Sashe 36
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ko kaɗan kin san bana damuwa da kuɗi saboda Allah suke yi, kuma Annabi da bazawara ya fara aure, kin ga ba ni da hujjar da zan hana shi aurenta. Ba na son haɗa zuriya da ita sannan abin da kike tunani hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, ko mata sun ƙare Damir ba zai so ta ba, tun da ya kasa don wata 'ya mace bayan Batula."
"Ni kuma jkina yana ba ni zai so ta, na san cewa za ta fuskanci wulaƙancin a girinsa, amma tana da haƙuri kuma in har ya cutar da ita dole ya yi nadama."
"Ki bar wannan maganar hakan ba zai yiwu ba." Ta ce mata tare da fara tafiya tana ganin wautarta na wanann maganar.
"In har ba kina gudun haɗa zuriya da ita saboda tana talaka bane, to Mommy ki amince, domin ita ne kawai za ta iya kawo farinciki a rayuwarsa."
Mommy shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba, tunanin abin da ta ce take yi, yayin da wani ɓangare na zuciyarta yana hango mata gaskiya."Anya Damir zai aminta ya so ta?" Ta yi ma kanta tambayar tana girgiza kanta tare da ƙarashe ficewa.
Da ta fita kai tsaye ɗakinta ta shige ta rufe ƙofar. Tunani take yi sosai gane da ta ce. Har ga Allah sam ba ta son Nasreen, amma kuma tana tausayinta. Tun ranar da Marwana ta gaya mata aurenta ya mutu kuma kuma ɗan uwanta ya ɓace ta fara tausayinta. A ranar da Marwana ta zo tana kuka ta gaya musu dukan da mijinta ya yi mata ta fara tausayinta, amma dai kuma lamarin ya caɓe tun lokacin da Batula ta rasu.
Kwana ta yi tana tunanin maganganun da ta gaya mata. Cikin dare ta tashi ta yi sallah, saboda yadda ta kasa bacci maganar na yi mata kuwwa a kai. Addu'a ta yi bayan ta gama istikhara sannan ta shafa ta koma ta kwanta.
A ƙalla sai da ta yi sati tana neman zaɓin Allah. A yadda ta ƙasa ta ga Damir ya ƙara aure za ta iya aminta da ko wace ce in har za ta kawo farin ciki a rayuwarsa. Ta auna ta ga ya cancanta Nasreen tun da aurenta ta mutu ta ga halin da ta sanya ɗan ta.
Washegari da safe Marwana tana ɗakinta ta fito daga wanka ta shigo. Kauda fuskarta ta yi ta ce,"Ina kwana?"
Ba tare da ta amsa ba ta zauna tana kallonta."Marwana fushi kike da ni ko?"
Ba tare da ta tanka ba ta tura bakinta sai kuma ta ce,"Ina son ki fahimci abin da na ke shirin yi ne."
"Na fahimta kuma na gane mai kike son yi, kuma na amince."
Da sauri ta juyo tana kallonta cikin tsananin mamaki.
Kama hannunta ta yi tana faɗin,"Marwana in har kina ganin Nasreen za ta iya sace zuciyarsa, ya dawo kamar da na aminta kuma zan yi masa dole ya bata aiki."
"Ina kyautata zaton hakan Mommy. Nasreen za ta iya sace zuciyarsa saboda tana da kyau da haƙuri ba ko wane ɗa namiji zai ɗauke idanunsa ba. Haƙurin da ta yi a gidan Faruk shi zai sanya Allah ya ba ta nasarar jefa soyayyarta a zuciyarsa, sannan shi kuma ya ba shi mata na gari kamarta."
"Shikenan, na aminta in har kina tunanin zata dawo masa da farincikinsa."
"In sha Allahu ina kyautata zaton haka."
Miƙewa ta yi tana faɗin,"Zan yi masa magana ya ba ta aiki."
Rungumeta tana hawaye cikin tsananin murna ganin ta shawo kanta. "In sha Alah Nasreen za ta dawo da Ya Damir kamar yadda yake da."
Tana zaune a falo ya shigo cikin falon. Ɗauke kansa ya yi, ba tare da ya kula ta ba. Shi a dole har yanzu fushi yake da ita."Ya Damir, sannu da shigowa." Ta ce masa tana masa dariyar mugunta ƙasa-ƙasa.
Ba tare da ya amsa ba ya ƙara ɗauke kansa. "Da ki ci gaba da fushin ki gani in zan aminta da buƙatarki, saboda ba ni da hankali sai na ɗauki wacce ta yi sanadin da na rasa matata? Tana farinciki ina ciyar da ita."
Ganin bai amsa ba sai ta fashe da dariya tana kallonsa har ya shige ɗaki Hajiya, wanda hakan ya tabbatar mata da kiransa ta yi.
Cikin girmamawa ya zauna yana kallonta."Mommy gani."
"Yauwa zauna magana na ke son mu yi."
Gabansa ya faɗi domin a tunanin da ya ɗauka wani auren ta jajibo masa, don haka ya sha kunu."Maganar da Marwana ta zo mini da shi, na auna na ga tana da gaskiya. Ita ma tana da haƙƙin da zata iya kawo kowa a cikin kampanin, don haka na amince ka ba wa Nasreen.."
"Yanzu Hajiya za ki iya ɗaure mata gindin ta kawo wannan yarinyar kampaninmu ta yi aiki?"
"Haƙƙinta na ke ƙoƙarin a bata. Tun da ta kafe dole sai mu bata, ai tana da gado a ciki."
"To shikenan, yadda kike so haka za a yi. In dan ma duka share ɗin ta zan bata sai na fitar mata da nata ta kula da gurin." Ya faɗa a xafafe cikin ɓacin rai ganin ta biye mata.
"Ba wannan nake nufi ba tun da ta kafe sai a bata."
"Ok, ta bawa Muhsin takaddunta." Ya ce tare da ficewa daga ɗakin.
In ana son na ci gaba da posting safe da yamma sai na ga ruwan comments.
WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_
Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun
8144072423
Jamila lawal opay
Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423
Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 19

Ganin ya fito kamar fusataccen zaki sai ta miƙe za ta gudu. Da sauri ya fincikota ya dawo da ita."Sakayyar da za ki nuna mini na fifita ki da na yi? Na gode tun da kika nuna bare ta fini, baren wacce ta jefa rayuwata cikin damuwa." Ya furta tare sakinta zai fice.
"Ya Dami..."
Wani irin kallo da ya yi mata ya sanya ta yi shiru.
Yana fita da daka tsalle murna domin fusatar da ya yi, kawai zai tabbatar da ya amince bisa dole.
Ɗakin Mommy ta shiga tana faɗin,"Ya amince?"
"Na yi masa dole sai ya ce ta bawa Muhsin takaddunta." Na gode sosai in sha Allahu sai shigowarta ya zama alkhari. Ta ce tare da ficewa cikin ɗakin tana tsallen murna.
Ɗaki ta shiga ta shirya a gauguace ta fice. A hanya sosai take jin daɗin nasarar da ta samu gane da Mommy. Hakan ya ƙara ƙarfafa mata gwiya sosai. Tana yin parking ta fito sannan ta shiga cikin gidan
Raihann na ganinta ta taso da gudu ta rungume ta."Anty Marwana oyoyo." Ta ce tare da ƙara rungumeta
"Oyoyo, ina Ummun ki?"
"Tana islamiya."
"Ok, mu shiga ciki Mama na nan?"
"Eh yanzu ta shiga bayi za ta yi wanka." Kai tsaye ɗakin ta shiga bayan ta tayi sallama.
Ba ta jima da shigowa ba Mama ta fito."Yar halal ta ƙi ambato, kafin ta tafi islamiya ta gama mini hirarki, wai ta yi kewarki."
Dariya sosai ta yi jin abin da ta ce,"Ni ma Mama kewarta ya sanya na zo."
"Allah Sarki ita ma ta na ta maganarki." Ta ce tare da zama gefenta suka gaisa.
Bata jima ba ta shigo sanye da hijabin islamiyarta. Dariya ta yi tare da ƙarasowa kusa da ita."Wai kina nufin niƙabi kike sawa?"
"Eh, kin san maza unguwarmu kan ba ka riƙe mutuncin ka ba, sai su yi ta maka kallon mutuniyar banza."
"Haka ne in kika sanya ba lailai a gane ki ba."
"Wallahi har na je na dawo." Ta ce mata tare da zama kusa da ita.
"Da alkahiri na zo." Ta furta tana kallon ta cikin farin ciki.
"Ai kullum ganinki alkhari ne saboda ko fuskarki na kalla ina jin farinciki."
"Aiki na samar miki ina son ki bani takaddunki?" Ta ce tana kallonta.
Tsananin mamaki ya bayyana a fuskar ta."Aiki?" Ta ce tana kallonta.
"Aiki fa kika ce? Aikin share-share a gidan mutane?"
Takaicin abin da ta ce ya sanya ta kai mata duka."Ubangiji ya tsare ni da ganin ranar da za ki yi wannan aikin ina raye. Aiki a campany na sanar miki aiki mai kyau wanda zai inganta rayuwarki."
"Mama, zo ki ji abin mamaki wai Marwan ta samar mini babban aiki." Ta furta cikin tsananin mamaki tana kallon ta yayin da hawaye ya cika idanunta.
"Aiki fa kika ce?"
"Eh, Mama ni ma yanxu take gaya mini."
"Masha Allah, Alhamdulillah!" Ta furta cikin tsananin farin ciki.
Ganin yadda suka ruɗe sai ta lalle ta ta ce,"Aikin yana buƙatar ki mayar da na hankali dole ki ije islamiya, in har kika natsu rayuwarki za ta canza ciƙin ƙanƙanin lokaci za ki manta ƙunci rayuwar da kika shiga."
"Allah na gode maka. A ina kenan?" Ta yi mata tamabayar cikin farinciki.
Zuciyarta ta buga domin ta san cewa in har ta gaya mata, da wuya ta amince."A wani campany ne na samar miki, wani cousin ɗina ya sanar mini suna buƙatar ma'aikata shi ne na sanya ya samar mini."
"Ni kam Marwana ba ni da abin da zan saka miki, sai dai na karashe rayuwata ina miki addu'a." Ta ce cikin tsananin murna tana hawaye.
"Addu'ar ma ta wadatar ina godiya, sannan ki riƙe aikin kar ki yi wasa da shi."
"Na gode sosai." Ta ce tare da kama hannunsu ta haɗa tana kallonta.
"Tsakaninki da Nasreen sai Allah. Ubangiji ya biya ki, domin na rasa kalmar da zan miki godiya da ita."
"Babu kalmar da zamu iya faɗin mu saka mata, sai dai addu'a." Nasreen ta furta.
"Allah ya baki miji na gari."
"Amin," Ta amsa cikin jin kunya.