← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 112

Sashe 5

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maa sakinah kuwa Wani irin nauyi kafafuwanta sukai ta tsaya cak zuciyarta tayi wata irin bugawa da maganar tenya data shiga kunnuwanta cewan ‘ga Leylah yar mai girma yunar da amaryarsa Zuhrah.

Kallo daya Maa sakinah tayiwa Leylah tanajin Wani irin farin ciki da kauna me tsafta da takewa Zuhrah tana sauka Akan Leylah amma idanuwanta na sauka kan Bahar dake gaban Leylah din tana jere mata kayan marmari a gabanta jin tayi zuciyarta na tsananta Wani sabon nauyin Wanda yake ragewa farin cikinta karfi ta dauke kallanta daga kan Leylah din ta Dora Akan Bahar zuciyarta na sake sosuwa.

Numfashi me dumi ta sauke tana daga kafafunta ta qaraso a hankali tareda dan sake murmushi tana karban aikin Bahar din tace su tafi kawai zatai aikin.

Cikeda jin dadi tenya datasan sbd kaunar datake wa Leylah ce ta saka zatai serving nata da kanta Wanda itama taji hakan hakama itama Leylah jin tayi dadi yana shiga zuciyarta na ganin Maa dince zatai serving nata sbd har sun fara kaunarta dan haka murmushi me kyau takeyi tareda dagowa daidai lokacinda aka bude kofar palon Kurya din Wanda ya saka Bahar dake kokarin barin gurin tsayawa cak zuciyarta na Wani irin harbawan datake jin tamkar mahaifinta zata juyo ta gani a bayanta sbd wadda take bayan nata rayuwarsa gabaki dayanta.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:49 am] Asia ahmd: *_HAYATEEM_*
Mamuhgee

75
Leylah wadda tata zuciyar itama take sauya bugawa ahankali miqewa tayi tsaye a hankali cikin wani irin yanayin da batasan menene take ji ba amma ganin matar data haifi namijin datake so take shirye da rasa rayuwarta akansa ya saka zuciyarta da idanuwanta Wani irin sanyi da cikewa da tsananin kwarjinta da wasu irin kammanin datake ganin suna fizgar kamannin mahaifiyarta bata saniba ko dan mahaifiyarta bata da zance saina yabo da zuzuta kyau da matsayin wishmah din Masarautar BOYEM AYANAH GHAZ Shiyasa Ayau da idanuwanta suke ganin macen datafi kowace saar miji da ‘da take ganin kaman suna fizgar wasu kamanni da mahaifiyarta.

Bahar da idanuwanta sukai Wani irin sanyi tareda cikowa da wasu hawaye suna sauya Kala Lumshe idanuwa tayi bugun zuciyarta na tsayawa cak kaman yanda gangar jikinta ke jin kowane irin yanayin Wanda mahaifinta ne yakeda haqqin ganinsa shine ya cancanta ganin wannan lokacin dan haka taji sam bazata iya juyowa ba ta daga kafarta a sanyaye zata bar gurin batareda ta juyo ba.

‘AYANAH BAHAR’

Maa sakinah ta Ambaci cikakken sunanta zuciyarta cikeda rauni itama Wanda ya saka Ammi dake kokarin sauke idanuwanta Akan Leylah dakatawa tana Juyawa a natse da Wani irin sanyi ta kalli inda Bahar din take juyowa cikin nutsuwa kanta a qasa ta sauke idanuwanta akanta tareda tsayawa cak tana kallanta batareda zuciyarta ta buga ma komai nata ya tsaya cak kallan nutsuwa take yiwa Bahar din wadda har lokacin ta kasa dagowa sbd idanuwanta sun kasa bata zarrar karban lokacin dayake na mahaifinta ne,

Ahankali Ayanah ta dauke idanuwanta daga kan Bahar jikinta na mutuwa ta saukesu Akan Leylah wadda itama Bahar din da Ammin ta kafawa ido tana kalla sbd jin sunansu dayake iri daya.

Tenya kallo daya tayiwa Bahar ta dauke kai tana dawo da kallanta kan Ayanah dake kallan Leylah cikeda farin cikin dayake kasa boyuwa a zuciyarta tace

‘Yar mai girma YUNAR da Amaryarsa Zuhrah’

Kasa motsawa Ayanah tayi sbd bugun zuciyarta daya kasa dawowa daidai hakama maganar tamkar saukar mashi a tsakiyar zuciya taji ta so keta ba tsammani,

Kafe idonta tayi Akan Leylah kafafunta na wata irin rawa suna Neman kasa daukanta tayi baya a hankali tenya tayi saurin tareta tana Kama hannunta tareda kamo hannun Leylah din ta Dora Akan na Ayanah wadda Wasu hawaye masu tsananin zafi suka ciko idanuwanta ta Kama hannun Leylah din a cikin nata ta riqe a natse tareda Zaunawa tana jin Wani irin zazzafan kauna me sanyi da nutsuwa tana ratsata bakinta da baya hayaniya ta bude a hankali tace

‘Ina mahaifiyarki?
Tana lafiya?
Tana cikin koshin Lfy?
Ta sauya?
Ta girma?
Tana cikin kwanciyan hankali da nutsuwa??

Da mamaki da farin ciki Leylah take kallan Ayanaah din zata bude baki ta amsa Bahar dake jin kowace kalma da muryan Ayanaah dake sauka kunnuwanta suna narkar da zuciyarta ta nufi kofa zata fice Maa sakinah da bazata iya barinta ba ta ajiye abinda yake hannunta tabi bayanta tareda Kama hannunta batareda an Ankara dasu ba ta shige dakinta da ita.

Suna shiga rungume Bahar din a jikinta tayi zuciyarta na shiga damuwa da tausayinta mai tsananin sbd gata ga Dayar zuciyar mahaifinta amma ba damar kowace iri ta bayyanar da hakan a tsakaninsu,

Wasu hawaye ne masu dumi suka gangaro daga jikin Bahar din tana kwance jikin Maa sakinah din batareda ta furta komaiba,

Tabbas ta San yar Zuhrah din mahaifinta ce ake magana a gabanta Bayan AYANAH GHAZ wadda itace ma mahaifin nata,
Ita daban take a cikinsu sbd mahaifinta ma daban yake a cikinsu dan haka batada gata ko hurumin alaqa dasu zata tsaya iya inda aka ajiyeta ta Kama matsayinta da shine ya cancanceta.

Dagota Maa tayi daga jikinta tareda Zaunawa da ita suka zauna Akan sofa ta kalleta itama bata iya cewa komai ba bayan

‘Bahar kici gaba da hakuri da riqe kaddararki wadda lokaci zai zo da zata sauya,
Banda yanda zanyi nima Alkawari ne da iko da ban dashi suka daureni daga hanaki samun walwalan data kamaceki a gaban macen da itace zata fi kowa so da kaunarki a duniya,zata kaunaceki fiyeda kanta da duk wani Wanda yake rayuwarta,zata kauna ce ki fiyeda ‘danta data haifa sbd kece jini daya tak da hasken rayuwarta ta bata a duniya ya tafiyarsa ya barta’

Hannun Maa din dake share mata hawaye ta Kama tana Dakatar wa da nata ta bude bakinta da sauti me sanyi tace

‘Maa kaunarki kadai ma ta haskaka Wani duhun na rayuwata da baya buqatan hasken da yawa dan haka a hakan ma rayuwar da kuka bani nayi anan gode’

Rasa abin fada Maa tayi sbd zuciyar Bahar batada abinda ta sani ta sabu dashi din bayan duhu dan haka takejin kaman bata buqatar kauna da yawa daga wainda suka cancanta.

Bata Bari ta kuma fita ba tace ta tube tayi sallah tayi zamanta kawai.

Tubewa tayi tayo Wani wankan harda alwala ta fito ta zauna shiri.

Acan palo kuwa Ayanah Ayau jin takeyi zuciyarta tana samun karfin data rasa sbd ganin jinin Zuhrah dinta Ayau a gabanta a tareda ita.

Farin cikinta a bayyane yake Wanda yake sake saka tenya jin nata farin cikin yana qaruwa.

Maa sakinah ma nuna farin cikin takeyi duk da a qasan zuciyarta Bahar ce a ciki da babu Wanda ya San da wanzuwarta a duniya gabaki daya ma.

Leylah ma samun kanta tayi a sabuwar duniyar da bata taba tsammani ba sbd Karbuwan data samu da kauna me karfi daga Ammin NUAB da Maa tenya harma da Maa sakinah duk da farin cikinta da kaunarta a bayyane batai tasu ba.

A bangaren ta wuni har dare sosai kafin ta koma bangaren Maraki.

Washe gari tinda safe Bahar ya fice daga bangaren gabaki daya tareda su Naimah sbd karfafawa rayuwarta matsayin da aka ajiyeta akansa.

Tenya kuwa dakin Ammi daya dayake palonta kusa da nata bedroom din ta saka aka sauyawa komai sabo sbd Leylah da zata dawo bangaren.

Sauran bayin bangaren ne sukai aikin Wanda bai dauki lokaci ba aka gama komai,

Leylah da kanta tareda bayinta ta tattaro Kayanta suka dawo bangaren batareda sanin sultan ba sbd Ayanah sirikarta ce da ba lallai abar ta zauna bangarenta ba.

Bayan sun gama parkinga bayinta sun gama jere mata komai wanka ta sake yi ta sauya kaya zuwa doguwar Riga me ado sosai datake daukan idonta rufe kanta ta fito suka ci abincin rana tareda Ammi cikin wata kulawa dake sake saka Leylah jin duniyarta na kammala.

Acan bangaren na ASIM shima Ayau yafara kokarin bayyanar da kulawansa kan Bahar wadda batajin tsananin tsoro da shakkarsa kaman yanda su Naimah ke yi dan haka koda ya fara kokarin jefa tambayoyinsa Akan sunanta da nahiyar data fito kai tsaye ta basa amsa da sunanta da kuma sunan nahiyar mahaifiyarta sbd batajin zata iya fadar sunan ghaz ne asalinta sbd ayanah ghaz da matsayinta a masarautar.

Koda lokacin tashinsu yayi suka fito suna isa ko zama basu yiba aka sanar da NUAB zai shigo bangaren dan haka duka bayin miqewa suka koma gefe suna rabe wa a Jere kansu a qasa.

Ita kuma kokarin barin gurin tayi Wanda yayi daidai da sako Kansa yana sanye da black qananun Kayan RL gashin Kansa a daure tsakiyar Kansa batareda matsesa ba tin jiya daya dawo bai fito ba sai yanzu din sbd hutawan dayayi dakyau.

Aleey dayake bayansa shine idanuwansa suka sake sauka Akan Bahar wadda take kokarin ficewa cikin girmamawa me tsaftar da ubangidansa kadai yake bawa se iyayensa ya dan sadda kai yana bude baki ya gaidata a girmame.

Bata ji ba dan bata taba kawowa ita tanada matsayi ko darajar da zata samu gaisuwa a gurin wani dan haka wucewarta tayi a natse.

NUAB dinne kadai ya wuce ciki zuwa kai tsaye palon mahaifiyarsa na Kurya Wanda ya taddata Zaune da Leylah a gefenta.

Leylah na ganinsa ta miqe tsaye a hankali cikin nutsuwa ta masa Barka da zuwa muryanta na saka Ammi din sake sanyayyan murmurshi a sanyaye a zuciyarta kuma Wani daci da radadi ne ya yanketa sbd fatar inama ace ‘yar Abaas ce a gabanta take yiwa NUAB wannan kallo da gaisuwan sbd cikar burinsu.

Numfashi ta sauke tareda jin jikinta ya mace
NUAB kuwa da hannu ya iya amsa gaisuwan batareda ya iya bude bakinsa ba dan haka ta fice daga palon dan basu guri.

Bai fitoba sai magrib ya fita ya fice.
Chapter 5 · 0% Book details