← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 92

Sashe 39

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah ki sanya ba ku ta yi aiki nan, wallahi a zuciyata ba ni da nufin ta yi aikin don a tozartata. Tun ranar da na ji matsalarta nake burin mu kammala karatu, na sanya Yayana ya ba ta aiki, don ta tallafi kanta, sai kuma ƙaddara ta sanya ki komai ya rikice."

Mama shiru ta yi tana kallonta, yadda fuskarta ya tabbatar da abin da take faɗi."Kina ganin babu cutarwa ga ɗan uwanki?"

"In har akwai ba zan yarda ta yi ba, saboda duk yadda na ke son ta da burin ganin farincikinta, ba zan so na ƙuntata wa ɗan'uwana da yake kamar uba a gare ni."

"To shikenan, in sha Allahu za ta yi..."

Jin abin da Mama ta ce sai ta yi saurin kallonta tana faɗin,"Mama..."

"Ki yi aikin kar ki tsorata ki yi fatan alkhairi." Ta katseta tana faɗin haka.

Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Tunanin yadda za su rinƙa haɗuwa take yi, saboda tsoronsa zuciyarta bugawa take yi kamar za ta fito waje.

Ganin ta yi shiru ta zauna tana tunani sai ta zauna a gefen ta."In sha Allahu za ki ga yadda rayuwar ki za ta canza, sannan ki kama mutuncinki kar don kina tunanin sun fi ki arziki mutanen gurin ki ce za ki ɗauki wulaƙanci."

Shiru ta yi har yanzu zuciyarta ba ta gama amincewa da aikin ba.

"Bari na wuce gobe in sha Allahu zan zo na ɗauke ki na kai ki har ciki.".

"Shikenan Allah ya kaimu." Ta furta cikin sanyin murya tare da miƙewa.

Jin abin da ta ce sai ta cika da farinciki.

Da dadddare ta gana shirinta tsaf wanka ne kawai ba ta yi ba, amma har kayan da za ta sanya ta cire. Cikin dare kasa bacci ta yi tana ta juye-juye tunanin yadda za ta yi aiki a kamfanin take yi. Tana kwance har aka kira sallar asuba. Ta miƙe ta ɗora ruwan zafi a gawayi. Wanka ta fara yi wa su Raihann ta kwantar da su. Sai da ta gama shirya kanta, sannan ta tashe su ta gyara su.

Raihann da za ta wuce makaranta, ta saka mata biskit a jakarta bayan ta ba ta ruwan koko ta sha.

Tana gyara fuskarta wayarta ta yi ƙara ganin Marwana ce sai ta ɗaga."Please, ina ƙofar gida, mun yi latti ba zan shigo gaida Mama ba."

"Ok, tana gaishe ki gani nan." Ta ce tare da kashe wayar, ta kama hannun Raihann da za su sauke ta a makarantar su.

"Musaddik, na tafi bye." Ta ce masa tare da shafa kumatunsa da yake hannun Mama. Tuni ya saba da zama a gurin ta in za ta fita.

Hannu ya ɗaga mata yana mata yana dariya har ta fice.

Da ta fita ƙofar gidan ta same ta a cikin motar tana jiranta. Ba tare da ɓata lokaci ba suka tafi. Raihann suka sauke sannan suka wuce.

A hanya tun da ta ga sun dumfari get ɗin gidan, gabanta yake dukan tara-tara har sai da Marwana ta fahimci haka.

"Don Allah ki zama jaruma babu wanda zai wulaƙanta ki, sannan kar ki sake ki bayar da fuskar da wata ko wani zai kawo miki raini. Kowa haƙƙinsa ya zo nema. Yadda kika miƙe a gidan Faruk kika ƙwaci 'yancin kanki, haka za ki yi rayuwa anan, domin wasu mutanen in kina tsoronsu, sai su nemi su taka rayuwarka yadda suke so."

"In sha Allahu zan yi iya bakin ƙoƙarina." Ta ce mata tare da fita daga cikin motar.

Kama hannunta ta yi suka shiga cikin kampanin ganin yadda ta ɗan tsorata. Nasreen mamaki ta rinƙa yi yadda ake girmama Marwana tana wani shan ƙamshi.

Har ofishin Muhsin ta kaita. Yana zaune da waya a hannunsa. Ganin ta ya ɗauke fuska."Ya Muhsin ga Nasreen ta dawo."

"Ok, ta zauna na yi mata wasu tambayoyi."

Zama ta yi babu musu tare da furta,"Ina wuni?"

Amsawa ya yi fuskarsa babu yabo babu fallasa.

Tambayoyi ya yi mata cikin harshen turanci, tana ba shi amsa, sannan ya sanya ta yi dogon magana da turanci.

Yadda ta yi maganar cikin rashin tsoro ta yi introducing kanta, sai abin ya burge shi sosai. Murmushi ya yi yana kallon ta."Akwai ma'aikacinmu da ba ya jin daɗi, ina ga za ta yi replacing ɗin sa kafin ya dawo. Marwana je ki haɗata da Khausar za ta nuna mata aiyyunkan da za a iya ba ta ɗaya a ciki. In ta ɗan kwana biyu, sai na san abin da za ta iya."

"Ok, Yaya." Ta ce tare da miƙewa ta kama hannunta suka fita.

"Zan kai ki gurinta, sannan zan haɗaki da 'yar ƙanwar Momi, kuma wacce da Ya Muhsin yake so. She is very nice za ki ɗan saki a cikin kampanin."

"Na gode Marwana, Allah kawai zai biya ki." Ta furta cikin farincikin.

Ofishin Hajar ta fara shiga wacce take zaune a kan kujera, mai irin juyawar hankalinta na kan kamputar dake gabanta. Idanunta sanye da farin gilas ta ci kwalliya tamkar za ta je gasar kyau. Ganin su ya sa ta saki murmushi ta miƙe tare da zare gilashin fuskarta.

"Sis! Kece da ziyarar bazata?" Ta yi mata tambayar tare da rungumeta.

"Ya kike kwana biyu kin ɓuya?"

"Wallahi ya Damir ne, You know how strict he is, tun da ya rasa matarsa ya tsaurara doka, mutum dole sai ya cika aikinsa. In na koma gida na gaji kuma..."

"Ke dai ki faɗi gaskiya kunyar Mommy kawai kike yi, wai ke a dole ga surika."

Dariya ta yi jin abin da ta ce."Bana son sharri Marwana Mommy, uwa na ɗauke ta ina nan zan kawo miki ziyarar bazata." Ta ƙarashe maganar tare da isa gaban, ƙaramin frij dake ofishin ta ɗauki musu drinks.

"Wannan fa ƙawarki ce?" Ta yi mata tambayar tana zama a gefen ta idanunta na kan Nasreen.

"Eh, ƙawace sabuwar ma'aikaciya ce a gurin nan, shi ne na kawota gurinki. Ki kula da ita kamar yadda za ki kula da ni, tana da matuƙar girma da matsayi a gurina. She is like sister to me."

"In sha Allahu kar ki ji komai. Kin san da ba ni da matsala, Allah ya sa za ta iya jure surutuna?" Ta yi tambayar tana kallon ta.

Dariya suka yi gabakiɗaya ɗaya. "Bari na kai ta gurin Khausar ita za ta nuna mata aiki." Ta ce tare da miƙewa.

"Ok, mu je na raka ku am less busy." Ta ce tana nuna hanya.

A hanya suna tafe suna hira har suka shiga ciki. Ganin yadda Khausar ta karɓe ta sai ta ji sanyi sosai.

Zama ta yi kan kujerar ma'aikatan tana kallon Marwana da ta ce,"Zan wuce ina da lecture. Allah ya ba da sa'a."

Kasa magana ta yi dai hawaye da suƙe ƙoƙarin zubo mata. Da sauri Marwana ta girgiza mata kanta sannan ta fara tafiya. Ganin haka Dukansu suka rako ta.

Bayan ta tafi Khausar sai hanya da jira take yi. Ganin haka ya sanya ta ɗan saki jikinta. Tana kallon aikin da take yi a cikin kamputar tana mata bayani.

Wuni ta yi tana mata bayanin duk abin da take yi, yayin da ta tattara hankalinta ta mayar kanta. So take ta iya aikin don Marwana ta yi alfahari da hakan.

Da rana aka kawo musu lafiyayyen abinci a take away. Soyayyar doya da ƙwai sai drinks mai sanyi da ruwan gora faro. Kasancewar rashin sabo ta kasa cin abincin sai dai Khausar ta sanya mata a jakarta. A cikin ofishin ta wuni har lokacin ta shi ya yi.

Hajar ce ta leƙo ofis ɗin tana faɗin,"Ko kwana za ku yi Khausar? Na san ki in kika kama computer ba kya mata da wasa."

Dariya ta yi tana faɗin,"Mun gama ai aikin da oga Damir ya ba ni nake son na ƙarasa, kar a samu matsala kin san halin shi?"

"Haka ne aikin oga kwata-kwata ne dole a mayar da hankali." Ta furta sai kuma ta mayar da hankalinta kan Nasreen da take tsayar saɓe da jakarta.

"Zan wuce na ce bari na yi miki magana, saboda Marwana yanzu ta kira ki na rage miki hanya, da alama tana matuƙar ji dake?"

Murmushi ta yi jin abin da ta faɗa tana kallonta.

"Ok, mu je." Ta furta cikin sanyi.

"Ni ma a motarki zan koma gida. Jiya na kai yawa gurin gyara, an sanya ƙanina ya ɗauko mini Allah ya sa ya gyara."

"Amin mu je."

Su uku suka rankaya zuwa cikin motar.

Da ta koma gida cikin tsananin murna ta sanar da Mama duk abin da ya wakana."Mama, na kasa yarda cewar nice na ke aiki a campany nan, kin ga kyan sa kuwa? Mutane ne masu aji da class suke aiki a gurin, wallahi ji na ke yau rayuwata kamar mafarki."

"Ba mafarki bane lamarin Ubangiji ne da yake azurta bawa a lokaci guda. Tsakanin mu da yarinyar nan babu abin da za mu ce sai godiya."

"Sosai Mama na so ace Yaya Ahmad yana nan, ya ga inda na ke yin aiki sai ya yi alfahari da ni."

"To yayanki tun ina tunanin zai dawo har ba fara cire rai, saboda an ɗauki tsawon lokaci."

"To ni ma kaina ina shiga damuwar hakan, amma duk lokacin da na yi kuka na yi addu'a, sai na ji na samu natsuwa da kwanciyar hankali."

"Allah ya bayyana mana shi."

"Amin, " Ta amsa tare da miƙewa don ta yi sallar magariba.

A cikin sati ɗaya da fara aikin ta fara sakin jiki da gurin, musamman yadda ta ga ma'aikatar gurin suke rayuwa cikin sanin darajar ɗan adam.

Abin da ya ƙara kwantar mata da hankali, yadda tun da ta zo bata ƙara da haɗuwa da shi ba. Sai dai ta ji an ce oga Damir ya shigo yana kiran wance ko ya yi wa wane kasa. Yadda ba ta ganinsa sai abin ya yi mata daɗi. Ga abinci mai rai da lafiya har karin safe duk anan suke yi. A cikin sati biyu ta fara kyau da ƙiba, saboda abincin dare kawai take nema. Shi ma ba kullum ba in har ta ci ta ƙoshi a gurin aiki, sai kuma gobe da safe za ta kara cin abinci.
Chapter 39 · 0% Book details