← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 112

Sashe 51

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan sakin fuskarsa yayi yana daga mata tasa girar shima wanda hakan ya saka shuraim dake tsakaninsu jin wani iri sbd kaman ba yanxu suka gama fada ba harsun shirya da dagawa juna gira cikin sexy way bama tareda kila sunsaniba da manta yana guri.

Barin palon Leylah tayi ta nufi dakin da akace mata shine na Bahar shima kofarsa tana dan daga lungu kadan tana isa kai tsaye ta bude kofar dakin wanda qamshin Bahar din me wata irin ratsa kai da zuciya na hadin Oud na gyara tenya daya gama kama jikinta sbd kusan duk bayan kwana biyu tenya ke gyaranta shiyasa hatta fatar jikinta koyaushe qamshi takeyi bare sitirarta da kuma dakinta ko undies nata hatta jerin handbags nata kamshinta sukeyi sbd sun riga sun kama.

Sanyin aircon ne da qamshin suka daki fuskar Leylah tareda shiga hancinta kai tsaye ta dago a yanayi na tsananin mamaki da mutuwan da jikinta yayi na kamshin kadai data shaqa ta kalli cikin dakin wanda komai yake a tsare da tsarin wayewa da turawa da kuma gata da luxuries da koina ke nunawa.

Akan Bahar din dake tsaye gaban mirror ta daure gashinta da band sako sako sbd tayi shirin bacci already kayan bacci ne a jikinta na riga da wando masu santsi maroon mai kyau dataiwa fatarta kyau sbd duhun kalar.

Ita kanta Bahar juyowa tayi a hankali da wata irin nutsuwa tana kallan kofar da aka bude kai tsaye,
Ganin leylah ya sakata mamaki sosai amma bata nuna ba ta baro jikin mirror din tana tahowa a cikin takun nutsuwanta data zama tamkar jan ajinta.

Kasa dauke idanuwa daga kanta leylah tayi tanajin hankalinta kaman yana tashi da halittar datake gani gaban nata tana tinkarota.

Bahar bata qarasa har gabanta ba ta tsaya tana dauke kallanta daga kan leylah ta bude baki a natse tace

'Zaku tafi ne??

Sai a lokacin leylah ta iya hadiye wani 'dacin daya mamaye bakinta tana dan dauke kallanta daga kanta tace

'Yes zasu tafi ni ina nan sai bayan kwana biyu zan tafi so gasu can zasu tafi'

Dan shiru bahar tayi na jin leylah na nan har kwana biyu bayan sam basa jituwan da zasu iya kwana biyun a guri daya amma bata nuna komaiba ta basar tace

'Ok' a taqaice tana juyawa zuwa ina wayarta da sauran su ipad dinta suke ita kuma leylah juyawa tayi kafin zuciyarta ta buga da baqin ciki ta sanar musu ta fada mata tana zuwa.

Bahar kuwa tinda ba cewa leylah tayi ana nemanta ba batai yunkurin tafiya ba sbd ta dauka kawai ta fada mata ne zasu wuce,

Wayarta ta dauka tana kallan time taga 8 ta wuce kuma take taji gidan yana fita ranta sbd batason hayaniya ko damuwan da suke shiga a baya na zama guri daya da leylah dan haka taji inama baa samu matsalar bayyanar NUAB ba a jiya data tattara ta tafiyarta hostel har sai ankwana biyu leylah ta tafi,

Wayarta ta dauka ta saka kiran Neesah ta rarrasheta tazo ta tayata rokarsu Maa akan su tafi hostel gobe sunada wani class tinda sassafe karfe 7.

Tana saka kiran Neesah din itama tana kokarin komawa hostel kenan daga fashion house nasu da bahar din bata samu zuwa ba yau dan haka tana fada mata tace me motar ya juya da ita zuwa gidan akan koda baa barsu tafiyarba ita Neesah zata tsaya ta taya bahar din kwana biyun.

Su Asim jira suketa faman yi na fitowan bahar amma babuta shuraim sai sake son jiran ta fito yakeyi duk da yana kallan time sosai sabanin Asim da duka hankalinsa ya tashi yaji tafiya yakeson yi tin kafin NUAB din da akace ya iso gidan ya sake samunsu shi yanzu bayason matsala a rayuwarsa da kaddara me muni dan haka gwara ya lallaba ya samu bahar din da salama.

Mintina ashirin da biyar ne suka cika take akai Knocking kofar data saka Asim miqewa bai jira komaiba ya nufi kofa yana kasa yiwa su maa saida safe ma,

Shuraim ma miqewa yayi yana bin bayan Asim din yana jin da kaman ya sake aikawa kiran Bahar din ita kuma leylah dazai aika ma tana kitchen da rawar jiki ta saka hannu aikin hadawa NUAB din duk abinda ake kokarin hada masa sbd itace take son takai masa idan yaxo sbd su gaisa.

Bude musu kofa security guard din yayi batareda ma ya iya ce musu komaiba ya basu hanyar datake seti da gate na ficewa gidan alaman su saka kai kawai.

Asim dayake gaba saukowa stairs na kofar yafara yi wanda yayi daidai da bude gate din dakai hasken mota ya haskesu tas suna fitowa da saukowa zuciyarsu na dan shiga shakka.

Qarasa shigowa da motocin guda biyu masu daukan ido duk da dare ne amma akwai haske daya saka ake iya ganin ba kudin banza ya siyesu ba akai harabar gurin ana parking nasu a natse.

Asim bai tsaya ba ya fice gate din gabaki daya,
Shuraim ne yaso tsayawa ya gaida Sultan din Aleey daya fara fitowa ya sanar dashi yaje yanzu ba lokacinda ya kamata bane ya bari sai wani lokacin.

Shuraim na jin hakan ya saka kai shima sbd a yanayin aleey kadai ya gane akwai bacin rai,

Suna ficewa aleey ya sanar da security a rufe gidan a kuma rufe shigowan kowa a gidan saida bincike da izini.

Budewa NUAB din kofa yayi wanda kallo daya idanuwansa sukaiwa Su Asim din dake fitowa a lokacinda motarsu ta sako kai gidan ya dauke idanuwansa daga kansu sbd zuwa yanzu ya gama fahimtar mutanen dake cikin gidan makashi sukeson ya zama.

Fitowa yayi a kame yana nufar ciki kai tsaye idanuwansa a take sukai mugun sauyawa amma baice komaiba bai kuma nuna komaiba wanda duk wanda yake karkashinsa yasan ya harzuqane take da fushi da bacin rai duka wanda wannan gidan dai da ba iyayensa ne a ciki ba dukansu mata da ko waye yake maida gidan tamkar gidan gala da tin jiyan bazaiga safiyar yau ba sbd zai zama makashinda dai suke son ya zama.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:55 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

124
Ko daya shigo palon tsit yake sai masu aiki dake sake gyarasa daman fitar su Asim din suke jira kuma kaman sunsan sultan din yana hanya suna ficewa qamshin palon suka fara sauyawa daga qamshin su Asim din suma me tsada daya kama palon.

Kuma dayake ba wata gyara da palon yake buqata sbd dukansu ba yara bane maza ne masu nasu ajin da wayewa da ilimi kawai dai dan abinda baa rasaba sukeyi.

Suna jin bude kofar aleey kadai suka iya gani sukai saurin zubewa qasa batareda ma sun bari idanuwansu sun kalli wanda kallansa tafi karfin idanuwansu suna sauke kansu qasa da tsananin girmamawa suna yin tsit sbd basuma da damar bude muryoyinsu a gaban sultan matiqar ba an buqaci hakan daga garesu bane.

Qamshinsa ne ya ratsi palon yana doke nasu Asim din dama wanda aka kawar danasu dashi ya sauya niiamar palon bai tsaya ba bai kuma ko kalli inda bayin suka zubeba sbd baima lura dasu ba jininsa tafasa yakeyi me tsananin datake bayyana a fuskarsa sbd jan datai musamman kunnuwansa ya wuce kai tsaye dakinsa.

Yana wucewa suka miqe a take suka bar palon kuma suda sake barin ya gansu shikenan,

Aleey ma rufe kofar yayi ya juya ya fice ya nufi dakinsa bayan ya qara tabbatarda karfin umarnin daya bata akan kowane irin baqo bazai shigowaba batareda izininsa ba.

Bayin na shigowa kitchen suka sanar da maa sakinah sultan me boyem ya iso yana gidan,

Shiru tayi kafin tace musu su tafi kawai sai kuma gobe su fito aikinsu daga dakinsu.

Suna barin gurin ta qarasa hada komai da zata hada ta fiddo shi dining ta ajiye tana nufar daki ta sanar da Tenya da batada aiki sai faman kiran ayanah ta fada mata NUAB yana gidan.

Leylah kasa zuwa dakin Bahar tayi hakama bazata iya zama a cikin su maa ba dan haka dakin Ammi ta tafiyarta ta zare kayanta ta fada wanka sbd shirin bacci bayan ta tabbatarda ta gaisa da NUAB.

Tinda ya shige babu wani motsi me karfi daya sake tashi a gidan ko hayaniya sbd kiyayewa dan haka koina ya dauki tsit wanda har bahar datake dakinta hakanan taji kaman koina din yayi tsit batai wani mamaki ba sbd tasan kila su Asim dinne sun wuce dan haka time ta kalla har 9 ta wuce kuma har lokacin bataga neesah ta iso ba dan har kusan kayanta ta hada a qaramar suitcase me kyau,

Fitowa tayi daga bedroom dinta daga ita sai kayan baccin nata tana duba wayarta dan kokarin sake kiran neesah hankalinta kwance,

Jin tsit din yayi yawa kuma tin karfe 9 batareda dare yayi sosaiba yasakata fasa saka kiran tana kallan koina kafin ta nufi kitchen zata saka masu aiki su dafa mata madara da zuma ta tadda babu kowa anma kashe hasken kitchen din dan haka fitowa tayi zata nufi dakinsu Maa idanuwanta suka sauka akan hanyar dining room ta hango kayan teaset a jere dan haka juyawa tayi ta nufi can tana fatar tea dinne tasha.

Tana isa ta miqa hannu ta taba taji da zafi sosai take ta san akwaisa kuma da alama baa dade da gama hadasa ba dan haka zaunawa tayi ahankali ta dauki cup ta zuba sosai a ciki ta dauka tafara sha a natse.

Kurban farko datai jin tayi taste din kaman yayi mata karfi amma sbd hankalinta yana kan wayarta saita cigaba da sha bata ma ankaraba harta shanye tas ta qara ta shanye tana kokarin qarasa shanye na karshen kiraj neesah ya shigo mata ta miqe tana hada wani irin zufa ta nufi palo dan tinanin ta iso amma ga mamakinta bata ganta ba dan haka ta daga wayar kafin tace komai neesah tace 'ki fito kigani'
Chapter 51 · 0% Book details