Sashe 52
Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta kalle shi cikin mamakin yadda ya dawo."Ahmad ka ba ni labarin guduwa da ka yi ka barmu a halin gaba kura baya siyaki, sannan arzikin da ka yi a ina ka same su? Saboda bana fatan ka..."
"Daɗina dake wallahi kina da matsala. Yaro ya dawo da abin alkhairi, amaimakon ki yi ta murna rayuwarmu za ta ci gaba, amma sai ki tsaya kina tambayarsa inda ya samu?"
Jin abin da Baba ya ce sai ya ɗaure musu kai."Ya zama dole na tambaye shi domin rayuwarsa damu da shi, ba abin duniya ba. Bana fatan daboda halin da muke ciki, ya faɗa cikin mummunar rayuwa. Gara ya bar ni na mutu a halin dana ke ciki."
"Kina wannan zancen, an gaya miki yawancin masu kuɗin yanzu ta hanyar Allah suke samu? Murna kawai za mu ɗanmu ya yi arziki."
Mamakin abin da ya ce ya ƙara kamasu Ahmad ya katse shi ya ce,"Baba duk talaucin da na ke ciki ba zan kauce hanya ba, arziki na da gumina na yi, zan gaya muku yadda na yi arziki zuwa gobe in sha Allahu."
"Ni wallahi ba sai ka gaya mini ba ai kai ɗan kirki ne kawai mu ci arziki." Ya ce tare da sakin labulen ya fita cikin murna.
Girgiza kai ya yi yana faɗin,"Baba yana nan da halinsa Allah ya shirye shi."
"Hummh dama zai canza ne? Ai sanin hali yafi sanin kama." Nasreen ta ce Mama kuwa takaici ya hanata magana.
A daren ranar san ba su rintsa ba haka suka kwana hira, domin gani suke kamar zai ɓace. Dariya ya rinƙa yi musu cikin farinciki yana ƙara jin ƙaunarsu. Da suka ga bacci ya ƙi zuwa miƙewa suka yi suka yi ta sallah suna godiya ga Allah.
Da asuba ya fita sallah sannan Zainab ta tashi ta ɗora musu abin kari. Mama bayan ta yi sallah ta miƙe ta gyara ɗakin.
Da safe suna karyarwa sai ga Baba tsulum ya shigo."Saboda Allah kuma karyarwa da irin wannan ƙaton biredi, amma ba za ku kira ni ba? Na fa lura so kike ki rinƙa nuna mini iko da yarannan, kin san dai nine mahaifinsu, don haka wallahi ba zan yarda ba, ai ina lura haka kike baza iko da arzikin Nasreen, ni kuwa sai abin da kika dama suka bani."
Kallonsa suka yi dukkanin su babu wanda ya tanka musu. Ganin haka ya ɗauki sabar biredi ƙato, wanda Ahmad ya siyo musu ya zauna tare da jan ruwan tea na gaban Nasreen. "In ba za ba ni ba ina da hannu ai."
Zainab ce ta shigo da filet na ƙwai da ta soya. Kafin ta ije ya kai hannu ya iba."Yauwa yar albarka ije na ci arziki." Ya furta tare da turawa a cikin bakinsa
Shiru suka yi masa yana ta sumbatu har ya gama ya tashi, sai kuma ya koma ya zauna. Anan zan rinƙa zama saboda na lura cutata kike son yi. So kike komai sai dai su yi miki, bayan inda ba ni ai ba za ki haife su ba.
Mama dai ba ta ce uffan ba ta miƙe Ahmad ya buɗe baki zai yi magana ta dakatar da shi. Ganin haka ya miƙe,"Bari na je gidan ogana akwai kayan da za a kawo mana gidansa."
"Adawo lafiya Amadudu yaron kirki." Baba ya ce tare da miƙewa ya fita.
"Mama sai na dawo Nasreen bari na je."
"To a dawo lafiya." Suka amsa suna kallonsa.
Sai da tafiya Nasreen ta kalle shi."Mama wallahi Baba ba shi da ta ido. Kina ganin abin da yake yi? Ko da yake na daina mamakin tun lokacin da na fara samun nawa ya canza na zama shalelensa."
"Allah ya shirye shi duk wanda ya bashi shine nasa."
"Hmmmmh! Lamarinsa sai shi." Ta ce tare ƙwalawa Zainab kira don ta kwashe kayan da suka karya.
A lokacin da Marwana ta tashi safe ɗakin Momi ta shiga cikin farinciki ta rungume.
"Momi kin san mai ya faru?"
"A'a amma na san daga ganin yadda kike farinciki alkahiri ne."
Murmushinta ya ƙaru ta ce,"Eh Momi Ya Ahmad ɗan'uwan Nasreen ne ya da..."
"Da gaske kike yi?" Ta furta cikin tsananin murna tana zare idanunta.
"Eh, momi wallahi ya dawo."
"Masha Allahu Alhamdulillah! Dole na je na yi musu murna. Ya jikin Nasreen ɗin?"
"Da sauƙi jiya ai ba ta damu da ciwo ba ganin Ya Ahmad."
"Dole ke kuwa, a wannan zamanin da zumunci ya yi ƙaranci a cikin al'umma."
"Wallahi Momi ai Ya Ahmad ya yi."
"Allah ya saka mishi in sha Allahu da yamma zan je na yi musu murna."
Jin abin da ta ce sai farincikinta ya ƙaru."Da nayi farincikin haka, yanzu zan shirya na ƙara duba jikinta in zan wuce makaranta."
"Ya kamata ke dai da Nasreen Allah ne ya haɗa ku." Ta furta tana kallon ta gani yadda take murna.
"Allah ne kuwa saboda jin ta nake kamar 'yar'uwa ta jini. Momi wataƙila don ba ni da 'yar'uwa na mace ne."
Dariya ta yi tana kallonta ita kuma ta shige ciki don ta shirya. A hanya tan tuƙa mota tana ayyana farincikin da take ciki. Har ta isa kofar gidan. Shiga ciki ta yi a lokacin da ta yi sallama. Nasreen tana kwance kan kujerar tana chatting da Ingawa. Sanar mishi da dawowar Ahmad ta yi. Sosai ya taya ta farinciki.
Jin sallamar Marwana ta ije wayar tare da amsawa. Zama ta yi gefenta baya ta shigo."Ya kike jin jikin na ki?"
Ta tambaya tana daga hannunta da ya kumbura." Na ji sauƙi sosai saboda farincikin da na ke ciki, sam bana jin zafin ciwon."
"Dole ki yi farinciki ko ni da kyar bacci ɓarawo ya sace ni."
"Mu jiya ba mu yi bacci ba."
"Da ma ba za ku iya bacci ba."
Bayan ta gama duba ciwon suka shiga hira.
Nasreen ta kalle ta ta ce."Marwana na gode da kulawar da kika ba ni sosai, amma na aje aiki har na rubuta resignation letter ki kaiwa Ya Damir."
Miƙewa ta yi a zabure tana kallonta cikin tsanannin mamaki."Sakayyar da za ki yi mini kenan Nasreen? Na tsaya na kula da rayuwarki, ina fatan ki saka mini ta hanyar dawowa da dan'uwana cikin hayyacinsa, amma saboda kin ga Yayanki ya dawo da abin duniya ya yi kuɗi shi ne za ki guje ni? Ko da ace za ki yi butulci bai kamata ki yi mini ba, musamman da kece silar faruwar komai."
"Na sani kuma na yarda ni ce na sanya shi cikin damuwa, amma duk abin da za ki ce na riga na gama yanke shawara, saboda Ya Damir ba zai taɓa sausauci a gare ni ba. Ko da ace Ya Ahmad bai dawo ba, wallahi na yi ninyar aje aiki. Shi ne ya ya watsa mini ruwa a hanya har na faɗi na ji ciwo."
Zare idanunta ta yi cikin tsananin mamaki tana jinjina rashin imaninsa."Kina nufin shi ya watsa miki ruwa?" Ta yi tambayar cikin zallar mamaki.
"Shi ne ya watsa mini ruwa a yadda ya so ina tunanin buge ni zai yi, saboda in har da ban matsa ba sai ya ture ni."
Ranta ne ya ɓace har ta yi dana sanin gaya mata.
"Ya Damir mutuwar Anty Batula ya sanya shi rashin imani har zai iya kisa. Shikenan na yarda ki aje aikin bazan yi miki dole ba. Ya Ahmad ya dawo gareki zai kula dake. Shi kuma ki bar shi ya ƙare rayuwarsa a haka, har ya je ya samu wacce ya yi wa alƙawarin sai su ci gaba da rayuwa a can." Yadda take maganar cikin zafi ya tabbatar mata data harzuƙa.
Kama hannunta ta yi tana faɗin,"Ni ban gaya miki don ki je ki gaya masa babu daɗi ba. Bana son ki yi abin da zai sanya ya ja babu daɗi. Duk abin da ya yi mini na cancanta, amma zan aje aiki don na yi nesa da shi, kamar yadda ya buƙata."
"I understand, babu matsala ki bani resignation letter ɗin zan kai masa. Kuma kar ki tunanin hakan zai kawo matsala a tsakaninmu, kina nan a matsayinki na yar'uwata."
"Na gode da kika fahimce ki." Ta ce tare da umurtar Zainab ta kawo mata takaddar.
"Zan wuce makaranta ki kula da kanki."
"Sai kin dawo in sha Allahu." Ta furta sannan ta yi mata murmushi tare da ɗaga kanta ta tafi.
Mama ta fito daga ɗaki tana kallonta."Mai ya sa kika ake aikin yarinyar nan ba za ta ji daɗi ba, saboda tana iya ƙokarinta a kan ki."
"Mama aje aikin shi ne mafita a garemu Gabakiɗaya. Sam ba ya jin daɗin ganina har ta kai ga yana ƙoƙarin taɓa lafiyata. Gara na haƙura dama tuni na yanke shawarar haka, ga kuma ya Ahmad ya dawo cikin rayuwarmu."
"To Allah ya sanya haka shi ne mafi alkhairi."
"Amin." Ta amsa.
A fusace ta fice daga gidan, saboda abin da ya yi wa Nasreen ya bata mata rai. Saboda ranta da ya ɓace ba ta lura da Ahmad da ya faka motarsa ya fito don yazo su gaisa ba. Da gudu ta ja motar ya yi zuru yana kallonta.
Har sai da motar ta ɓace, sannan ya kashe na sa ya fito yana tunanin mai ya ɓata ranta a gidan. Mutane suka yi masa caaa ana murna. Da ƙyar ya samu ya shige cikin gidan bayan ya sallame.
"Sannu da dawowa Yaya." Ta ce tare da tashi ta zauna.
"Yauwa, Marwana ta fita cikin fushi da wa ya ɓata mata rai."
"Nasreen ce saboda ta ce ta ije aikin da ta samar mata a kampanin su." Mama ta ba shi amsa.
"Saboda me?"
"Kasan abin da ya faru Yaya tsakaninta da yayanta."
Kansa ya ɗaga, sai ta ba shi labarin ɓacewarsa da kuma komawa gidan Faruk da yadda suka rabu har ta samar mata aiki.
Hawaye ya share cikin mamaki ya ce."Faruk ya cutar dake ɓacin albarkacin su Raihann sai na maka shi kotu, amma ya ci albarkacin haihuwa. Marwana kuwa kamar ke na ɗauke ta. Tabbas ta zama ƴar'uwarmu, duba ga irin yadda tasha artabu da su har suka amince ta dawo cikin rayuwarki. Anya ana samun ƙawance haka?"