← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 112

Sashe 14

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya Aleey ya fidda ya saka kiran NUAB yana dauka cikin baccin daya koma take aleey ya sanar masa abinda yake faruwa a kofar na Bahar ta tsaya Akan saita bi Maa.

Katse wayar yayi tareda saukowa gadonsa ya fito wannan Karan babu komai a jikinsa Bayan tight short din Wanda ya saka lafiyayyar fatar jikinsa bayyana sosai tana Wani daukan ido tareda kakkarfan jikinsa
A yanda yake yana bacci a hakan ya fito babu abinda ya damesa yana fitowa dukkaninsu suka sauke Kai sbd girmamawa suna gaidasa.

Akan Bahar idanuwansa masu tada tsigan jiki a daidai lokacin sbd baccin daya taso suka sauka tana jin saukan idanuwansa akanta taqi juyowa saima sake riqe hannun Maa tayi wadda itama bata juyoba tana cigaba da tsiyayo hawaye.

Kallan seconds yayi mata batareda yace komai ba kafin ya kalli aleey yace a barta ta tafi kawai sbd yasan bama Wanda Zai iya komai akanta.

Bai bude Baki ya furta ba kallan aleey kawai yayi ya Juya Wanda aleey yasan me hakan ke nufi ya kalli securities yace su bari ta tafi kawai.

Bada hanya sukai suna bata hakurin da bataji bata gani fatarta kawai tabar gurin.

Suna barin bangaren ta sake riqe hannun Maa da dan karfi tana goge hawayenta da hannu daya zuciyarta na dan samun sassauci.

Suna isa bangaren wishmah Kai tsaye daki suka wuce Bahar na shiga ta sauke ajiyan zuciya me sanyi a boye tana Zaunawa kan sofa ta dafe goshinta tana rufe ido tinaninta na dawowa damuwa da tsananin jin tsanar nan din yana sake shigarta da gaske takeyi ANJOM take so tafi son can Akan nan din.

Maa sakinah toilet ta shiga tana fitowa ta samu ta dan kwanta dan kanta ciwo yake itama sosai sbd bata rintsa ba kuma a yanzu ma da Bahar din ta biyota tsoronta da zulluminta yafi qaruwa.

Baccin da bata tsammata bane ya saceta me karfi Wanda Bahar ma data dade Zaune shiru cikin damuwa Salmah na shigowa gyaran dakin da zata fita sai kawai ta miqe a sanyaye da babbar doguwar Riga a jikinta ta bita zuwa kitchen cikinsu ko zata samu dan sassaucin damuwan datake ciki.

Karfe goma na safe NUAB ya da securities dinsa suka bar cikin masarauta zuwa Wani business da shine dole zaiyi sealin nasa hankalinsa kwance ya tafi sbd yasan koma me ASIM zeyi hukuncin da zai masa ko mahaifinsa bazai qwacesaba dan haka ya tafi ba shakkar komai.

Karfe biyun rana tanayi dukkanin shirye shiryen wankan lalle dana fara gyaran Amarya Leylah da mahaifinta ya aiko dukiyar gaske dan gyaranta da zaa fara daga yau din a inda ake gyaran kowace macen jinin BOYEM kuma a gurin ake gyaran kowace imebeti sbd itama sultan zata zama tasa dan haka NUAB na ficewa takardar ranar auren ta kuma fitowa daga sultan wadda ta sake rikita masarautar da fara shiri da murnar auren Wanda zaayi a sati biyu masu zuwa.

Komai da komai na musamman na gyaran mace zuwa matakin karshe na fitowanta mace ya kammala daga bangaren tenya dan haka Kai tsaye Bayin bangaren ta fara tarawa batareda Shan wuya ba kuwa ta samu Bahar din a cikinsu dan haka ko toilet bata bari ta tafi daga inda take tsaye tasa aka jata zuwa inda zasu.

Suna fitowa sakon kira daga sultan ya samu tenya dan haka ba bata lokaci ta aika su ita kuma ta wuce.

Bata jimaba ta dawo da umarnin sultan me Zafin gaske daya sakata cikin wasu irin manyan shakka da zullumi harma da tinani me tsoro Kala Kala sbd Kai tsaye kebataccen gurin da daga Bahar har Leylah bazasu fitoba sai Angama musu komai tas tukuna hakama babu Wanda zai san a ina suke a cikin masarautar har a kammala ko wanene bazai sani ba wannan umarninsa ne dan hatta ita bazata fitoba sai komai ya kammala.

Cikin shakka aka kaisu Wani sabon bangaren da babu Wanda yasan dashi an riga an tanadar musu komai dan haka ko yawo babu me shiga bare fitowa daga su se bayin da aka tanadar musu.

Koda suka isa Bahar na cikin mummunan halin damuwa me girma da baqin cikin da batasan ma yata zata furta ba sbd kowace dama an rufe mata dan haka Kai tsaye Wani lafiyayyan babban dakin dayake komai iri daya da Wanda aka kai Leylah aka kaita tareda rufo mata kofa aka barta tsaye tsakiyar dakin tana bin kofar da idanuwanta da sukai jajir.

Silalewa tayi ahankali tsakiyar dakin tana zubewa qasa tareda dunqule jikinta guri daya tana Jin hawayenta na kafewa sbd girman halinda take jinta a ciki.

Tayaya zata zama imebetin kowa a duniya Bayan ita din ba baiwa bace,
Ba siyanta akai ba,
Jinin sarauta ne yake yawo a jikinta kuma komai lalacewan tata sarautar mulki dai mulki ne,
Tayaya zata zama macen da amfaninta kwanciya da biyan buqata ne?
Tayaya zata zama imebetin Wani wanin ma Wanda yake matsayin dan uwa ga wanda akwai igiyoyin aurensa akanta Wanda a yanzu koma yayane tana fatar zafinsa ya kubutar da ita ga wannnan masifar data samu kanta.

Tenya kuwa babban gyara zatai wannan Karan sbd Matar NUAB dinta ba matar da zatai wasa da gyaranta bane ko kankani hakama imebētin ta ASIM zata samu komai dakyau daidai da Leylah sbd ta cika umarni da tsarin al’ada.

Karfe hudu daidai tana bugawa aka fiddo su zuwa gurin wankan dayake cikin inda suke bayi na jere suna jiransu.

Bahar ganin inda kaddara me muni ta kawota kuka ta fasa mai tsima zuciya tana qanqame jikinta a lokacinda ruwan lallen masu dumi sosai da Wani irin kamshi suka fara ratsata.

Leylah dake cikin baqin cikin ganin Bahar din da zallan asalin kyau datake dashi batareda tambo ko daya a jikinta ba komai nata nutsuwa da kwanciyan hankali kawai yake nuna duk da a cikin kuka na Wani irin mummunan baqin ciki da tashin hankali take Wanda hakan kuma yake dan sanyaya zuciyar Leylah din tareda ganinta cikin ruwan lallen auren NUAB dinta.

Dukkanin yanda al’ada ta tanada na jiqon su a cikin ruwan lallen masu dumi da qamshi tareda wasu abubuwan haka akai musu wuni guda sai yamma sosai suka koma dakunansu zuwa lokacin qarfin Bahar ya fara qarewa gurin kuka yanzu tsoro taji yana shigarta tana fatar zuwan NUAB a Karan farko na rayuwarta sbd shirin gaske gadan gadan akeyi na tabbatarda zamanta imebētin da tafison ta mutu tabar duniya da hakan ta kasance da ita,

Acan kuwa Maa sakinah koda ta farka bataga Bahar ba Jin tayi tana Neman zarewa sbd samun tabbacin an tafi da ita kenan.

Rawa da Wani irin fizga jikinta ya fara yi ta kasa zama ta kasa tsayi sai ta nufi hanyar dakin Ayanah ta dawo sbd batasan me zata fada ba tinda a daure take da mugun Alkawarin da Ayau bataga ranarsa ba duk da sunyi hakan ne dan hana dawowan ciwon Ayanaah dan kila bazata iya daukan labarin Abaas baya duniya ba ya tafi yabarta bar abada sedai a mafarki.

Fitowa tayi a karo na biyar tana zuwa duba NUAB ko ya dawo amma bai dawo ba dan haka ta sake dawowa.

ASIM duk da bangaren mahaifiyarsa tamkar Ayau Ana zaman makokin mutuwarsa ne sbd tarin baqin cikin da suke ciki tamkar zuciyoyinsu zasu bindiga su watse haka suke ji amma shi a zuciyarsa yau tafi masa kowace rana sbd tabbacin zuwa Yanzu imebētinsa ta shiga ruwan wankan lallen daya wanketa daga budurwa zuwa macen da zata tare.

Tsananin farin cikin dayake cikinsa ne ya saka a fada ya wuni cikin manyan fada da aketa meetings da zama Kala Kala Akan auren NUAB da imebetin ASIM.

Sai dare sosai motocin NUAB suka sako Kai masarautar dan haka Kai tsaye Hutu yake buqata yana shigewa aka rufe kofar bangarensa sai safe kuma.

Asubar fari tenya ta tadasu tareda jiqa su a cikin ruwan madarar da wasu abubuwan Wanda suka saka jikinsu mutuwa sosai basu kammala ba sai karfe goma kowacensu na komawa daki baccin abinda yake cikin abinda suka sha ya daukesu a buge babu Wanda ta sake motsawa alaman farkawa bacci sukeyi sosai me karfin gaske.

Karfe Tara Maa sakinah na safe ta isa bangaren NUAB bai farkaba a lokacin dan haka zaman jiransa ta dasa sbd tin jiya wayoyinsa a kashe suke haka ta wuni kira babu me shiga gabaki daya ta fice hayyacinta sbd hatta bangaren da Bahar zata zauna a matsayin imebeti har an fara shirinsa da sunanta da komai.

Aleey ne ya fara fitowa yana ganin Maa ya mata kallan seconds take ya hango ba lafiya gaidata yayi tareda kallan kofar dakin da Bahar take ya dawo da kallansa kan Maa din wadda gabaki daya hankalinta kaman baya jikinta dan kuwa ko rufewa idanuwanta da sukai jajir basu yiba a Daren bare rintsawa.

Time Aleey ya kalla yaga lokacin tashin NUAB beyiba amma bayajin ko wace matsala ce Maa tazo da ita zata bari ya barsa sbd dole abu biyu ne kodai Amminsa ko GHAZs princess.

Kai tsaye hanyar bedroom dinsa datake a killace baa ma ganin hanyar ya nufa yana daga wayarsa dan saka kiransa batareda shiga dakin ba.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

84
Cikin bacci a natse ya miqa hannunsa ya dauki wayar da aleey ne kadai yake kiransa da ita sbd emergency,

Yana dauka baya buqatan magana maida sexy idanuwansa na bacci masu tayar da gashin jiki yayi ya Lumshe maganar Aleey daya fara masa bayani a natse tana shiga kunnuwansa daya bayan daye a kammale.

Bude idanunwan nasa yayi a gabaki daya a hankali batareda ya motsa ba bare cewa komai,
Kashe wayar yayi Bayan ya dan Lumshe ido yana jefar da ita gefen gadonsa dayake tsakiyar dakinsa cikin wani irin tsarin dayake da daukan ido da kyau da aji.

Baro aleey yayi yana fitowa daga hanyar wadda ta saka Maa sakina kallan hanyar sai taga ba NUAB din bane ta miqe tareda ficewa Bayan ta cewa aleey tana Neman NUAB din da gaggawa idan ya fito.
Chapter 14 · 0% Book details