← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 112

Sashe 103

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kansu su Aslam yana fada musu murnan jin hakan sukai tareda sakawa cikin wata irin kauna da soyayya me karfi da tsafta sbd sanin hakan na daya daga cikin burin mahaifiyarsu ganin zuriar Asim dinta a duniya sbd soyayyarsa daban take a duka cikin yayanta.

Irin yanda suke nunawa Leylah kulawa ya saka su ayanah sake jin nutsuwa dasu dan haka sai suka basu daman kulawa da leylah din yanda ya kamata hakanne ma ya saka koyaushe idan bata bangarem mijinta tana bangarensu tareda su ana hidima da ita rayuwansu na dan sauyawa daga kadaici da jinsu kaman mujiyoyin da aka ware daga cikin mutane.

***Tinda tayi sallan asuba maa sakinah ta shigo dakinta ta kawo mata tea me kauri sosai da dan cake taci ta koshi ta koma ta kwanta bata farka ba ayau din bacci takeyi sosai sbd ta samu sauki sosai tama warware sbd daman zuba ne cikin yayi kuma tinda ya zuba din bai sake komaiba itama tinda ta gama jinyar kwana biyun ta warware amma sam duk da hakan babu abinda ake barinta yi ko doguwan motsiba bare tafiyan datake son suyi zuwa boyem suma su duba sultan.

Karfe kusan goma na safe ta motsa kadan ahankali tana jan numfashi me sanyi da mutuwan jikin bacci sbd qamshin dataji ya shiga hancinta wanda ya saka jikint sake macewa daga kwancen.

Cigaba tayi da baccin dayake neman yankewa sbd qamshin dayake shigarta har lokacin,

Kai tsaye kamshin ya sake shigarta yana isa ga kwakwalwanta da zuciyarta dan haka ta bude idanuwanta ahankali cikin sanyi batareda ta motsaba.

Zaune yake a gefen gadon dataken kwanci ya zubawa kyakkyawar fuskanta idanuwansa dake wani irin zafi zafi ma sbd samun ganinta bayan tsawon lokaci.

Black Armanis ne a jikinsa da suka maidasa asalin baturen Moscow da kuma bayyanarda tsantsan jinin mulkin dake yawo a jikinsa.

Bata motsaba idanuwanta kadai ta zuba masa tana masa wani sanyayyan kallo sbd kasa yadda datai shi dinne a gabanta a cikin dakinta a gefenta yana kallanta.

Hannnunsa daya ya daga ya miqa akan nata ya dafa cikin nutsuwa ya bude baki zai ambaci sunanta ta motsa da wani irin mamaki tana tashi zaune sbd jin hannunsa akan nata haduwan fatarsu ya sakata tabbatarda shine a gabanta..

Shine ya qarasa tadata zaune sai kawai ta fada jikinsa ta zagayesa da hannuwanta biyu ta qanqame tana rufe ido tace

'Kaine??
LEUL ALMAZZ....

Kasa sauke numfashinsa dayake tokare da kirjinsa yayi tinda ya samu labarin yanayinta sai daya saka hannuwansa duka biyun ya rungumeta gabaki daya yana qanqameta cikin sanyi a jikin jikinsa tukuna ya sake numfashin me zafin daya sauka akan fatar bayanta dake bayyane sbd rigar jikinta vest ce da iyakacinta cinyoyinta.

Rungumar mintina kusan goma yayi mata bai saketa ba yana jin bugun zuciyarta a kirjinsa yana hawa da sauka hakana dumin jikinta yana shigarsa kafin ya saketa a hankali tareda dagota a natse daga jikinsa yana kallan fuskanta ya ambaci sunanta yana kallan cikin idanuwanta yaga alaman da gasken bata cikin wani yanayi na ciwo ya sauke ajiyan zuciya me sanyi yana cewa

'Wane irin bacci ne yar Ammi takeyi haka har pass ten?

Hannunta ya hade da nasa yana sarqewa a hankali tareda kallan cikin idanuwanta da suke tattare da nauyin baccin data farka yace

'Kin tabbata a hakan kina missing na mijinki kuwa?

Dauke idanuwanta daga kansa tayi murmushi me kyau yana taho mata ta bude baki tace

'Yaushe ka taho?
Ka dade da isowa?
Ya akai ka taho ka baro su Ammi acan?
Meyasa kazo yanxu baka jira su ba?
Yaya jikin Sultan?

Hannuwansa biyu ya saka ya cirota gabaki daya daga cikin gadon da bargon dayake rufe da rabin jikinta ya zaunar da ita akan kafafunsa yana kallanta da kyau yana bin kowane sauyin datai da ido sbd tayi wani irin haske sosai da wata irin cikowa da glowing na daukan ya miqa hannunsa akan fuskanta ya shafi hancinta dayake wani kyalli ya maida idonsa cikin nata yace

'Bana buqatan jiran kowa idan zan taho ga iyalina shiyasa ban jira su Ammin ba okay?

Hannunta daya ta daga tana dafe nasa daga shafan dayake wa hancinta tace

'Meyasa baka fadamun zaka taho ba to??

Motsata yayi da dan karfi ta sake matsewa da jikinsa a zaunen ya saka hannunsa daya a wuyanta yayi mata shafar data saka tsigar jikinta gabaki daya miqewa yayi qasa da murya sosai yace

'Idan na fada miki akwai tarban da shiryawa miji ne bayan wannan dana samu na samunki kina bacci in a very very sexy way....... ya qarasa fada da wata muryan dake qasa qasa sosai yana saka kansa a wuyanta yai kissing hankaki yana sake matse hannunta da nasa.

Lumshe ido tayi tana jin wani yarrrr sbd ba zato taji saukan lips din nasa a wuyanta.

Janyewa tayi kadan tana dago idanuwa ta kalli fuskansa da shima ita yake kalla yana jin ya rasa yaya zaiyi da ita sbd tsananin soyayyarta me karfin gaske da kuma kewanta da shauqinta...

Miqewa tayi da sauri zatabar jikinsa ya sake dawo da ita ahankali yana sake zagayeta da hannuwansa yana shinshinanta kaman wanda yake a buge yana jan qamshinta a cikin hancinsa yana jin cikinsa da ruhinsa na cika da duk abinda suke buqata.

Shaqarta yayi da kyau kaman oxygen din rayuwansa kafin ta rokesa ya saketa ta nufi bathroom tana waiwayensa.

Wanka tayi kaman yanda ta saba ko data fito baya daki dan haka hakan yafi mata ma,

Cikin nutsuwa da farin cikin ganinsa ta shirya tana gamawa aka shigo da breakfast dinta ta zauna tafara ci a natse tana duba wayarta da chats dinta dan tasan shima a yanzu yana can yana hutawan doguwan tafiyar da sukayo.

Tana cikin cin abincin Maa sakinah ta shigo dauke da madarar data dafo mata ta kawo ta miqa mata ta zauna gefenta tana fada mata isowan NUAB din duk da tasan yazo har dakin ya duba bahar din yana isowa.

Fira suka fara kaman yanda suka saba Bahar din nayi tana chatting dinta hankali kwance cikin nutsuwa kaman yanda suke zamansu kullum.

Maa sakinah tayita kiran wayarsa taji ko ya tashi daga hutun a kawo abinci a jera a dining amma bata samu Aleey ma data kira baccin yakeyi dan haka sai ta kyalesu su huta kawai har zuwa lokacin da NUAB din zai tashi.

Kwata kwata bai fito ba basu gansa ba sai bayan sallar magrib,

Ko daya shigo bahar na bedroom dinta maa sakinah ce kadai a palon tana waya.

Cikin nutsuwa ya zauna tana ajiye wayar itama suka gaisa daidai nan bahar ta fito tana wayar itama da Ammi data kasa fadawa NUAB din yana nan sbd kunyar fada takeji.

Tinda ta taho tana wayar idanuwansa sukai mata wani natsatsen mayen kallo so daya ya dauke idanuwansa akanta sbd Maa dake zaune zai iya rasa kansa.

Likitan dazai dubata ne ya buqaci komai ya zama ready ta taho dan haka Maa ce ta rakata har private dakin ganin likitan dake cikin masarautar me tsari da komai da zaa buqata.

Babu bata lokaci kuwa suna zuw likitan ya fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa tareda scanning daban daban wanda babu abinda bai fidda kwarrwansa ya duba ba gameda lafiyanta dana cikin.

Har ishai baa gama ba yaje yayi sallah batareda anbari kowa yasan sarkin boyem yana anjom dinba.

Suna dawowa dukkanin bayanin daya shafi lafiyar cikin kai tsaye Dr fuat yayi masa akan komai a yanzu is normal hakama satikan cikin bakwai.

Maa bata tsayaba likita na gama bayani ta wuce,

Tana isa dining room dayake babbar palon masaukinsa dake cike da lafiyayyan duniyar dauka ta shirya masa da kanta ta kira aleey ta sanar masa tukuna ta shigewanta.

Aleey har palon ya sakasu bai shiga ba ya dakata daga kofa yana juyawa sbd a nasa dakin zaici abincinsa.

Itama abincin kawai zata tayasa ci kaman yanda ya buqata shiyasa ta biyosa suna nufar dining room din komai shiru qamshinsa ne kadai daya fara gauraye gurin yake tashi.

Zaunawa sukai a dining yana waya da Mahaifinsa cikin nutsuwa yana kallan yanda take zuba masa abincin cikin nutsuwa da sanyin jiki.

Tana gamawa zata zauna ya kamo hannunta yana zaunar da ita akan kafafunsa yana kallan hannunta datai aikin dasu yakai bakinsa yayi kissing yana kashe wayarsa ya ajiye yana kallan bayanta inda abincin data zuba masa.
#MAMUH
09033181070
[17/01, 3:25 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

177
Abincin itama ta juya ta kalla a natse kafin ta juyo da kallanta akansa zatai magana taji saukan hannunsa cikin rigarta yana dorawa akan fatar cikinta data sakata jan numfashi da karfi ahankali sbd wani sanyin hannunsa daya ratsa fatarta.

Rufe idanuwanta tayi ahakali tana dan motsawa kadan kafin ta bude idanuwanta ta kallesa jikinta na mutuwa da kallan dayake mata me tsananin sanyin dake bayyanarda kaunarsa da batada iyakar da baki zai furta akan abinda yake cikinta yanajin jikinsa na mutuwa da dumin fatar cikin nata dake shiga tafin hannunsa dayake kai.

Shiru sukai bata iya cewa komaiba bare motsawa tana sauraran yanda yake fidda numfashi me sanyi da nutsuwa,

Da sanyi da nutsuwa ya bude baki ya furta

'Thank you Ayanah Bahar'

Kallansa tayi tana kasa cewa komai har lokacin sbd batasan me zata fada ba.

Hannunsa ya janye cikin sanyi yana cirowa daga cikin rigarta yana zagayeta da hannuwansa ya janyota cikin jikinsa sosai suka hade ya shaqi qamshinta me sanyi da kashe jiki yana cewa

'Tin yaushe kikasan da babyn NUAB ALMAZZ a tareda ke??

Kallansa tayi tana dan yin baya kadan tace

'Ammi fa??

Murmushi ya sake me shegen kyau da sauti yana sake dawo da ita jikinsa sosai yana rungumeta da kyau yace

'Ok yaushe kikasan da jikan Ammi ko 'dan yar Ammi zance??

Sake janyewa zatai tana masa wani kallo tana murmushinta fita ya matseta yana ciro hannunsa daya daga zagaye qugunta ya baro dayan yana sakawa a cikin wuyan zuwa bayan wuyan ya matso da fuskanta gap da tasa yana saka fuskansa ciki wuyan nata yafa shaqar qamshinta da kyau ya rufe ido cikin sanyi ya bude yana kallan fatar wuyanta datai wani haske da fresh tana daukan hankalinsa,
Chapter 103 · 0% Book details