← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 112

Sashe 16

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ASIM da duniyarsa ta tsaya cak wutarsa daukewa tayi jinin jikinsa na tsinkewa zuwa ga daskarewa a take sbd kunnuwansa da basu ji abinda yaji din ba a daidai.

Kaman bugun iska haka yaji Wani mahaukacin karfi Yazo masa ya zaburo daga inda yake har yana kifewa ya kasa miqewa ya rarrafo daga Wani irin karfin gaske gaban sultan Wanda ya kafe NUAB da idanuwansa tasa wutar na kunnuwa da Zafin ikon dayake cikinsa mai karfin da a yanzu zai nunawa ‘dan nasa shine ubansa kuma ko me yake ji a gurinsa ya debosa,

Hannu ya miqawa kadir Wanda ya iso da babban tray din dayake tamkar na gold dauke da stamp da inda ake rubuta decree na masarautar ya dauki alkalamin da yake fidda gold rubutu ya shirya tsaf da fara rubuta abinda sultan zai fada.

Cikin muryan data amsa Wani kausashen Amo a cikin fadar daya tada gashin jikin duk Wanda yake gurin sultan yace

‘Duk magaji wanda yake jinin BOYEM tin tsawon tarihin kakannin farko babu Wanda ya taba auren macen da ba jinin BOYEM ba dan haka Ayau magaji LEUL BOYEM wato Zakin BOYEM NUAB ALMAZZ YASAR ya karya wannan dokar da babu Wanda ya karyata Kai tsaye NI SULTAN ME BOYEM DA ZAGAYENTA,ME IKO DA MULKIN DUK ME RAN DAYAKE BOYEM NA YANKE WA YARINYAR HUKUNCIN KISA A GOBE DAIDAI WANNAN LOKACIN sbd kawar da fitinar da zata shiga tsakanin magadan guda biyu Akan macen da daman jininta ya halas ga BOYEM sbd karya dokar Masarauta’

ASIM da hankalinsa ya gama ficewa jikinsa kafin sultan yakai karshe baisan lokacinda ya manta shi waye ba ya Dora hannu akai ya zunduma ihu me karfin gaske yana rarrafowa gaban sultan Wanda take kadir ya miqa masa rubutun hukuncin nasa ya dauki stamp ya buga masa yana dawo da kallansa kan NUAB.

Manyan fada gabaki daya rikicewa sukai jikinsu na daukan wata irin rawar da basu shirya ba sbd ganin yanda NUAB yake rikida yana ja tamkar hawainiyar dataji muguwar rana me Zafi jijiyoyin kansa suna wata ratsowan data sakasu sake shiga mummunan halin matsanancin tsoron ruwan Harbin da zaa iya yi a kowane lokaci da kuma shock na hukuncin sultan din dama shock na jin wata a matsayin matar NUAB duk sun rikice a Zaune ba damar motsi sai Wani irin zufa mara tsaiko ko kadan da suke fitarwa.

Cikin idanuwan NUAB sultan ya kalla sbd kafesa da ido da NUAB din yayi batareda motsawaba,

Aleey dake baya a tsaye shima fitowa jijiyoyin kansa suka ringa yi ya sauke kansa qasa yana kasa dagowa sbd yana jin radadi da wutar dake cin jini da zuciyar LEUL dinsu a jikinsa harma da Sauran duka yaran.

Miqewa sultan yayi batareda qara kalma ko dayaba yabar fadar dake ci da wata wutar da baa gani sedai radadinta dake ratsa kaf jamaar gurin.

Kadir umarnin dayake a rubucen ya iso gaban Aleey ya Dora masa a hannunsa ya juya yabi sultan ta kofar daya fice.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

86
Asim dayake bin bayan sultan da wani irin rikitaccen rarrafen tashin hankali yana Neman afuwa me tsananin gaske akan hukuncin da aka yankewa rayuwar Bahar din da idan tabar duniya bazai iya rayuwar dazai moru ba yana kawowa da rarrafen kadir na rufe kofar hanyar wadda Kai tsaye hanyar palon farko na sultan din Zara kaika daskarewa yayi a gurin hawayensa na tsantsan tashin hankali da rikitaccen yanayi suna kasa riquwa ya zube zaune a gurin yana jin har lokacin duniyarsa na juyawa cikin wutar tashin hankali,

Su kuwa gabaki daya yaran NUAB dake kofar gurin fidda bindogoginsu da munanan makamai sukai daga jikinsu suna tsare kofar tareda jiran motsi kadan da bazasu qara second daya ba batareda sun fasa kan koma wanene ba,

Tsit gurin yake sake dauka Babu wanda ya motsa sbd baa isaba
Halin da ubangidansu yake ciki Babu wanda zai motsa bayan sultan da bazasu aikasa kwanciyan Hutu ba,

Motsi bayan na fitar numfashi gabaki daya fadar Babu wanda yake yinsa zufansu ne kadai yake gangarowa daga fuskokinsu yana jiqa jikinsu musamman ministan hukunci na masarautar da hatta yatsun hannuwansa gumin gaske me zafi suke fitarwa da cikin kunnuwansa sbd shine me hukuncin zartar da cikawan wannan hukuncin dayake Kai tsaye umarbin sultan ba gudu da ja da baya Amma ayau bayajin rayuwarsa ma Zata iya kaiwa goben bare ya shedar da hukuncin dayake nufin qarshen rayuwar zuriarsa kaf Dan kuwa ko a tarihi idan ana badawa akazo gurin irin mutuwar da zaiyi sai an zubda masa hawaye bana baqin cikiba sedai na tausayin zuriarsu ta qare tas a dare daya Babu saura,

NUAB dake tsaye har lokacin bai motsaba sbd mummunan yaqin dayake yi da masifaffar wutar dake cin zuciya da duka kowace tsokar dake jikinsa,

Kowane irin hukuncinsa me kyau ko mara kyau suke Jira su aikatar batareda tausayin kowace Rai dake gurin ba Dan haka suke a tsaye a shirye da makamansu da fit daya zasu raba gangar jiki da bugawan numfashinta,

Babu abinda suke so kaman ya basu daka su wanke bangon cikin fadar da jinin munafukan dake ciki a zaune,

Bude idanuwansa da sukai jajir din da tinda yake basu taba yi ba ya saukesu akan kujeran karagar mulkin boyem dake daukan ido wadda sultan ya tashi akai,

Wata sabuwar wuta ce take babbaka a cikin jininsa tana sake sauya kammaninsa da suka koma kalar tsoro ba kyan gani sbd tamkar bai taba sani hankali ba bare Imani haka ya koma tamkar zakin daya gama kaiwa maqurar karshen rashin Imanin tausayawa mutum dayake gani a nama a gabansa,

Juyowa yayi yana takowa zuwa kofar ficewa fadar na sake yin tsit cikeda tsoro da Fargaba tareda tashin hankali me tsananin shakkar kada yana ficewa yaransa su Bude musu wuta Dan shafe tarihi wannan ranar.

Yana kawowa Kofa suka sauke Bude masa hanya batareda sun saukar da kowane makaminsu ba hakama basada niyar hakan,

Aleey ne yabi bayansa da security biyu ya Dan tsaya ya Bude Baki da muryansa datai mugun nauyi yace

'daga nan har gobe kada wanda ya fita daga fadar har sai Ghaz princess ta bayyana idan hukuncin da aka yanke yana Neman tabbata a tabbatarda sune zasu tarbeta a inda Zata din'

'zakonchil Ser(done sir/angama)' team leader din na securities din ya fada yana yiwa muguwar bindigarsa wani arnen gyaran daya saka cikin ministan hukunci fidda wani sautin kukan daya saka idanuwansa rufewa cikin mafi munin tashin hankalin ganin wannan ranar da yaqin tada masarautar boyem yaxo musu bazata bagatan,

Bin bayan NUAB aleey din yayi yana jin karfin shirinsu tsaf akan abinda zai iya biyowa goben da Zata iya zama ranar yaqin boyem badan karban mulkin ko dukiyar qasa ba sai Dan ran mutum daya ita kadai.

Kai tsaye bangarensa ya nufa wanda take securities na nan din suka miqe yana shigewa Aleey ya bada umarnin kowa duniya kada a bari ya shigo idan ba Ammi ce tazo da kanta ba,

Suna shigewa securities suka shirya aikata komai akan duk wanda zai ratso bangaren.

Asim da kansa ya gama kuncewa gabaki daya miqewa yayi shima ya nufo kafar baya ko ganin gabansa ya fice daga fadar batareda an hanasa ba sbd shi Banda shi manyan fada akace su tsare,

Tamkar zai mutu yakeji sbd yanda zuciyarsa ke mummunan bugawan da bana lafiya ba sbd bazai taba iya bari ba bare kallan a raba Bahar da rayuwarta ba,
Duk yanda yake jin yana tsananin sonta ta wuce hakan a zuciya da rayuwarsa,

Babban tashin hankali da shock biyu ne suke Neman zarar dashi jin NUAB dake a ambaci kalman aurensa akan Bahar din da tasa ce tin farko da kuka hukuncin sultan akanta da bazai taba iya daukaba Koda kuwa hakan na nufin qarshen tasa rayuwar to sedai yabi Bahar su mutu a tare.

Bangaren Wishmah ya nufa Kai tsaye hankalinsa na sake rikicewa ya manta tareda ajiye dukkanin tsanarsa a karan farko ya shiga bangaren Wishmah,

Yana shiga bangaren bayin dake bangaren da basu taba ganin hakan ba zubewa qasa sukai da saurin gaske suna sauke Kansu a qasa cikin rawan jiki suna gaidasa Amma sam bayajin komai,

Rasa inda ma zaibi ya shiga palonta yayi daidai lokacin Maa sakinah da itama bata cikin sukuni ko walwala ko daya sai tashin hankali da zullumi ta fito,

Ganin Asim ya sakata dakatawa da karfin gaske tana kallansa zulluminta na qaruwa musamman yanayin halin data gansa a ciki ta Bude baki Zata cika al'adar gaidasa a matsayinsa na magajin masarautar boyem din,

Katseta yayi cikin mummunan yanayin daya sake sakata shiga zullumi me girma yace

'Ina tsananin buqata da son sanin a wane bangaren Bahar take kafin wayewan safiyar gobe,
Hakama Ina buqatar sanin gaskiar matsayin Bahar Dan tabbatarda maganar auren da NUAB yake magana nasa yana kanta.'

Kallansa Maa tayi tana tambabar tambayar tasa tareda tsananin mamaki da fargaban be off kafin ta tattaro nutsuwar da batada yawa ta Bude baki tace

'Suna kebantaccen gurin da babu wanda yakeda sani sedai idan sun fito kuma'

Kasa yadda da hakan yayi ya kalleta da sauri yana jin zuciyarsa na sake daukan nauyi da tsananin zafi yace

'kada ki boyen hakan idan har kinsani sbd a yanzu nine kadai wanda zai iya cetan rayuwarta'

Kasa gane inda yake dosa tayi Dan haka ta riqe bakinta daga fada masa komai wanda hakan ya sake Kai zuciyarsa dake Neman bugawa a wuya ya dauke idanuwansa daga kanta yana maidawa akan Wishmah dake fitowa a natse cikin wani irin sanyi
Bayin suka qara sauke Kai suna mata barka da fitowa sbd bata cika fitowa ba har wajen palon gabaki daya,

Da tsananin mamaki itama take kallan Asim din zuciyarta na harbawa sosai da zullumin dayake qara shigarta.

Kallansa yakeyi shima kallan tsaf yana kallan macen data haifa masifa da balain rayuwarsa,
Macen data kawo masa baqin cikinsa Dana uwarsa a duniya,
Macen da sultan ya nunawa duniya itace din dai a lokacinda ya maida ta cikakkiyar Wishmah dinsa.

Dauke kallansa yayi daga kanta yana jin wani Abu me karfin gaske yana danne kirjinsa da radadi me zafi da kaifi,
Chapter 16 · 0% Book details