Sashe 28
Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayau da babu rayuwarsa a duniya itace macen datafi komai da kowa daraja a zuciyar namijin da ayanzu kuma shine ya shigo rayuwarta,
Bayan duka maza biyu ita kanta wani irin yanayi me karfi da bazata iya fadan koma menene ba take ji akanta duk da babu kusanci ko wata haduwa a tsakaninsu,
Fuska da kammanin mahaifinta sak da sak take gani a kowane gefe na kammanin fuskar Ayanah ghaz wadda takeda matsayin da kaf a duniyar mazaje biyu zuwa uku da babu me shi,
Wasu hawayen kewan Baa dinta ne suka ciko mata idanuwanta wanda take jin inama ba itace ayau din take haduwan fuska da fuska ba da Ayanah ghaz,
Inama mahaifinta ne wanda hakan shine burinsa har ya bar duniya,
Ya ganta amma a daidai lokacinda daqiqun zamansa duniya ya qare,
Ya ganta a numfashinsa na qarshe batareda ya ambaci sunanta ta amsa ba kaman yanda shine burinsa,
Sauke idanuwanta tayi ahankali tana kasa iya cigaba da kallan halittar da zuciyarta take jin kaman tana kallewa mahaifinta itane dan cika masa burinsa amma zuciyartata bazata iyaba sbd shine kadai take gani a fuskar ta ayanah ghaz dan haka ta fara kokarin dauke idanuwanta kanta na yin qasa.....
Hannun Ayanah dake rawa sosai ta dago ta tare fuskar Bahar din tana hanata yin qasa da kanta ta zuba mata nata idanuwan itama tareda kafe gurbin idanuwanta dasu wanda shi kadai ne kammannin Abaas dake tattare da Bahar din wadda da alama komai na kamminta na mahifiyarta ne,
Dayan hannunta dayake rawa ta daga ta kamo hannun Bahar din wanda yake dauke da lambar Abaas ta maida idanuwanta akan numbar tareda kafeta da idanuwanta dake jajir tana jin zuciyarta na wata irin karaya da rawa me karfi ta kankame hannunta tareda dago nata hannun me lamba ta hada dana bahar din ta rintse idanuwanta tareda gangaro da wasu irin hawaye masu tsananin zafin da suka sauka akan hannun Bahar ta rintse idanuwa itama nata hawayen na gangarowa sbd a jikin mahaifinta bai rasu ba sainda yayiwa jikinsa lambar ayanah a jikinsa bayan yayiwa Bahar din tasa lokuta da dama saiya hada hannuwansu ya zubawa hannuwan nasu ido yana ji a jikinsa bazai sake rayuwa da Ayanah da zuhrah ma kaman yanda iyayensu suka tafi suka barsu har abada kila shima a shi kadai zai qare ganawa da haduwansa da 'yan uwansa ta qare,
Rawa jikin Ayanaah yakeyi sosai wanda yake tsananta gudun hawayenta zuciyarta na radadin da kaman zata tarwatse ta janyo Bahar jikinta da wani irin yanayi na karfi da sarewa daga dukkanin buri ta rungumeta da karfin gaske a cikin jikinta tana fasa wani irin kuka mara sauti tana jin kowane gaba da tsigar jikinta tana karba da Jin bahar a cikinta tana jin tamkar Abaas dinta ne a jikinta sbd jin jininsa a jikinta ya sakata tinawa da asalin yanda dumi da qamshinsa yake a duk lokacinda ta rungumesa a jikinta tin yana qarami sosai.
Qanqame Bahar tayi tareda cigaba da wani irin kuka mai ratsa kowane lungu na zuciyar Bahar din da Maa sakinah da itama hawayen takeyi na yanda a yanzu Ayanah dole zata san Abaas dinta baya duniya bazai taba dawowa ba bazata taba ganinsa ba harta bar duniya kaman yanda take fada sedai ta kalli jininsa daya bar mata Bahar wadda batada kowa a yanzu bayan Ayanah din da 'danta.
Tenya ma data kasa zama so takeyi taxo ta ga yar Abaas da basu saniba suka tashi aikata babban kuskuren da zai damesu har abada shigowa tayi dakin kai tsaye sai ta tarar da yanayin wanda ya saka jikinta mutuwa gabaki daya ta qaraso daqyar ta tsaya gefen Sakinah tareda kallan Sakinah din wadda ta kasa dagowa ta kalli kowa a cikinsu sbd kada ma a tambayeta Abaas batareda tanada amsar badawa ba sbd NUAB shine me alkawarin sanar da mahaifiyarsa rasuwan qaninta da kansa sbd shi kadai ne zai iya bata sassaucin halinda zata iya shiga.
Bahar hawaye masu tsananin gudu da zafi take fitarwa batareda ta iya cewa komaiba ko motsawa ba sbd yanayin datake jin yana shigarta a karan farko data ji wa mahaifinta dumin rabin rayuwarsa hakama a karan farko da wani asalin jinin daya daga cikin mahaifinta ya rungumeta taji dumin asalin kauna ta jini daga dangin iyaye,
Tsananta hawayen sukai da zuba ta daga hannuwanta biyu a hankali ta qanqame Ayanah din cikin wani irin sanyi wani irin kuka me sauti na zuwar mata sbd burin mahaifinta ya cika na haduwanta da ayanah ghaz dayake cewa ita ya haifawa ita koda basu haduba har abada ita ya haifawa yarsa Bahar,
Ayau ta hadu da ita din amma bayanan.
Kukan Bahar ya saka kukan Ayanaah tsagaitawa tana sake rungumeta dakyau tana jin asalin kauna da kowace uwa ke abinda ta haifa da cikinta me karfin gaske tana ratsata akan Bahar dan haka rintse ido tayi kaman daga sama ta bude baki tace
'Ayanah Bahar ina mahaifinki hasken rayuwata shi nake jira tsawon shekarun nan,
Shine hasken daya rage babu a rayuwata,
Abaas nayi tsananin kewa da rashinka ina yake?
Ina zan samesa?
Meyasa baizo ba ya aiko ki gareni bayan hadda shi din ina tsananin kewa da son gani.......
Kalamanta suka saka Sakinah kasa riqe kanta ta fita da sauri tana rufe fuskarta sbd wani irin kuka daya taho mata mutuwar Abaas dinma ta dawo masa sabuwar datake jin radadinta a cikin tsakiyar zuciyarta da kirjinta.
Tana ficewa ma bahar kuka me tsima zuciyar ta sake tana kuka da bata samu tayiba na rashin mahaifinta wanda ya saka kafafuwan Ayanah sanyi suna fara wata irin rawa wanda ya sakar da jikinta da sauri tenya ta iso tana tareta idanuwanta itama jajir sbd tana hango abinda ayanah din bata hango ba a tattareda da bahar din da sakinah na Abaas baya duniya kila dan haka hankalinta yayu mummunan tashi jikinta yayi sanyi ta rintse idanuwa ta zaunar da su duka biyun a kujera har lokacin hannuwan bahar biyu suna riqe cikin na Ayanaah ta kasa sakinta jikinta na wata irin rawa sosai wadda ta saka Bahar yin shiru tana tsiyayar hawaye amma ta kasa dagowa ta kalli Ayanaah sbd bazata iya fada mata Baa dinta ya rasu baya duniya ba.
Gabaki daya Ayanaah jin tayi tana rasa nutsuwa da kanta da tinaninta tareda kasa iya hakura da komai buqatan sanin inda Abaas yake kawai takeyi dan haka haka ta sake dagowa ta kalli Bahar data kasa kallanta da jajayen idanuwanta koina jikinta yana tsananta rawa da sautin daya saka hankalin tenya fara tsananta tashi ta juya ta fice dan tambayar sakinah me yake faruwa dan suyi saurin kiran SULTAN NUAB ko Sultan yasar idan ayanah tasan abinda bai kamata ta sani ba batareda shiri ba.
Tana fitowa a palon ta tadda Sakinah ta rufe fuska tana kuka sosai wanda ya saka tenya kai tsaye bude baki kirjinta na harbawa tace
'Ya rasu ne??
Fadar hakan datai ya saka sakinah sake rufe fuskarta tana jin wani irin radadin kalmar sbd haka take a tabbace,
Tenya zubewa tayi a kujera da karfi zufa na keto mata hannuwanta na dan daukan rawa sbd shiga tashin hankali me girman gaske dan kuwa koda bata taba ganin abaas ba tasan waye shi da tarihinsa da matsayinsa me girma a gurin Ayanah wanda kusan ta wani bangaren yafi 'danta ma data haifa matsayi a xuciyarta.
Cikin tashin hankalin tenya ta kalli sakinah tace ki sanar da Sultan NUAB abinda yake shirin faruwa sbd Wishmah ta tsananta tana neman rikicewa gabaki daya tanason sanin komai a gurin bahar wadda bazata iya daukan pressure dinba ta kasa fada dama ta rashin fada din.
Sakinah datasan ma hakan zai iya taba bahar sbd itama fama takeyi da maraici da ciwon rashin iyayen da rayquwar quncin data taso da ita dan haka idan Ayanah ta tsananta son sani Bahar zata iya fada mata wanda duka su biyun abin zai iya tabawa dan haka wayar tenya din dake ajiye gefenta ta dauka sbd tata tana daki ta saka kiran Aleey sbd Sultan LEUL din yanada wuya samunsa kai tsaye.
Aleey ma bako wane lokaci ba kuma kowace kira yake dagawa ba amma bai taba wasa da kira ko text din duk wanda yakeda matsayi a gurin LEUL dinsu ba dan haka kai tsaye ya daga kiran wanda babu wani tsaiko ta sanar dashi komai ta kashe wayar ta ajiye.
Dagowa aleey din yayi ya kalli NUAB wanda yake zaune a dining da aka cike da breakfasts kala kala da fruits da teas kusan kala uku zuwa hudu shima wanda sai a lokacin zaiyi breakfast din.
Farin kyakkyawan teacup din daya dauka zai kai bakinsa ya ajiye a natse batateda yayi magana ba jin aleey baice komai ba bayan kammala wayarsa wadda ya tabbatarda daga bangaren Amminsa ne tinda yaji an ambaci Maa.
Dago fararen idanuwansa yayi masu kyau da tada tsigar jiki yayi ya kalli aleey din yana dakatawa daga komai ya bude baki cikin nutsuwa da wani irin iko da kamewa yace
'Uhumm???
Dagowa aleey din yayi ya kallesa a natse tareda bayyanarda girman kulawa da girmamawansa ya fada masa komai akan Ammi ta riqe ghaz Bahar da sai ta fada mata inda Mahaifinta yake wanda zai iya zama trauma ga ghaz princess din hakama itama Ammin.
Lumshe idanuwansa yayi wani irin yanayi yana sauka zuciyarsa me nauyi da dumi wanda baiso zuwansa a yanzu ba sbd yaso ne ya sanar da amminsa rashin dan uwanta a lokacinda zai bata cikakkiyar lokacinta dan rage mata radadin daya san saiya kusan zautar da ita wanda hakan ya saka yasa tayi masa alkawarin bazata tambayesa ba kuma tayi amma a yanzu bahar datake tambaya bazata iya sanar da mutuwar mahaifinta ba wadda itama har yanzu bata gama fitowa daga tashin hankalin rashinsa ba dan ma tayita shiga tashin hankali a zuwanta boyem wanda ya dan shiga gaban halinda take ciki wand ayanzu zata iya komawa ciki.
Numfashi ya sauke me dumi mara sauti kafin ya miqe a natse yabar dining din yana cewa aleey ya dauko masa sakon Abaas din daya barwa Amminsa.