← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 92

Sashe 28

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sakin ta na yi, saboda a rayuwata ba a yi macen da za ta ce za ta duke ni na ƙyale ta."

"Alhamdulillah! An zo gurin dama na san cewa watarana dole hakan zai faru. Dole watarana za ta kai hannu jikinka ta rama dukan da kake mata."

"Aikuwa ma koya mata hankali saboda ban sake ta ba, sai da na yi mata jina-jina." Ya ce kamar ya aikata abin kirki.

Kallon sa ta yi cikin tsananin takaici."Tur da halin ka Faruk! Tur da halin WASU MAZAN da ba su san darajar mace ba. Wallahi tun da ka yi gigin rabuwa da ita, ka yi asarar mace na kirki. Ina yi maka jaje a rayuwarka. Ina tausayin ranar da za ka zo kana kuka a kan rabuwa da ita da ka yi."

"Haba Yaya Asiya wannan fata kike mini ko so kike haka ya faru da ni?"

"A'a abin da zai faru na ke gaya maka. Ka san wace ce ita? Kasan kyautar da Allah ya yi maka da ya ba ka ita. Nasreen uba ne kawai ba ta dace da shi ba, har Allah ya sa ta shigo rayuwarta, amma wallahi ba sa'ar aurenka bane. Ba ka da kyawawan halayen da ya kamata ka zamo mijinta."

"Ni dai ba wanann ya kawo ni ba ina matar da ta fita. Kece kawai kike ganin qualities ɗin nan a gurinta, amma ni a gurin mace ce mara tarbiya wacce ba ta samu uba wanda ya bata tarbiyar ƙwarai ba."

"Lokaci ne zai nuna mana haka, amma ina maka jaje na rashin matar kirki kamar ta."

Ƙaramin tsaki ya ja ba tare da ya ce komai ba.

"Yara na kawo miki don Allah su zauna a gidanki. Ɗan Iskan mahaifinta ya hana ta riƙe wa."

"Ya yi mini daidai ai gara da ya yi maka haka, sai ka san akwai inda zai iya ƙuntata maka."

"Ni dai ki taimaka mini ki riƙe su."

"Ni? Allah ya kyau, wallahi ba zan riƙe su ba. Ina matar da kake ganin ta kirki ce?"

"Ta ƙi karɓarsu."

"Sai ka yi rainon su tun da ka saki uwarsu, abin da ya sanya ba zan kira Mama ba. Ya kamata ta rabu da kai ta je ta samu mijin da zai daraja ta."

Tsuka ya yi bai ce mata komai ba.Miƙewa ya yi a tutaninsa wasa take yi za ta riƙe su. Ganin ya tashi ta kama hannun yaran ta ce,"Wallahi ka tafi da su ba zan riƙe su ba. Nawa ma ya na ƙare da su?Kana sane da malamar makaranta ce ni." Ta ce masa tare da saka masa kamar kayansu a mota.

Ganin da gaske ta ke yi dai kawai ya fi motarshi ya fice. Ƙuta ta yi tana kallon get ɗin da ya fita."Za ka yi dana sani mara amfani." Ta ce tare da juyawa ta shigo ciki gidan.

Farouk damuwa ta yi masa yawa, ya rasa yadda zai yi da yaran. Da ya koma gida zaunar da su a falo ya yyi ya fice daga gidan. Haka suka ta walangiya har yamma ta yi. Raihann ta kama hannunsa suka shiga cikin kicin.

Kujerar ta ije sannan ta hau sama zata ɗauko abinci."Anty ci." Musaddik ya ce mata yana nuna kula.

"Yanzu zan ɗauko maka." Ta ce tana ƙoƙarin janyo ƙular.

"Ke!" Ta ji muryar Rashida wanda ya sanya ta saki ƙular abinci ya zube a ƙasa.

"Kan uban nan! Kika zubar da abincin bayan kin san maƙoƙon ubanki ba ƙara mana zai yi ba? Ai ko yau din uwarki sai kin kwana da yunwa." Ta ce tare da kai mata mari wacce ta firgice. Kuka ta sanya tana bata haƙuri.

"Yi mini shiru din ubanki in kika ƙara buɗe baki sai na fasa miki shi." Ta ce tare da kai wa bakin duka.

Jin abin da ta ce, ya sa ta yi shiru ko tari ba ta ƙara ba."Ku fita yan banza kawai." Ta ce tare da daka musu tsawa.

Da sauri ta fice saboda tsoro Musaddik a gurin ta barshi. Ganin ta fita tana kuka ya ruga shi ma. Duka ta maka masa a ɗuwawu."Yan banza gayyar jaraba." Ta ce tana huci.

Kuka sosai suke yi, ganin sun dame ta sai ta kai su waje ta rufe ƙofarta ta kunna kallo. Haka suka wuni a rana har sai da ta gaji don kanta ta dawo da su. Abinci wanda ya zube ta kwashe ta ba su, saboda yunwa haka nan suka ci. Ganin dare ya yi ta tura su ɗaki ta sanya su baccin dole.

Farouk kuwa sai ya fita sabgarsu bai damu da ya duba ko sun ci abinci ba. Gabakiɗaya sun dame sun fita hayyacinsu. Makaranta kuwa tun yana kai ta a makare har ya kasa ya daina.

Hankalin Nasreen ya tashi sosai da ta je makaranta gaba da za a tashi. Har cikin aikin ta je, amma sai malamar ta gaya mata rabin da ta zo makaranta.

Hawaye ta share cikin tashin hankali."Na gode." Ta ce cikin muryar kuka tana ƙoƙarin haɗiye kukan da yake son goce mata.

Ji ta yi kamar ta je gidan, amma ta san hakan ba zai yiwu ba. Gidan Maman Muwaddat ta je. Ganin ta hankalin ya ya tashi."Yanzu sai da kika biyo yarannan? Ya kamata ki ɗauke idanunki na wani lokaci."

"Ya kike so na yi? Ina son yarana. Makarantar Nasreen na je, amma malamar su ta gaya mini ta daina zuwa. Na san cewa tun da na bar gidan nan, rayuwarsu tana cikin wani hali. Haƙiƙa Baba sam ba ya yiwa rayuwata adalci da ya raba ni da su." Ta ƙarashe maganar cikin kuka. Sannan ta ɗora da cewa,"Ina ga zan je na ɗauki su, sai na bar masa gidansa. Na je can na yi rayuwata da yarana. Zan tashi na nemi abin da za mu rinka ci."

Hannunta ta kama ta rungumeta ganin yadda take kuka."Ki yi haƙuri Allah yana tare da ke. Ki kauda idanunki a kan yaran nan. Farouk ba zai iya riƙe su ba, yana dawo da su sai ki muna wa Baba in har zai kore su sai dai ki bar masa gidansa."

"To," Ta ce kamar ƙaramar yarinya tare da share hawayenta. Ta jima tana bata baki sannan ta haƙura ba za ta je gidan ba. Ganin yadda hankalinta ya tashi sai ta rako ta har ta bar layin.Tana hanya tana kuka har ta isa gida.

Saboda sauro da yake cizon su cikin dare zazzaɓi ya kama Raihann. Tashi ta yi ta zauna tana faɗin,"Umma, ruwa zan sha sanyi." Ta ce cikin muryar kuka tare da kyarmar sanyi.

Jin ba ta amsa mata ba sai ta tuna inda suke. Zazzabin ya ci ƙarfinta ta kasa magana sai kyarmar sanyi. A haka ta kwana har gari ya waye. Da safe kuwa jikin ta ya gashe kamar wuta. Tana kwance a kan gadon Faruk ya shigo cikin ɗakin ganin ba ta fito ba. Musaddik yake zaune a kan gadon yana kallonta. Alamun fuskarsa ya ci kuka ya ƙoshi.

"Raihan, lafiya?" Ya ce mata tare da janye bargon da ta lulluɓa. Da sauri ya toshe hancinsa jin ɗakin yana wari, Musaddik ya yi fitsari ga shi bayin ba a wankewa.

"Ba ni da lafiya." Ta furta masa cikin muryar kuka hawaye yana zirarowa ta gefen idanunta.

Jikinsa ne ya yi sanyi sosai har ya ji babu daɗi."Anya na kyauta ma yaran nan kuwa?" Ya yi tambayar cikin damuwa. Ƙaunarsu da tausayin su ya cika masa zuciyata.

Ɗauko ta ya yi tare da kwantar da ita a falo. Sai a lokacin ya lura da yadda suka rame sosai. Babu wanka ga kayansu sun yi dadti.

Ɗakinta ya wuce ya samu Rashida wacce take ƙudundune cikin bargo. Duka ya ɗaɗa mata. Cikin sauri ta miƙe za ta ƙunduma ashar. Ganinsa ya sanya ta fasa tana mazurai."Saboda me za ka duke ki ina bacci?"

"Abin da yafi wannan ya kamata na yi miki. Anya kia da tausayi kuwa? Dubi yadda yaran nan suka lalace ina ga ko abinci ba kuma basu?"

"So kake na kashe kaina saboda su? Ni fa ban ce maka rabu da uwarsu ba. Ba zan iya wahala da su ba, sai dai ka kai su gurinta, kuma wallahi duk ranar da ka ƙara sanya hannu ka buge ni sai na rama, saboda ni ba banza bace da zan bari ka rinƙa dukana."

"Ashe ko watarana zan karya ki, don duk ranar da kika kuskura kika duke ni dai na yi miki abin da ya fi wanda na yi wa Nasreen."

"Za dai mu karya juna a tunaninka zan zauna kamar ita ka duke ni? To ko ubana ba zan yarda yanzu ya duke ni ba, ballanatana kai da ka ganni da haƙorana."

"Lailai watarana zan zubar miki da haƙorar."

"Ni kuma duk ranar da ka yi mini haka na rantse maka sai na ƙona gidan nan, saboda ba ka sanni bane shi ya sa kake mini rashin mutuncin da ka ga dama. To ni zan iya ƙunan wake duk a mutu a huta."

Ya buɗe baki zai yi magana sai ya fasa ya saki tsaki ya fita daga ɗakin, ganin ta koma ta kwanta tare da jan bargo ta rufe fuskarta."Jarabbabe matsayaci kawai, wallahi na yi dana sanin aurenka, kuɗin da na saki baki zan ci ban samu ba, sai jarabar tsiya da rashin mutunci, da sannu zan yi maganinka" Ta furta hakan cikin takaici tare da jan tsuka.

Ɗaukar ta ya yi suka je asibiti, a maimakon ya tsaya a binciki lafiyarta, sai kawai ya ce a ba shi magani. Bayan sun dawo shi da kanshi ya yi musu wanka ya ba ta magani.

Kwana biyu ta yi ta ɗan samu sauƙin ganin ta warke ya ci gaba da sabgarshi. A rana na uku yana gurin aiki zazzaɓin ya dawo. Falo ta zo ta kwanta. Tana makyarkyata. Rashida wacce ta fito daga kicin hannunta ɗauke da filet na shinkafa.

Ganin abincin tana ci Musaddik ya ƙura mata ido. Tsawa ta daka mishi tare da yi masa daƙuwa."Ma za ke ɗauke shi ku shiga ciki kar ku sanya na kware mayu kawai." Ta ce tana zare musu idanu.
Chapter 28 · 0% Book details