Sashe 92
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
"In sha Allahu." Ta ce cikin sanyi.
"Umma, happy birthday!" Suka haɗa baki gurin faɗin haka har da Damir suna tafi. Mamaki sosai ta yi gain haske da walƙiya yana tashi.
Kallon Ahmad da Marwana ta yi da yaransu. Ashe suna bayanta ba ta sani ba. Babu shiri ta saki dariya, saboda ta manta cewar yau ne birthday ɗin ta.
"Muna miki murnar ƙarin shekara. " Ahmad da marwana suka ce, sannan suka miƙa mata gift ɗin su.
Karɓa ta yi, cikin farinciki tana murmushi. Damir ya mika mata makullin mota ya ce,"Happy birthday my wife." Karɓa ta yi tare da rungume shi.
Yaran suka rinƙa miƙa mata na su gift ɗin. Duk damuwar da take ciki dai ta ji babu. Dariya sosai take yi, ganin yada suke son sanyata a farinciki. Kallon ƙananan yaran ta rinƙa yi, da suke ta wasa da ball suna guje-guje.
Da aka zo yanka cek Nasreen ta yanka, ana kallonta suna tafi kowa ya buɗe bakinsa. Rasa wanda za ta sakawa ta yi, duba mahimmanci da suka yi a rayuwarta. Da ta yanko sai ta bi Ya Ahmad Marwana sai kuma ta sakawa Damir.Ihu suka ɗauka suna tafi shi kuma ya rungume ta.Yaran ma suka haɗata da shi suka rungume. Marwana da Ahmad suka rungumu su. Ƙarshe!
Alhamdulillah
Na sadaukar da littafi WASU MAZAN, ga duk wata mace da take sha wahala a gidan aurenta. Idan mai shiryuwa ne Allah ya sa ya shiryu kamar Faruk. In kuma ba mai shiryuwa bane Ubangiji ya ba ta miji kamar Damir.
Godiya
Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji, da ya ba ni baiwa da fikra da na rubuta labarin WASU MAZAN domin haƙiƙa ya ciri tuta. Ba zan iya cewa komai ba a kan littafin WASU MAZAN, saboda gaskiya Alhamdulillah. Ina godiya ga masoyana masu kirana da kuma waɗanda suka rinƙa biyu ni pc suna faɗin basirar da na saki a littafin. Masu comments, Allah ya saka da alkahiri kuma ina rokon za a yi mini zafafan comments, a sabon littafina, kamar yadda kuma yi a WASU MAZAN domin comments ɗinki yana sanya ni nishaɗi. Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna ƘIYYAYAR JINI. Kun dai san alkalamin mutuniyar taku ba ya shirme.