← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 92

Sashe 51

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka suke yi sosai Mama ta haɗu ta rungume tana hawaye. Sun daɗe a haka cikin farinciki, sannan suka zauna suna kallon juna.

Ahmad na shirin magana wayar Mama ta fara ringing."'Yar albarka Marwanaa take kira, dama na san hankalinta ba zai kwanta ba." Ta ƙarashe maganar tare da amsawa ta kanga a kunninta.

"Hello Mama ina kofar asibitin don Allah a fito a shiga dani."

To bari na fito." Ta ce mata tare da kashe wayar.

"Marwana tana waje bari na shigo da ita."

"Mama zauna bari na shigo da ita." Ahmad ya ce tare da fara tafiya. Jin haka ta koma ta zauna tana kallon sa cikin farinciki. Nasreen ita ma kallo da take yi gani take kamar dawowarsa a mafarki ne.

Ahmad kuwa sai watsa idanunsa yake yi, burinsa kawai ya kalli Marwana da ta kula da 'yan'uwansa a lokacin da ba ya nan. Sosai yake ganin girmansa da ƙimarta. Sau biyu ya taɓa ganinta, don haka ba zai iya shedata ba, a ranar da ya ganta ranar ba shi cikin hayyacinsa sakamakon lamarin da ya faru. Wannan dalilin ya sanya shi karɓar wayar Mama.

Numbarta ya kira wanda ringing ɗaya ta ɗauka."Hello Mama, ina waje har yanzu cikin motata."

Zuciyarsa ya ji ta yi wani tsau jin zazzaƙar muryarta. Rintse idanunsa ya yi yana jin matuƙar girmanta. Da ƙyar ya yi nasarar buɗe bakinsa ya ce,"Ok," Tare da kashe wayar.

Muryarsa ta doki kunnenta har sai da ta cire wayar tana kallo.

Wayyo Ya Ahmad ya dawo💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Na ga murnar kowa a comment

Wayyo Yaya Ahmad ya dawo yau dadi kashe Ni 💃💃💃💃💃

WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 27

Muryarsa ta doki kunnenta, har sai da ta cire wayar tana kallo a tunaninta ko ba layin ta kira ba. Ƙaramin tsuka ta ja saboda a yi tunaninta Ingawa ne.

Ahmad cikin tafiya a hankali ya ƙaraso gurin motar. A lokacin da ya isa ta fito, sai ya tsinci kansa da shiga cikin wani irin yanayi. Zuciyarsa na bugawa ya ɗago ya kalle ta.

Idanu suka zuba wa juna na ɗan wani lokaci."Nasreen ta ƙara samun wani saurayin ne?" Ta yi wa kanta tambayar hakan cikin zallar kishin yayanta.

"Mama, ta ce ki biyo ni." Ya furta cikin natsuwa tare da juyawa. A da ya yi nufin ya fara mata godiya, amma tun da ya kalli idanunta sai ya ji ya kasa, saboda yadda zuciyarsa ke harbawa da sauri.

Marwana kuwa da sauri ta kauda idanunta, saboda ƙwarjinin da ya yi mata. Sai kuma ta saci kallonsa don sun so su yi kama da Nasreen. Kauda tunanin hakan ta yi nan take.

Da suka shiga cikin ɗakin da sauri ta ƙarasa gurinta cikin damuwa."Nasreen garin yaya kika faɗi? Sannu ya jikin mai ke miki ciwo?" Ta yi mata tambayar cikin damuwa tana tattaɓa jikinta.

"Idan akwai abin da ke damuna ɗazu yanzu babu."

"Masha Allah sannu ya jikin?" Ta ƙara ce mata.

"Marwana dole na warke saboda ranar yau ba zan taɓa mantawa da ita ba."

"Mai ya faru?" Ta yi mata tambayar ganin yadda yake cikin tsananin farin ciki.

Hannunta ta daga tana faɗin,"Ya Ahmad ya dawo gare ni...."

Zare idanunta ta yi tana kallon inda take nuna mata."Don Allah in wasa kike ki daina Ya Ahmad ɗinki, ina yake?"

Kara nuna mata shi ta yi cikin mamaki ta ɗago tana kallon sa. Mamakin wayewa da shigar ɗaya yi ta yi. Sosai ya yi kyau kuma ya yi mata kyau.

"Wai da gaske wannan ne Ahmad ɗin ki?" Ta yi mata tambayar kamar zata zauce.

Ƙarasa gabansa ta yi kamar za ta rungume shi, sai kuma ta ji kunya ta kama hannunsa."Alhamdulillah Allah mun gode maka." Ta ce tare da sakin hannunsa ta rungumeta duk suka fashe da kuka.

Ahmad sai ya tsaya cikin tsanannin mamaki yana kallonta, ganin yadda take hawayen murnar dawowarsa. Shi kuwa ba shi da abin da zai saka mata face ya ƙarasa sauran numfashinsa yana mata addu'a, ganin yadda ta ɗauki ahalinsa a matsayin nata.Yana wannan tunanin ta ji muryarta tana faɗin,"Ya Ahmad ina ka shiga ka sanya xuciyoyinmu cikin damuwa? Kasan halin da suka shiga kuwa?"

Murmushi ya yi yana mata wani irin kallo."Ayi haƙuri a gafarce ni, sannan a shirye na ke da duk hukuncin da za ku yi mini, duk da cewar na aikata hakan cikin rashin mafita, amma kuma nayi farinciki da na dawo na ga sun samu wacce ta zama tamkar ni. Haƙiƙa ya zama dole na yi miki godiya."

Murmushi ta yi tana cewa,"Duk mai imani ya ji halin rayuwar da take yi da Faruk dole ya tausaya mata. Nasreen tamkar 'yar'uwata na ke jinta, bana buƙatar ka yi mini godiya, amma don Allah kar ka ƙara tafiya ka barsu."

"In sha Allahu ina tare da su har ƙarshen rayuwarmu."

Sun jima a asibitin har zuwa dare aka sallame su. Marwana ta wuce gida da nufin za ta dawo.

Damir tun lokacin da ya ji ba a ganta ba sai ya ji damuwa har ya kasa ci gaba da kallon. Ɗakinsa ya wuce a karo na farko ya damu da abin da ya yi mata. Zama ya yi yana tunanin inda ta je. Fitowa ya yi ya zauna a falo yana kallon Marwana da ta rikice tana ta kiran waya. Hankalinta ya kwanta da Mama ta ta kira ta tana asibiti.

"Mommy bari na je na ga halin da take ciki."

"Da kin bari zuwa gobe tun da kin ji inda take."

"Ba zan iya bacci ba, ai ba zan daɗe ba." Ta ce tare da fita da sauri.

Wani banzan kallo ya watsawa hanyar da ta wuce. Haushinta yake ji yadda take nuna sonta kamar ƙanwar uwarta. Ajiyar zuciya ya saki ya koma ɗaƙinsa. Ga mamaki sai ya ga ya samu kwanciyar hankali da aka san inda take. Ya daɗe ya kasa bacci yana tunanin ruwan da ya watsa mata ya sanya ta faɗi har ta ji ciwo. Nan take ya ji abin da ya yi bai kyauta ba. Daga ranar ya sanya ba zai ƙara shiga sabgarta ba, soyayya ce dai ba za ta yi masa a campany ba, saboda in har ya ganta sai gabansa ya yi ta fadi yana jin xuciyarsa na harbawa. In kuwa da wani ya ganta ji yake kamar ya je ya rufe su da duka. Rashin adalci da Marwanata yi masa wanda yake tunzura shi har ya yi mata wulakanci, da ya bukaci ta yi aiki a campany, domin shi kaɗai ya san mikin da take tayar masa, duk a lokcin da ya ganta ko ya tuna tana cikin kampanin, wanda ya ɗauki hakan duk a rashin matarsa da ta sanya ya yi.

A lokacin da Marwana ta dawo cikin farinciki don ta gaya musu, amma sun kwanta. Mommy dama wuni tayi bayanta yana danunta. Ganin babu kowa a falon sai ta shiga ciki ta tube kayanta. Kwanciya ta yi cikin farinciki sosai. Ta yi murna da Ahmad ya dawo kuma da alamun ya samu abin duniya, duba ga yadda ya canza ya zama ɗan gayu. Ita kanta ya tafi da hankalinta. Gaskiya talauci musiba ne, duk da a lokacin da ta ganshi ba za ta gane suffarsa ba, amma ba za ta taɓa haɗawa da yanzu da ya goge ya samu masu gidan rana ba. Motar da suka shiga shi ya ƙara ɗaure mata kai, har ta fara tunanin wane irin aiki ya samu har ya kuɗance lokaci guda. Ta yi musu murna sosai da sosai domin ta san daga yau sun gama bankwana da baƙinciki. Rayuwar su za ta yi kyau kuma su samu ingantacciyar rayuwa.

Nasreen gani take kamar har yanzu mafarki take yi, musamman da suka ƙarasa motar da ya ce mallakinsa ce. Hawaye sosai take yi ta ce,"Ya Ahmad in addu'ar Allah ya sa burin son mu fita daga rayuwaar talauci bai sanya ka kauce hanya ba? Saboda garamu dauwama cikin ƙunci, kan ka bi hanyar daba ta dace ba don ka fitar damu."

Shafa kanta ya yi yana murmushi."Kar ki damu ƙanwata. Labarin mai tsawo ne zan gaya miki zuwa gobe, amma kafin nan ki muje gida ki huta." Ya ce tare da kamata ya suka shiga ciki yayin da take ta kallo da shafa motar ta yi tare da jan numfashi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da yake fitowa a cikin motar. Mamaki take yi sai yau shi ne da mota. Ba ta ƙara shiga cikin mamaki ba sai da ta ga wata irin waya mai tsananin kyau a hannunsa. Tsungulin kanta ta yi domin ha yanzu gani take ganin lamarin tamkar hikaya.

Suna shiga gidan Baba ya sheƙo da gudu ya faɗa jikinsa. "Ashe da gaske ne abin da mutane suke faɗi, ba kanzen kurege bane. Amaduuna ya dawo ya yi kudi." Ya furta yana rungumi shi har da hawaye. Sai kuma ya ƙara zabura ya rungume shi yana faɗin,"Wayyo Amaduuna ya zama mai kuɗi ka ga yaron albarka ya fita bariki a sa'a? Kai ni dai Bukar na iya haihuwa."

Kalaman da ya faɗa suka sanya su cikin duniyar mamaki. Ahmad ya ja jikinsa daga gare shi, cikin yanayin da ba za ka fahimci abin da yake zuciyarsa ba.

Kama hannun Mama da Nasreen ya yi za su shiga ciki. Da sauri ya biyo su yana ta kallon sa yana yi wa Allah godiya.

Da suka zauna Nasreen kamar za ta shige jikinsa ta zauna kusa da shi, tare kama hannunsa.
Chapter 51 · 0% Book details