← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 112

Sashe 95

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaunawa tayi gefensa gap dashi sosai tana dagowa ta bude baki cikin bayyanarda nadama ta basa hakurin abinda ta fada a dazun.

Sai a lokacin yaji tausayinta me yawa ya shigesa da ratsasa musamman da ramarta da figewanta duka suka bayyanar masa ya kafeta da ido yana jin inama zai iya fada mata nasiha taji ta dauka akan bazai taba wulaqantata ba ko tozartata akan aurensa kodan darajar shekarun da sukai tare da manyan yayansu dake tsakaninsu amma yasan babu abinda zai fada mata taji bare yadda wanda dazatai hakan data samu nutsuwa da kwanciyan hankali tareda zaman lafiya.

Numfashi ya sauke yana karban banhakurinta tareda miqa hannu ya karbi tea din datake miqo masa yana mata godia kadan a natse yakai bakinsa ya bude yafara sha duk da baya buqatansa dan bai jima da gama sha ba amma sbd ya bata nutsuwa da kwanciyan hankali sai yasha din.

Idanuwanta cikowa suka fara yi da hawaye masu tsananin radadi da quna tareda dacin shedar da wannan rana wanda shine ya janyo musu wannan kaddarar.

Tana kallo ya ringa sha ahankali harya shanye rabi ya ajiye a natse tareda dawowa da bayansa yana jingina ya kalleta hawaye na gangarowa daga idanuwanta mamaki ya kamasa bude baki zaiyi magana ta taresa dukkanin imaninta na barin kirjinta ta share hawayenta tana kallansa itama dakyau ta bude baki tace

'Meyasa ka zabi ayanah ghaz akan kowace mace Sultan??
Meyasa ka lalata rayuwan mata da yawa da basada adadi ka qare akan ayanah ghaz?
Meyasa se ayanah ghaz?
Baiwa ce qanqantacciya,imebēti ce macen da ake kwanciya da ita dan biyan buqata,wishmah ma data zama batai darajar mu da muke da aurenka akanmu,
Meye ne jinin ghaz suke dashi da kowa yake sonsu yake mutuwa akansu?
Menene a jininsu bayan mummunan kaddara da baqar rayuwa,
Meyasa zuciyarka bata iya bani soyayyarta ba bayan shekarun da mukai a tare muka tara yaya sai akan baiwar datake ragin kusrawa.....

Rufe idanuwansa yayi a natse kalmarta ta qarshe tana yiwa zuciyarsa yanka me karfin da idanuwansa suka sauya hadda fuskansa sbd radadin yankan,

Bude idanuwansa yayi batareda ya kalleta ba sbd gabaki daya jin yayi babu abinda ya tsana a daidai wannan lokacin bayan iya kallanta dan haka baice komaiba wayarsa ya daga ya saka kiran Asim sbd yace yaxo ya tafi da mahaifiyarsa dan da alama akwai matsala me girma a cikin kwakwalwanta,
Bazai tankawa kowace irin haukanta ba kaman yanda bazai iya cigaba da saurara ba dan haka gwara danta yaxo ya tafi da ita salin alin.

Koda kiran ya fara shiga wayar Asim a lokacin Asim din ya dawo yana tsaye kofar office din NUAB zai shiga a karan farko da zasu fuskanci juna sbd tafiyarsa tagama kammaluwa stamp na sultan din boyem na yaddar barin boyem a matsayinsa na jinin boyem yake nema kadai a takardarsa ta li'uli Asim ya sakasa zuwa dan haka tin safe ya sanar da Aleey a waya cewan ya sanar da Sultan LEUL din yana son ganinsa ba bata lokaci kuwa cikin girmamawa Aleey din ya amsa da yes ya kuma isar da sakon ga NUAB wanda yace koyaushe Asim din ya tashi free yake da zuwa ganinsa ba shamaki.

Bayan aleey ya sanar dashi godia kawai yayi bai samu zuwa ba sbd bai zauna ba sai daren ya kira yaji har lokacin NUAB yana office shiyasa ya fito yazo sbd gobe tinda safe zai bar boyem ya fara wucewa amma ba anjom ba sai antashi daurin auren zai tafi anjom daga can ya wuce da iyalinsa dan ita ma komai na tafiyanta ya mata.

Shigowan kiran sultan yayi daidai da zai shiga office din Aleey na tareda shi cikin sakewa da girmamawa dan haka daga wayar yake kokarin yi a natse da mamakin ganin kiran Sultan a lokacinda baa taba kiran kowa dan idan dare yayi irin hakan baa kiransa baya kira shima.

Yankewan kiran ya sakasa dakatawa yana sake shiga mamaki kafin ya saka kiran wanda tafara ringing amma ba alaman zai dauka.

Acan kuwa haile na lura da kira ya saka ta saka hannuwanta biyu ta fizge wayar tana ja da baya wanda zuwa lokacin ransa da zuciyarsa sun gama zuwa sama gabaki daya da bacin rai idanuwansa ya dago jajir da zallan bacin rai me tsananin gaske ya kalleta ya bude baki zaiyi magana jini yafara fitowa daga hancinsa a hankali wanda ya sakasa kallan gaban rigarsa daya fara diga ahankali.

Dagowa yayi a hankali ya kalleta itama shi take kalla tana ji wayarsa na ringing a hannunta ta daga wayar ta buga da qasa da karfi take wayar ta watse.

Miqewa yayi tsaye tareda daga hannu zai kamota cikin tsananin bacin rai da zafin zuciya amma ko taku biyu baiyiba kafafunsa sukai wata irin majirya me karfi suna sanqarewa tareda sarewa suka daki qasa da karfi hannunsa daya daga ya sanqame shima yana wata irin rawa da qamewa jinin dake fitowa hancinsa ya qaru da karfi yana fitowa sosai bakinsa kuwa kumfa mara kyan gani dake hade da jini yake fitarwa.

Zubewa yayi a gurin duk yanda yaso karfin halin dayake jininsa gangar jikinsa kasawa tayi sbd tsananin karfi da kaifin poison din take kalar jikinsa ma tafara sauyawa tana duhu jinin na tsananta fitar masa.

Tsaye take tana kallansa zuciyarta da idanuwanta a rufe buri da fatarta kawai ransa ya fita yabar jikinsa Ayanah ghaz ta rasashi kaman yanda suma suka rasashi hakama shima ya rasa ayanah ghaz ta hanyar barin duniya kaman yanda ya zabeta akan komai da kowa.

Jajir idanuwanta sukai hannuwanta na rawa ta qanqamesu sosai tana kafe dashi da ido batareda fargaba ko shakkar a kamata ba indai ya mutu ta yadda a kamata dan koda baa kamata ba indai yana raye mutuwan baqin ciki da wulaqanta zatai a banza gwara tasan ta cika burinta na ganin mutuwansa kafin ta mutun.

Asim dayake kiran wayar tana dena shiga jin yayi hankalinsa ya fara kasuwa kashi biyu yana shiga shakka.

Aleey daya fahimci hakan shima suna shiga office din fitowa yayi ya saka kiran kadir ya sanar dashi Sultan ya kira Asim amma kiran ya dena tafiya kuma hankalin Asim din ya rabu biyu ta yanda bazai iya nutsuwa yayi magana da ubangidansa ba dan haka a dubo ko da akwai yiyuwan sultan na neman Asim dinne saiya je ya fara ganin sultan din kafin NUAB sbd sam bai hada duk wanda zai tsayu a gaban Nasa sultan dinba da komai.

Yana gama wayar ciki ya shigo a natse yana kallan Asim da duk yanda yaso tsaida hankalinsa guri daya a gaban NUAB kasawa yayi musamman gashi ba sabo ko kusanci ko qanqani a tsakaninsu hasalima sai ayau suke tsayuwa a gaban juna face to face haka iya su kadai zasuyi magana,magana wadda bata komaiba saita fahimta da nutsuwa da bawa jinin dayake tsakaninsu mahimmanci.

Qarasowa Aleey yayi ya tsaya gefen Asim din cikin nutsuwa yace

'Kadir zai dubo Sultan idan nemanka yakeyi zaka iya kwantar da hankalinka mai girma li'uli'

NUAB dake zaune akan sofa me fadi da laushi cikin wata irin nutsuwa da kamewa tareda zallan kwarjininsa dayake cike da gurin zuciyarsa a wani yanayi me sanyi da kowace tinani babu a cikinta empty yake jinta haka kawai dagowa yayi a natse ya kalli Asim din wanda ya zauna suna facing juna shima dagowa yayi ya kallesa jin abinda aleey yace wanda ya basa nutsuwa da dawowa daidai ya fuskanci Dan uwansa da kyau ya bude baki cikik nutsuwa da nasa ikon jinin boyem dayake yawo a jikinsa ya miqa masa gaisuwa me girmansa a matsayinsa na sultan me mulki.

Numfashi mara sauti da nutsuwa NUAB ya fidda yana kallan Asim din wanda alamun sabon mutum ne a yanzu suke bayyane a tattare dashi shima kwarjininsa na jinin sarauta yana fita daga idanuwansa kafin ya bude baki ya amsa tareda miqa masa tasa gaisuwan a matsayin dan uwansa kuma yayansa daya basa mintina qalilan a fadowa duniya.

Daganan aleey bai tsayaba ya fice daga office din yana basu guri tareda komawa kofa inda Keelah yake tsaye ya tsaya gefensa suna magana.
#MAMUH
09033181070
[14/01, 2:52 pm] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

169
Acan ciki magana su Asim din keyi wanda shine yake jero maganganun a natse cikin kwanciyan hankali da kamun kai akan duka abubuwan da suka faru basai ya tsaya dawo dasu ba kawai yana roko ne da fatar idan ya bar boyem mahaifiyarsa da 'yan uwansu biyu da basuyi aure ba kada NUAB ya bari su wulaqanta a qarkashin mulkinsa sbd su matan yan uwansa ne koma yayane hakama itama mahaifiyarsa matar mahaifinsa ce taci wannan darajar koma menene,

Hakama yana rokon alfarma ta karshe akan ya janye hukuncin Sultan akansu na hana zuwa kowa neman aurensu ya bada damar da kowa zai iya fitowa da zuwa neman aurensu sbd koda sun manyanta suma rayuwansu ta samu walwala ko yayane.

Yana gama rokon wannan alfarmar da bayajin a matsayinsa na dan uwa kuma wanda ya miqa roko na farko kuma na karshe NUAB zai hana masa hakan ya fidda takardarsa me tsayi da kyau da stamp dinsa yake jiki na sultan me mulki kawai yake jira ya ajiye a kan table din gabansu gaban NUAB din tareda dago idanuwansa ya kalli NUAB wanda shima shi ya dago ya kalla kafin ya maida idanuwansa akan takardar gaban nasu wanda duk wanda yake jinin boyem matiqar idan har zai bar masarautar yaje yayi rayuwa a wata duniyar daban ba karkashin masarautar jinisa boyem dole sultan zai saka masa hannu a basa wannan damar da shikenan zai iya rayuwa koina ba a cikin masarautar da ake riqesu ba kaman marasa yanci.

Wannan shine yancin da duk wani jinin boyem daya san meye dadin yanci yakeso na ficewa daga masarautar yayi rayuwansa ba dokoki ba sharudda yanda yakeso,
Chapter 95 · 0% Book details