← Book details Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 92

Sashe 70

Nasreen Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasreen tana shiga cikin gidan tagan su a falo suna tsaye cirko-cirko."Saboda me zai ɗauke mini yara? Wallahi bai isa ba, saboda ko zan ƙarar da komai nawa sai na ƙwatonsu." Ta ce daidai lokacin da Ahmad ya kamata ya zaunar da ita.

"Ki yi haƙuri na je makarantar sun ba ni numbarsa. Na kira shi tun da ya ji muryarta ya kashe kuma abin damuwa suna ta kuka."

"Kin ji ko Mama, na san cewa ba zasu ƙaunace sa ba, mutumin da ya wulaƙanta su?" Ta ce tare da sakin kuka sai kuma ta ce,"Damuwa ta Musaddik ya ba shi da lafiya, har nayi tunanin ko ba zai je makarantar ba, amma sai na bashi magani ya tafi."

"Za su dawo in sha Allahu yanzu ki karɓu numbarsa ki kira shi."

"To,"Ta ce tare da share hawaye. Tana kiransa ya ɗaga cikin fushi ta miƙe ta ce,"Faruk ka dawo mini da yarana saboda baka da alaƙa da su." Ta ƙarashe maganar cikin fushi jin kukan Musaddik.

"Yaranmu dai don Allah ki dawo mu riƙe su, wallahi na yi nadama ina son ki Nasreen."

"Yaudarar kanka kake yi, saboda na san taɓa ƙaunarka ba."

"To shikenan, tun da wannan ɗan iska yana hure miki kunne sa ki je ki haifi wasu da shi, amma matuƙar ba za ki dawo gare ni ba na ƙwace yarana." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar.

"Farouk ka dawo da su ko yanzu na kai ƙararka hukuma." Kallon wayar tayi ganin ya kashe sai kawai ta fashe da kuka.

Rarrashinta suke yi, amma kamar suna tunzura ta. Su kansu hankalinsu a tashe yake domin sun shaƙu da yaran sosai.

"Ina ga ba za a kira babanku ba?" Mama ta yi musu tambayar tana kallonsu, ganin har yanzu ƙarfe biyar bai kira ba, ballantana su yi tunanin za su dawo.

"Baba ƙara rikita lamarin kawai zai yi. Mu bari ya dawo da su ta lalama, dai mu canza musu makaranta kawai."

"Ni zan je gidansa, domin ba zan iya kwana babu su ba." Ta furta tare da miƙewa.

Ahmad ya koma da ita ta zauna."Don Allah ki yi haƙuri dole ya dawo da su, saboda babu shaƙuwa a tsakaninsu ina tabbata miki yanzu haka sun addabe shi da kuka." Ya ce mata cikin tsigar rarrashi. Zaunawa ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Ganin har magariba Isha ta yi sai kawai ta sanya musu kuka. Su kansu duk sun damu sosai. Tana zaune kiran Marwana ya shigo. Sosai ta ba ta baki sannan ta kwantar mata da hankalin cewar za su dawo..

Ta shi ta yi zuwa ɗaki, ta yi sallah sannan ta zauna a daddumar tana addu'a.

WASU MAZAN na kuɗi ne, 500 ne kacal, in kuma aka kammala ya zama document 800. 'Yar'uwa ki biya ki karanta hankalinki ki kwance. 🙏_

*08144072423*

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuɗin ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waɗannan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta ɗaya daga cikin wannan numbar ta What

*WASU MAZAN*

BOOK 2

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
And now
Wasu mazan

08144072423

PAGE 37

Ta shi ta yi zuwa ɗaki, ta yi sallah sannan ta zauna a daddumar tana addu'a.

Damir da ya koma gida hankalinsa ya kasa kwanciya. Wayarsa ya ɗauko ya kira ta, duk da Marwana ta gaya mishi har magariba bai dawo da su ba.

Tana zaune kan daddumar kiransa ya shigo. Kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta tuna mutuncin da yayi mata, domin halin da take ciki ya shanye mamakinta. Wai yau ita Damir ya damu da halin da take ciki har ya kawo ta gida?

Ɗaukar wayar ta yi, tare da yin sallama da muryar da ta bayyana alamun anci kuka.

Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce,"Nasreen still crying?" Ya yi mata tambayar cikin damuwa.

"Na daina." Ta ce masa tana share hawaye.

"No you are still crying muryarki ta bayyana haka. Please ki kwantar da hankalinki. In har bai dawo dasu da safe ba, gobe mu shigar da ƙara."

Da sauri ta ce,"To," Jin ya karfafa ta a je kotu saɓanin su Mama. Kwantar mata da hankali ya rinƙa yi cikin sanyin murya har ta yi mamakin dama haka yake.

Ba don ya so ba, ya kashe wayar ya kwanta cikin tunanin halin da take ciki.

Farouk ya yi kwanar wahala, saboda yadda ya ga rana haka ya ga dare. Yaran sun ƙi bacci sai kuka ga jikin Musaddik cikin dare ya rikice su da ya kai shi asibiti. Ko da ya dawo kin shan maganin ya yi sai da ƙyar. Kuka suke yi sosai ga shi sun ƙi cin abinci.

Washegari da sassafe, gari bai gama washewa ba ya kwashi yaran gidan Asiya.

Ta idar da sallah kenan ya yi kiranta don a buɗe basa gidan. Saboda tunanin abin da ya kawo shi cikin sauri ta buɗe masa da kanta.

Ganinsa da yaran, sai mamaki ya kamata ta yi turus tana kallonsa. "Yanzu Faruk duk kashedin da na yi maka sai da ka ɗauko su? Kasan yadda Nasreen take da masifar son yara tsanarka za ta yi?"

"To ya kike son na yi Anty Asiya? Nasreen ta ƙi saurara, kuma wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." Ya ƙarashe maganar hawaye yana zuba a ƙuncinsa.

"Ka yi sake Faruk ka cuci kanka, amma dole ka mayar da yaran nan. Ka kwantar da kanka, sannan ka zama tamkar maraya ƙila ta dawo gidanka."

Shiru ya yi yana tunani, ganin haka ta yi masa dubara har ya aminta zai mayar da su.

Miƙewa ya yi tamkar marayan zaki ya fita. Kallon tausayi ta bi shi dashi, domin ta san ihu yake bayan hari. Nasreen ta riga ta yi masa nisa."

Daga gidan ƙofar gidan su Nasreen ya je, saboda tsoron kar su yi masa rashin mutunci, musamman Baba yafi tsoronsa, sai ya tura yaran ciki, bayan ya tura mata kalamai na ban haƙuri da ƙauna.

Rungume su ta yi, tana farinciki sosai. Dukanninsu sun yi murnar dawo da su da ya yi.

"A canza musu makaranta kawai, saboda duk ranar da ya ji za ki yi aure zai aikata abin da ya fi haka." Mama ta ce tana shafa kan Musaddik.

"Hakan za a yi Mama, zan duba makaranta sai a canza musu." Ahmad ya faɗa.

Saboda murna kasa zuwa aiki ta yi, haƙata wuni da su cikin farin ciki. Ta girka musu wancan ta siyo musu wannan.

Marwana ma ba a barta a baya ba, domin da ta tashi zuwa sai da ta yi musu siyayya.

A lokacin da Damir ya kira ta sai ta ɗauka cikin farinciki."Ya Damir sun dawo na gode da kulawarka." Ta ce masa saboda yadda ya nuna damuwarsa ta ji daɗi sosai, domin duk wanda zai damu da su Raihan za ta ba shi matsayi.

Da ya ji yadda take farincikin sai hankalinsa ya kwanta. Oder kayan ciye-ciye ya yi musu, sannan ya kira Marwana ya sanar mata. Murmushi ta yi, ganin ta gama kauce-kauce ya fara nuna mata soyayya.

Lokcin da aka kawo aka aka kira ta sai ta fita ta amso. Sosai ta yi murna kuma ya ƙara samun matsuguni zuciyarta.

Da safe da ta shirya za ta je aiki. Wanka ta yi musu suka tafi tare, tun da ba su makaranta ba. Yaran sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu.

Mota suka shiga sannan suka tafi suna ta murnar za ta je da su.

Cikin sa'a a ranar sai Damir ya zo little Marwana. Tana tsaye sai ya sauko zuwa ƙasa zai ɗauko Teddy da Marwana ta manta da shi a mota, kuma take ta yi mishi ƙorafin za ta sakko ta ɗauko, don haka ya kama hannunta suka saukko

Ganinta ya cika da mamaki, don bai yi tunanin za ta zo ba. Murmushi ya saki ganin sun haɗa idanu ta yi ƙasa da kanta. Yana son yi mata magana, amma ganin idanun mutanen da suke gurin yana kansu, sai ya buɗe motar ya ɗauko mata Teddy wacce ta saki hannunsa ta ruga gurin su Raihan.

Tsayawa ya yi, yana kallon su domin sun burge shi. Ganin haka sai ta kama hannun Marwana suka ƙaraso gurinsu.

"Ina kwana."

Kasa amsawa ya yi sai kuma ya yi motsi da bakinsa.

"Na gode jiya Ya Damir."

Murmushi kawai ya yi wuce ba tare da ya ce komai ba. Karo na farko ta bi bayan shi da kallo.

Little Marwana tun da ta gansu Raihan ta ƙi zuwa gurin Damir. Tana zaune gurinsu suna ta wasa sosai. Ganin haka sai ya ci gaba da aikinsa.

Suna gurin ta dukanninsu sai lokacin da za a yi lunch, sannan little Marwana ta kama hannunsu Musaddik zuwa gurinsa.

Yana ganin su, ya yi murmushi tare da sakin aikin da yake yi. "Daddy they are my friends."

"You love them kina son ki yi rayuwa da su?" Ya yi mata tambayar yana nuna su.

"I want musamman yaron nan Musaddik na rinƙa goya shi." Dariya ya yi tare da jan kumatunta jin abin da ta ce.

"Wato kin girma ko?"

"Daddy let's go and buy chocolate." Ta ce mishi tana jan hannunsa.

"Ok, go."Ya ce tare da kama hannunsa suka fita.

Nasreen tana hangen da ta window har suka fice. Sosai take mamakinsa ashe yana da sauƙin kai haka. Ko da yake Marwana tasha gaya mata, mutum ne mai kula da iyalinsa kuma koma ba shi da damuwa. Abin da ya faru ya canza shi zuwa haka.

Murmushi ta yi ta koma ta zauna ta ci gaba da aikinta.

Tana aikin Ingawa ya shigo."Nasreen ina kids ɗin mu na ɗauka za ki kawo su mu fita?"

Kallon sa ta yi jin abin da ya ce. Gabanta ya faɗi, amma sai ta daure ta ce,"Yaya na ga ka yi busy, wannan dalilin ya sa ya ban kawo su ba kar su dame ka."

"Ok, where are they now? Saboda am less busy."
Chapter 70 · 0% Book details