← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 112

Sashe 93

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da shirin tafiya da farin ciki suka tashi musamman ayanah da sakinah da sukejin finally zasu koma qasarsu suyi rayuwa,
Qasar da suka cire rai daga saka zuwanta a rayuwarsu sai gashi sun tafi yanzuma zasu koma gida da farin cikin da yariga yayi gibin da bazai taba cika ba sbd wainda aka bar gida taredasu aka fara tafiyar dasu,
Anfara dasu baa gama dasu ba wanda kaman koyaushe gibin da Abaas da Nurat suka bar musu bazai taba cikewaba duk kuwa farin cikin da zasu samu a rayuwa.

Sultan NUAB ya shigo bangaren da karfe goma na safiyar ya shiga ya gaisa da iyayen nasa kafin yayi magana da Ammi tsawon lokaci kafin ya fito ya fice.

Harya shigo ya fice Queen din boyem tana bacci bata farka ba har lokacin shima kuma daman baima saka ran ganinta ba sbd yasan bata farkaba dan sunyi magana da asuba yasan zata jima bata farkaba sbd yanda suka jima suna maganar a waya da asuban.

Karfe sha daya na rana ta farka tayi wanka dasu brush da sauransu ta fito tana jin jikinta ya samu karfi.

Shiryawa tayi ta fito ta nufi dakin Ammi ta gaidata Ammin na binta da ido ta fito tayi dakin Maa tenya ta tadda maa sakinah acan suna magana dan haka anan tayi zamanta salmah ta kawo mata abincinta anan taci tana shiga firarsu a natse ba hayaniya.

Tana gamawa mum zuhrah nashigowa sbd lokacin tafiyansu ya kusa.

Karfe daya da rabi jirginsu zai tashi dan haka karfe goma sha biyu da arbain harma da mintina akai Bayi suka fara fidda kayansu inda motocin dake jere suna jiran fitowansu ana sakawa.

Gama fidda kayansu akai kaf kafin suka fito kowannensu a shirye cikin nutsuwa da mulki da wayewan da duka ta ratsesu tareda daula.

Tin daga iyayen har yayan designers ne a kafafuwa da hannuwansu maana shoes and bags dinsu dan kuwa su chanel ne da Lv dasu Dior ke hannuwansu daban daban wainda kudin kowace zai baka mamaki idan kaji,

Bahar kai tsaye ita da maa tenya da sakinah wucewa gaba sukai sedai zuhrah da Ammi da leylah ne suka tafi har bangaren haile dan yi mata bankwana amma bata iya ganinsu ba sedai meryam tace musu bacci takeyi bata jin dadi,

Haka suka fito batareda sun gantaba suka wucewansu zuwa mota,

Motoci ne a jere na alfarma da suke daukan ido saina securities acan gaba suma a jere suna jira dan kuwa ba qananun securities aka hadasu dasu ba dan kuwa kusan zuciyoyin masu boyem ne dika aka hada guri daya da babu wanda bai bada nasa securities dinba akan matarsa musamman NUAB da wasu manyan murdaddun securities aleey ya bayar,

Sultan ma ya bada securities ga ayanah duk da yasan na NUAB ya ishesu,
Shi kansa Asim bai nutsuba saida ya bada securities biyu wa tasa matar hakama Zuhrah kusan bayi biyar zata dasu daga bangarenta bayan wainda suke acan anjom da aka tanada masu yawa da tsari da sanin komai na aikinsu.

Motocin suka shiga dan zuwa airport,

Aleey ne ya iso da motar da NUAB kadai ne yake shigarta tasa ce ta hawansa ya kara a gaban bahar da kansa ya tuqota ba kowane driver ba,
Ko ubangidansa baya tuqawa sbd akwai drivern NUAB din da dashi suka taho tun daga Moscow amma ayau NUAB shi ya bawa umarnin ya tabbatarda isar dasu Airport da kansa dan hakane ma ya zabi daukanta da kan nasa dan tabbatuwar hakan ya faru.

Ammi motar tata mijin da aka bude mata ta shiga batareda ta shiga ta Aleey ba daya fito ya bude musu kofar.

Bahar ce ta saka kafarta a natse ta shiga motar ya rufe yana komawa ya shiga ya tada sukabi bayan sauran motocin a natse suka fice daga masarautar boyem.

Ko da suka isa airport ba sautan time sozai dan haka kai tsaye wucewa sukai ciki suna duba time wanda Allah yasa basu wani bata lokaci ba jirginsu ya daga qasar.

***Tafiyan wuni guda sukai me kafin duka sauka a inda duk gajiyansu basu tsaya sun kwana ba haka suka dauki hanya da wata sabuwar private bus data da komai da suke buqata a ciki suka wuce Anjom nanma motocin securities dinsu na biye dasu da wani irin tsaro.

Tinda suka kama hanyar da dukansu sukaga bata ruwa bace mamaki da shakku masu karfi suka rufesu musamman ganin hanyar titi ce suke bi wanda yake sabo a bayyane bawai tsohon aiki ba da alama kenan an bude hanyar zuwa garinsu ba dole saita hanyar ruwa ba.

Ga mamakinsu hadda motocin kasuwa dake tafiya wasu kuma fitowa daga hanyar garin tareda mashin mashin harma da masu tafiya a qafa jefi jefi wanda yeke nuni da hanyar zuwa garin jamaa sosai ne suke kokuma garin kasuwanci.

Kasa mahana kowacensu tayi suka zuba idanuwansu suna bi da kallan ikon Allah da mamaki da farin ciki duka a zuciyoyinsu lokaci daya.

Symbol suka gani shima babba dayake dauke da sunan garinsu baro baro hade da sunan masarautar garin ta ahalinsu wato ANJOM GHAZ.

Bahar kanta farin cikine takeyi sosai ganin garinta da mahaifinta ya dawo cikakken gari a yanzu abinda Abaa dinta yaso Allah bai basa damar cika wannan burinba gashi bayan ransa an samu cika hakan.

Basu sake shiga mamaki ba saida suka iso cikin garin wanda yake garin gaske ayanzu hakama manyan shaguna da malls malls da manyan gurare daban daban hakama ga wutan lantarki.

Baban ginin dayafi kowane gini a garin suka tsaya mai hawa biyu da wani irin girman gaske gate har mataki biyu da securities da fadawan da aka dauka aiki aka qara da securities da tarin bayin hidima suka tsaya ginin na dauke da sunan GHAZ Empire acan sama da manyan baqaqe na kalan zinari yana daukan ido da haskawa.

Bude musu gate din farko akai suka shige aka rufe suka isa gate na biyu aka budesa shima motar ta shige sauran motar securities kuwa a harabar gate din farko ta tsaya tareda bayin da suka taho dasu sedai su suka isa da kafa zuwa ciki bayin.

Su kuwa ana parking a babban harabar gurin da girmansa yayi yawan da zai dauki motoci fiye da takwas a bakin babbar kofar shiga main entrance ta farko wadda kana shigarta bangarora ke kashi kashi da suke a tsare cikin wani irin kyakkawan gini da tsarin zamani na turawa da daula aka tsaya dasu aka bude motar suka fito.

Suna fitowa bayin dake jere suna jiran isowansu kansu a qasa suka fara musu barka da sauka cikeda girmamawa kafin suka fara daukan kayansu a natse suna wucewa ciki dasu.

Shigowa sukai wanda tin daga nan babbar jakadiyar gidan datake bada umarni ga bayi itace tayiwa kowa iso bangarensa da babu bangaren da babu duniyar jin dadi a cikinta.

Bangaren Ayanaah shine bangaren mafi girman gaske wanda yake dauke da dakuna kusan guda biyar da palo uku sai toilet a kowane daki da kitchen da dining room me girma da babu luxury dun da baa zuba ba.

Bayan bangaren Ayanah sai bangaren da Sakinah zata zauna wanda yake komai iri daya dana ayanah sedai ita 3 bedrooms ne da palos guda biyu da babban master bedroom mai hade da palo,

Bangaren Zuhrah ma irin hakan ne saina Bahar wanda yake shima iri daya sak sai babban bangaren da aka ware can gate din farko akai hadaddiya wadatacciyar fada me tsari datake dauke da offices kusan guda biyar masu tsari da kuma babban dakin taro maana meeting da sauransu.

Acan baya kuma bangaren bayi ne da maaikatan gidan da kuma bangare daya daban dakin securities dinsu ne a jere da suma daidai gwargwado ba abinda babu.

A jikin bangaren Ammi wani lafiyayyan bangaren da Sultan zai zauna yake wanda yake tamkar shine bangaren da daace Abaas yana raye zai zauna sbd shine na namijin gidan,

Akwai palon daya hada bangaren dana Ammi wanda ta cikinsa kawai zata fada bangarensa hankali kwance.

A bisa tsarin ginin asalin iya jinin GHAZ din akai ginin aka warewa kowa bangarensa kaman rabon gado,
Ayanah,zuhrah da bahar wadda ita kadaice a cikin yaya take asalin jinin ghaz sbd mahaifinta ne ita bawai mahaifiyarta ba kaman yanda su su NUAB da leylah sedai ace jinin boyem ne su.

Sakinah ta zama jinin ghaz kaman yanda suke fada dan hakanne akai gunin da ita wanda koda aure ko ba aure tanada bangaren data mallaka a cikin masarautar ghaz da itace asalinta yanxu.
#MAMUH
09033181070
[13/01, 6:43 am] Dasoo: HAYATEEM
Mamuhgee

167
A bangaren Ammi dukansu suka sauka banda zuhrah data sauka nata bangaren da bayinta da tini suka fara aikin jera kayanta a wardrobe suna sake gyara komai daidai da yanda tsarinta yakeso.

Suma a bangaren Ammin Dakin Ammin shine a kurya me hade da palo me tsari sai sauran bedrooms din a jere a hallway saina maa tenya a main babban palo wanda hake hade da qaramin palo a cikinsa shima sbd itace zata zauna din din shiyasa nata yake hade da palonta dan haka nasu dakunan basuda palo.

Akwai gajiya me tsananin gaske a tattare dasu dan haka kowa daki ya shige dan rage gajiya da ibada.

Wanka da ruwan zafi tayi masu cire gajiya,
Tara ruwan ma tasaka Naimah tayi mata a bathtub kafin taxo ta shiga tana rufe idanuwa sbd ratsata da ruwan sukai suna fara rage gajiyan datake ji musamman kafafunta da suka dan kumbura kadan sbd zama.

Wanka tayi sosai a natse bayan ta gasa jikinta tukuna tai brush da sabbin komai da aka jere musu na buqata a toilet dinsu komai a kwai.

Tana fitowa sama sama tayi shirin ta saka riga da wando masu kauri da hula ta saka doguwar riga akai tayi sallar asuba da akai suna hanyar anjom din.

Tana idarwa tea me zafi ta saka aka kawo mata har daki sika hado da cake me laushin gaske sabo da akai tinda uwar asubar,
Tas ta shanye tea din kafin taci cake din daya tasha ruwa kafan ta kwanta tana shigewa barko tareda kashe wutar dakin ta qarawa ac din karfi kadan take bacci me karfin gaske ya rufeta sbd ko gani batayi sosai sbd baccin.

Kusan kowama hakan yayi ya kwanta dan suna cikin gajiya matiqa.
Chapter 93 · 0% Book details