← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 112

Sashe 34

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baicewa Ammin komaiba akan tafiyar haka ya miqe ya tafi zuciyarsa kaman zatai bindiga sbd yasan koma menene da ina wannan tsarin ya fito ya fito ne daga mahaifinsa dan haka shima zai san ya tabasa,

Yana dawowa bangarensa kai tsaye aleey ya kalla da jajayen idanuwansa ya basa umarnin a nemawa Ammi komai na tafiyar bahar da ita zaa koma UK din tabar boyem har sai bahar ta kammala su dawo tare.

Kallansa aleey yayi da dan sauri cikin fargaba da mamaki amma baida ikon fadar komai haka dan haka cewa yayi angama kawai ya juya fice yana daga wayarsa dan samar ma da bayanin komai akan tafiyar ta bahar da inda zata zauna da inda zatai karatun wanda ba iya Ammi kadai ba hatta su zai samar da komai na tafiyarsu ya ajiye sbd daga yanzu qasar zata zama gurin zuwansu kowane lokaci.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee

106
Bahar har zuciyarta tafiyarta karatun yayi mata daidai tareda bata dukkanin nutsuwan datake jin tana buqata na rayuwa a wajen Boyem sbd a cikin wani irin tsananin tsaro suke rayuwar babu yancin shan iskar rayuwar da duk kake buqata,

Damuwarta daya ce rabuwan da zatai da Ayanah wadda a yanzu kauna ce me karfin gaske a tsakaninsu sbd ita kallan Abaa dinta takeyi mata kaman yanda itama ayanah din kallan Abaas dinta takeyi mata hakama a yanzu da suka san juna suke tare da juna suke kuma kaunar juna a bayyane a zahirance babu shamaki ko daya,

Kauna ce ta asalin bayyane dake cikin jininta ayanah kewa bahar din wadda kusan a hankali duk wanda yake tareda dasu a masarautar suke sani,

Itama bahar a yanzu tana kokarin sakewa da Ayanah din kaman yanda ta sabu da maa sakinah dinta dan bawa ayanah din dukkanin sanyin zuciyar datake buqata daga gareta,

A bangaren daya tenya da Maa sakinah gabaki daya soyayyarsu suma da kaunarsu akan bahar din take duk da suna nunawa Leylah tata kaunar sosai itama amma sbd kaunar da sukewa Bahar ta bangare uku ce zuwama hudu sai tata din tafi bayyana,

Ta farko asalin kaunar mahaifinta ce,
Ta biyu ta zamtowanta mata a gurin 'dansu da suke tsananin so wato sultan LEUL,
Ta uku kasancewanta Rabin zuciyar ayanah da bata hada da komai,
Saina karshe shine zamtowanta marainiyar da batada uwa batada uba saisu,

Ita kanta Zuhrah kauna me karfi mara sirki takeyiwa bahar din wanda taso saka hannu sosai akan bawa bahar din ilimi da inganta rayuwarta amma Ayanah ta dakatar da kowa daga hakan bata son kwandalan kowa a gurin bawa Bahar din ilimi sbd har abada tako wane bangaren bata son ayiwa Bahar gorin komai na rayuwa matiqar dukiya zata nema ta samar mata dashi koma menene.

Hakan ya saka ta sake ta fidda dukiya me yawan gaske dan sauya rayuwar 'yarta zuwa duk inda 'ya mace me gata zata kai,

Bedroom daya aka warewa Bahar din acikin bangaren itama aka gyara matashi da komai sabo me tsadar gaske da duk wani jin dadi da tsarin da zai tabbatar maka daka shigo dakin mace yar gata me aji,

Closet din gaske aka kira masu shiryawa suka shirya mata da wasu irin designers na kasashe daban daban fiyeda a tsaya kirgawa,

Undies da kayan bacci ma haka aka taho dasu masu kyau da tsada ba adadi aka jere kafin suma designer shoes and hand bags harma suitcases na tafiya da tirarika da wasu duk abubuwan da akasan mace na buqata an kawo an jere su a dakin an kammala mata komai tamkar ba wadda zatai tafiya ba tabarsu kuma taje can a siya wasu kayan,

Ba iya kayan designers aka tsaya ba hatta sitirun sarauta dana Al'ardarsu an kawo su masu tsada an jere mata su tareda Tirarikan da Maa tenya ta hado mata da kanta wainda suna kama jikinka to shikenan ka gama zama mai ratsa zuciyar duk wanda zai shaqa qamshin wanda komai na irinsa akwaisa zaka samu a gurin (SHUWA INCENSE AND MORE 07042293387)

Maa Sakinah ganin rayuwar Bahar ta sauya sawu zuwa kyakkyawar rayuwar da kowane dan gata me uwa da uba zai samu ya saka zuciyarta da hankalinta kwanciyan da a yanzu babu abinda take so da buqata arayuwa bayan gamawa lafiya.

Ayanah ma kasancewan Bahar din a rayuwartata ya saka dangana me karfi da tawakkali da cire dukkanin wani qunci a ranta suke shigeta tasan bazata taba manta rayuwar data fito da kaddara me girma da muni ba amma kuma samun Bahar ya lullube mata kaso me girma a cikin baqin ciki da quncinta ga kuma ganin Zuhrah a tareda ita da 'yayan Zuhrah dan haka ta rungume sabuwan rayuwan data zo mata da hannu biyu dan hana 'yayansu shiga damuwa da quncin da zasu ringa fuskanta da gani a tattare dasu.

Zuhrah da itama ta samu hadin kai sosai daga mai girma yunar akan kasancewa da yar uwarta ba shamaki sakewa tayi suna bayyanar da kaunarsu da aka raba ta shekarun da sun riga sun rasa dan ba lallai su maimaita irinsu ba..

Duk wannan shirin da akeyi da kokarin inganta rayuwar Bahar LEUL baya ciki sbd sosai zuciyarsa ta tabu da hakan dan babu inda ko shawara Amminsa tayi dashi dan haka yaqi cewa komai ya kuma dena shiga komai din dan kuwa ita kanta Bahar bayajin zai sake bi ta kan rayuwarta kwata kwata zebarwa Amminta ita koma me sukeso suyi,

Ya rage shigowa sosai bangaren na Amminsa sbd ayyukan gabansa da sukai masa yawa da kuma tattara komai nasu da yayi ya ajiye musamman koyaushe bangaren kusan a cike yake da Zuhrah da 'yayanta dake wuni bangaren basa taba tafiya sai dare duk da leylah har lokacin a bangaren take bata koma bangaren iyayenta ba,

Sultan ma dayake bangarensa hutun gaske yake samu babu kowane irin damuwa da tinanin mulki dayake kansa dan haka shirye shiryen barin qasar yakeyi zuwa dogon hutun da kansa sai sake bayan shekaru masu yawa akan mulki,

Leylah duk inda hankalinta yake baya cikin jin dadi ko kadan kowane dare da baqin ciki take wuni hakama kowane wuni da baqin cikin take wuni sbd yanda aka jingine maganar aurenta tsaf a gefe da sultan me mulkin boyem an maida hankali akan yanda zaa inganta rayuwar wadda take ganin aikin banza ne kawai sbd har abada bazata samu ilimin da zai saka LEUL me boyem sonta ba harma ya iya zaman aure da ita sbd alamu suna nunawa mulkin yanzu da zai wakana a boyem na sauyin zamani da ilimin boko ne da baa buqatar duk wani mara ilimin a cikinsa.

Bahar bata taba damuwa da kiyayyar datake gani a idanuwan leylah ba sbd tana daukan hakan ne a matsayin rashin sabo da sakewan da basa dashi kwata kwata a tsakaninsu dan sam ko guri daya basa zama sbd ita kanta hakanan bata jin shaawan zama idan leylah din ta fito a guri sbd irin kallan datake mata da magana a cikin rashin mutuntawa ko nuna darajar dan adam gareta ita kuwa sam bata iya zama da duk wanda yake hakan dan batajin tanada rashin darajar da har zaa ringa mata kallan qanqantacciya dan haka saima tafi leylah din rashin son zama a duk inda take sam bata buqatan zamowa inuwa daya da ita.

Shuraim kuwa tinda ya dora idanuwansa akan bahar a ranar farko yaji zuciyarsa ta nutsu da ita nutsuwan dayake jin zai iya rayuwa a duk inda take dan haka sai bayada gurin zama fira a boyem din idan baa bangaren Ammi ba a tareda iyayen nasa da Bahar wadda take wata irin sauyawa tamkar ba ita dinba dan kuwa sosai ayanzu tenya take mata gyara itace ke kulawa da komai na bahar din musamman kasancewanta mace akwai abubuwan buqatarta da amfani da dole sai masu kyau da tsari da banbance ta da sauran matan daba jinin sarauta ba data tanadar mata suna jere birjik toilet dinta da gaban mirror dinta a tsare.

Sosai shuraim yake shigewa Bahar wadda sam bata saba muamala da mutane sosai ba dan haka bata wani sake masa duk da a cikin salo da nutsuwa da kauna tareda saka alaqar zumunci me karfin da suke dashi ya ringa janta a jikinsa duk da yasan akwai auren NUAB a kanta amma a yanda a yanzu Ammi ta tabbatarda aurenta da NUAB idan tanada raayi ne zaaci gaba idan batada shi sam babu zaa raba sbd bata damar rayuwa da zaban duk wanda takeso dan haka kafin ta fara karatu koma karatun yayi nisa ayi wannan zaman tambayar yana buqatar shaquwa da kauna a tsakaninsu dan kuwa a shirye yake da aurenta daga lokacin da auren NUAB ya sauka akanta daman kuma yanada tabbacin ba iddarsa akanta dan kuwa zai kafe ya tsare ya tabbatarda iddar NUAB bazata taba hawa kanta ba,

Leylah ma data samu wannan bayanin batai wani farin ciki ba duk da tafara karantar halinda shuraim yake ciki amma batajin zata iya barin shuraim ya mallaki bahar din dan kuwa shima zai cutu idan ya aureta ya wuce wannan ajin dan haka bazata bari yana rabin jikinta ba ya kwashi sauran wani duk da tana shakkar idan ma NUAB din ya amsa auren bare cikesa da kusantar Bahar da batada dogon banbanci da bayin masarautar a gurinta.

******A daren da washe gari Bahar zasu tafi a daren NUAB ya isa bangaren Ammin da kansa dan isar mata da sakon tafiyar da zaayi din hadda ita,

Tinda fadawansa suka fara isowa kofar bangaren tareda securities suka jeru a natse suna bawa bangaren kariya take bayin bangaren suka fito gabaki dayansu suna rabewa gefe sosai inda bama zai gansu ba dan sai bayi ma masu mahimmanci suke iya ganin Sultan me mulki a masaurautar duk da bayin bangaren Ammin kaf suna yawan ganinsa su kam sbd girman darajar Amminsa da kusan tafi ta kowace macen cikin boyem a yanzu kafin sultan din yayi auren da duniya zatasan matarsa a matsayin matar Sultan LEUL NUAB duniya da yan media su shedar da hakan.
#MAMUH
09033181070
[12/01, 10:50 am] Asia ahmd: HAYATEEM
Mamuhgee
Chapter 34 · 0% Book details