← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 112

Sashe 20

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maa sakinah dake dakin da ayanah take a sume ana kokarin ganin ta farfado kai da kawo takeyi cikin wani irin zullumi da fargaba tareda rashin nutsuwan zuciya me tsananin gaske datake ji dan har wani rawa hannuwanta ke yi,

Kallan ayanah ta juyo tayi taga likitoci biyu ne a kanta ga tenya itama data dawo da ita sai kaida kawon takeyi sun kasa cewa juna komai sbd babu wanda yake cikin hankalinsa,

A daidai wannan lokacin ne sautin qarar sanarwar sabon sultan ya ratsa kunnuwansu wanda ya saka kowacensu dakatawa tareda tsayawa cak,

Tsawon mintina kowacensu ta kasa motsawa sbd shock da tsananin tsoron da yasa maa sakinah jin idanuwanta sun ciko da wasu irin hawayen da kafin su sauka kuka me tsananin karfi ya kwace mata sbd tabbatarda 'dan Ayanah ne ya hau milkin qasa me girma kamar boyem ayau.

Tenya ma rawa jikinta ya dauka hawaye masu tsananin zafin gaske suna gangaro mata ta zube qasa tayiwa Allah sujjada sbd ayau burinta dayake qume a zuciyarta ya cika NUAB dinsu ya zama mai mulkin boyem,
Duk akan takurawar sultan ne sun tabbata amma ayau din ranar da dukkaninsu bazasu taba mantawa bace harma da duniyar boyem gabaki daya bazasu taba manta wannan daren ba.

Maa sakinah kasa iya hakura tayi sbd a yanzu bahar tafi zamowa a cikin mummunan hadari dan haka kai tsaye tambayar tenya tayi inda suke ko gama fada tenya batai ba ta nufi kofa da sauri ta fice kafafunta na wata irin rawa.

Bangaren haile ta fara nufa da wani irin sauri sedai ko isa bataiba aka dakatar da ita tareda cewa bata ciki,

Hakan dataji shine ya kusan jefo zuciyarta waje dan daman son tabbatarda haile na bangarenta takeyi dan shine zai bata yar nutsuwar bahar dake can tenya dake basu dan tsaro bata nan,

Kai tsaye bangaren sultan datasan NUAB na can bai isa barowaba ta nufa da saurin gaske dan sanar masa akwai yiyuwan bahar na cikin mummunan hadari.
#MAMUH
#SULTAN LEUL NUAB YASAR ALMAZZ
#BEST LOVE
#ROMANCE
#ROYALTY
#BAHAR GHAZ BOYEM
#CRAZYLOVE

HAYATEEM novel
700
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

91
Tana isa ba damar shiga sbd tsaro dan haka ta saka aka kira mata kadir shima sbd ansan daga bangaren wishmah mahaifiyar Sultan LEUL take ne dan haka take aka tafi kiransa da sauri.

Tin kafin ya iso NUAB dinne ya fara sako kai yana gaba kadir din na bayansa wanda take securities da bayin dake tsoron bangaren suka zube qasa akan Gwiwowinsu dan bada asalin girmamawa ga sultan LEUL NUAB.

Bai ko kallesu ba akan maa sakina ya sauke idanuwansa da sukai jan da sai da gabanta yayi mummunan faduwa jijiyiyin fuskarsa da wuyansa duka sun fito sbd asalin Bacin rai da tsabagen fushin dayake yawo a kowace jijiyan dake gudanar da yawon jini a jikinsa.

Dan sassauta kallanta maa sakinah tayi sbd ko yana matsayin 'danta shi a yanzu sarki ne na qasa guda,
Sarki ne da dubban miliyoyan mutane,
Sarki ne da manyan kasashe da dama suke qarqashinsa,
Shi sarki ne a yanzu da zai mulki duk wani me rai dayake qasar boyem da zagayenta
Shi sarki ne da zai mulki har iyayensa tinda suna qasar,

Bayani tayi masa wanda baice komaiba kai tsaye ya wuce idanuwansa na tsanantuwa da halinda suke ciki yanajin dukkanin abinda yake ji a xuciya da gangar jikinsa yana qaruwa sbd zata tabbata ne a safiyar goben dole akwai wainda zasu tafi a maimakon tasa matar.

Maa sakinah bin bayansa tayi zuciyarta na sake tsananta rawa sbd qarar harbin datake jiyowa wanda har kayan cikinta rawa sukeyi sbd jin abinda bata taba ji ba.

Yana doso gurin aleey ne ya fara ganinsa take suka riqe tasu wutar wadda ta saka sauran suma dakatawa tin daman kowa kariya yake kokarin bawa nasa bangaren.

Gabaki daya gurin dauke wuta yayi bayyanar sultan NUAB da kansa a gurin dan haka take kowa ya bude sun ja da baya tareda sauke kawunansu a qasa.

Baice komaiba bai kuma tsayaba hanyar isa bangaren ya nufa kai tsaye aleey da mutum uku suna bayansa a shirye da bindigoginsu sbd ihun da suke jiyowa daga ciki yana tashi.

Salman jin harbe harben ya tsaya ya sakasa shiga sabon mummunan tashin hankalin daya qarasa rikitasa gabaki daya yana cigaba da jan Asim dan su samu gurin boyewa dan tsira sbd gabaki daya Asim din ya zama kaman gawa baya motsin komai idanuwansa a bude sai jini dayake fita hancinsa har lokacin,

Qara ce take sake tashi sosai a bangaren ta mata cikin tsananin neman ceto wadda tana ratsa kunnuwan Asim ya dago a hankali yana kallan hanyar qarasawa can qurya inda matan suke ya bude baki da sautin daya fito daqyar yace

'Bahar,Bahar,Bahar na cikin hadari.'

Miqewa yafara kokarin yi a rikice jikinsa na rawa tamkar mara hankali yabi hanyar da wani irin gudu kafafunsa na neman kifewa yayi ciki.

Salman da yake neman zarewa sbd masifar dayake hango musu babba kiri kiri bin Asim din yayi da sauri shima kafafunsa na rawa da wani irin tsallen tashin hankalin qamshin mutuwa daya fara jiyowa.

Suna shigewa NUAB shima yana sako kai aleey na kallan jini daya fara gani a gurin cikin tsananin mamaki yana fidda dayar bindigar dake jikinsa ya hada biyu a hannunsa.

Haile ma da idanuwansu suka gama rufewa kai tsaye dakuna suka fara bi suna banka kokafin da karfin gaske suna kashe duk ran da suka hadu da ita wanda ya rikita bangaren gabaki daya da wani irin ihun tarin bayin dake bangaren masu dan yawa suna gudun neman tsiran da babu hanyar fita ganin kisar da ake musu ta rashin hankali da imani.

Leylah da Bahar da gabaki daya bayin ma dake bangaren daman a cikin matsanancin tsoro da tashin hankali suke na irin harbe harben dayake daga wajen bangaren tin farko shiyasa su sam basu ma samu hankalin jin sautin karar daya tashi ba,

Bahar da bata taba jin karar bindiga ba a rayuwarta wani irin matsanancin tsoron da bata taba shigaba ta samu kanta tana shigewa bayan gadon dakinta ta boye tareda rufe kunnuwanta da duka hannuwanta biyo koina jikinta yana wata irin muguwar rawa zuciyarta ta gama tsinkewa da bugawa idanuwanta sunyi jajir harma bata iya gani dakyau dasu zufa ne me tsananin gaske take fitarwa tareda ficewa hayyacinta.

Leylah ma cikin tashin hankali jikinta na rawar da bata taba shigaba tayi karfin halin fitowa jikinta na tsima,

Jinin datake gani kusan koina ne da ihun dayake tashi me tayar da tsikar jiki na bayi da masu kulawa dasu dake gurin ya sakata ja baya da karfi cikeda matsanancin tsoro da tashin hankalin da bata taba sanin akwai ba ta juya da gudu jin ihun yana sake gauraye koina.

Baya ta koka inda ta fito da gudu kafafunta na neman kifewa a rikice ta wuce dakinta bata sani ba tana isa dakin dayake na karshe gabaki daya ta fada,

Tana fadawa ciki taga babu kowa hankalinta ya ninka tashi gashi bazata iya sake fita ba sbd yanda komai na jikinta ne tsananta rawa tsoronta na tsananta sosai shima.

Kuka ta fasa me rikitarwa tana nufar bayan gadon dakin itama zata boye tana fadawa da karfi idanuwanta suka sauka akan Bahar wadda idanuwanta ke rintse da karfi hannuwanta na toshe da kunnuwanta komai na jikinta na wata irin rawar dake nuna bata hayyacinta cikin mummunan firgici take.

Tsallaketa leylah tayi komai na jikinta itama yana rawa sosai ta wuce qurya ta durqusa itama tareda qanqame jikinta kukanta na qaruwa sosai ta saka hannu tana rufe bakinta da sauri jin yanda aka banko kofar dakin da wani irin karfin gaske.

Wasu samudawan marasa imani biyu ne a gaba gurin shigowan bayan sun bankewa haile kofar dakin kafin ta shigo komai na jikinta itama rawa yakeyi gabaki daya ta zare takejinta gawa kawai zata maida bahar ta samu nutsuwa dan haka a haukace ta nufi toilet ta banka kofar da karfi tana fadawa ciki ta duba babu kowa.

Fara birkita dakin da nema sukai cikin rashin hankali daidai lokacin Asim ya fado dakin a haukace bayaji baya gani ko gabansa
Cikin mummunan tashin hankali ya bude baki zai ambaci sunan mameen tasa salman yayi saurin rufe masa baki sbd baa taba zuwa aikata laifi irin wannan ayi magana sbd abinda zai iya biyowa baya.

Ture hannun salman yayi kokarin yi cikin tsananin tashin hankalin abinda idanuwansa suka gano masa a hanyar koina na bangaren wanda duk aikin mahaifiyarsa ne.

Bahar yake son bude baki ya tambayeta idan batai mata komaiba amma salman ya saka dukkanin karfinsa ya hanasa magana wanda yafara kokarin kokawan kwacewa amma haile tayi alaman kada ya kuskura ya bari Asim din yayi magana dan jikinsu duka ya basu akwai mutum a dakin.

Samudawan datazo dasu din ta kalla ta bude baki da sautin da bame ji idan ba su ba tace a tabbatarda mutuwar ko waye a dakin dan tinda bata ga bahar koinaba ta tabbatarda nan ne dakinta kuma tana ciki.

Bayan gadon Daya daga cikin yaran nata yake kokarin nufa shi kuma salman cikin karfi ya fara jan Asim shi da daya daga cikin yaran suna toshe masa baki da karfinsu suna kokarin ficewa da shi.

NUAB ne ya shigo palon Aleey na saurin shigewa gabansa dan basa kariya tareda nufar dakunan suna fara dubawa,

Ganin irin mummunan al'amarin daya faru a bangaren ba kyan gani koina jini ya saka Jinin NUAB kaiwa matakin karshe na tafasa da konuwa dan haka da kansa ya ringa bankar dakunan da kafarsa yana duba dakunan idanuwansa na tsananta ja hakama jijiyoyinsa.

Aleey kuwa yaransu dake waje ya kira kai tsaye suna dauka yace

'Duk motsin daya fito daga nan ko shadow na dabba ne kona mutum koma waye idanuwanku basu ga kowa ba bayan shadows na marasa gaskia just open fire,
I repeat open fire ga duk motsin dazai fito ta kowane bangaren dayake zagaye da nan din.'

'Zan tabbatarda na fasa qashin duk wanda zai fito daga bangaren na bullet dina,wannan alkwari na ne sire'
Chapter 20 · 0% Book details