← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 112

Sashe 19

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asim ma a wannan lokacin ya biyo duhun daren ya nufi inda su Bahar din suke da wata irin mummunar wuqar da zai kashe duka wainda suke bangaren Dan tafiya da ita ciki kuwa hadda Leylah baida niyar barin kowa Salman na tareda shi shima da wata muguwar takobi me muni a hannunsa.

Haile ma a wannan lokacin bangaren ta dosa tareda masu kakkarfan bayi biyu da zasu daukan mata ran Bahar kafin Asim yayi tinanin isa ta gama ta koma Dan hakan kadai zai saka ya dangana ya kama abinda yake gabansa.

A lokaci daya kusan dukansu suke kokarin isa bangaren wanda tin daga nesa securities din da sultan ya saka suka fara fitowa Dan bawa bangaren kariya da rayuwarsu su kuwa su aleey Kai tsaye suka Bude wuta kawai wanda ta saka gabaki daya masarautar daukan dirar fitar bullet din daya saka duniyar boyem daukan tsit ga haile da Asim duka suna cikin bangaren a gurare daban daban take kowannensu ya tsaya cak cikin mummunan tashin hankalin da baa saka masa rana ba kafafun haile na jiqewa da wani irin zufa kaman yanda kunnuwan asim ke tsiyayo wani zufan da bai san daga Ina yake fito masa ba sbd mummunan tashin hankalin da baida kama.

Wata irin kakkarfan sautin karar data karade gabaki daya ciki da wajen masarautar boyem tana ratsa cikin gari da qasar ne ya dakatar da komai da kowa dake boyem da zagayenta  cikeda firgicin da baa taba shiga ba sbd sauti ne na bayyanar da sabon sultan a karagar mulkin boyem me tarihin da duniya tasan dashi.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

90
Coming kunnuwan aleey sautin yake ratsawa yana tayar da kowace tsigar jikinsa yana sbd sanin LEUL dinsu ne kadai Wanda ya isa ya amshi mulkin sarautar boyem kaf duniya a lokacin,

Sauran yaran gabaki daya dauke wutar dasuke sakice sukai wadda take jijjiga har qasar masaurautar sbd duk inda kake a masarautar kana jin yanda qasa take amsa irin wutar da aka bude ana sakewa wanda ya saka duniyar boyem daukan tsit.

Duk inda kake a ciki da zagayen masarautar harma da garin gabaki daya sautin yakai maka na hawan sabon sultan a tsakar daren abinda baa taba yi ba a tarihi dan haka komai ya sake daukan tsit din da babu motsi,

Aleey ne ya fara kai gwiwowinsa a qasa daga inda yake tsaye cikin tsananin
Girmawansa ga sultan LEUL NUAB da matarsa dake cikin gaban inda suke tsaye,

Gabaki daya kowa zubewa yayi qasa ba iya su kadai ba kaf duk wanda yake masarautar zubewa kowa ya fara yi akan gwiwowinsa suna sadda kai qasa hatta manyan fada dake zaune cikin tsaka me wuyar gaske da zullumi me girma shigar sautin kunnuwansu ya saka kowannensu dagowa a cikin matsanancin tashin hankali da mummunan fargaban dayafi wanda suke ciki dan kuwa hawan sabon sultan da tsakiyar daren da babu wanda ya sani hakama ba sanin waye ya sakasu shiga zullumi me karfin gaske daya saka tashin hankalinsu komawa akan sultan din koma waye amma a haka suka zame qasa suna zubewa akan gwiwowinsu dan bada girmamawa me karfin gaske tsigar jikinsu na tashi da shigar sautin da babu karya a cikinsa zuwa cikin kunnuwansu.

Su kansu securities din da suke tsare dasu zubewan sukai tin daga fada har wajenta har securities dake gate na farko dana biyu dana uku dake wani irin kokari da gaggawan isowa ciki da nasu mahaukatan makaman sbd kukan bindigogi masu karfin gaske dake tashi a cikin masarautar saukar sautin ya saka kowannensu dakatawa daga inda yake yana zubewa qasa kawunansu a suna tabbatarda akwai abinda yake faruwa a cikin masaurautar dan haka sautin da mintinan da ake dakata komai dan bada cikakkiyar girmamawa suke jiran ya cika su fada inda ake bude wutar su bawa masarautar tsaro da kariya daga dukkanin abinda yake kolarin biyowa baya.

A daidai lokacinda sautin ya ratsa kunnuwan Haile wadda take cikin mummunan tashin hankalin harbin bindigogin daya fara tashi kawai tako ina ba tsammani dakatawa tayi cak daga bude kofar bangaren datai harta saka kafafunta a ciki manyan samudawan data zo dasu suna bayan,

Wani irin dummmm taji kunnuwanta na daukewa daga jin komai na duniya bayan sautin dayake cigaba da ratsa kunnuwanta yana wucewa kai tsaye zuwa ga kwakwalwanta wadda itama tin kafin sautin ya gama isar mata ta dena aiki ta dakata da kowane aiki cak idanuwanta ma fara dauke gani sukai a cikin seconds din da basu kai uku,

Wani irin mummunan zufan dayake hade da maiqon kitsen jikinta dayake narkewa take ne yafara gangarowa daga cikin rigarta zuwa kafafunta da sukai mummunan nauyin dayafi na buhun siminti,

Girgiza kanta tayi cikin wani irin slow sbd dawo da jinta dayake barinta da ganinta amma sam babu alaman gangar jikinta zata sake moruwa ko dawowa daidai daga wannan mummunan shock din na karshen rayuwarta....

Zubewa tayi gabaki daya jikinta na wata irin fizga da jijjiga tareda mummunan zafin jikin daya gauraye jikin nata a take sbd yanda jininta yake wata irin konewa bama tafarfasa ba,

Da sauri baiwarta daya data taho da ita tayi kanta tareda tareta tana kokarin ambatar sunanta amma ba damar hakan dan haka riqeta kawai tayi da sauri tana hanata qarasa zubewa jikinta yana rawa sosai sbd tsoro da fargaban halinda suka ga tana shiga dan kuwa da gasken gaske mummunan balain da masifar da kunnuwanta suka ji mata dauke jinta da ganinta yayi tareda dakatar da kwakwalwanta daga aiki dan haka jikinta ke wani irin rawa yana qarawa tana kokarin bude baki tayi magana amma bakin nata juyewa yake kokarin yi sbd wannan shine shock na karshe da rayuwarta ta samu wanda yake tabata tana ji gefenta daya na kokarin kasawa dan haka ta fara kokarin yunqurawa da karfi ko zata mutu ko rabin jikinta ze dena aiki saita tabbatarda ta kawar da bahar kaman yanda ta kudurta idan ta aikata lahira zata san waye ya hau wannan mulkin da shine abinda take ganin tazo duniya nema,
Koma waye a wannan daren ya karbi mulki matiqar ba Asim bane wlh bazata taba shaqar numfashi me karfi ba saita fara kawar da sultan daga duniya kafin ta tarwatsa mulki da masaurautar boyem gabaki daya.

Wani irin mummunan jan da baida kyan gani idanuwanta sukai hannuwanta da kafafunta na wata irin rawa da zufan gaske wanda yake tsiyayo mata ba kakkautawa ta ta miqe tsaye tareda miqa hannu aka saka mata wata mummunan karamar wuqar da batada kyan gani ta riqeta da kyau a hannunta datake jin yana kasawa sbd paralysed din gaske take neman kamuwa da shi dan yanda jininta yake hauhawan gaske yana kokarin harbawa cikin kwakwanta da zuciyarta dake bugawa da mummunan karfin gaske.

Jan da idanuwanta sukai har wasu hawayen dake bayyane da tsanani tsananin baqin ciki tsagwaronsa da tashin hankalin daya fiddata hayyacinta ta bude baki kai tsaye muryanta na rawar tsananin baqin ciki me girma dayake sake kumbura zuciyarta tace

'Duk me rai dayake bangaren nan kada abar kowa da rai,inason kowane bango na bangaren nan ya qawatu ya koshi da jini,kada rai ko daya ta fita.'

Tana fadar hakan ta daga kafafunta dake rawa basaji koina jefawa sukeyi tayi gaba tana saka kai a palon wanda baiwar dake bakin kofar daga ciki kai tsaye kafin tayi motsin komai ta ratsa wuqar hannunta me kaifin gaske maqogoronta wanda take wani irin jini ya feso da karfi har yana bata fuskarta gabaki daya amma bata tsaya ba ta zare wuqar da karfi yana wucewa ciki idanuwanta a tsananin rufe hakama zuciyarta a rife kaman yanda kwakwalwanta ta gama rufewa ruf.

Wainda suke bayanta suma ba imani suka hau cika umarnin data basu suna kashe duk baiwar da suka hadu da ita a bangaren babu imani ko tausayi ko daya a fuska da idanuwansu.

Asim dayayi mutuwar tsaye tin lokacinda sautin ya sauka a cikin kunnuwansa yana ratsa zuciya da kwakwalwansa shima haka ya ringa jin ganinsa na kokarin daukewa da jinsa kafafunsa kaman wanda aka saka kafa aka kwashe haka ya zube a gurin mummunan jiri na dibansa daga zuben a qasa kawai komai yake ganin yana juyawa dashi numfashinsa na kokarin daukewa zufa na gangarowa ta kunnuwansa ciki da waje,

Salman dayake cikin mummunan shock din abinda yaji din shima da tashin hankali me tsananin gaske na harbin da daman shine ya fara Girgiza duniyarsu da rikitar da ita zubewa qasa yayi tareda kokarin Asim dayake wani irin layi daga qasan dayake a zube kan gwiwowinsa,

Jini ne ya fara gangarowa daga hancin asim din me kaurin gaske da yawa wanda ya saka Salman sake shiga wani irin mummunan tashin hankali jikinsa na sake daukan wata irin rawa,

Kokarin sake kamosa yakeyi yana kasa goge masa jinin a daidai lokacin soldiers din masarautar suka iso gurin da makamansu suka bude tasu wutar data saka su aleey sake bude tasu wutar aleey ya bude baki da karfi yana bawa yaransu umarnin kada su saurara matiqar ba Queen din su ce ta dawo hannunsu ba.

Hakan daya fada tamkar ya zubawa wutar dake cikin zuciyoyin nasu soldiers din fetur ne dan kuwa su abinda suka iya kenan hakama matiqar wani abin ya samu tasu princess din da seconds da suka wuce ta koma queen ta shiga hannunsu ba a shirye suke da cigaba da bude wutar da zata qawata masaurautar boyem da fresh jini me dumi.

Irin wutar da ake budewa ta saka salman sake shiga mummunan tashin hankali yaci gaba da kokarin tada asim din ko jansa su bar gurin dan kuwa matiqar yaran LEUL din suka shigo suka samesu bazasu bata second daya ba batareda sun fasa kawunasu da bullet ba a banza dan haka yake gaggawar jan Asim din shima yana wani irin zufan mafi girman tsautsayin daya kawosu.

Jan Asim din yafara yi zufansa da rawar jikinsa na qaruwa gashi sun riga sun shigo baisan ta inda zasu fita ba dan wutar gaske ake budewa wadda qararta ya saka komai na duniyar baka ji bayan wata irin jijjiga.
Chapter 19 · 0% Book details