← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 92

Sashe 48

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ingawa ya daure yana kallon sa ganin yadda ransa ya bace, kamar ya ga su suna aikata masha'a sai ya ce,"Wallahi ban canza daga yadda ka sanni ba, son ta nake yi kuma aurenta zan yi. Na samu labarin ƙawar ƙanwarka ce in har zaka shige mini gaba, a shirye na ke na aur.."

Wani irin kallo ya watsa masa kallon daba shi ba, hatta Nasreen sai da ta yi mamakin kallon.

Ta rintse idanunta cikin tashin hankali, ganin yana matsawa kusa da shi. "ka je gidan iyayenta ɗan ƙaruna ka aureta, amma ni na wuce ƙarfin na yi maka gaba ka aureta, kuma daga yau na ƙara ganin ku a tare, wallahi saina sallame ku." Ya furta cikin ɓacin rai yana huci.

Har ya fara taku sai kuma ya dawo ya kalli Nasreen da ji take kamar ta yi ihu, ganin yadda ransa ya ɓaci. Buɗe baki ya yi zai yi magana, sai kuma ya murza mata yatsunsa guda biyu, ya wuce da sauri yabar su da shaƙan daddaɗan turarensa .

Har ya ɓace daga gurin sun kasa magana. Zoben dake hannunsa ya kalla, sai kuma ya ɗago ya watsa mata kallo. Kallon data kasa gane wane iri ne. Ganin haka ta fara tafiya za ta bar gurin."Nasreen," Ya kirata tare da fara taku zai bita.

Da sauri ta bar gurin zuwa ofishinta hawaye sosai take yi. Ta rasa wane irin zuciya gare shi har yau ya kasa yafe mata. Yake tijarata a gaban kowa.

Ingawa tsaya ya yi har ta shige. Hankalinsa ya tashi sosai ganin abin daya faru. Idanun Damir yake hangowa lokacin da yake magana. Gabansa ne ya fadi da ya yi tunanin wani abu. Ya daɗe a gurin yana tunani cikin rashin mafita, sannan ya ja jiki ya haye sama zuwa ofishinsa. Ko da ya shiga kasa aiki ya yi, yayin da zuciyarsa ke ta auna masa, fushin da ya bayyana a fuskar Damir yana tunanin wani abu.

"Tabbas akwai alaƙar da ta haɗa su." Ya ce tare da cige biro a bakinsa.

"Amma why ta ki gaya mini duk da yarda muka shaƙu da juna?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa.

Damir kuwa da ya shiga ofis cikin fushi ya buga ƙofa. Kansa ya buga da gini tare da kaiwa bango naushi.

"Mai yasa na ke damuwa da ita baya abin da ta yi mini?" Ya yi wa kansa tambayar yana dage kasa da take barazanar rabuwa gida biyu.

Rintse idanunsa ya yi, yana hangen a yanayin da ya gansu. Tamkar zai yi hauka, domin zuciyarsa wani irin tafasa take yi.

Yana cikin wannan yanayin Bilal abokinsa kuma yana aiki a gurin ya shigo. Ganin halin da yake ciki ya karasa yan kallon sa.

"Lafiya Damir?"

"Na tsaneta bana son ganinta?"

"Wa kenan?" ya yi masa tambayar cikin damuwa.

"Wancan yarinyar da ta kashe mini mata, sannan ta zo har kampany na ta soyayya bayan ta sanya mini tabon dana kasa aure."

Mamakin abin da ya ce ya yi."Damir yaushe za ka manta da abin da ya faru? Bata hana ka aure ba, saboda Mommy ta yi maka aure amma ka saki matar."

"Saboda ta sanya tabon da ba zan iya gogewa na auri wata mace ba."

"Ba ta da lafi in har tana da shi hakuri shi ya fi, domin Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana, kuma ni dan har ya bana ganin laifinta."

"Ai dama ba za ka gani ba, abu daya na sani tun da ta yi gigin kashe auren ta ta kuma shigo kampanin nan ba ta yi aure ba."

Da mamaki ya kalle shi."To mai kake nufi, ko zuwa za kayi ta rinƙa ɓata ta a gurin waɗanda suke sonta? In ma wannan ne gara kar ka wahalar da kanka, saboda in ka hana wani WASU MAZAN zasu zo. Yarinyar tana da kyau da hankali ko ni zan iya nem..."

Wani irin juyowa ya yi yana kallon sa."Get out of my office na raina ajinka."

Yadda ya daka masa tsawar ya sa shi dariya."Har wani aji namiji yake da shi a gurin mace? Damir yadda ka razana ko...."

Kafin ya ƙarashe maganar ya bishi wanda ya sanya shi rugawa da gudu yana fice yana dariya.

"Ni na san mai zai yi."

Wayarsa ya zaro ya tura wa Muhsin tsakon ya haɗa meeting na gaggawa. Kowa mamakin meeting ɗin yake yi. A lokacin da Ingawa da Nasreen suka ji sanarwar meeting ɗin, hankalinsu ya tashi sosai, domin sun ɗauka tozarta su zai yi, musamman Nasreen da ta ji kamar kar ta je.

Haka dai ta daure ta shiga meeting ɗin. Yana zaune a kan kujerar sai huci yake yi. Duk wanda ya shigo ya kalle shi, ba ya fatan ya yi na biyu, saboda yadda ya haɗe fuska kamar an aiko masa da tsaƙon mutuwa.

Nasreen kanta a kasa ta shigo ba ta kallon kowa. Tana shigowa ya saki tsaki cikin jin haushinta.

Da sauri Muhsin ya kalle shi sai kuma kalli ƙofa. Ganin Nasreen jikinsa ya yi sanyi, domin ya fara zargin a kanta zai yi meeting. Kallonta ya yi ganin yadda ta natsu bata kallon kowa, sai tausayinta ya kama shi, saboda ya fara jin haushin tsanar da yake nuna mata.

Ba tare da bata lokaci ba, ya shiga gasa musu magana yana faɗin kalaman da suka gaza fahimtaarsa. Nasreen da Ingawa kawai suka san inda zancen yake.

Nasreen shiru ta yi, har wasu hawaye suke taruwa gefen idanunta. Tun da ya fara magana ba ta daga kanta ba, sai muryarsa da yake faɗin kalamai cikin zafin rai take dukan kunninta.

Ingawa kallonsa yake yi wani abu yake zargi, amma ba ya son ya tabbata domin shi ne zai kwana ciki. Yana ta tsit har ya gaji ya sanar da su dalilin taron

Kalmar da ta ƙarshe ya sanya cece-kucece a ɗakin taron. Suka ɗago da sauri suna kallonsa cikin mamakin abin da ya furta.

Ganin yadda suka razana sai ya miƙe idanunsa a dake ya ce,"Maganar da na fada muku, duk wanda ya saɓa ya sallami kansa. Na hana soyayya a kampanin nan, saboda ban ɗauke ku don ku zo kuna mini ba."

Bilal ya miƙe cikin tsokana zai fara magana."Yallaɓai kana nufin har mu da matanmu suke gurin kar mu yi soyaya?"

Wani banzan kallo ya watsa masa."Eh, in har hakan na nufin waɗanda ba su da aure za su yi. Aiki na ɗauke ku baku zo kuna soyayya ba." Ya faɗi cikin zafi yana huci.

Kallon sa ya yi yana ƙoƙarin ɓoye dariyarsa. Tuni ya harbo jirginsa.

Ganin sun kaure da hayaniya sai ya fice daga ɗakin. Haka suka rinƙa magana kan dokar sannan suka fita.

Nasreen ta yi shiru ta san cewa duk abin da yake faɗi da ita yake yi. Namijin ƙoƙari ta yi don kar hawaye su zubo mata, saboda bata son kowa ya gane da ita yake yi.

Da suka fito ita da Khausar da Nasreen sai Hajar. Kallon su Hajar ta yi ta ce,"Amma fa Yaya wallahi ya sanya doka mai tsanani, saboda bana tunanin zan iya haɗuwa da ya Muhsin na ƙyale shi. Shi ma ya san wannan dokar ba za ta je ko ina ba. Haka kawai don shi baya soyayya, sai ya hana kowa? Tun da matarsa ta mutu ya kasa ɗaukar ƙaddara?"

"Gaskiya lamarin ya yi tsauri ina ta kokarin gina soyayyata, sai dana samu an karɓa ya ce kar a yi soyayya? To wai mai ya faru ya sanya wannan dokar?" Ta yi tambayar cikin damuwa.

"Wallahi ban sani ba, wataƙila ya ga ba a kula da aiki ne." Hajar ta ce.

"Ai kuwa muna ƙoƙari wallahi."

Jin suna ta magana tare da ta tanka musu ba. Sai Hajar ta ce,"Nasreen,"

A hankali ta ɗago idanunta da suka yi ja ta kalle su. "lafiya kin yi kuka ne?"suka haɗa baki gurin tambayarta.

Girgiza musu ka ta yi ba tare da tace komai ba, sai wasu guntun hawayen da take ƙoƙarin mayar da su, suka ganganro kan fuskarta.

Hajar ta kalle ta cikin mamakin hawaye."Ya Damir ya gan ki da wani ne?"

Jin tambayar da ta yi mata da sauri ta girgiza kanta alamun a'a.

"To lafiya mai ya sanya ki kuka?" Khausar ta tambaya tare da share mata hawayen.

"Babu komai." Ta ce ta wuce da sauri.

Idanu suka raka ta da shi har ta ɓule.

Tana shiga ofis ingawa ya kirata. Wayar ta ɗauka ta kanga kunninta. "Ina son mu yi magana please in an tashi zan zo gidanmu."

"Allah ya kaimu." Tace tare da kashe wayar ta yanke shawarar ta gaya masa kar ya yi tunanin wani abu da daban.

Damir a ranar cikin ƙunci ya wuni, da ya rufe idanunsa sai ya hango ta zai saka mata zobe.

Saboda takaici lokacin ta shi bai ba ya kwashi tarkacensa ya fice.

A falo ya samu su Mommy suna zaune. Little Marwana tana bacci kan kujera, yayin da Hajiya ke zaune Marwana tana gyara mata farce.

Ya shigo da sallama fuskarsa babu annuri. Sallamar da ya yi suka amsa."Ya Damir barka da shigowa." Marwana ta furta tare da mayar da hankalinta aikin da take yi.

Bai amsa ba sai ya fara magana cikin fushi "Dama kin sanya na ɗauke ta aiki ne, don tana tara mini maza tana zawarci a kampanina?"

Da sauri suka ɗago jin tambayar da ya yi musu."Lafiya mai kuma ya faru?" Momi ta yi masa tambayar tana kallon sa.

"Momi kamata ya yi, ki raba Marwana da wannan yarinyar, saboda ba tada tarbiyya."

"Ita Nasreen ɗin mai kuma ta yi?" Momi furta tambayar tana kallonsa.

"Da idanuna na ga ta miƙa wa gardi yana sanya mata zobe a hannunta."

Zare idanunsu su ka yi, saboda sun ɗauka sai ce ya ganta tana aikata masha'a, ganin yadda yake tada jijiyan wuya.

Marwana sai ta yi murmushi tana kallon sa. Hajiya kuma ta jinjina kanta, suka haɗa idanu suka yi murmushi.

Ganin sun mayar shi kamar mahakaci dai sai ya kaɗa kansa ya ce,"Na rantse sai na kori yarinyar nan, ko kuma na bar kampanin sai ki je ki kula da shi."
Chapter 48 · 0% Book details