← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 112

Sashe 12

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fetto na fitowa sakon na isowa dan haka da sauri ta qaraso tana zubewa qasa gaban manzon sakon tana masa Barka da isowa tareda kirari ga sakon na sultan.

Hannuwanta biyu ta dago tana miqawa dan amsar sakon Wanda ya saka Salman sake saukar da Kansa qasa zuciyarsa na Wani irin tsima da tsananin tashin hankali yana ma kasa kallan sakon.

Fetto kuwa tsabar Murna jikinta har wani rawa yakeyi ta amsa tareda zuba godia ta juya ta shige ciki da sakon.

Ko data iso palon da suke Zaune gabaki dayansu suna cin abinci har lokacin ASIM ne idanuwansa suke fara sauka Akan hannuwanta biyu dake dauke da takardar fadar sultan dan haka ajiye cup din hannunsa yayi a hankali yana kafe idanuwansa Akan hannuwan nata ba kyaftawa zuciyarsa na cikewa da Wani irin farin cikin da tinda yake bai taba jinsaba.

Aslam da meryam kallan yanayinsa sukeyi da mamaki kafin suka Waiwaya suna kallan inda yake kalla da wannan yanayin da suma basu taba ganinsa a ciki ba.

HAILE ma juyawan tayi ahankali ta kalli inda suke kalla gabaki dayansu taga fetto na qarasowa dauke da takardar da dole daga sultan ta fito tana daukan ido sbd kyallin kalar gold dake jikinta.

Wani irin farin cikin taji itama ya cikata Wanda ya sakata ajiye spoon din hannunta taba daukan tissue ta goge baki tareda miqewa tsaye take suma yayan nata suka fara miqewa daidai nan fetto ta iso da takardar wadda ta miqawa ASIM.

Cikeda farin cikinsa dayake sake bayyana ya karba tareda budewa a hankali yana karantawa jikinsa har tsima yakeyi ganin cikakken izinin mallakar Bahar a matsayin imebētinsa wadda samunta a rayuwarsa shine matakin farko na nasarar rayuwarsa da zai fara daga yanzu,

Sunanta daya aikawa sultan shine a bayyane Baro Baro a rubuce cewan ta zama imebetinsa daga yau dan haka rufe takardar yayi hannunsa na dan rawa ya miqawa fetto ya kalleta da dukkanin idanuwansa yace

‘Ki Kai bangaren wishmah wannan sakon na tenya ne a gobe nake buqatan wara haka imebeti dina tana bangarena’

Da tsananin mamaki fetto ta kallesa tana amsar sakon hannuwanta na dan rawa sbd shock da fiyayyan mamakin Jin sunan imebeti a bakinsa Bayan Leylah jinin sarauta ce meya hadata da sunan imebeti kuma?

HAILE kallansa tayi tana dan Kama Fuska zatai magana Aslam da bazata iya jiran bayani ba karban takardar hannun fetto tayi tana budewa Kai tsaye tafara karantawa rubutun Wanda yake a rubuce da yarensu da manyan baqaqe masu kalar zinari na alkalamin sultan me mulki.

Meryam data Riga Aslam gama karanta sakon Wani irin sanyi kafafunta sukai me tsananin gaske suna kasa daukanta ta zame ahankali tana Zaunawa idanuwanta na dagowa da Wani mugun kallo tana kallan ASIM dan tabbatarda farin cikine bayyane a fuskarsa na abinda yake rubucen.

Aslam miqa masa takardar tayi tana masa Wani kallan mamaki me tsananin gaske ta bude baki tace

‘Kaga menene a ciki?
Ka fahimci abin dayake cikin sakon kuwa?
Kasan me aka aiko maka?

Miqawa fetto sakon ya kuma yi yace ta fice ta Kai ya kalli Aslam zaiyi magana HAILE datake Jin yanayin zuciyarta na sauyawa ta Dakatar dashi da cewa

‘Menene yake rubuce a ciki?
Ba auren Leylah bane a cikin sakon?

Meryam datake Jin kanta na Juyawa ce ta iya bude Baki jikinta na tsananta mutuwa da Wani irin yanayin da bazata iya fassarawa ba tace

‘Imebēti aka basa a maimakon auren Leylah’

Aslam data kasa Hadiye tsananin baqin ciki da fushin dayake taso mata ta Dora da cewa

‘Kuma da alama yasan da hakan sbd farin cikin dayake bayyana a fuskarsa,

HAILE dataji kaman bata fahimci zancen da kyau ba kallan ASIM din tayi da duka idanuwanta fes a Kansa zuciyarta na sauya bugawa ta bude Baki tace

‘Imebetin?shi sultan dinne yaga ya kamata ya baka imebeti Bayan ya bawa ‘dan mistress dinsa auren jinin yunar?

Juyowa tayi Akan Aslam da meryam tace

‘Sunan ASIM dinne kuwa kuka gani a rubuce ciki kokuwa sbd sakon bazai taba kasancewa nasa ba dan ba yanda zaayi yana matsayin me jiran gadon kujeran BOYEM ya fara da imebeti batareda yayi aure ba hakama yayansa manya su fara zuwa daga imebēti,
Tayaya hakan zai taba yiyiwa?
Ba sakonsa bane?

Aslam data gama kaiwa qarshen baqin ciki dafe goshinta tayi tana bude idanuwanta jajir tace

‘Mamee yana sane fa,kuma da alama shine a buqaci hakan’

Kafesa da ido HAILE tayi sbd tanason ji daga bakinta idan sakarai ta haifa bata saniba

Kallan Hailen yayi yana matsowa gabanta ya Kama hannunta cikin tausasa harshe yace

‘Mamee ba imebeti ce kadai ba sonta nakeyi so me tsananin da zan iya komai akanta ciki hadda rasa rayuwata,
Ba jinin sarauta bace baiwa ce dan haka Banda zabin daya wuce karbanta a matsayin imebē…….

Bai qarasa ba HAILE ta sauke masa Wani lafiyayyan Marin daya saka meryam miqewa tsaye da sauri Aslam ma cikin sabon tashin hankali take kallan Hailen da idanuwanta jajir.

Kasa dagowa ASIM din yayi idanuwansa na rikidewa zuwa jajir zuciyarsa na cikewa da Wani irin ‘daci da baqin ciki me girma.

HAILE ma kasa dauke idanuwanta daga Kansa tayi hannuwanta na wata irin rawa zuciyarta na tafarfasan da bata taba ba kowace gabar jikinta wutar baqin ciki ne take ciketa tana rasa abin fada.

Bata taba sanin sakarai mara tinani da hankali ta haifa a rayuwarta ba sai yau,

Baya tayi ahankali tareda Juyawa ta sake juyowa ta kalli ASIM din ta bude Baki kirjinta na tsananta nauyi tace

‘Me zakai da imebēti Banda zuciyarka ta mutu?
Har akwai abinda wata baiwa take dashi Wanda yakai na Leylah?
Baiwa zaka fara haifar yayan Ka da zasu gaji sarauta daga gareka?
Wane soyayyar kake magana?
Ka sani wlh tallahi indai ina raye bazan Bari Ka fara karban imebēti ba batareda Ka auri jinin sarauta ba musamman wannan da kake ikirarin kana so da zata iya sakaka rufe ido Ka zabi gaibu Akan jinin Leylah datake jinin boyem.

Dagowa yayi idanuwansa jajir ya kalli mameen ya bude baki yace

‘Mamee zan auri jinin BOYEM daga baya amma a yanzu ina tsananin son wannan ita zan mallaketa….

Aslam data rasa abin cewa Juyawa tayi cikin tsananin baqin ciki taba barin palon hakama meryam da zuciyarta ke gap da bugawa ficewa tayi.

HAILE ma cikin baqin ciki ta juya tabar gurin tana yanke hukunci a ranta baiwar kowace iri ce zata bar duniya dan bazata taba zama imebetin ASIM ba a yanzu.

Fetto kuwa tana fitowa Kai tsaye bayi hudu ne suke biye da ita zuwa bangaren wishmah dan miqa sakon ga tenya zuciyarta cikeda baqin ciki itama da damuwa dan ba hakan sukeso ba.

Suna tinkaro bangaren securities din dake gurin suka miqe tsaye kowannensu ba rahama a fuskarsa dan kuwa ko wane yare ma wainnan basa ji sai turanci kawai dan haka basada lokaci ko iya tambayar komai.

Kokarin isowa sukeyi ba tsammani sukaji Wata irin azabar data zubar da su qasa tana ratsa kwakwalwansu wadda tama kasa daukan azabar.

Fetto ce ta iya juyowa taga bayin a zube qasa gabaki dayansu jini a kafafunsa sbd harbin da akaiwa gefen kafarsu batareda ta ratsa qashinsu ba.

Juyawa taji idanuwanta da kanta sunyi sakon dayake hannunta yana faduwa qasa ta dago komai na jikinta na masifar rawar mummunan firgita da tashin hankali batasan lokacinda ta zube ba zata fasa Ihun hankalinta dayake kokarin barin jikinta ganin meya samu bayin Bayan.

Wata irin damqa akai mata tamkar daurin kasar da zaa yanka akai mata tareda soka mata wata allurar data sumar da ita aka bar gurin da ita Sauran bayin ma sbd Hana hayaniya tashi a kofar bangaren na Ammin daukansu akai aka aika su clinic din cikin masarauta suna barin gurin gabaki daya tareda daukan sakon suka kaiwa aleey Wanda bai Bari ya isa ga NUAB ba ya kona sa suka cigaba da shaaninsu tsit kake ji.

Kadir ne ya iso gefen sultan a cikin Daren ya rankwafo cikin nutsuwa ya sanar masa abinda ya faru din.

Numfashi Mara sauti sultan ya sake yana dago manyan idanuwansa daga abinda yake karantawa a Wani file ya bude baki Kai tsaye yace a sake aika Wani sakon Kai tsaye a gurin tenya ta tabbatarda an fara shirin imebētin ASIM din a gobe hakama a hada tareda sabuwar takardar auren NUAB din akaiwa mahaifiyarsa.

Sabuwar takarda kadir ya fitar wadda a cikin Daren ta isa bangaren wishmah batareda sanin Bangaren NUAB ba.

Isowan sakon Wanda ya saka Ayanah zubawa takardar idanuwanta da tsananin yanayin da takasa gane wa kawai dai tasan tana farin cikin auren yar Zuhrah da NUAB dinta Wanda take Jin ma a gaggauce take son Ayi auren dan haka cikin godia da farin ciki ta amsa sakon.

Tenya ma cikeda mamaki take kallan nata sakon Wanda ya sakata shiga wasi wasin Kai tsaye menene dalilin ASIM na buqatan imebetin kuma shine ya zabeta da kansa.

Maa sakinah dake fitowa daki kallan tenya tayi tareda kallan takarda hannunta wadda idonsa suka sauka Kai tsaye Akan abinda sakon yake isarwa da sunan Bahar.
#MAMUH

HAYATEEM
by
Mamuhgee
700
0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi
09033181070

Yan Nijar kuma
89825722
Depot my nita
Nissaiba laouali
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

82
Kasa yadda da abinda idanuwanta Maa sakinah tayi sbd kanta dataji yana Neman juyewa ta zagayo ta gaban tenya din tana sake tabbatarda abinda yake gani a rubuce ta bude Bakinta da Wani irin sauti tace

‘Wace Bahar din ce zaa bawa ASIM a matsayin imebeti?

Da mamaki tenya ta dago ta kalli sakinah tareda cewa

‘Wace baiwar ce Bahar?
A wane bangare take?
Anan bangaren take ne aka aiko mun sakon anan kokuwa ma tana ina ne ni Bansaniba ma’

Sakinah datake kasa yadda ga bugun zuciyarta na mugun tsananta harbawa da karfi tareda Wani irin tsoro me girman gaske sbd batama San tayaya wannan Masifar ta qullo ta bullo ba,

Wani faduwan gaban ta sake ji tana tinawa da Bahar tayi aiki a bangaren ASIM din Wanda sai yanzu taje dawo da tinanin Kai tsaye shine ya buqaceta dasu naima da komawa bangarensa aiki.

Kallanta tenya keyi sosai da kyau ganin yanda zufa yafara tsiyayo mata tana shiga tinanin datake sake shigar da ita tinani da zullumi itama.
Chapter 12 · 0% Book details