← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 112

Sashe 56

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana gama fada ya juya yabarta gurin sbd ransa yayi mummunan baci fushinsa ya bayyana wanda ita kanta bata taba saninda yana ma fushi ba amma duk da hakan itama zuciyarta wuya take kaman zata fashe take jin dan haka wlh karyane saiya fahimci abinda take nufi zata barsa.

Bin bayansa tayi a fusace ta isa gurin da wayarsa take ta fizgota daga caji ta miqa masa cikin zafi tana cewa,

'Yes da matsala a zuciyata shiyasa nayi maka kiran dayafi hamsin amma baka dauka ba a tinaninka zan iya maka kiran daya wuce daya ne idan ba dan da dalili ba?
Kana tinanin kanada matsayin da zan ringa kiranka irin haka dan kawai naji lafiyarka ko yaya ka kwana?
Baka dauki wayana ba shiyasa na tako na taho sbd kawai na tabbatarda kaji abinda nakeson kaji din wanda kake qin yadda,
Ka saurara dakyau Asim Almazz kaji,
Sultan LEUL NUAB ALMAZZ a daren jiya ya tabbatarda Bahar ghaz a matsayin matarsa,ya kwana da ita,ya kwanta da ita,ya maidata macensa,ya bata kansa,yayi sex da it.......

Bata qarasa ba wani lafiyayyan mari ya sauka akan fuskarta daya sakata kifewa kan gado tana rintse idanuwanta da karfi sbd tinda ta tabbatarda abinda ya faru ta rasa hankali da tinaninta sai ayanzu marin ya dawo da ita daidai sbd duka maganganun datake fadan tana yine da kowane yare da bayanin da Asim zai gane cikakken me take nufi,

Kuka ta fasa me karfin gaske tana kasa tasowa daga gadon ta dungule guri daya tana kuka tana jerowa Bahar Allah ya isa data kwace mata budurcin NUAB,

Asim da jikinsa ke wata irin rawa me karfi duka jikin na mazari idanuwansa jajir sukai kunnuwansa yana jin suna dummm haka zuciyarsa wata irin bugawan da har a kirjinsa ana gani kafe Leylah da idanuwansa yayi yana kasa motsawa maganganunta na amsa kuwa a cikin kunnuwansa dan haka baya yayi zan zube amma kuma kaman an fizgosa ya fado kan leylah ya riqota gabaki daya ya dagota ya juyota suna fuskantar juna ya jijjigata yace

'Kinsa abubuwan da kika fadamu?
Kinsan me kike cewa kuwa?
Idan zaki iya yiwa Bahar dina qazafi to NUAB din naki fa?
Meyasa zaki fada abinda kikasan bazai taba yiyuwa ba?
Meyasa zaki cutatar dani da wainnan kalaman?

Bude ido tayi tana sake gangaro da wasu hawayen tace

'Da gaske nakeyi NUAB da bahar sun zama daya'
Ya kwana yana making love da ita su Maa na can suna gyarata he roughly..... bata qarasaba ya rufe bakinta da hannunsa da karfi yana girgiza mata kai hawaye na ciko idanuwansa jikinsa na tsananta rawa.

Kuka itama takeyi har lokacin suna hade ya kasa sakinta ita kuma batama da karfin janyewa dan haka kukanta takeyi shima hawayen ne yake saukewa ahankali yana kasa cewa komai sbd har lokacin ya kasa digesting zancen a kwakwalwansa dan haka leylah ya kafe da idanuwansa yana neman karya a abinda ta fada masa din.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:58 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

129
Jinsa shiru ya sakata dago idanuwanta da sukai jajir ta kallesa idanuwansu suka hadu ta ita yake kalla baya ko kyaftawa yana fata da jiran abinda zai karyata zancenta dayake amsa kuwa sosai har lokacin a cikin kunnuwansa yana birkita kwakwalwansa,

Itama ganin hawayensa ya sakata tabbatarda zancen nata a yanzu ya shigesa dan haka ta bude baki zata sake maimaita masa details na daren jiyan
Yana ganin ta bude baki kwakwalwansa da zuciyarsa dake fita hayyaci kasa iya ji yayi hannuwansa duka biyu suna riqe da kafadunta da karfin gaske dayake jijjigawa yana so ta karyata kanta da abinda ta fada amma ba alaman hakan a idanuwanta cikin rashin imani da rashin nata hankalin daya gushe ta bude baki zata sake feso bayanin ya saka bakinsa da karfin gaske akan nata ya rufe bakin sbd kashesa takeson yi da maganganunta.

Dora bakin nasa kawai yayi a nata ya rufe wasu hawayen kasa yadda suna gangaro masa itama gangaro mata din sukeyi tana qarasa zubewa a jikinsa idanuwanta na rintsewa jikinta na sanyi da kaddarar da Allah ya zabar musu.

Shiru sukai a hakan babu wanda ya sake motsawa hawaye kawai sukeyi zuciyoyinsu a cike da mara adadin quncin dayake raba gangar jikinsu da kuzari da karfinta har tsawon lokaci,

Shuraim daya farka bacci ya tashi ya fara fadawa toilet yayi brush da wanka ya fito ya shirya sai a lokacin yayi ordern breakfast tareda zaunawa ya dauki wayarsa yana dubawa yaga misscalls na Leylah masu yawa,

Da mamaki ya saka kiranta yana sake shiga mamaki,

Bata dauka ba harta yanke dan haka ya sake kira amma still baa daukaba,
Shima bai tsayaba ya ringa kiranta ba kakkautawa,

Ganin baa dauka ya sakasa neman wayar maa sakinah ya saka kira tinda yasan tana can gidan,

Itama maa sakinah bata daukaba a lokacin tana kitchen tana hada abincin da gidan zaayi breakfast dashi tinda NUAB yana gidan da kuma dahuwan tea dinsu da babu me dafa masa tin acan baa idan ba su biyun ba ko ita ko tenya wanda ma kona sultan yasar tenya ce me dafa masa sai Maraki kaf rayuwarsa.

Ganin maa sakinah bata daukan wayar ya sakasa maida kiran akan Asim wanda shima ya kasa daukan wayar sbd har lokacin yana cikin wani mummunan hali,

Fitowa Shuraim yayi ganin shi Asim yana kusa dashi ya nufi lift yayi sama zuwa floor din dasuke yana isa kofar dakin ya buga a natse yana sake saka kiransa yana fatar kowa na lafiya sbd zuwa lokacin hankalinsa ya fara tashi da rashin daukan wayar na kowa da kuma tarin kiran da Leylah ta bar masa.

Leylah ce ta iya karfin halin zamewa daga Asim din ta sauko gadon ta nufi kofa tana share fuskanta ta isa kofa ta bude tana ganin Shuraim kallansa tai da sanyin jiki tana jin tausayinsa shika sbd ya riga ya rasa bahar har abada kila dan gwara shi akan Asim ma dan kuwa shi ko NUAB yana raye zai iya aurenta idan ta fito amma Asim kuwa baida wannan damar ya rasa.

Ganin yanayinta ya sakasa shiga damuwa hakama mamakin ganinta ya sake damuwan tsananta ta fado jikinsa ya rungumeta tana sauke ajiyan zuciya sbd tama gaji da kukan batama san a yanzu me zatai ba kawai abinda ta sani zuciyarta na buqatar hutu da nutsuwa sbd gangar jikinta ta huta.

Ganin Asim bai fitoba saiyai tinanin fada sukai dan haka sai baima shiga dakinba ya jata zuwa nasa dakin ya zaunar da ita a kujera ya fara mata wata irin nasiha akan kowane aure yana buqatan saika bawa kanka hakuri da nutsuwa tukuna zaka sameta idan ka daga hankali da saka fitina to ita zakaita gani hakama kome Asim zai mata saita koyi cire damuwa daga gabanta tana mayarwa bayanta zata iya jin dadi dan haka kada ta ringa irin wannan kukan tana sakawa kanta damuwa akan komai sbd kada ta manta su suna gefe suna tsananin sonta da bazasu iya ganinta a cikin wannan halin ba,

Dagowa tayi ta kallesa batareda ta iya cewa komaiba ta kwantar da kanta a kafadarsa tana sauke numfashi ahankali tareda jin sassauci a zuciyarta sbd kaman yanda ya fada ta sani tanada masu tsananin sonta da kaunarta da zasu iya komai akanta koda NUAB din baya sonta,

Sake sauke ajiyan zuciya tayi tana kokarin sakawa zuciyarta karfi da dawowa daidai.

Breakfast din daya buqata aka kawo dan haka tare ya lallabata sukaci taci ta dan koshi ta fice.

Ko data isa dakinsu Asim yayi wanka ya fice baya dakin dan haka itama wani wankan ta sake ta sauya kaya bazata iya zama kadaici ba damuwa zata iya kasheta dan haka ta fito zata fita wani gurin kiran Maa ya shigo wayarta tana tambayarta tana ina sai kawai tace gatanan zuwa tazo ta dauki kayanta ne.

Ko data dawo gidan suna dinin suna sai a lokacin suke breakfast hakama koina tsit yana fidda sabon qamshi na turaren da aketa fama yiwa Bahar na gasa qasanta dayake buqatan 'dumi sosai a ciki dan kuwa yanda zai ringa ratsata a yanda take farkon budewa ba qaramin dumamo cikinta zaiyiba ya kamata ta yanda zai ringa hana kowane iska ko sanyi shiga gabanta da kuma saurin maidata ya rufe kaman baa budeta duka ba.

Ajiyan zuciya ta sauke sbd yanda qamshin ya shigeta ya saka jikinta mutuwa ta dan danne halinda take ciki ta zauna cikinsu suna bata abinci itama taci sosai cikeda kulawa harma dai naman da akaiwa Bahar dahuwansa aka zuba mata tareda madara me zafi dataji hadin lafiya maa sakinah ta sakata taci sosai tasha ta koshi itama take ba jimawa taji bacci take ji sbd hadin madarar bacci yake sakawa me rai da lafiya wanda a hakan yake ratsa jikinka,

Dakin Ammi ta koma ta kwanta take baccin da harma da daren da bata samuba ya dauketa me karfi.

Itama bahar tinda tasha take bacci gashi har lokacin gama dawowa cikakken hankalinta bama sbd kuka takeyi har lokacin dan koina jikinta yayi mata tsamin gaske amma tana samun baccin da alama zata tashi da saukin komai.

******A asibiti kusan LEUL ya wuni sbd shima wani irin bacci me karfin gaske ruwan da aka saka masa suka sakarmasa,

Aleey kuwa baima bari kowa yasan inda suke ba dan wayar NUAB ma kasheta yayi hakama tasa.

Sai karfe 4 da rabi suka baro asibitin suka iso gida securities na ganinsu suka miqe dukansu suna masa barka da zuwa amma bai iya amsawa ba sbd hulan sanyin dayake sanye dashi har lokacin wanda ya rufe saman fuskansa sosai hakama ga gashinsa me daukan ido a sake daya sake hana fuskarsa bayyana sosai.

Baya buqatan ko magana dan haka kai tsaye ciki ya wuce aleey na biye dashi har main palo wanda Tenye ce kadai a zaune tana aikin nata na waya.

Tana ganin shigowansa Kallansa tayi cikeda kulawa ta masa sannu da dawowa ya dakata cak tareda dagowa yana zare hular kansa tareda saka hannu daya yayi baya da gashinsa gabaki daya ya kalli Maa din ya kasa amsa gaisuwanta ya dora mata tasa wadda ta amsa zatai magana ya katseta a natse zaiyi magana itama sanin abinda zai fada ya sakata katsesa da cewa
Chapter 56 · 0% Book details