masa maimakon xuwa da kanta sbd tasan a kwanakin da yayi bai saka Ammin da Bahar a idanuwansa ba yana tsananin kewansu da zai buqaci zuwanta a maimakon sakon.
Rashin ganin maa ya dan saka jikinta dayayi sanyi samun nutsuwa sbd kunyar yanda zata iya ficewaba kokuma maa tasan shi tayiwa aikin tinda bata fada mata aikin waye takeyiba a tinaninta Maa din bazata gane ba.
Daukan kayan sukai suka fice daga bangaren Naimah na dauke da basket din a bayansu a natse kanta a qasa.
Ga mamakinsu suna fitowa daga bangaren gabaki daya Aleey yana tsaye a gurin yana jiran fitowanta koda kuwa zata kai kowace lokacin bata fitoba.
#MAMUH
09033181070
[09/01, 4:37 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee
160
Da mamaki dukansu suka kallesa musamman leylah wadda tasan ko asuba aleey ze kai zai iya jiran cika umarnin ubangidansa.
Bahar kuwa kallansa tayi tana sauke ajiyan zuciya me sanyi sbd batai tinanin bazai iya barinta ta biyo hanyar ita dayaba a daren.
Aleey da kulawa da girmamawa yayi mata barka da fitowa tareda miqa hannu ya karbi basket din hannun Naimah yana cewa ta juya kawai.
Leylah ma dole daga nan ta juya kawai tabarsu Bahar din tayi gaba Aleey yana gaba tana bayansa a natse wayarta na hannunta tana jin shigowan sakonsa amma batama dubaba.
A maimakon bangarensa hanyar office din masaurautar suka nufa wanda yake hawa na karshe a cikin tarin offices din duk manyan fada da masarautar da masu matsayi a mulkin.
Koda suka isa babu kowa koina tsit amma wani irin haske dayake gurin gavaki daya tamkar rana dan kuwa ko alluranka ta fadi zaka ganta.
Securities ne suke qasa zagaye da gurin a tsaye kyam sbd shi dayake cikin gurin har lokacin,
Tana sako kafarta a hanyar gurin take daga dakin switch aka rage hasken gurin gabaki daya koina na yin dan duhu sbd aleey da tin kafin su iso ya tura sakon hakan.
Ciki sika qarasa a natse tana dago wayarta datake ta jin shigowan sako ta bude tafara dubawa a natse ba nasa bane ashe na Leylah ne dake ta jero mata su..
Karantawa takeyi tana jin kaman zatai murmushi amma sanyi jiki ya hanata hakan sbd hakanan jikinta taji yana sanyi da ganinsa da zatai bayan kwanakin datake jinsu kaman shekara..
Lift Aleey ya danna ta bude suka shiga zuwa sama gabaki daya,
Suna isa shine ya fara bata hanya ta fito a natse har lokacin duba sako takeyi tana tafiya a natse yana gaba.
Office dinsa ne kadai a duk fadin girman floor din wanda babu abinda babu a cikin Office din nasa sai Office din aleey daga farko kafin kayi yar tafiya ka isa nasa wanda kofarsa ma daban take dan a jikinta bayyane baro baro daga sama da wani kalar gold aka rubuta SULTAN LEUL NUAB BOYEM da manyan baqi.
Daga bakin kofar Aleey ya dakata tareda tsayawa cak ya saka hannu akan handle din kofar ya bude a natse tareda daga basket din ya miqa mata alaman iya nan zai tsaya.
Kallansa tayi tareda bude baki a natse da muryanta me sanyi tace 'Thank you' ta miqa hannu ta karba tana daga kafarta ta saka a ciki a cikin wata sanyi da nutsuwa.