Sashe 1
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WASU MAZAN*
BOOK 2
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan
08144072423
PAGE 1
Cikin tsananin bacin rai, da nuna ya isa da ita ya ɗaya hannu zai mareta, amma sai ya ga ta riƙe hannun tana kallonsa.
"Ubana bai haifar maka jaka ba Faruk! Tun da na rasa Ya Ahmad Marwana ta fita daga cikin rayuwata. Na riga na zauce da tunanin ɗaukar fansa. In har ka yi kuskuren kai hannunka jikina, wallahi ka ji na rantse sai na aikata abin da ba za ka taɓa tunani ba. Bari na gaya maka Faruk, tuni ka mayar da ni mahaukaciyar ƙarfi da ya ji." Ta numfasa tana kallon shi sannan ta ɗora da cewa." Cusgunawar da kake mini ya sanya na haukace na kuma kurumce. Ban dawo gidanka da ninyar zama ba, saboda ka fita a raina. Zan iya komai don na rabu da kai. Bani da yadda zan yi ne Baba ya dawo da ni. In har kace zaka ci gaba da wulakanta ni. Zan aikata abin da zai sanya ka yi danasani a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada. Zan aikata abin da zai sanya maza masu dukan mata su yi nadama, domin abin da zan yi maka zai sanya ya zama darasi a gare su."
Dariya ya kece da shi, jin abin da ta ce sai ya ƙwace hannunsa yana kallonta. "Na yarda kin haukace. Ko da yake tuntuni nake miki kallon mahaukaciya Nasreen tun ranar da kika fara bijire wa umurnina."
"To shikenan lokaci ya yi da zan tabbatar maka da cikakkiyar haukata. Lokaci ya yi da za k yi dana sanin aurena, duk dana sanin da kake cewa ka yi, wannan karon zai fi muni, domin xan aikata abin da duniya za ta la'ance ni. Ta katse shi tana faɗin haka.
"Kashe ni za ki yi? In kashe ni za ka yi then go ahead. Ke har kin isa ki gaya mini abin da zan tsorata da ke? Ke ɗin banza mara tarbiyya." Ya faɗa yana kallonta.
"Rashin tarbiyar xan nuna maka. So nake ka gane ba ka auri mai tarbiyya ba." Ta ce mishi babu kunya ko tsoro.
Zuciyarta tafasa take yi sam ta tsane shi ko inuwarsa ba ta son gani.
Ƙoƙarin zare bell ɗin sa ya fara."Ok, bari na fara dukanki tun yanzu sai na ga abin da za ki yi."
"Karka tsaya jira Allah ya ba ka sa'a." Ta faɗa fuskarta a dake. Duk da cewar ta a zuciyarta cike take da tsoro, amma dole ta zama mace kamar yadda Marwana take gaya mata, dole ta mike ta ƙwaci yancinta. In har ita ta yi saken da ya fara rainata, ta yi wa kanta alƙawarin ƙwato wannan 'yancin nata.
Faruk kuwa ya shiga ciki tsananin tashin hankali. Mamakin kalaman da ta ke gaya masa ya yi. Duk da cewar ya yi mamaki, amma sai ya daure ba tare da bari ta gane hakan ba. Kunya sosai ya ji yadda ya gaya wa Rashida ba ta isa ta ɗaya idanu ta kalle shi ba, amma sai ga shi yau ita take gaya masa za ta iya ɗaukar fansa ta aikata komai.
Bell ɗin ya ɗaga zai zuga mata, sai ta kai hannu za ta kama. Neman abin da za ta ƙwaci kanta da shi ta fara a falon.
Rashida ta riƙe hannunsa ganin yadda ya ɗaga da ƙarfi zai zuga mata. Mamakinsa take yi, saboda sam Nasreen ba ta yi kama da mai irin halin da ya bayyana mata ba. Bacin kishin sun haɗa miji za ta iya cewa, irin mutanen nanne da ka ga kamalarsu da suffarsu za ka kyautata zaton yan aljanna ne.
Ganin yadda ya rufe idanunsa kamar zai duki gardi, sai abin ya bata mamaki."Kenan watarana ni ma zai duke ni? Ta yi wa kanta tambayar haka, domin tana ji a yadda yake nuna maƙo da iya haɗawa mace magana, sam ba ta tunanin za ta jure halinsa. Ba ta da haƙuri Allah ya gani ba ta cikin matan da za su jure ƙankamo daga mazajensu. Jira take yi Malam ya kammala haɗin da zai yi mata, in har bai yi aiki ba. Alokacin za ta nuna masa ainihin kalarta. A lokacin za a yi yunwa halin kowa ya fito. Tana lura da shi da ya shigo kayan abinci ɗakinsa ya kai. Tun da suka yi auren bai taba yarda ta ga pin numbarsa ko inda yake ije ATM ɗinsa ba. A yadda ta fahimta da son kuɗinsa, ko shi bai yarda da kansa ba. In ya in ya ije ƙuɗi ya ringa dubawa kenan."Kenan ni ma watarana haka zai duke ni?" Ta yi wa kanta tambayar tana girgiza kanta tamkar kaɗangaren kutu. Domin hakan ba zai taba yiwu wa ba.
Hannunsa ta ƙara kamawa tana kallon Nasreen da ko gezau."Please honey ka ƙyaleta, kasan in aka ƙara wa mace kishiya mahaukaciyar take zama." Ta ce tare da kama jikinsa.
"In mahaukaciya ta zama ta san cewa nima mahaukacin kaina ne, saboda ko ubanta bana shakkarsa ballantana ita."
"Ka aitaka duk abin da ka ga dama Faruk mahaifina shi ne abin rainawarka, amma kuma ya gama maka komai saboda ya haifa ya baka."
"An gaya miki alfahari nake da aurenki? Sau nawa ina gaya miki na yi dana sanin aurenki? Kawai ba zan sake ki bane, saboda na san so kike yi na sake ki ki je can ki auri wannan ɗan iskan ne, ni kuma kin ji na rantse da na sake ki ki aure shi, gara na ga ranar mutuwata. Zan zauna dake ba zan sake ki ba, amma kuma rayuwarki sai kin gwammace mutuwa."
"Allah ya ba ka sa a in har rayuwata a hannunka take. In da ace bawa ya isa da rayuwar mutum da tuni ka kashe ni a duniya, amma da yake Ubangiji yake tsarawa bayinsa, har yanzu ina nan ban mutu."
"Nasreen, ina gargaɗinki wallahi kika ce rashin kunya da fitsara za ki yi mini, sam ba za ki ji daɗina ba zan munana rayuwarki. Kar ki biye wa sheɗaniyar ƙawarki, saboda dawowar cikin gidana ya isa ya nuna miki babu abin da za ta iya."
Banzan kallo ta watsa mishi, ta shige cikin ɗakinta tare da buga ƙofar da ƙarfi. Mamaki ya hana shi cewa komai, har na wani lokaci. Mamakin yadda ta canza yake yi, ashe dama ba ta da kunya ta iya rashin kunya haka.
Rashida ta watsa kishi banzan kallo ta koma kan kujerar ta zauna. Za ta iya yarda ya wulaƙanta, amma ba ta son dukan mace. Akwai dukan da mahaifinta ya yi wa mahaifiyarta, da ya zama sanadin da ta daina jin magana da ɗayan kunninta. Ta tsani dukan mace. Ta sha alwashin duk ranar da ya yi gigin taɓata lafiyarta, sai ta yi masa abin da zai gane kalar wacce ya aura.
"Lallai yarinya na san iskancin nan saboda na sake ki ne, kuma wallahi ba zan saki ba. " Ya ce tare da komawa ya zauna gefenta yana huci.
Nasreen kuwa da ta shiga cikin ɗaki matuƙar mamaki ya kamata. Ashe zan iya ta ce. Tana dage zuciyarta da take ta bugawa kamar za ta fito waje. Daurewa kawai ta yi, amma a lokacin da ya ɗaga bulalar ji ta yi kamar ta gudu.
Zama ta yi gefen gadon tana kallon yadda ɗakin ya yi ƙura. Bayan ta cire hijabinta ta shiga bayi. Ganin yadda ya koma sai ta fara kwalemar ɗakin.
Tana aikin tana jin dariyarsu a falo. Dariya suke yi har da shewa. Da gayya yake dariya don ya ƙular da ita. Ai kuwa ta shaƙa, tunawa da ko farkon aurensu bai sakin mata fuska ba. Hakan ya sa ta ji ta ƙara tsanarsa sosai a ranta, ganin bai ba ta daraja da mutunci ba. Tana aikin tana jin suna ta dariyar har suka gaji suka shige cikin ɗaki.
Hira suke yi da Raihan da take ta yi mata surutu, har ta kammala gyaran ɗakin ta wanke bayi. Turaren wuta ta sanya sannan suka yi wanka.
"Umma yunwa na ke ji." Raihan ta faɗa tana shafa cikinta.
"Ok, my angel. Muje ki in na samu abin da zan baku. Na ga Musaddik yaron kirki yana ta hamma. Ko dayake ni ma yunwar nake ji." Ta ce tare da ɗaukar Musaddik da yake kan gado ya miƙo mata hannu.
Ɗaukan shi ta yi tare da cilla shi sama tana masa wasa."Yarana kune farinckina Allah ya raya mini ku." Ta ce tana masa kiss
"Amin Ummana, ina girma na yi makaranta zan siya miki gida da mota, na kai ki makka, amma ban da Abba tun da ba ya sonki." Raihan ta ce fuskarta ɗauke da damuwar abin da yake cikin ranta.
"Allah ya yarda Raihan ya albarkance ku." Amsawa ta yi ta kama hannunta suka shiga kicin.
Lafiyayyen abinci ta ga sun girma. Shika fa da miya sai tsokan nama da basu wuce yanka tara ba. Dubawa ta yi ko ta ga zai ije abinci a store ko ita ma ɓoyewa zai yi. Wayam babu komai sai Lipton da gishiri a buhu. Ba ta san lokacin da ta saki dariyar takaici ba. "Wato Faruk a jininsa maƙo yake?" Ta yi wa kanta tambayar tare da iban abincin a filet ɗin suka fito falo.
Suna zaune ta kunna musu katoon suna kallo. Sun fara cin abinci sai ga shi sun fito.
"Ke! Ubansa ya ba ki ikon shiga kicin ki ibi abinci?" Ta ji muryar Rashida tsaye kanta, da wata 'yan iskan rigar baccin da tun da ta yi mata kallo ɗaya ta ɗauke kanta, saboda komai na jikinta ana gani.
Idanunta ta mayar ga Faruk da yake tsaye kusa da ita."Ba an dafa bane don aci?" Ta ce mata cikin rashin tsoro.
"Da aka dafa sai aka ce ki zo ki ke da 'yan iskan ya'yan..."
"Kul karki sake! Don't ever try it, bana yi wa yarana mummunar zagi, kuma ban zan yarda wata yar isa..."
"Ke Nasreen ki kiyaye ni wallahi." Ya daka mata tsawa yana faɗin haka. Sai kuma ya kalli Rashida da take jijjiga."Allah ya ƙara ɗazu xan duketa, ba hana ni kika yi ba?"