← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 92

Sashe 71

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sun fita da oga Damir har da yarinyarsa." Ta daure ta faɗa masa.

Jin abin da tace lokaci guda fuskarsa ta canza. Kallonta ya yi cikin zargi."Nasreen akwai abin da kike ɓoye mini ne?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai.

Kallonsa ta yi ganin yadda ya canza kishi ya rufe masa ido."Babu yarintarsa ce ta..."

"Please Nasreen kar ki rufe ni ta baibai, domin kwananan, na ga Damir yana kusanta kansa dake, domin dawo dake sakatariyarsa wannan ma duk shirin sane da. Duk da cewar abubuwan da suka faru a baya ya cancanta ya aurenki, amma ya yi saken da na shigo cikin rayuwarki, don haka sai dai mu fafafa, ba zan iya barin mishi ke ba, saboda ina sonki."

Jin abin da yace kanta ya buga kallonsa ta yi cikin damuwa sosai, ganin yadda ya canza yana huci. Tana matuƙar ganin mutuncinsa don sam ba ta son su yi rabuwar babu daɗi.

"Don Allah ka fahimce tsakanin.."

"In har kina son na fahimce ki, ki amince na tura iyayena gidanku mu zama abu ɗaya. Na yi miki alƙawarin zan ba ki kulawa, kuma zan kula da yaranki tamkar ni na haife su.

Idanu ta zura masa ta kasa ce masa komai, domin ko ta yi masa bayani ba zai gane ba.

Damir da suka fita, kai tsaye makarantar su little Marwana yaje da su, ya ba da sunansa kan gobe za su zo a yi musu rijista. Take ya biya maƙudan kuɗi domin makarantar mai tsada ce sosai, don tafi ta su. Uniform da textboks aka ba shi. Gobe in suka zo sai ayi musu rigister, tun da har interview an yi musu. Daga makarantar sai suka wuce shagon siyen chakulet ya yi musu siyayyya sosai, sannan ya kaisu gurin wasa yara. Sosai suka yi wasa yana musu bidiyo. Ganin lokaci zai ƙure sai ya sanya su a mota ya kaisu gida.

Mommy tana zaune ta ji little Marwana tana faɗin,"Mommy, Anty Mawarna come and see my friends." Ta faɗa tana jan hannun Raihann.

Shigowa ya yi yana dariya ganin abin da take yi. Mommy jin kiran da sauri ta tashi suka haɗu a falo. Marwana ma da take kwance a ɗakinta tasowa ta yi.

Ganin su Raihann, da sauri ta ƙarasa gurinsu tana mamaki."Raihann ku ne?" Ta ce mata tana kallonsu.

"Yaran Nasreen ne ko?" Mommy ta yi tambayar cikin farinciki.

"Eh su ne Little Marwana ta sanya na fita da su, saboda kuka ta saka wai abokananta ne." Ya yi maganar cikin basarwa ganin yadda suke farinciki.

Wani kallo suka watsa masa suna murmushi. Kallon ya ba shi kunya har ya fara ƙoƙarin hayewa sama.

"Marwana ba su abinci don Allah, zan mayar da su lokacin tashi ya kusa." Ya ce mata tare da haye wa sama. Wanka yayi sannan ya canza kaya, saboda Musaddik ya ɓata masa riga da chocolate.

Yana saukkowa ya ji little Marwana tana faɗin,"Anty Marwana guess what?"

"You know am not good in guessing, just tell me baby." Ta ce tana shafa kanta don ta yi mata wayo.

"No until you guess, Anty try."

"Daddy buy you a new teddy?" Ta yi mata cinkar da tambaya.

"No daddy enrolled my friends in my school."

Tsannanin mamaki ya kamata sosai ita da Mommy.

"Kai Marwana yaushe kika fara ƙarya?" Mommy ta yi mata tambayar cikin mamaki.

"Wallahi da gaske ne ga shi nan yana saukkowa You can ask him." Ta ce tana nuna shi da yatsa.

Damir sai ya ji kamar ya koma sama saboda kunya. Karo na farko da ya ji suruntunta ya yi yawa.

"Wai haka Damir?" Mommy ta tambaya.

Kansa ya shafa, cikin tsannanin kunya yana hararar little Marwana. Daurewa ya yi, domin yana jin lokaci ya yi da zai daina ɓoye-ɓoye ya samu muradinsa.

"Ganin yadda ta tashi hankalinta, sai na yi tunani na canza musu makaranta, sannan kuma na gaya musu iya waɗanda za su rinƙa ɗaukar su."

"Ai ko ka yi abin kirki Allah ya yi albarka."

"Amin." Shi da Marwana suke amsa. Sannan ya fita.

"Mommy Ya Damir da gaske yake yi?" Ta ce cikin zallar murna.

"Ya gama kumbce-kubcen sa, da ya tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi masa ƙafa."

Abincin ta basu sannan suka fito da su tafi. Sosai ya ji kunyar yadda suke ta kallon shi. Miƙewa ya yi ganin har lokacin tashi ya yi.

"Bari na mayar mata da yaran." Ya ce tare da fara tafiya suka bi shi. Sosai suka yi farinciki, musamman Marwana ashe dama ƙaunarta da take yi za su zamo dangi ɗaya, tun da gashi ita da Ya Ahmad kamar za su cinye juna. Damir kuma ya saukko ya fara nuna mata ƙauna

Nasreen tun tana tunanin za su dawo awa ɗaya, har ta cire rai ta fara tunanin yashe za su dawo? Ganin har an yi la'asar lokacin tashi ya yi.

Kowa ya fara fita ban da ita, tun tana jiransu ofis har ta fito ta tsaya harabar kampanin. Ingawa saboda kishi bai ce mata komai ba ya tafi.

Murmushi ta yi kawai tana kallon motarsa.

Kallon agogo ta yi tana mamakin abin da ya sa suka daɗe. Har ta ɗaga wayar za ta kira shi, sai kuma ya ga rashin dacewar haka, kar ya ga ta cika son yara.

Marwana ta so ta kira, amma tuna shaƙiyancin da za ta yi mata, sai ta fasa ta ɗan zauna. Wata zuciya ta ba ta shawarar ta koma gida tun da ya san gidansu. Wataƙila ya ga lokacin tashi ya yi ya mayar da su can.

Cikin motarta ta shiga hankalinta duk yana gurinsu. Sosai take murmushi saboda ta san cewa tana matuƙar son yara.

Ta tayar da motar, har an buɗe mata get sai ta ga motarsa zai shigo. Fasa fita ta yi don ya samu ya shigo da motar.

Cikin natsuwa ya shigo da motar, ta fito daga cikin motarta tana tsaye. Da gudu su Raihann suka fito tare da rungumeta."Oyoyo Mommy mun dawo. Daddyn Marwana ya yi yawo damu har ya kaimu mun ga Anty Marwana, kuma kin san me?" Ta ce mata tana kallonta.

Ba tare data amsa ba, sai ta fara ƙoƙarin zuwa gurinsa da yake shirin rufe ƙofar."Sannu da dawowa yau ka sha rigimarsu?"

A hankali ya ce,"Yauwa," Tare da satan kallonta.

"Yaran suna da natsuwa ba su yi wata rigima ba." Ya ce sai ya buɗe bayan mota ya ɗauko musu siyayarsu.

Kasa amsa yi tana kallonsa."Ya Damir sanya ka suka yi ka kashe kuɗi? Ke Raihan ba na hana ki cewa a siya muku abu ba?" Ta kuma mai da tambayar gurinta tare da zare mata idanu.

"Umma wallahi bamu ce ya siya mana komai ba, ko bindiga da teddy shi ya zaɓar mana. Umma kuma ya sanya mu, makarantar su Marwana kayan makarantar na ciki."

Mamaki sosai ta yi, tana kallonsa da ya haɗe hannunsa yana murmushi."Wai haka Ya Damir?" Ta yi masa tambayar cikin rashin dubara.

"Eh akwai buƙatar a canza musu makaranta. Na kaisu makarantar da Marwana take yi, sannan na gaya musu iya waɗanda za su rinƙa zuwa ɗaukarsu. Gobe za ki je da komai na su na yi musu rijista, sannan za su ba ki id card in har ba a zo da shi ba, to babu wanda ya isa ya ɗauke su."

Hawaye suka wanke mata fuska na farinciki."Na gode Ya Damir dama Ahmad yace zai canza musu, sai kuma ka riga shi. Allah ya saka da alkahiri."

"Stop crying please."Ya ce mata tare da ƙara ɗauko mata uniform ɗinsu da textbooks.

Cikin sanyin jiki ta kai hannu za ta karɓa. Miƙa mata ya yi yana kallon ta. Garin ta karɓi ledar hannunsu ya haɗu. Da sauri ya janye nasa jin shokin ya kama shi. Itama karɓar lefar ta yi, da sauri saboda yadda wani irin maganaɗisu ya taso mata.

"Na gode Allah ya ƙara buɗi." Ba tare da ya amsa ba ya fara tafiya zuwa motarsa. Sosai yaran suka burge shi hannu ya ɗaga musu tare da juyowa da sauri jin suna faɗin,"Daddyn Marwana thanks you bye."Sai ya ji kamar ya aureta yau su zama yaransa.

Murmushi sosai yake musu, har suka shiga cikin mota suka tafi. Kallonsa ta yi tare da murmushi, domin a tsakanin jiya da yau ya wanke duk wani haushinsa da take ji.

Motarsa ya shiga yana shafa kansa."Daddy ina son ka kai ni gida su na kwana."

Zare idanunsa ya yi jin abin da ta ce."Gobe za ku haɗu a makaranta kun zama friends ai."

"Yauwa sai na biyu gidansu."

"No Marwana in za take zata tai da ke." Shiru ta yi ta ba don ta so ba.

A mota tana tuƙa motar tana murmushi sosai ya burge ta, saboda kula da yaran da ya yi.

Da ta isa gida, Ya Ahmad yana falo suka faɗa jikinsa suna murna."Ya Ahmad Daddyn Marwana ya sanya mu a new makaranta ba za a ƙara sace mu ba."

Mamaki da dariyar abin da suka ce ya kama su. Kallonta ya yi lokacin da take ƙoƙarin zama a gefensa.

"Sis wai da gaske?" Ya yi tambayar cikin tsananin mamaki.

"Wallahi Ya Ahmad lamarin ya ba ni mamaki sosai, saboda ba ka ga yadda ya canza ba."

"Dama ribar haƙuri kenan, domin duk tsanar da mutum yake maka da cutarwa, in ka yi haƙuri sai komai ya zama tarihi. In kika duba yau Damir ya saki ya cire tsanarki a cikin ransa, shi kuma Faruk Allah ya saka miki."

"Haka ne Mama wallahi na ga ribar haƙuri."

"Shi ya sa ake son mutum, ya zamo mai haƙuri da kawaici wani lokacin." Ahmad ya ce yana kallonta.

"Allah ya ƙara mana haƙuri."

"Amin,"Suka amsa gabakiɗaya.

Cikin dare Nasreen ta kasa bacci, murmushin da ya yi mata ta kasa mantawa. Idanunta fuskarshi take zana mata. Sosai take mamakin kanta yadda ta kasa manta haɗuwarsu ta yau.

Rungume filo ta yi cikin tsanannin farinciki, ganin mutum da take ji ba ta kyauta masa a rayuwarsa ba ya daina damuwa har ya fara kula ta.

Wayarta ta janyo ta kunna data don ta samu bacci ya ɗauke ta. Har ta hau TikTok sai kuma ta koma Whatsapp ganin tsaƙon Marwana ya shigo.
Chapter 71 · 0% Book details