← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 92

Sashe 15

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da aka ce mata ana sallama da ita ta yi mamaki ƙwarai. Tun da ta fahimci shi ne ta ƙi fitowa. Babu yada Mama ba ta yi da ita ba, amma ta ƙi wanda daga ƙarshe sai ta sanya mata kuka. Ganin haka ta haƙura ta kyale ta.

Faruk da damuwa suka yi masa yawa ganin yadda ta shanya shi. A ransa ya ji sam ba za ta fito ba. Don haka ya juya zai shiga motarsa. Yana mamakin yadda ya tsaya gidan talakawa tana wulaƙantashi.

"Ɗan saurayi." Ya ji muryar Baba yana kiransa.

Waigawa ya yi tare da fasa shiga cikin motar.

"Na ɗauka ba za ka dawo ba?"

"Ni ma ban so na dawo ba." Ya ba shi amsa yana masa wani irin kallo.

"Takura maka aka yi ko jawo ka?"

"Zan iya cewa haka domin bani da zaɓi face na bi umurnin zuciyata."

"Soyayya ruwan zuma soyayya ruwan maɗaci.." Ya fara waka yana dariya.

"To yanzu da me ka zo?"

"Na kira ta ba ta fito ba."

"Nasreen ɗin?" Ya tambaye shi jin abin da ya ce.

"Eh, ita ɗin fa. Ta aiko mini cewar na yi haƙuri kar na ƙara zuwa ƙofar gidan nan."

"Inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan! Ita da za ta yi godiya Allah ya kashe ya bata. Ai daga ganin ka ba ka yi gadon tsiya ba. A maimakon ta yi wa kanta murna, na wannan tagomashi da Allah ya yi mata sai ta tsaya iya shege?"

Ya yi masa tambayar wanda bai ce komai ba, sai karkaɗa makullin motarsa yake yi.

"Jira ni ina zuwa." Ya ce tare da wucewa duk cikin gidan kamar guguwa.

"Nasreen, ina kike? Mara mutunci kawai!" Ya furta cikin tsananin fushi.

Da sauri ta miƙe jin hargaginsa tana zare ido." Ato, ba kya jin magana yanzu sai ki tashi ai." Cewar Mama tana gyara allayahu.

"Fito da mayafinki na ce mata hankali kawai! Saboda kamar wancan zankaɗeɗen yaron za ki wulaƙanta?"

Shiru ta yi sai hawaye daidai lokacin da Ahmad ya shigo gidan.

"Ahmad, da ma kai kake hure mata kunne ko? To walllahi bari na yi mata gargadi da kakkausar murya. In har kuka fake da karatu ba ta auri yaron nan ba, to karatun sai dai ta yi a wani gidan uban. In banda rashin godiyar Allah. Duk cikin yaran gidan nan wa ya gama sakandire. Kece kawai kika fita zakka, amma saboda ɗiban albarka za ki ce sai kin ƙare jami'a. To ko fara ta da kika yi babu yadda zan yi ne." Ya ce ciki kumar baki.

Ganin ta sanya kuka ya fara neman icce yana faɗin,"Bari na sheme ki sai ki yi kukan mai dalili, saboda yanzu na daɗi kike yi."

Da sauri ta ruga don ta san zai iya."Ka ga mini ja'irar banza!"

Fita ta yi tana hawaye ta je gabansa ta tsaya tana ba tare da ta ce komai ba.

"Ga ta nan in ta yi maka rashin kunya, ka gaya mini ka ga yadda zan yi da ita." Ya furta tare da shiga gidan.

Jin abin da ya ce ya sanya ta bude baki da ƙyar ta ce,"Ina wuni." Sai hawaye shar.

"Don Allah, ki daina kuka. San ban shigo rayuwar ki da nufin cutarwa ba. Sonki na ke da aure, kuma na yi miki alƙawarin in har za ki aure ni hatta kayan ɗauki zan yi miki."

Ba ta ce komai ba sai kuka. Duk maganar da ya yi mata, ta ƙi cewa komai.

Ganin haka ya ce,"Je ki gida."

Kafin ya gama faɗin haka ta juya da sauri ta shige tana kuka.

Raka ta da idanu ya yi, har ta shige. Sani irin ƙaunarta ke fisgarsa.

"Ina fatan ba ta yi maka rashin kunya ba?"

Da sauri ya juyo yana kallonsa da yake faɗin haka."Ba ta yi ba. Don Allah ga waya ka ba ta ina son jin muryarta."

"Madallah sannu da ƙoƙari, amma mai zai hana na riƙe wayar in ka kira sai na bata?"

"Na fi son duk na kira na ji a hannunta." Ya faɗa cikin zallar mamaki.

"To za a siya mini kenan ko ƙaramar din ni ma bani da ita. Tun da ta faɗa masai ban siya ba."

Kallon mamaki ya yi masa, sai ya fara ƙoƙarin shiga mota, ba tare da ya ce komai ba.

"Kai ba ka san ana ba da kuɗi ba in aka je zance?"

Tambayar ta yi matuƙar ba shi mamaki. Faruk akwai maƙo da son kuɗi. Lura da ya yi matuƙar bai saki kuɗi ba, ba zai ba shi yarinyar ba. Ya sanya shi zaro naira dubu biyar ya miƙa masa.

"Ga shi ka bata."Sannan ya ciro dubu biyu. "Wannan ka yi cefane."

Kallon kudin a raine ya yi domin shi ba haka ya so ba. A tunaninsa ruwan yan dubu-dubi zai yi masa.

"Wannan za a je da shi kuwa? Da babu gara ba daɗi." Ya ce a ransa sannan ta kalli kuɗin.

"An rufa asiri da shi. Ko shinkafa da mai da yaji a yi." Ya faɗi haka yana tuna in zai ƙara masa.

Nuna ya yi kamar bai ji ba sannan ya shige motarsa.

"Ɗan banza, daga ganinsa rowa zai yi." Ya ce tare da tura duka kuɗin aljihunsa.

Yana shiga cikin gidan ya faɗa ɗakin Mama."Ki jawa 'yarki kunne ta aminta da auran nan, domin matuƙar ta ƙi, wallahi ba za ku sha da daɗi a hannuna ba." Ya wuce yana bambami.

"Kina jin abin da ya ce?"

"Wallahi ni bana sonsa." Ta furta tare da fashewa da kuka.

Ahmad shiru ya yi cikin tausayinta, domin tun da ya ce sai anyi, matuƙar ba da wasa ya zo ba babu abin da zai hana. Abin da ya kamata ya yi shi ne ya rarrashe ta don ta amince.

"Kina ji ko kamar auren na sa zai fi? Tun da yana da kamala."

"Kai ma biyewa Baba za ka yi? Karka manta ko binciken halinsa ba a yi ba."

"Haka ne, ai dama sai na bincika na gane shi wane ne, saboda kin san ba zan yarda ayi miki zaɓen tumin dare ba."

"Ko dai ka gaji da biya mini kuɗin makaranta ne?"

Tambayar ta ba shi mamaki har ransa ya ɓaci."Matuƙar ina raye zan gaji da ɗawainiyarki ne?" Ya yi mata tambaya a maimakon amsa.

"To bana son shi, saboda ya ci ka gadara kamar ba zai yi haƙuri ba. Kuma Yaya, ina 'yar talaka wacce mahaifin ta ya zubar mata da mutunci. Kana ganin inya aure ni zai ganni da mutunci? Masu kuɗin nan sam ba sa girmama mace."

"In har yana sonki zai yi mana. Zan fara binciken halinsa."

Shiru kawai ta yi don ko hirar ba ta so.

Faruk kullum sai ya zo zance. Ganin yadda Baba ke son abin duniya, ya sanya shi ƙoƙarin rage mako sa yana kawo abu gidan. A ranar da ya fito masa buhun shinkafa. Sujjada ce kawai bai yi masa ba, amma har da kuka ya yi a gabansa.

"Da ma rabon da mu ci shinkafa, tun ranar da ka yi mana kyautar nan. Sai ga shi yau za mu ci 'yar gwamnati."

Kallonsa yake cikin mamakin baƙin talaucin da suke fama da shi. Yana mamakin girman kanta da kauda ido ga abin wani. Duba ga yadda mahaifinta yake kamar zai yi ƙwace.

Baba maganar aure yake yi ba tare da ya yi bincike ba. Ahmad ne ya je ya fara binciken, inda aka sanar da shi ba shi da matsala, domin yana da abin hannunsa da tanƙamemen gida ya gina. Mahaifiyarsa tana Saudiya tun lokacin da yake yaro ta tafi, bayan ta yaye shi. Da auren mahaifin su, saboda matsanancin talaucin da suke fama da shi. Wata 'yar'uwarta ta yi mata hanyar zuwa takaru. Tun da ta tafi ba ta dawo ba, amma tana tura musu da kuɗi. Da haka suka samu suka fita daga talaucin da suke ciki, har suka samu su ka yi karatu.

Su biyar bakwai mahaifiyarsa ta haifa. Uku mata biyu maza. Matan duk sun yi aure sai Faruk da shine babba a namiji. Da kuma ƙanninsa da yake jami'a yana karanta agriculture.

Yayinda mata masu hannu da shuni suka aura. Tun suna sanya ran mahaifiyarsa za ta dawo, amma har mahaifinsu ya mutu ba ta dawo ba. Sai da aka yi rasuwar ta zo ta yi wata biyu. Wata biyu na cika ta tattara inata-inata ta koma.

Matsalar da ɗaya zafin rai da rashin haƙuri, saboda wannan sam ba shi da tanƙamemen aboki, domin da sun fara za su ɓata, sannan ba shi da kyauta sosai.

Ahmad ya sanar da Baba binkicen da ya yi. Dariya ya yi tare da kallonsa ya ce,"Ni ban damu na yi bincike ba, tun da ba za ta rasa ci da sha a gidansa ai shikenan. Mata nawa suke zama da maza su babu ci ba sha?"

"Bincike a aure yana da kyau baba. Na tabbata da ace kai za ka je sai an gaya maka abin da ba a gaya mini ba. Rashin bincike da ba'a yi, ya sanya yawan mace-mqcen aure a tsakanin Hausa Fulani."

"To ubana gaya mini gaskiya, kuma tun da ka yi karabbanin yi ai shikenan."

Har ofis ya samu Faruk. Bayan an yi masa izinin shigowa. Ya buɗe ƙofar ya shiga da sallama.

Ganinsa Faruk ya amsa sallamar fuskarsa babu yabo babu fallasa, don sam jininsa bai haɗu da na Ahmad ba, musamman yadda yake cin magani da girman kai shi ba ɗan kowa ba.

"Na zo kan maganar auren ka da ƙanwata Nasreen."

"Ok," Ya ce masa tare da cigaba da aikinsa.

"Game da karatun ta ne." Ya daure ya ce masa yana kallon yadda yake cin magani.

Shi kansa da yana da halin a za ayi auren nan ba, musamman da ba ta so. Ya san cewa ko sun amince ko ba su amince ba, tun da ya sa ya ran dole ayi, to babu makawa. Don haka ya yanke shawarar ya aminta kawai.

"Nasreen, na son makaranta.."

Cewa na yi ba zan biya ba? Ai ban yi maka kama da jahili wanda bai yi boko ba. Don haka ba zan so matata ta kasance jahila ba."
Chapter 15 · 0% Book details