← Book details Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 112

Sashe 71

Hayateem Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Leylah ma dake bangaren mahaifiyarta tinda ta dawo shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya da jin farin cikin dawowan Ammin sbd komawa bangarenta zai rage mata damuwan datake ciki sbd irin yanda su maa sakinah da Ammin ke nuna mata kulawa da kauna duk da tanajin wani irin nauyi a kirji na ganin Bahar da zatai amma kuma zata fuskanci hakan ta hadiye kowace irin radadi da nauyin da zataji harta saba ya dallashe ta dena jinsa sbd bazata illata rayuwarta akan abinda bazata taba samuba koda tanada rabon samun a gaba to gwara yaxo mata a bazata amma a yanzu tana buqatan healing duk da batajin zata samu hakan a kusa sbd damuwa data aureta harma ta zamar mata ciwon daya kasa warkewa tinda ta dawo,

Damuwa ce tai mata yawan da batada kowace irin walwal koyaushe tana kwance a daki cikin rashin karfi da zazzabi,

Abinda yake sake shigar da zuhrah damuwa da tinani kala kala akan auren leylah din shine babu ranar da Asim din baya zuwa bangaren ganinta,

Zai shigo ya gaida mum din su gaisa a girmamawa da mutuntawa tukuna ya shiga dakin Leylah din kai tsaye acan yake zuwa su gaisa ya dubata hakama yayi yai akan kiran likita ya dubata taqi yadda sbd batason mum dinta taji tana cikin damuwa me yawa ne tafara tambayarta abinda yake faruwa tinda ta tsaya akan batada lafiya ne yasa ta dawo bangaren.

Da farko mum din ta dauka laulayi takeyi sai kuma taga kaman Asim din a cikin damuwa sosai shima saita dauke tinaninta daga kan laulayin ta shiga damuwan itama ga shuraim yana kwana biyu bai shigoba batasan sakasa wata damuwan akan wadda take ganin kaman yana ciki shima ta ayyukan sarauta shima dan haka sai bata fada masa ba tayi shiru ta nema yar uwarta Ayanah ta fada mata.

Sai yamma lis kusan kowa ya samu fitowa daga dakinsa lokacin kowa yaci ya koshi ya samu hutu iya hutu,

Su Maa ne ke palo zaune cikin hutawa maa tenya tana waya tana fadawa yarta akan ziyarar da zata kawo a boyem itama,

Ayanah ce ta fito cikin shigar doguwan rigar bahrain me kyau da tsada mara ado sosai ta qaraso ta zauna tana ajiye wayarta gefenta su salmah suka fara shigowa suna jere fresh kayan marmari da sukai sanyi a tsare.

Suna gamawa suka bar gurin daidai nan zuhrah ta shigo bayinta biyu na bayanta suka tsaya daga kofar palon farko suna komawa gurin bayin bangaren dan zaunawa acan su jirata.

Itama leylah da bayinta biyu suke biye da ita dakatawar sukai suna bin bayan bayin Mum dinta.

Suna shigowa palon Ayanah ta zubawa yar uwarta idanuwa cikeda kauna me tsanani tana jinta har cikik jininta ta miqe suka rungume juna Zuhrah ta kama hannunta tayi kissing cikeda kauna kafin itama ayanah din tai kissin tsakiyar kanta tana ambatar sunanta.

Cikeda kauna itama Sakinah dasuke jinta a zuciyarsu ta maye gurbin nurat da babu a cikinsu zuhrah ta rungumeta tana kissin tsakiyar kanta sunawa juna barka da haduwa cikin aminci.

Akan leylah Ammi ta maida idanuwanta tana kalla cikesa mamakin ramar datake gani tattare da ita da wani irin haske data qara fayau ta ware mata hannu ahankali tana cewa

'Zo Yene leylah'

Tahowa leylan tayi a natse tana jin hawaye na ciko idanuwanta sbd jin kaunar da Ammi kewa mum dinta da ita.

Rungumeta Ammi tayi a jikinta sosai da kyau cikeda kauna da kulawa tana cewa

'Insha Allah koma menene damuwan zai zama alkhairi kinji Leylah'

Gyada kai leylah tayi a natse suna zaunawa gabaki dayansu a kujera tana gaida su maa sakinah cikin girmamawa suka amsa Sakinah na mata kallan kulawa da damuwan ramar datake gani a tattare da ita
Maa tenya kuwa yanayin fatar Leylah din take kalla tana shiga nazarin sauyawanta.

Zuhrah ce ta bude baki zata tambayi Bahar sai ga bahar din ta fito a natse cikin riga da wandon Flairs Purple masu fadi sosai da sukai mata kyau sosai sbd sun qara fidda haskenta sosai da sauyawan datai itama na sauyin rayuwan data samu.

Zuba mata ido Zuhrah tayi tana kallanta da dukkanin kaunar datake wa Abaas da jinin duk wani ghaz da suka rasa tana jin inama itama zata iya dawo da baya da itace zata nemo bahar ta bata dukkanin kauna da soyayyar uwa da uba data rasa.

Hannu daya ta miqawa bahar din tana ambatarta da sunayen da suke ambatar abaas dasu da yana yaro na kaunar da batada sirki.

Qarasowa bahar din takeyi itama Ammi ita ta dago tana kalla tata kaunar da soyayyar ta daban ce kaf duniya akan bahar dan haka ko data iso itama saida ta kalli Ammin cikeda kauna da kewa na fushin datake yi da ita kwana biyun kafin ta kama hannun Mum zuhrah tana zaunawa gefenta a jikinta tana bude baki ta gaidata.

Amsawa zuhrah tayi tana tambayarta karatu da uk.
Amsawa tayi tana maida kallanta akan Leylah ta ambaci sunanta a natse tana gaidata.

Amsawa leylah tayi tana mata ya hanya a natsen itama tanajin ma bataji nauyin kirji da zafin datai tsammanin ji dinba dan haka ta dan sake jikinta a cikinsu tana tinanin halinda Asim yake ciki a yanzu data tabbatarda yaji isowan Bahar din a cikin masarautar.

Firar ahalin dake kaunar juna da babu matsaloli suka ringa yi hankali kwance suna ciye ciyensu wanda ya saka Ammin aje damuwarta a gefe tana jin dadin kasancewa a tareda ahalin da suka rage mata a duniya,

Ita kanta leylah jin tayi damuwarta ta rabe gefe tana samun nutsuwa da walwala dan haka basu tashi daga zaman ba saida akai magrib suka tashi sallah,

Dakin Bahar taje tayi sallah cikin karfin hali sbd tanason cusawa kanta salama,
Ita kanta Bahar bata damu ba daman ba itace me matsalarba dan haka dan sake mata tayi har sukai dan firar zuwan nasu uk da dawowansu kafin suka fito cin abinci wanda sukaci dukkaninsu da iyayensu.

Sai bayan ishai Zuhrah tabar bangaren ta koma tabar leylah anan wadda tace anan zata kwana.

Dakin Bahar din still tayi zamanta wanka tayi ta fito ta zauna tafara shirin bacci sbd yanzu da wuri take bacci,

Sabbin layan bacci ta dauka a cikin closet din Bahar ta saka masu kauri riga da wando da sukai mata kyau sosai sbd bata saba saka kayan bacci riga da wando ba tafison riga kawai wadda zata sauka kokuma qarama ta bacci.

Tana kokarin miqewa daga gaban mirror kiran Asim ya shigo wayarta sbd yaje can bangaren kaman yanda ya saba bai sameta ba.

Ajiyan zuciya ta sauke tana komawa zaune a hankali ta dauki wayar ga mamakinta cikin nutsuwa yace mata yana bangaren Ammin yazo ganinta.

Bata taba dauka zai iya tahowa bangaren ba kodan mahaifiyarsa da kuma bahar dan haka miqewa tayi a sanyaye sbd tasan dole zuciyarsa na cikin wani irin mawuyacin hali na zuwansa nan din.

Bata iya saka komaiba akan kayan jikinta ba sbd damuwa hakanan ta fice daga dakin hula ce kadai a kanta wadda itama gashinta dayake sake bata rufesa ba.
Palo ta fito daidai lokacinda Maa sakinah data gansa a waje tsaye tai masa iso har cikin palon cikin kulawa da kauna sbd a yanzu shi nasu ne.

Zaunawa yayi a natse yana kasa dagowa ta wuce taje ta sanarwa Ammi Asim yace yanason gaidata.

Leylah kuwa qarasowa tayi tana kallansa tareda kasa dauke idanuwanta akansa zuciyarta na wani irin harbawa ahankali da sanyi sbd tausayinsa shima dagowa yayi ya kafeta da idanuwansa masu kyau da sukai sanyi yana kallanta tareda jin confidence da karfin zuciyar iya fuskantar komai.

Fitowan Ammi ta dakatar da ita daga isa garesa sbd tasan ba qaramar quna yake ciki ba akanta ya daure ya danne ya shigo dan haka dauke idanuwanta tayi daga kansa tana saukewa qasa.

Qarasowa Ammi tayi cikin kalama da kulawa tana ambatar sunansa da sakewan data sakasa dago idanuwa ya kalleta yana jin kwarjininta har cikin idonsa dan haka ya dan sauke ido yana gaidata da mata sannu da zuwa cikin girmamawan dataji dadi tai masa sannu da kokari da kuma basa hakurin sunje bata nan.

Sama sama sbd rashin sabo duka danyi magana kafin ta miqe tabar palon.

Tana barin palon leylah zubawa hannuwansa dake rawa ahankali ido tayi yana boyewa kada kowa ya lura take idanuwanta suka sake cikowa da hawaye ta tako ta iso gabansa bata iya cewa komaiba ta kama hannunsa a hankali ta miqar dashi tajasa suka bar palon suna ficewa daga bangaren.

Hanyar bangarensa take kokarin nufa dashi ya dakatawa a hankali kafin ya cire jacket din dake saman kayansa ya saka mata sbd batada rufa a jikinta duk da dare ne.

Yana saka mata ya dauketa cak daga qasa sbd hadda takarmi ta manta bata sakoba ya nufi bangaren nasa da ita yana jin gashin jikinsa na miqewa da irin lafewan datai a jikinsa tareda saka hannuwanta biyu ta zagayesa dasu sbd irin daukan da yayi mata.

Suna barin bangaren karfe tara da rabi ta buga a lokacin Ammi ita kuma ta fito dan tafiya magana da sultan wanda ta dakatar daga zuwan dayaso yi bangarenta wanda tasan tsaf zai iya haduwa da NUAB a bangaren dan shima yanada wuya ya kwana bai taho gaidataba amma ganin har 9 ta wuce baizo ba ya sakata ficewa xuwa bangaren sultan din bada niyar karban kwana ba sam.

Tana ficewa tara da talatin da hudu manyan securities dinsa biyu da duk inda ya saka kafa a cikin masarautar suna bakin gurin suka iso kofar bangaren nata suka tsaya 9:40 a natse sukuma tukuna sai gasa ya sako kai a cikin wata lafiyayya sanyayyar nutsu da izzar ikon mulki da kamewa tareda kwarjininsa me karfin gaske yana sanye da fararen Armanis da sukai masa kyau tareda fidda kyau da samartakansa.

Aleey ne a gefensa suka iso suka shigo wanda take bayin ciki suka fice daga bangaren a natse suka bar gurin gavaki daya har saiya bar hanyar gurin ma kwata kwata.

Su Maa sun shige dukansu dan haka kai tsaye palon Ammin ya nufa bai ganta ba ya fidda wayarsa ya saka kiran Maa sakinah wadda ta fito a natse suka gaisa ta sanar dashi Ammin bata nan taje gurin sultan.
Chapter 71 · 0% Book details