← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 112

Sashe 68

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu fada mata cewan yazo ba wanda kenan baizo dinba amma kuma shi kansa Shuraim din tinda yace ya gansa kenan ya gansa din
To kenan baizo nan gidan ba qasar yazi kadai ko me??

Kasa cigaba da magana tayi ta cewa zuhrah ta bari da safe zasuyi magana,
Tana fadar hakan ta kashe wayar tana rasa wane tinanin zata kama ko wane zata fara kira ta tambaya.

Shuraim ta kira a waya wanda yana ganin kiranta cikeda girmamawa da kulawa ya daga ya gaidata ta amsa a natse kafin ta dan fara da nasihar su rage saka mahaifiyarsu a damuwa koma menene damuwansu su idan wadda zasu iya sanar mata ne su sanar mata su dena sakata damuwan ganinsu a wani yanayi mara dadi.
Tana gama nasihar ta jefa masa tambayar ashe yaxo uk din batanan ta dan yi tafiya,

'Eh Ammi nima dayake ba dadewa zanyiba ina gama dan aikin daya kaini na juyo sbd kadama Sultan LEUL ya rigani baro uk din ya dawo sbd akwai ayyukan dake a qasa'

Ajiyan zuciya Ammin ta sauke tana ji dai NUAB din yaxo uk din kenan,

'Ai nama dauka tare sukayo tafiyar sbd tinanin ko tafiyar data shafi aikin masarautar ne'

'No ba tafiyan masarauta bane a rana daya dai muka isa dan nama rigasu isa nan gida gurin su Maa sbd muna can dukanmu dasu leylah ya iso gidan.'

Masha Allah' Ammi tace daqyar tana masa sallama sbd tagama jin cikakkiyar zancen daya saka jikinta mutuwa gabaki daya wayar hannunta ta zame ta ajiye tana jin tashin na rifeta na damuwa da shakka tamkar NUAB dinne ubanta haka taji fargaba ta rufeta.

Zufa tafara gogewa daga fuskanta sbd tasan ya gama samun cikakken sani ga gani ya shedar ya tabbatarda bata nan tana tarera sultan yasar,
Kwana nawa yayi yasan batanan?
Ya sani amma bai taba nuna mata yasaniba?
Yasan tana tareda sultan amma ya iya danne zuciya da fushinta bai nuna ba?
Meyake faruwa?

Kasa motsawa tayi duk da tanason motsawa taje ta tambayi su Sakinah taji me zasu fada mata akan wannan babban lamarin da bazasu ce sun manta fada mata bane dan kuwa lamari ne girman gasken daya kamata ace shi suka fara tarbonta dashi amma sukai shiru,
Akwai dalilin daya saka suka boye mata wanda ko wane irine me girma ne sbd babu abinda yakeda girman daya wuce fada mata zuwan NUAB da batanan a yanzu.

Sake shiga rudani da shakka tareda damuwa me girman gaske tayi sbd kenan akwai tashin hankali a tsakaninsa da Sultan suna haduwa dan haka taji zuciyarta na sake rasa nutsuwanta gabaki daya ta dauki waya ta nemo numbern sultan ta saka kira dan sanar masa NUAB yasan bata nan tana tareda shi tsawon wannan lokacin.

Shiru yayi shima sbd a bazata zancen ya shiga kunnuwansa dan haka ya shiga tinanin kenan lolacin da NUAB din zaisan ya shiga gabansa shima yayi dan kuwa a yanxu zai sanar dashi igiyoyi aurensa uku reras ne akan mahaifiyarsa dayake ikirarin ya rabasa da ita,zai kalli cikin idanuwansa ya fada masa har koyaushe shine gabansa sbd shine ubansa kuma a yanxu daya mallaki Ayanah ghaz ya gama dashi gamawan da har abada dole ya bisa dan a mutuwa ce kadai zata cireta daga hannunsa.

Kwantar mata da hankali yayi bata tabbacin zai nemi ganin NUAB din da kansa ya fuskance ya sanar masa da komai.

Sake tashi hankalinta yayi dan kuwa tasan idan NUAB din yaji tayi tafiya da sultan ya iya danne zuciyarsa da fushinsa idan yaji cewan aure sukai a yanzu batareda ta sanar masa ba ko neman izininsa batasan yaya zaiyi ba shi da sultan dan haka taji gabaki daya boyem din take buqatan zuwa a cikin daren sbd koma yayane ta fuskancesa a lokacin da zaiji zancen ta bawa zuciyarsa salama da sassaucin halinda zai shiga sbd tasan zata qona zuciyarsa fiyeda yanda zai tsammata.

Kasa rintsawa tayi a cikin daren ta ringa shiga wasi wasi da dana sani kala kala musamman tinawa da alkawarin da sukaiwa juna a tsakaninsu na uwa da 'da wanda babu wanda ya sani sai Allansu sbd bata taba sanin zuciyarta na maqale da sultan a cikinta ba,

A matsayinta na uwa ta karya masa alkwarin dazaiyi shattering nasa hakama duka abinda yayi yanayi ne sbd bata ingantacciyar duniya da kwanciyan hankali tareda kariya da rayuwar data rasa a baya.

Sanyi jikinta yayi gabaki daya taji kunyar kanta da baqin ciki tareda dana sani sun gama lalata rayuwarta babu abinda take tsananin buqata a yanxu irin tafiya boyem taga NUAB din dan haka zata tafi tareda tenya tabar Bahar da sakinah.

Ko da gari ya waye da sassafe kafin kowama ya fito su Bahar sun fice makaranta dan haka koda Ayanah ta fito cikin damuwa me tsananin gaske take bata fara komaiba bayan fuskantar su Sakinah kai tsaye ta tambayesu NUAB daya taho kwanansa nawa?
Meyasa suka boye mata ya zo??

Shiru sukai cikeda sanyi jiki sbd ba sauran boyo,

Sake maimaita tambayarta tayi cikeda damuwa da bacin rai tace

'Akwai dalilin boyemin zuwan nasa ne?
Akwai wani abin ne bayan zuwan nasa da bazaa fada mun ba??

Tenya ce tayi karfin halin cewa

'Satinsa kusan uku amma baa nan yayi su ba,
Kuma munyita kokarin sanar dake tin kina can amma baa samunki kuma kafin ki dawo ya wuce shiyasa baa fada miki ba sbd ya riga ya wuce kuma ba wanda ya fada masa ga inda kika je ya sani amma ya zabi shiru muma mukai shirun'

Shiru Ayanah din tayi tana sake shiga rudanin zuciya sbd ta tabbatar Allah ne kadai yasan abinda yakeji a zuciyarsa ya danne,
Kuma satika har uku yayi yaga bata nan?
Innalillahi' ta fada a zuciyarta tana jin kanta na nauyi.

Bata iya sake cewa komaiba suma sukai shiru ba wanda yace komai haka ta miqe daga dinin ta koma daki batareda ta iya cin abincin kirki ba,

Kasa kiransa tayi kaman yanda ta saba sbd bazata iya magana dashiba,

Kiransa ya shigo wayarta still kasa dagawa tayi tana kallo ta tsinke tana jin dole ma taje boyem.

Sai yamma su bahar suka dawo basu wani gane komaiba a gidan sbd kowa yayi tsit gidan ba kanta dan haka suma abinci sukaci suka fada karatu har dare ba wanda ya fito ko abinci kowama daban daban yaci nasa,

Bahar cikin damuwa take sosai batareda kowa ya saniba gabaki daya tarasa gane kanta karatun ma yinsa takeyi tana jin kaman baya shiga sbd hakanan take jin damuwa da fushi akansa lokaci daya hakama gashi Ammi ta gane tayi tafiya kowane minti da second tsoron kada Ammi ta gane ko ta fahimci dashi tayi tafiyar take amma duka wannan fargaban da tashin hankalin ita kadaice takeyi shi yama manta da ita da abinda zai biyo bayan idan Ammi ta sani dan haka fushi da bacin rai take ciki sosai wanda ya sana hadda wayarta ta hada haushin ta kashe kwata kwata ta ajiye.

Washe gari Neesah ta tattara ta koma hostel tabar gidan tabarsu a cikin yanayin da suke ciki,

Ammi tafiyarta boyem tafara shiryawa a lokacin ne Bahar taji maganar tafiyan a bakin Maa tenya da laifinsu na boye zuwan NUAB dan haka hankalinta yayi mummunan tashi ta shiga rawar jiki da rudanin jin Ammin tasan da zuwan NUAB,

Dakinta taje da gudu ta rufe ta zauna a qasa ta ringa kuka kaman ranta zai fita tanajin rayuwarta tagama tsayawa tinda Ammi taji abinda ya faru,

Wuni tayi tana kuka mai tsima zuciya daman kukan ne yake cikeda kirjinta tsawon wannan lokacin dan haka a wuni guda kammaninta suka sauya tayi jajir idanuwanta sukai luhu luhu ko ruwa ta kasa fitowa tasha.

Har dare bata fito ba bata bari kowa yaga yanayin datake ciki ba,

Harta kwanta aka bude kofar dakin aka shigo a natse.

Ammi ce ta iso har bakin gadonta ta zauna tareda dan qara hasken dakin kadan tana kallanta.

Cikin damuwa ta kalli fuskanta data kumbura sosai kammaninta sun sauya tace

'Subhanallh Bahar??

Kafin ta sake wata maganar Bahar din ta fashe da sabon kuka tana tashi zaune ta sauko qasa ta zube gaban Ammin tana kama kafafunta tace

'Wallahi Ammi shine yamun dole bada son rainaba,
Ammi ko su Maa zasuyi shedan dole yamun,
Hakama ko tafiyar Birmingham daga zuwa ganin likita ya tafi dani bada son raina ba dan Allah Ammi kiyi hkr kada kiyi fushi akan hakan ki tafi Boyem ki barni Ammi bazan sake ba dan Allah kiyi haku.....

Somewa kusan Ammin tayi daga zaune idanuwanta na tsayuwa cak akan Bahar din cikeda mamaki me girma na jin sabon zance kuma bayan wanda takeji a kwanakin kullum,
Me bahar din ke nufi?

Miqewa tayi hannuwanta na dan rawa ta kasa cewa komai sbd ita lura da yanayin sanyin Bahar din daya saura rayuwanta a kwanakin ya sakata jin tausayinta takejin ko zata tafi da ita ta yawato ta dawo ko zata koma daidai duk da batasan meyake damunta ba ya sakata zuwa dakin amma tana jin sabon zancen tashin hankali.

Kafe bahar din da ido tayi tana rasa abin cewa har lokacin tana qare mata kallo zuciyarta na bugawa da abinda ke shirin faruw tace

'NUAB dinne ya miki dole?
NUAB dinne ya tafi dake Birmingham daman?
Me kukaje yi acan?
Meye hadinki da tafiyarsa?
Duka su sakinah suna me harya kwasheki kuka tafi?
Tafiyan wuni guda ce ko kwana?

Rikicewa bahar tayi da tambayoyin tayi shiru tana tsiyayo hawaye wanda ya saka Ammin jin tafara fusata dan haka juyawa tayi tabar dakin ta nufi dakinsu sakinah kai tsaye.

Tana zuwa tambayar data jefa musu shine meya faru tsakanin NUAB da Bahar?

Da mamaki suka kalleta kafin sukai shiru take tinaninta yake inda bata son yaje wani baqin ciki da bacin rai take ya rufeta ta rasa abin fada ta juya tabar dakin tana zuwa wayarta ta dauka ta kira tace ticket din tafiyarsu takeso na tafiya dukansu a goben.

Tana kashe wayarta numbern NUAB data kasa dauka kwana biyun ta kira ido rufe.

A natse ya dauka cikin kwanciyan hankali sbd tinda ya dawo boyem baya cikin nutsuwansa sbd ayyuka da 'yarta data tsayar da rayuwarsa guri daya cak.
Chapter 68 · 0% Book details