← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 112

Sashe 22

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya meryam ta dauka cikin rawar jiki ta kira likitansu a boye tareda sanar dashi abinda ya faru dan haka ba shiri ya hado duk abinda zai bugata ya nufo bangaren aslam din cikin duhun daren.

******Duk abinda akeyi Sultan yana jin qarar komai a kunnuwansa amma sbd a yanzu baida hurumi ko daya na shiga ko daukan mataki a matsayin shugaba kokuma me mulkin boyem sedai a matsayin uba ko me bada shawara idan ta kama dan haka shiru yayi a zaune batateda motsawaba a zuciyarsa yana fatar a cikin yayan nasa duka da matansa babu wanda yabi sharrin zuciyarsa yayi abinda zai zama matsala ga rayuwan dukkaninsu.

Har daren yayi tsit aka dena harbin dare ya qara tsalawa koina ya sake dauke motsi batareda anyi sautin mutuwar jinin boyem ba ya sakasa sauke wani boyayyan numfashi me sanyi da nutsuwa kafin ya miqa hannunsa a natse ya dauki wayarsa ya saka kiran wayar tenye.

Babu bata lokaci tenya ta dauki wayar cikeda girmamawa ga tsohon sultan duk da dare ne sosai su kam bazasu iya bacci ba a wannan daren sbd tsimayin dake zuciyoyinsu na shedar da wannan daren na alkhairi a garesu.

Magana daya zuwa biyu yayi da ita ya kashe wayar ya sake sauke ajiyan zuciya a karo na babu adadi bayan saukarsa a matsayin sultan cikin daren tukuna ya miqe a natse cikin kamewa da samun cikakken yancin da ayau zai fara samun rayuwar da zuciyarsa ke tsananin muradi tin daga ranar daya fara dora idanuwansa akan AYANAH GHAZ.

Kai tsaye fitowa yayi batareda yan rakiyar kowaba cikin samuwan cikakkiyar nutsuwan yanci daga mulkin dayake tauye da abubuwan rayuwarsa da dama wanda a yanzu yasan NUAB zai kawo sauyi daga mulkin dayake na takura da rashin yancin kai zuwa mulkin da zai baka nutsuwa da yanci tareda hana kowace irin al'ada me tsananin datake sanadin rayuka da dama.

Kai tsaye bangaren wishma dinsa ya nufa wadda ta farka a daidai lokacin itama jikinta a tsananin sanyaye tana kokarin dawo da tinanin dukkanin abinda ya faru zuciyarta na wani irin nauyi.

Shigowansa ya saka gabaki daya bayin bangaren ficewa kofar bangaren suka tsaya gefe daya a jere har sai lokacinda ya fice.

Tenya da sakinah ma cikin tsananin girmamawa tareda farin cikin kasancewansa ayau tareda ayanah suka fito gabaki daya
Maa sakinah ma bangaren NUAB ta nufa cikin daren batareda tsoro ba dan dubo halinda Bahar take ciki.

****kai tsaye yaba baro can bangaren da ita bangarensa ya nufa wanda har lokacin tana jikinsa ta kasa dena kukan matsanancin tsoron data samu kanta a cikinsa.

Bude masa kofar shigewa palon farkonsa akai da sauri cikin nutsuwa yana qarasowa ya shige take aka rufe kofar kuma bame shiga sai gobe nadin sarautar da duniya zata sheda tinda safe.

NUAB na shigewa waya aleey ya buga fada yace KEELA babban wanda shine yake bin aleey a matsayi yace a saki manyan fada sbd nadin sarautar gobe da safe.

Ba bata lokaci kuwa aka sakesu take kowannensu ya fice jiki yayi tsami da sauri suna matsuwan gobe tayi susan waye sabon sultan din na boyem.
#MAMUH
#BEST LOVE
#SULTANS
#AYANAHS

HAYATEEM novel
700
0022419171 AccessBank maryam sani gummi
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

93
Yana shigewa kai tsaye bai iya ajiyeta bedroom din data sama zama ba sbd bazai taba samun nutsuwa ba gabaki daya jin yake duniya kaf bai yadda da kowa da komai akanta ba dan haka hanyar nasa bedroom din ya nufa da ita har lokacin kukanta me fita a hankali na ji da shedar da balain da bata taba ji da ganiba a rayuwarta bai dena fitowa ba yana ratsa kunnuwansa.

Bude kofar bedroom dinsa da babu wanda wanda ya taba shiga bayan mutum biyu rak masu aikin gyaransa a cikin yaransa ya shige tareda rufewa yana nufar tsakiyar dakin inda lafiyayyan king-size royal bed dinsa yake komai na dakin qamshinsa yakeyi dan kuwa hatta niiman da zaa shaqa a dakin kowace iri qamshinsa ne yake tashi a cikinta hakama sanyin aircon dayake ratsa koina qamshin nasa ne shima kusan yake ratsa koina din dashi sbd komai nasa ya riga ya kama qamshinsa da babu me irinsa a masarautar masu nayan shi.

Zaunawa yayi a bakin gadonsa da ita a jikinsa yana yin shiru a natse idanuwansa na dan lumshewa kadan sbd sautin dayake ratsa kunnuwansa har lokacin yanawa komai nasa illa musamman tinaninsa dayake jin wata irin wuta na cin kirjinsa na iya daukan kowace irin mataki akan wainda suka iya haukatar da kwanciyan hankalinta zuwa ga duka tashin hankalin data shedar.

Ita kanta kasa motsawa tayi a jikin nasa har lokacin jikinta yar rawa yakeyi tana dan sake qanqamesa kukanta naci gaba.

Shiru ba motsin komai ba sautin ko fitar numfashinsu a dakin saina kukanta tsawon mintina sosai a hakan kafin tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya mara karfi sbd jikinta daya gama mutuwa da rashin karfi tayi sanyi sosai,

Shi ma shirun ya sake yi har lokacin baice komaib bai kuma motsaba tana rungume a cikin jikinsa tana qamqame dashi,

Bayan tsawon mintina bayan ta dena kukan ajiyan zuciya ta ringa jerowa a hankali cikin sunyi jikinta na qara sakewa,

Fara sakinsa tayi a hankali tana jin nutsuwanta tana dawowa jikinta,

Dago kanta tayi a hankali daga kirjinsa tana kasa kallan fuskarsa ta dan motsa tareda qasara sakinsa gabaki daya idanuwanta da sukai jajir suka kumbura suna kasa kallansa.

Qugunta daya zagaye da hannuwansa masu karfi laushin fata da wata irin dumi ya dan sassauta riqon yana saukar da idanuwansa akan fuskarta data sakasa kasa qarasa sakinta sbd yanayinta yana sake bayyanar da zarewan data kusa yi a halin data shiga.

Shiru tayi ajiyan zuciyarta na kukan datasha yana sake fita akai akai tana jin hannuwansa sun kasa saketa wanda ta kasa doguwar motsi itama tana rufe idanuwanta sbd nauyin idanuwan dana hannuwansa dake rungume da qugunta tana jikinsa sosai,

Dago idanuwanta tayi a hankali batareda ta motsaba tana san kallan fuskarsa amma zuciyarta na hana hakan,

Maida kanta tayi qasa tana son sake rabuwa daga jikinsa,

Sake kallanta yayi yana jin dukkanin motsinta a jikinsa,
A natse ya saketa tareda tayar da ita zaune daidai a kan kafafunsa yana qin kallanta sbd zuciyarsa dake wani irin zafi da radadin abinda ya kusan faruwa da ita a daren wanda zuciyarsa ta kasa sakewa ta kasa iya cirewa daga idanuwa,zuciya,kwakwalwan da tinaninsa shiyasa babu sauyi ko daya daga yanayinsa na fushi da tsantsar baqin ciki da bacin rai a daren wanda tabbas bazai mancesa ba sbd abubuwa da yawan da suka faru a cikinsa,

Yanda ya zaunar da ita akan kafafun nasa ya sakata dagowa a hankali jiki a mace ta kallesa sbd jin shiru har lokacin bai iya furta kowace kalma ba hakama hannuwansa tabi da kallo taga jijiyiyin jikinsa duk sun fito alaman jininsa tafasa yakeyi,

Tasan yanada yawan fushi da zafi ga duk abinda aka tabasa akansa amma bata taba ganinsa a irin wannan yanayin ba wanda ya sakata jin jikinta ya sake mutuwa ta dago idanuwanta dasukai mummunan nauyi sbd kuka ta kalli fuskarsa wadda tayi jajir tana kasa dauke idanuwanta sbd shima dagowa yayi a wani yanayin daya saka tsikar jikinta gabaki daya miqewa ya bar idanuwan nasa akanta har lokacin babu wanda ya iya cewa komai a tsakaninsu bare motsawa.

Ahankali ya sauko da idanuwansa zuwa ga wuyanta da jini yake kwance a jikinsa zuwa cikin rigarta daga gefen kafadarta,
Fuskarta ya dawo da idanuwansa kafin ya sake maida kallansa akan jinin wanda da alama rauni ne taji wanda itama bata san dashi ba.

Idanuwanta ta dauke akansa a sanyaye tana dorasu akan inda yake kalla da dukkanin jajayen idanuwansa dake qaruwa a lokacin,

Ganin jini a jikinta ya sakata jin kanta ya sara da karfi hannuwanta na dan daukan rawa tsananin tsoro da wata irin firgita na shigarta ta daga hannunta dayake rawa sosai a rikice zata dora a gurin ya kama hannunta da nasa yana hanata tabawa tareda zuba mata idanuwansa cikin wani slow dayake tafasa jininsa,

Wasu sabbin hawayene suka ciko idanuwanta wainda ya kalli cikinsu baya iya cewa komai sbd idan yakai karshen qonuwa a bacin rai da fushi baya magana sam sam.

Hannunsa yakai gurin kai tsaye a cikin wata nutsuwa ya kama rigarta ba tsammani taji ya saukar daga kafarta wanda ya sakata saurin kama hannunsa da tafin hannunta tana dagowa ta kallesa hawaye dake cikin idanuwanta suna gangarowa a hankali.

Bai kalleta ba idanuwansa na kan raunin ya saka hannunsa dayake bayanta ya mannota sbd bayan datai kadan ta manno da kirjinsa sosai ya zagaye qugunta da hannunsa daya tareda qarasa saukar da rigarta daga kafadarta wadda ta sakata rintse idanuwanta da karfi bugun zuciyarta na fita da karfin dayake iya gani a saman fatar kirjinta fara tas datake wani daukan ido.

Jinin ya zubawa ido tin daga inda ya fara zuwa inda ya sauka wanda ya tsananta wani nauyin karjinsa sbd ba raunin dataji jinin wani ne ya dauka a jikinta wanda ya sakasa jin hannuwansa na dan rawar data sakata bude idanuwanta ahankali tana fara saukewa a fuskarsa wadda ya dago jajayen idanuwansa ya zuba gabaki daya akanta yana mata wani irin kallan daya ringa saka bugun zuciyarta qaruwa ta maida kallanta akan gurin wanda itama taga tamkar jinin ne kawai ta daga hannunta dayake rawa ta nufi gurin zata taba ya sake riqe hannunta da karfi yana hanata taba jinin dayake jin yana neman yanke numfashinsa sbd nauyin da kirjinsa yayi sbd tabbatarda jinin a cikin mazan biyu ne da suka tarar a dakin.

Miqewa tsaye yayi batareda yace komaiba ya dauketa kai tsaye toilet dinsa da baya taba iya sharing da kowa a rayuwarsa baya iya sharing toilet da bakwancinsa da kowa tin yana yaro bai taba iya hada gurin kwanciya da kowa ba bare hada toilet,

Ciki ya nufa da ita kai tsaye sbd shi kansa bazai iya saka hannunsa a jinin wanda iya ganinsa tafasa nasa jinin yakeyi ba bare barin ta saka hannunta,

Girman da toilet din nasa yake dashi ya saka suna shiga wani sanyin gaske ya ratsa har zuwa cikin naman jikinta ta rufe ido tana jin wani iri.
Chapter 22 · 0% Book details