← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 112

Sashe 81

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binsa Ammi tayi da kallo hawayenta na sake gangarowa tana daga kafa kaman zata bisa ta rungumosa Sultan ya saka hannuwansa biyu ya riqota yana rungumeta a natse sbd a yanzu NUAB din na buqatan space sbd ayau yaji abubuwan da zuciyarsa zata jima tana tafasa bata saukoba kafin ya fahimci gaskiyar da suke kokarin fada masa ya dawo daidai dan kuwa shi kansa yasan kaman yanda yake tsananin kaunar dansa haka NUAB yake kaunarsa kawai zafi ne na rabuwa dasu daya kasa cirewa aransa tin yarintar.

Kuka Ammin keyi a hankali a jikin sultan din tana jin kaman kalamanta sunyiwa NUAB din tsauri.

Zaunar da ita sultan yayi ransa ba dadi shima ya rungumeta yana kasa cewa komai dan haka sukai shiru dukansu.

Shi kuwa yana sako kai kofar Aleey ne ya fara ganinsa fuskansa kawai ya fara kalla bai iya qarasa kallan idanuwansa ba yayi gefe yana buda masa hanya idanuwansa na sauya take sbd ganin halinda ubangidansa yake ciki wanda kusan hayaniya sosai suka jiyo daga ciki a tsakaninsa da iyayensa wanda ba dan adam dayake da daman shiga dan haka duke a tsuru suna jiran iyayen gidansu dukansu.

Wata irin aura ce ta zafinsa kawai ta bugi dukkaninsu dake kofar take kowa yayi qasa da kansa fadawa ma dake hanyar ficewa bangaren zubewa qasa sukai da sauri kansu a qasa sbd tamkar guguwan wuta haka suka ga tahowan tasa cikin wata zafi da zafaffen izzar mulki.

Aleey da keelah ne suka bi bayansa babu wanda idanuwansa basu sauya ba a cikinsu musamman aleey shi keelah kuwa a lokacin ya samu damar wani me laifin akansa abinda suke ji din zai sauka.

Kai tsaye bangarensa suka nufa wanda suna tinkarowa tin daga nesa kowa ya miqe suna shiga wata irin nutsuwa sbd a tafe suna iya hango yanayin ba daidaiba.

Koda ya iso an wangale masa kofa hatta kofar shigewa palo an an bude masa dan haka yana isowa shigewa kawai yayi aleey ya rufe kofar yana juyowa ya bada umarnin ba shiga ga kowa kaman yanda aka saba duk da daman babu me zuwa bangaren bayan masu aikin da suna gamawa suke barin bangaren.

Yana shiga kai tsaye palonsa ya wuce na qurya shima yana isa kokarin daidaita kansa yayi da zuciyarsa ya nufi inda zaiyi sallah ya tada sallar ishai da aka aka fara yabi jam'i daga nan batareda ya iya tafiya masallacinba dan gabaki daya fuskansa ba kyan gani,

Ana idar da sallar jin yayi numfashinsa na sarkewa yana kasa fita daidai hakama wani irin zufan gaske yake fitarwa idanuwansa har wani rufewa sukeyi yarintarsa da duk abinda ya taso a cikinsa yana dawo masa da tinanin da radadin da kaunar dayake wa mahaifinsa me karfi da kishinsa dayake tada duka wani fushinsa,

Miqewa yayi bedroom dinsa ya nufa bai tsaya komaiba tin daga kofar bedroom din yafara bude botiran gaban rigarsa ya zare ya jefar yana zare komai daya baya daya kai tsaye ya nufi glass door din dake dakin ya budeta gabaki har qarshe yana saka kafarsa batareda komai a jikinsa ba bayan tight CalvinK short underwear dake jikinsa fara qal ya isa bakin lafiyayyan pool din dake gurin ruwan ciki na daukan ido yasaka kafa yana shigewa ciki ahankali harya gama shigewa gabaki daya ya rintse ido sanyin ruwan na ratsasa tsananin zafin jikinsa da jininsa ka neman fara karbuwa su daidaita.

****Ammi da Sultan kusan babu wanda ya iya cewa komai a yanayin da suke ciki har ya fice sallan ishai bai iya cewa komaiba bayan ce mata da yayi kada ta damu NUAB din zai sauko daidai babu yanda zaiyi bayan ya gama bacin rai da fushi kuma dole ya bisu hakama daga yau aurensu dasu sun samu cikakkiyar yanci da duniya zata san da sun zama maaurata kuma masu tsananin son juna duk wanda zai mutu ma ya dade bai kwanta ya mutu ba.

Yana ficewa itama barin bangaren tayi ta fito Maa sakinah data kasa tsayawa sbd tension din yayi yawa na abinda yake faruwa a ciki ya sakata komawa tabar bayi biyu suna jiran fitowan tata palo ta zauna tinda ta dawo tayi shiru cikin tsananin damuwan NUAB da itama takeson ya hakura ya aje komai yabi mahaifinsa wanda a yanxu duniya tafara sanin sirrinsa dake boye a ransa cewan babu wanda yakeso fiyeda ransa a cikin yayansa da duniyarsa kaman NUAB din.

Maa tenya ma datasan suna can din hankalinta bai kwanta ba saida sakinah ta dawo kallo daya tayi mata ta fahimci komai ya dauki zafi dan haka itama zaunawa tayi palon tana dan kallan tv sama sama.

Ammi na shigowa yanayinta kadai suka kalla jikinsu yayi sanyi sbd idanuwanta da sukai jajir zuciyarta cikeda daci.

Kallansu tayi tana sauke numfashi me zafi ta qaraso ta zauna tana dafe kanta a hankali tareda sake sauke numfashi ta dago tace

'NUAB ya kasa fahimtar abinda nakeson ya gane,ya kasa fahimtar abinda mahaifinsa yake son ya gane
Bansan tayaya zan fahimtar dashi batareda ya dauka ina zabar bangare bane,
A tsakaninsa da sultan ba maganar na zaba bane maganar ya fahimta ya yadda a yanzu aure mukeyi ba zaman baiwa da ubangidanta ba,
Ayau ya saka na fada masa abinda bansan ya akai bakina ya furta ba.'

Shiru sukai suna sauraranta damuwan sakinah na bayyana ta bude baki tace

'Kada ku ga laifinsa duka sbd duk abinda yakeji yake ciki an dasa masa shine tin yana yaronsa dan hakane ab8j ya tsaya a ransa hakama auren da kukai kun boye masa musamman ke dayake ganin komai yana yinsa ne sbd farin cikinki da baki kariya,
A qalla kafin auren ya kamata ku zauna dashi kuyi sharawa tinda shine waliyin dakike dashi amma tinda duka baayi hakan ba yanzu daukan zafi duka ba shine mafita ba hakuri zaayi a basa lokaci ya fuskanci komai da kansa.'

Shiru sukai dukansu tenya ta amsa zancen da itama fara jero tarihin irin yanda yayi rayuwa tin tashinsa a cikin ganin shi din da uwarsa ba kowa bane face abin takawa a wulaqanta a banza a masarautar karkashin mulkin mahaifinsa wanda shine ya fito ya nunawa duniya din su ba kow bane face mistress dinsa daya gama amfanuwa da ita da 'danta da kuma yanda aka rabasa da uwa da qasarsa aka kaisa qasar da baida kowa baida komai aka jefar dashi tinda qananun shekarun har girmansa ba wanda ya taba nemansa tayaya ake tunanin zuciyarsa zata sake wannan zafin duka a lokaci daya?dole sai ahankali insha Allah zai sake komai.

Hawaye sosai Ammi take gangarowa da jin irin yanda tenya ke jero quncin da suka rayu a cikinsa a cikin masarautar wanda NUAB ya taso a cikinsa ya kangarar masa da zuciya,

Komai dawo mata yayi ta rintse idanuwanta tana jin zafin abinda tayiwa NUAB din sosai kirjinta na nauyi.

Maa sakinah ma nauyin kirjinta yayi ta kasa cewa komai idanuwanta jajir kaman yanda na tenya din sukai sbd sune kadai sukasan radadi da zafin quncin da suka rayu a wancan lokacin a cikin masarautar data zamar musu tamkar maqabarta sbd qunci da baqin ciki tareda kadaici da damuwa.

Bahar datake tsaye duk abinda suke fada da faruwa a kunnenta nauyi kirjinta yayi idanuwanta suka ciko da hawaye tana kasa motsawa musamman ganin hawayen Ammin da kuma yanda ake fadar rayuwar da sukai wadda itace ta busar ta kangarar da zuciyar NUAB wanda ya taso ba soyayya da kulawan kowa ya rayu shi kadai sai soyayyar uwarsa da bata hayyacinta bata san ta kaunacesa ba a lokacin.

Kasa tsayuwa tayi jikinta na tsananin mutuwa da wani irin sanyi zata bar gurin Ammi tafara fadar abinda ta gaya masa ayau din wanda take jin nadamar fada masa hakan duk da tayi hakan ne sbd sakasa ajiye komai ya shirya d mahaifinsa.

Shiru suka sake ba wanda ya iya cewa komai sbd bama me daman tinkarar NUAB din yanzu dole saiya nemesu da kansa zasu iya samun damar magana dashi su dan taushesa.

Bahar data sake yin sanyi dakinta ta koma ta zauna a kan sofa tana kasa motsawa zuciyarta cikeda tinani.

Leylah dake kwance shiru itama tana fama da kanta zuba mata ido ganin yanayinta kafin ta rufe idanuwanta bacci ya dauketa.

Ita kuwa kasa motsawa tayi daga inda take din zaune har tsawon lokaci abubuwa da yawa na yawo cikin kanta cikeda damuwa da mutuwan jiki sbd bayan damuwan da Ammi ke ciki akansa harda fushi da bacin rai me girma tana ciki kan NUAB din wanda shima a daidai wannan lokacin tasan yana cikin matsanancin halin da baya buqatan kowa amma kuma tasan dole wani yana buqatan kasancewa dashi.

Sallar ishai da akai tin dazu ta tashi jiki a mace tayi tana idarwa tai shirin bacci har lokacin jikinta a matiqar sanyaye tana jin rashin nutsuwa.

Zaunawa tayi bakin gadonta tareda dago idanuwanta ta kalli agogon gefen gadonta taga karfe goma har tayi.

Numfashi ta sauke a sanyaye a natse kafin ta miqe tana rasa nutsuwanta kwata kwata ta dauki hijabi har qasa ta saka tana daukan wayarta ta fice daga dakin.

Ko data fito palo babu kowa koina yayi tsit alaman kowa ya shige sbd yanayin da ake ciki na damuwa.

Kofar ficewa take nufa daidai zata saka hannu ta bude kofar aka kirata a natse
Tsayawa tayi cak cikin faduwan gaba me karfi daya sake sanyaya jikinta.

Juyowa tayi daidai Maa sakinah na isowa gabanta dauke da tray me kyau dayake dauke da white and gold tea set masu daukan ido sabbi dal na amfanin LEUL din ta miqa mata sbd daman dakinta zata kai takai masa sai gata ta gani tasan kuma can din zata.

Bata ce mata komaiba miqa mata kawai tayi tace takai masa.

Bayi biyu ne mata naimah da salmah tace su rakata su dauki tray din wanda aka saka sukutum a cikin wata basket me girma da fadi.
#MAMUH
09033181070
[07/01, 11:49 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

154
Itama Bahar din bata iya cewa komaiba kuma bata iya dagowa ta kalli Maa dinba sbd kunya da macewan jiki dan haka juyawa tayi a natse ta wuce su Naimah din na bayanta da zazzafan hadin tea din dazai warware kan NUAB din cikin sanyi insha Allah.
Chapter 81 · 0% Book details