← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 112

Sashe 45

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jefar da wayarta tayi gefenta tana rintse idanuwanta da suka sauya tareda jin bazata iya ba ta gaji da rayuwar datakeyi gwara tasan takabarsa takeyi akan mugun baqin cikin datake kwasa dan haka kai tsaye fatar kada Allah yasa ya dawo tafara yi masa ya mutu a hanya kowama yayi takaba ya huta asan babu sultan yasar batada 'yaya baqin cikinta kadan ne na mutuwar tasa.

Sultan na barin boyem wani sabon farin cikin yayiwa Asim da leylah yawa dan shima suna shakkar ya hana tafiyar cikin saa kuwa sai gashi tafiyarsu ta kammala amma jirgin yawo ne suka samu saiya tsaya qasa kusan uku kafin ya isa dan haka tafiyar zata zama ba direct ba amma basu damu ba kawai sedai su mummynta sukaji zatai tafiya tareda mijinta.

Da mamaki zuhrah tayi farin ciki sosai ganin Leylah din na farin ciki kaman ta hakura ta karbi auren dan haka da murnarta itama ta bata turarika masu karfi a zuciyar namiji ta qara da yar nasiharta ta rakata har gurin abbinta tayi masa bakwana ta koma bangaren Mamee itama tai mata bankwana harma ta dan zauna acan zuwa dare Asim din daya shigo suka koma tare haile nata jin dadin cigaban datake gani a tattare da rayuwan danta.

Washe gari tinda safe motoci suka kaisu airport karfe 9 jirginsu ya daga daga boyem suma.

Bayan tafiyarsu da kwana biyu shima shuraim ganin ba wani aiki tinda sultan me qasar baya nan saiya hada tasa tafiyar dan zuwa Gurin Ammi da Bahar da ko numbern wayarta bayada sedai suna gaisawa sosai da wayar Ammin idan ya kira amma kwana biyun shiru ko wayar Ammin baya samu idanma ya samu baa dauka kwata kwata.

Shima babu dogon jira sosai tafiyarsa ta kammala ya daga zuwa uk din.

*******
Sultan Yasar ne ya fara sauka a Uk din wanda kai tsaye yanada masaukin kansa da duk yaxo qasar anan yake sauka,

Lafiyayyar royal suite ce da babu me sauke se me babban matsayin da harya mallaki pass na gurin dan hakanne tsaro da duniyar gurin daban take,

Guri ne da tamkar baa duniyar mutane ba sbd ko sautin komai baa yadda ayi ba a gurin sbd duk wanda yake gurin babbane wanda daula ta ratsa baya buqatan hayaniya,

Pass din gurin matiqar ka mallakesa to kayi nisa a daular duniya dan haka koda suka sauka daga royal din aka tafi Airport aka daukosa tareda securities nasa dama wainda aka tanadar masa anan.

Ana daukosa suka dawo kadir ne kadai yakeda daman daya shiga palon farko na hutawan dakin amma sam bayada ikon shiga na biyun bare isa ga bedroom dinsa dan haka yana ajiye komai da zai ajiyewa sultan din yasaka aka kawo masa abinci kala kala dayasan yana buqata aka jere suka fice masu jerawan shima ficewa yayi tareda rufe dakin gabaki daya ya hau lift ya sauka zuwa nasa dakin dayake bangare daban dana asalin manyan.

Wanka da sallah tareda samarwa kai isashen hutu sultan yayi har dare bai nemi kowa ba bai kunna wayarsa ba saida safe ya kunna yana zaune a natse ta kira tenya wadda tai sharing location na inda suke sbd an sallamosu a daren jiyan sun dawo gida.

Da mamaki tenya ta sanar da sakinah sultan yana qasar cikin yar fargaban kada NUAB yasan da hakan gashi daman sunata faman yi masa boyan rashin lafiyar da Ammin tasa tayi.

Sakinah ma jin tayi ta dan shiga fargaba amma tin da dai sultan din yanada ikon zuwa gurin Ayanah ba yanda zasuyi bayan kawai su hana NUAB sani.

Yamma lis motocin sultan yasar suka iso bakin entrance na street din gidansu da akwai yar security sosai a street din dan haka a natse motar dayake ciki ta isa har kofar gidan ta tsaya a kofa ta security system nasu suka bude masa gate daga ciki take qaramar gate din mara tsaya ko kadan ta bude kadir ya sako kai ciki yayi parking.

Su tenya da suka san da zuwan nasa harma itace ta bude masa gate din ta ciki fitowa sukai cikeda girmawa me yawa suka tarbesa suna kasa kallansa sosai sbd kwarjinsa da wata irin kyan fuskarsa.

Bahar da batasan da shi ba tana bedroom dinta tana video call da Neesah akan skancare routine class da suka shiga kwana biyu bata samu zuwa ba sbd jikin Amminta school kadai take iya zuwa ta dawo ta dena zuwa koina sabanin yawon da koyaushe suke kan yi na shopping,saloons,spas da classes barkatai da kowanne shiga sukeyi.

Yana shigowa Maa sakinah ce taje har dakinta ta sakata tazo cikeda girmamawa da faduwan gaba da tsoro ta gaidasa kanta a qasa tana kasa kallansa sbd jin tayi itama kwarjininsa yayi mata yawan da bazata iya qwaqaran motsiba irin na 'dansa.

Kallanta yayi da idanuwansa na dattijantakar hutu da nutsuwa ya amsa yana tambayarta karatunta ta amsa har lokacin bata iya dagowa ba.

Ammi ce wadda tenya ta isarwa da sakon zuwansa ta fito a sanyaye cikeda mamaki da jin jikinta yana mutuwa da tsananta sanyi da ganinsa musamman yanda ya kafeta da ido take kowa ya matse aka bara palon gabaki daya kofar kitchen suka nufa suna barin cikin gidan zuwa baya inda swimming pool na gidan yake suka zauna a kujerun hutawa,

Tenya komawa tayi takai kayan marmari da duk abinda tasan sultan zai iya ci ko sha ta jere a rable ta baro ta dawo cikinsu Maa sakinah din ta zauna suna fira hankali a rabe da tinanin NUAB duk ranar da allah yasa tsautsayi yasan sultan ya ziyarce su.

Bahar wayarta ta isa bakin pool ta zauna taci gaba dayi tana saka kafafunta cikin ruwa daman short wando ne a jikinta da sleeveless shirt sai babbar rigar data doro a kai ta fito dan haka cire rigar tayi suna zuwa bayan ta ajiye tana qarasa abinda takeyi hankali kwance fatarta na wani daukan idanuwan Maa sakinah dake kallanta sbd hutu da lafiya da tsadaddiyar rayuwar datake yi tamkar yar datafi kowace 'ya gata a duniya duk da a gurin su sukam hakan ne babu yar datakai musu tasu dan haka ne ma tayi sauyawan da babu wanda zai kalleta bata shiga ransa ta kwanta ba.

Sultan bai wani jima ba kadir ya kira tenya a waya suna bayan ya fada mata sun tafi harda Wishmah zata ga likita na kwana biyu kafin ta dawo.

Shock tenya ta shiga gabanta na faduwa ta rasa abin fada dan batama dashi kawai to tace sbd bata isa cewa komaiba akan kowane hukuncin sultan yasar me boyem da sultan din boyem.

Sakinah data ji abinda tenya ta fada dagowa tayi zata kalleta kiran NUAB ya shigo wayarta dake hannunta wani irin mamaki sabo ta shiga sbd yanda kiran ya shigo Ammi na ficewa da Wanda aka dawo da ita nan sbd shi gashi basuda ikon fada.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

118
Tenya ma data ajiye tata wayar tana rasa abin cewa kallan wayar sakinah din tayi tana NUAB ne take kafin ta sakinar ta yanke ta kashe tata wayar gabaki daya sbd yana gama kiranta bata daga ba tata zai kira ita kuwa tasan baifi Ammin tasa yake nema ba sbd kwana biyun bai samu jinta ba a jiya kuma koda aka sallamosu sunyita kira basu samesa ba harma yau da safe sunyita kira harda ita Ammin amma basu samesa ba duka.

Duk yanda maa sakinah taso ta daure ta daga wayar kasawa tayi sbd tsoron kadama yace kai tsaye a basa Ammin dan haka ta ajiye wayar a hankali gabanta tana kallo harta yanke,

Ajiyan zuciya suka sauke a tare bayan wayar ta tsinke dan haka suka miqe suka tattaro suka koma ciki banda bahar da batada ma niyar komawa ciki lokacin tayi nisa sosai a wayar datake ta zubawa har lokacin.

Sultan yasar bayan motarsu tabar gidan da anguwan gabaki daya hanya suka dauka ya juyo a natse ya kalleta da idanuwansa da itama ta dan dago tana kallansa ta sauke nata idanuwan sbd bazata iya jure kallansa ba musamman yanda yake ya kasa daukesu akanta cikeda wata irin kewa da shauqi.

Hannunsa ya daga yakai zai kama nata a cikin nasa din ya dakata sbd tinawa da ayanzu babu halasci ya tabata sbd an yantata ta tashi daga kowane matsayin datake dashi na zama halak dinsa a baya,

Ajiyan zuciya ya sake a hankali a natse kafin ya dan lumshe ido ya sake sauke su akanta yana tabbatarda kowane bangare na jiki da zuciya tareda jininta sunji kallan tareda isar da sakon da kallan yake tattare dashi,

Cikin sautin muryan daya saka tsigar jikinta tashi ta dago ta kallesa da nata idanuwan dake kashe masa kamewansa ba tsammani taji kalmar da har abada bata taba saka ran jinta ba sbd ta gama cire aure a rayuwarta har abada tin daga ranar data zama cikakkiyar imebēti.

Kada dauke idanuwanta akansa tayi hakama kasa cewa komai tayi saida ya sake maimaita mata kalman da shikuma itace burinsa akanta da bai taba cire rai ba tindaga ranar data zama cikakkiyar imebētinsa da data kama zuciya ruhi da rayuwarsa.

Wasu hawayen da bata san dasu bane suka ciko idanuwanta suka gangaro ta bude baki da wani irin sauti tace

'Dana bazai bazai baka aure na ba'

Numfashi me sanyi ya sauke sbd jin 'dan nata ne matsalar bawai ita din ba dan haka shima yace

'Danki nine Ubansa nine nakeda iko dashi bawai shine yakeda iko damu ba,
Zan aure ki zan kuma miqa sadakin aurenki ga hannun danki daga baya da kaina ba aike ba ba sako ba amma ayau zan tabbatarda cikar burina na dora igiyoyin aurena akanki ayanah ghaz.'

Dauke idanuwanta daga kan nasa tayi sbd bata iya daukan kallansa ta dake bude baki ta ambaci sunan NUAB wanda sultan ya miqa hannu zai sake kama hannunta ya sake dakatawa yana girgiza mata kai tareda jifarta da kalaman da suka sanyata sauke ajiyan zuciya tana jin yanayi na sanyin jiki yana ratsata.

Kai tsaye gidan wani tsohon Amininsa wanda yake babban Masanin Addini Asalin balaraben Morocco dayake qasar tin lokacin samartaka gashi har an manyanta ya tara iyali sosai shima yama yi retire shima a yanxu harkar addini kawai yakeyi.
Chapter 45 · 0% Book details